Hausa Novels

Ya Cire Mata Kaya Complete Pdf Download

Ya Cire Mata Kaya Complete Pdf Download

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

♔︎ ♔︎
ℕℍ

 

ASHANTY LOVE.

 

☆’ ☆☆

 

Chapter
16/20.

 

 

Tafiya nake ina sharar hawaye suna biya dani. Tunanin mak’omata cikin wannan masarautar nake. Tsawon minti hud’u muka dauƙa muna tafiya kafin na fara hango tangamemen ginin daya raba mu da cikin masarautar. Dakarune kewaye da ita ta ko ina tun daga farkon ta har k’arshen katangar da baka ganin sa. Ajiyar zuciya na sauke mai k’arfi zuciya ta fal tsoron abunda zan tarar. Da sauri naga sun wuce ni zuwa bakin k’ofar suna wa katon Gaurd dake gadinta magana. Shi kaɗai ma ya isa yasa ka juya da gudu tun kafin ka k’arasa.

Katon gate d’in suka buɗe da aka yi da zallar Crystal stones. Baki na hangame na tsaya chak ina kallon wannan masarauta kaman aljanna duniya. Hak’ika babu abun yabo da bauta sai Allah. Shike bayarwa kuma shike hanawa ga wanda yaso.Gaskiya dole su shagala da duniyar da Allah ya basu su manta cewa zasu koma gareshi.

Ji nayi kawai sun tankad’ani nayi taga-taga kaman zan fad’i Allah ya taimake ni na tsaya da k’afafuna. Tsawa suka daka min

“Wuce mana kinja kin tsaya. Ko kinsan illar barin KING AZRAH zaman jira?”

Bance komai ba na cigaba da tafiya bansan inda zanyi ba don yaune karo na na farko dana shigo cikin wannan Palace. Lura da hakan da suka yi suka k’ara wuce ni na cigaba da binsu a baya. Katon gini muka shiga mai masifar kyan gaske da doguwar hanya kaman corrido. Shima saida muka yi y’ar tafiya sannan muka bulle wani irin Garden mai tsananin kyau dayafi na b’angaren mu. Ta cikin sa muka shiga sai gamu mun bullo Royal Palace.

Download Fuska Uku Hausa Novel Complete

Ido waje nake kallon ginin. Kunne nayi baki nayi. Sosai na zama y’ar kyaune na hangame baki ina kallo. Tankamemen falo muka shiga da ke dauke da kujerun gold da garden cikinsa kai harma da kwani na ruwa a tsakiyar sa ga wasu tattaburu farare dake shawagi kansa. MashaAllah hak’ika Allah ya basu duniya saura lahirar su kuma.

Glass staircase dake can k’arshen falon ya kewaye shi ta ko ina suna nufa na rufa musu baya. Kaman dai yanda ko ina yake zagaye da dakaru haka shima falon yake tun. Saboda yawan benen saida na gaji na d’an yunƙura zan hutu suka k’ara dakamin tsawa na miƙe da sauri na cigaba da binsu. Ajiyar zuciya naja mai k’arfi na dafe gefen cikina ganin mun kawo k’arshen benen. Kai wannan wahala da yawa take. Mutum in mai k’iba ne ai cikin kwana biyu zai ya zazzage gaba d’ayan sa. Hanya muka bi doguwa nan ma kaman corrido mai d’auke da kofofi wajen shida ko wacce a gark’ame da matakan tsaron a bakin ta. K’ofar dake tsakiya warda tafi ko wace girma da kyau tana fuskantar mu ,mu ka tsaya.

Kai na d’aga ina kallon jibgegiyar k’ofar da aka yi kaman da gold sai shek’i take saman ta an rubuta EMPEROR EZKE’IL CHAMBER da stone’s na crystals abun sai ya k’ara armashi sosai. Dakurun dake zube gaban k’ofar na maida hankali kai ina kallo cikina na bada sauti saboda matsanancin tsoro. Sai yanzu nake jin irin bugun da zuciyata take da mugun gudu kaman zata tsaga kirjina ta fito. Gyaran murya d’aya daga cikin dakarun da suka titsiyoni nan ya yi nayi saurin maida hankali ina kallon su. Kai ya jinjina ganin na maida hankali ina sauraran shi ya fara magana.

“Idan an buɗe kin shiga kar ki kuskura ki d’aga kan ki har sai ya baki umarnin hakan. Ki kiyaye kallon sa ba tare da izni ba kinji ko”

Sakato na tsaya ina kallon Gaurd d’in. Wane irin abu ne kuma haka? Tsawa ya dakamin

“Kinji abunda nace?”

