Ya Ta’ba Yin Zina Da Mahaifiyarta, Shin Aure Ya Halatta Atsakaninsu
YA TA’BA YIN ZINA DA MAHAIFIYARTA, SHIN AURE YA HALATTA ATSAKANINSU ?
TAMBAYA TA 2785
*******
Assalamu Alaikum.
Akkaramakallahu barka da war haka.Allah ya qara basira da nisan kwana..
Malam ina da wata tambaya ne wacce wani ya tambayeni ita, Haqiqa tambayar tafi qarfina shine Nqce masa ya bari zan tambayo masa nima
Malam Yana tambayar Halaccin Auren wata yarinya da yake nema ne, Amman abin cikensa ya gano Cewa Ya ta6a soyayya da uwar yarinyar a Wani gari can shekarun baya da suka wuce Har sun ta6a Zina da uwar ..
Yanxu Kuma ya tsinchi kqnsa a wannan yanayin, A cewarsa Yanxu sun shaqu da yarinyar har sun fara maganar Aure…..Amman fa yarinyar Bata San wannan labarin ba.
To shine yake tambayar Ya halatta ya cigaba da neman auren yarinyar ko Kuma Aure ya haramta a tsakanisu Saboda wannan dalilin?
Allah ya taimaki Malam wannan ita ce tambayar.
AMSA
***
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ita zina haramun ce. Kuma babu sa’bani atsakanin malamai game da girman laifin dake cikinta, Amma duk da haka bata haramta abinda aure ke haramtawa.
Don haka ya halatta ka auri ita wannan yarinyar mutukar dai ba kaine kayi sanadiyyar zuwanta duniya a wannan zinar da kayi da mahaifiyarta ba..
Ibnu AbdilBarri acikin littafinsa Al Istizkar (Juz’i na 5 shafi na 463) yace “Malamai sunyi sa’bani game da shin idan mutum yayi zina da wata mata, shin ya halatta gareshi ya auri ‘yarta ko mahaifiyarta? Ko kuma m idan ya ta’ba aikata zina da wata mace, shin ya halatta dansa ko mahaifinsa ya aureta? Shin zina tana haramta abinda aure ke haramtawa?
Malik ya fa’da acikin Muwatta cewa “Yin zina da mace ba zai sanya mutumin da yayi zinar da ita din ya haramta ga ‘Yarta ko mahaifiyarta ba. Amma idan mutum ya aikata zina da mahaifiyar matar da yake aure, to wannan bazai sanya matarsa ta haramta gareshi ba, sai dai za’a yanke masa hukuncin kisa ne (ta hanyar jefewa) zina bata haramta abinda halastaccen aure ke haramtawa.
Wannan shine fatawar Ibnu Shihab Azzuhriy da Rabee’ah, kuma ita ce fatawar Laythu bn Sa’ad da Shafi’iy da Abu Thaur da Dawuduz Zahiriy kuma ita ce fatawar Abdullahi dan Abbas (ra). “.
Karshen abinda na cirato daga chan din kenan. Amma wasu malaman suna bada shawarar cewa kada mutum ya auri ‘yar matar da ya ta’ba zina da mahaifiyarta saboda yin hakan zai Qara sanya yawan haduwa ko chudanya tsakaninsa da waccen matar (wato uwar matarsa) saboda gudun kada shaitan ya sake rinjayarsu zuwa ga komawa cikin laifin nan da suka ta’ba aikatawa.
WALLAHU A’ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (19/07/2020 28/11/1441).
Leave a Comment