Da sauri na d’aga kai cikin firgici. Kai ya d’aga ya juya. Ina kallo yaja numfashi mai k’arfi kafin ya d’aga hannu ya buga k’ofa sau biyu ya koma baya ya wani k’ame ko motsin kirki baya yi kaman an zare masa laka bashi kad’ai ba gaba d’aya dakurun sun k’ara k’amewa kaman basu numfashi. Tun daga nan na fara hango makomata. Tsawon minti goma muna tsaye babu alamun za’a amsa bugun k’ofa bare a buɗe. Kafafuwan har sun fara gazawa na fara k’ok’arin sunkuyawa sai kawai naji wata irin murya mai shegen gard’i da sanyi gata so, so Deep tayi magana daga cikin d’akin a kasalance kaman wanda maganan kewa wuya.

“Minnnn ?” (Waye?)

Ai tuni hanjin cikina suka k’ara kad’awa na gyara tsayuwata da sauri kaman yanda naga dakarun sunyi. Jiki na rawa ya bashi amsa.

“Mune KING AZRAH. sakon da kace a kawo maka gashi mun tawo dashi”

Sak’o? Ban ma isa a kirani da mutum ba kenan?. Nan ma dai sai da ya d’auki sama da wajen minti goma kafin ya bada amsa. Wannan wace irin rayuwa ce?. Wace irin isa ce wannan?wai shin da mai kuɗi da mulki, arziƙi ,talaka duk ba d’aya suke ba gurin Allah?. Me yasa wasu mutanen idan sunga Allah ya basu duniya sai su dinga ganin kaman sunfi kowane?. Bafa dabara ko iyawa tasa Allah ya basu wannan matsayin ba. Duk wani abu da zai samu bawa a wannan duniyar jarabawa ce a gareshi. Wani zata kaishi wuta wani ta kaishi Aljanna. Ga wad’an da suka fifita duniyar su kenan a kan laharir su. Sun manta cewa duniyar nan ba komai bace.

Maganan gaskiya iya fusata nayi. Wannan wulaƙanci ya yi yawa. Yasa an kawoni ba tare da nasan abunda nayi ba. Nazo kuma sai iko yake mana. Anya kuwa zan iya jure wannan isar?

A kasalance naji ya yi maganan da saida na kasa kunne sosai naji. Cikin harshen nasara yanzu yace

“Let her in”

Kallo na gaurd d’in ya yi ya matsa k’ofar da sauri don ya buɗe yana cewa

“Kar ki manta gargad’in da nayi miki. Kar ki d’aga kai har sai ya baki umarni”

Ban bashi amsa ba na d’auke numfashi bayan buɗe k’ofar da ya yi duhun d’akin ya yi min sallama da wani irin kamshi da sanyi mai ratsa bargo da kashin mutum. Da kyar na d’aga kafata da suka yi nauyi na tura kai cikin d’akin bakina d’auke da siririyar sallama. Bana iya ganin komai saboda duhu sai y’ar fitilar dake can kan wata tebir katon gaske mara haske. Ido na buɗe sosai ina kallon kaman mutum ne zaune gaban tebir din ya d’an jingina dashi. Cikin duhun na fara bin kafafunsa da fitilar ta d’an haska min da kallo. Kaman wando ne na suit a jikin sa daya dan kama shi sai farar riga mai botira da kusan gaba d’ayan su a balle suke hannuwansa harde a kirji ya tattare hannun rigar zuwa gwiwar hannun nasa. Cigaba nayi da kallon nasa na d’aga ido na zuwa wuyan sa dake sanye da wata irin sarkar data kwanta kan faffaɗan kirjin sa dake a murd’e sai shining yake ga gashin kansa dake zube wajen kafad’unsa wasu sun zubo kan kirjin nasa sun kwanta.

Ido na k’ara d’agawa zuwa dogon wuyan sa wajen Adam Apple nashi (makwalato) na cigaba wajen fuskar sa sai diff wutar ta d’auke gaba d’aya. Tuni na dawo cikin hayyaci na na tuna da gargad’in da aka yimin. Innalilllahi meke damuna na ne? Nashiga uku ni Nadine. Rarraba ido nake saboda matsanancin duhun d’akin baka ganin komai. A mugun hankali naji kaman takun tafiya na kasa kunne inda nake jin takun da baya fita kaman wanda ke sand’a sai kuma naji diff shima ya d’auke. Yanzu nake jin ciwon rashin ganina cikin duhun da banayi. Da Sam ban damu ba amma yanzu saboda wannan mugun naji ina ma ya dawo ko na samu naga abunda yake kar naje ya kashe ni a banza.

A hanzarce na kai hannu na kare ido na saboda wani irin haske dal da dakin ya dauka lokaci d’aya. Murmushi (chuckling) naji anyi mai birkita lissafin mutum nayi saurin juyawa inda naji sautin. Sai da na kusa zubewa a k’asa lokacin da kwayar idon mu suka had’u jikina ya hau kyarma bansan sanda na d’aga hannuna na nuna saba. Yana zaune yanzu kan kujerar katon glass tebir irin ya dogara duka gwiwar hannun sa kanshi ya talleb’e hab’ar sa da yatsun sa daya had’a su guri d’aya.

Innalilllahi wa Inna’ilaihi raji’un. Baza kuso kuga irin matsanancin tashin hankalin dana shiga ba wannan lokacin babu abunda ke yawo a kwanyar kaina sai kalmomin dana furta ranan kaman

” , , ”

Innalilllahi wa Inna’ilaihi raji’un shi ne King AZRAH. Shine na gama zagin sa kan idonsa cikin rashin sani duk da cewa wasu kalmomin da hausa na fad’e su. Na shiga Uku, Na shiga Uku.

Da kyar na d’aga ido na na kalle shi har yanzu yananan yanda yake fuskarsa babu wani expression a kanta. Kwayar idansa da ke da girma gata baka sid’ik kaman midnight dake bada wani calm expression ya zubamin kaman mai ganin hanjin cikina. D’aga gira ya yi gefen bak’in sa shima ya d’aga (smirk) da alama tsoron sa da ya gani kwance kan fuskata ya bashi enjoyment. Magana ya yi a kasalance muryar sa a kausasashe

“Masmik?”

Saboda firgici na kasa bashi amsa sai kai kawai da nad’aga. Gira ya k’ara d’agawa da alama kaman yin hakan nature nashi ne. Da sauri yanzu nace murya na rawa

“NADINE”

A d’ai-da’i ce ya kira sunan nawa “NA-DI-NE.. hmm”

Sunayen Allah kawai nake kira cikin raina da duk wata Addu’a data zo baki na. Murmushi ya k’arayi na lura da double dimples nashi a ko wane kunci. Tun daga sama har k’asa ya kalle ni sai kuma ya tashi daga zaunen da yake ya zagayo gaban tebir d’in ya zauna kaman yanda ya yi d’azu dana shigo.

Kuttt na had’iye yawu ina kallon sa na matse kafafuwana dake rawa guri d’aya. A take yanayin fuskarsa ya chanza zuwa wani deadly calm expression. Magana ya fara da calm voice cikin harshen turanci

” what is that you say?”

Kuttt na k’ara had’iye wani yawun, naji kaman na juya a guje na fice. Ga mamakina sai naji yana maimaita abunda nace harda hausar da nayi.

” Kayi hankali cikin masarautar nan idan kai sabo ne. Tunda har ka shigo masarautar nan nasan kasan wane KING AZRAH. Ba sai na tsaya ina maka dogon bayanin rashin mutuncin sa da rashin Imanin saba,amma dai kayi hankali da takun ka ”

Yana dasa aya na kusa zubewa k’asan gurin. Duk irin matsanancin sanyin na d’akin wanda tsab mutum zai daskare cikin sa zufa na had’a kaman wadda aka zubawa ruwa. Gashin kaina dana tufke shi a tsakiyar kai na d’ora hula a kan nawa ina jin yanda gumi ke biyowa ta cikin gashin yana bin wuyana da goshina. Shi kanshi gashin ya jike jagab. Ban gama shiga tashin hankali ba sai da naji ya k’ara magana yanzu da Hausa.

“Ko kinsan tsawon lokacin dana d’auka ina koyan wannan yaren naki saboda na gane ma’anar kalman MAI KAN AGWAGWA DA KATON CIKI?”

“You dare to insult me like that?, mene ma ki ka ce .Bani da Mutunci da Imani?, why not na nuna miki rashin Imanin nawa zahiri yanda zaki ji dad’in bada labari da kyau?, . You disrespect me in the worst way possible. I know you have being told not to look at me, amma gaki kina kallo na ido cikin ido?”

Da azama na sauke ido na k’asa jikina na rawa kaman mazari. Wani murmushi naji ya k’ara yi da nasan babu alkhairi cikin sa.

“So Nadine. Daga yau zaki zauna a nan don ki sheda rashin imani na da rashin mutunci na. Aikin ki ya dawo cikin masarauta daga yau. Know Dismiss..”

Baima k’asara ba na juya a sukkuwanne na fice da mugun gudu daga d’akin.

 

 

 

 

 

Share pls

Leave a Comment

error: Content is protected !!