Ya ya mata Hausa Novel Complete

Ya ya mata Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*’YA ‘YA MATA*

 

( *Kyautar Ubangiji* )

 

“`MALLAKIN“`

 

*Fad’imatu Musa Usman*

( _Mmn Khairi And Muslim_ )

 

P.g 1&2

 

 

لبسم الله الر حمن الر حيم

 

 

“`Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangiji mad’aukakin sarki me kowa da komai wanda ya ba ni iko da damar rubuta wannan littafi, dan haka ina k’ara mik’a godiya ta a gare shi“`.

Ya ya mata

“`Ya ubangiji na ka k’ara tsira ga MUHAMMADIRRASULULLAH da zuri’ar sa da Sahabban sa baki d’aya“`.

 

*TSOKACI*

*Ban rubuta littafin nan dan wani ko wata ba idan kuka ci karo da wani abu da yayi dai-dai da na ku labarin to a rashi ne, dan Allah a kiyaye zargi*.

 

 

 

 

 

______________Wata budurwa ce wacce a k’alla baza ta wuce 18years ba, zaune a kan kurerar zaman tsakar gida da kayan wanki a gaban ta tana wanki hawaye na ambaliya a fuskar ta kai daka gan ta kasan ba’a son ran ta take wankin ba duba da yanayin yadda take chud’a kayan da kuma yadda hawaye ke ta sintiri a fuskar taba tare da sautin kuka ba.

 

Wata budurwa ce wacce ita kuma a k’alla shekarun ta baza su wuce 16 years ba ta shigo gidan da sallama cikin uniform d’in islamiyya.

 

“Assalamu alaikum!, salamu alai…”

 

Fasa k’ara yin sallamar ta yi lokaci guda ta rik’e k’ugu gami da cewa.

 

 

“Kambun bala’i Anty Kalisa me nake gani?, uban wa ya saki yi masa wanki? da wannan lokacin haka magaruba ta taho?, da alamun ma fa yau ba’a barki kinje islamiyyar ku ba ko?”.

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
‘Dagowa wacce aka kira da Kalisan ta yi cikin sauri gami da yiwa wacce ta mata maganar alama da ta yi shuru kar a jiyo ta.

 

 

Ya mutsa fuska yarinyar tayi sannan cikin k’unar zuciya tace.

 

 

“Akan me zan yi shuru?, tunda ke baza ki iya magana ba ni ki barni na yi inya so a tsire ni, sabida ni wallahi kinsan bana d’aukar k’ananun rainin hankali………”.

 

 

“Inye to rasa kunya b’eran tanka wato kin dawo zaki fara wa mutane rashin kunyar taki ko?, to wallahi bari wannan d’an ya dawo sai nasa ya koya miki hankali shegiya kawai mara mutunci me bak’in hali irin na uwar ta”.

 

 

Wata Mata ce take ta surfawa yarinyar masifa a lokacin da ta fito daga d’aki d’auke da wasu kayan wankin a hannun ta, ta tarar yarinya .

 

Shuru yarinyar ta yi bata kuma cewa komai jin matar tace zata had’a ta da Yayan su dan haka ba tare da ta kalli inda matar take ba ta d’auke kai tayi cikin d’akin su tana ‘yan k’unk’unai.

See also  Ni da Yaya Marwan Love and romantic story

 

 

Tana wucewa matar kamar jira take ta watsowa Kalisa wankin a fuska gami da cewa.

 

 

“Dan uban ki kiyi maza maza ki gama min su yanzun nan ko kuma ran ki yayi masifar b’aci, ita ma Nihlan da take zuga ki wallahi duk sai nayi maganin ku ai ita d’in ma ba tsoran ta nake ba gani take dan ina rabuwa da ita a wasu abubuwan tamkar tsoran ta nake to zata gane bata da wayau, daga ku har bak’ar dagar uwar ta ku duk a tafin hannu na kuke wallahi tunda albarkaci na kuke ci tunda ni ce me ‘YA ‘YA MAZA a cikin gidan nan ba yadda zaku yi dani dole na juya ku yadda rai na ke so domin kuwa yara na su suke fita su nemo su kawo ku baje ciki ku jibga ba tare da kunsha wuyar komai ba, sabida haka dole nayiwa uwar ku abinda naga dama kuma ta hak’ura tunda ba zuciya kare ya lashe”.

 

 

Tana gama zazzaga masifa ta d’auki buta ta shige ban d’aki.

 

 

I ta kuwa Kalisat tun tana kukan zuci har ya fara fitowa fili kuka take me tsuma zuciya………

 

 

__________________Zaune suke su biyu akan benchi suna ta b’asgar rake, suna ta sambatu, bayan sun gama shan raken d’aya ya juyo ya fuskanci d’ayan sannan yace.

 

 

“Wai kuwa KUNU ya maganar mutuniyar ka kuwa?, nifa kwana biyu bana jin kana min zancen ta kamar yadda ka saba yi a ko da yaushe, ko dai ka hak’ura da auren na ta ne?”.

 

 

Saurin zaro ido wanda aka kira da Kunun ya yi cikin d’an firgici ya wage wawakeken bakin shi nan take jajayen hak’oran sa wanda gansai duk ya cika gefe da gefen hak’oran tabbatar alamun basu tab’a ganin burush a cikin su ba balle makilin, yace.

 

 

“Tab uban wa ya gaya maka zan iya hak’ura da KALISA? lallai baka da hankalin IRO, to ko wanne irin wulak’anci zata min ko kuma wannan fitinanniyar k’anwar tata NIHLA ta min wallahi bazan ce na fasa auren ta ba, tunda Babban Yayan su ya riga yace ko mutuwa zatai ni ne dai mijin ta gama hange-hangen ta shi ni yaga nafi kowa dacewa da ita dan haka ni zai ba, to kuwa a min wannan alk’awarin na zo nace na fasa inaaaaa………”.

 

 

“Dakata” Iro ya katse Kunu sannan ya cigaba da cewa.

 

 

“Maganar gaskiya abokina wallahi sam-sam Kalisa bata dace da kai ba, ka dubi yarinya kyakykyawa irin wannan zubin matan sarakai ko hamshak’an masu kud’i ko masu mulki, sannan kace da kai ta da ce?, dube ka fa Kunu wani gaja da kai……”.

 

 

Ya mik’e tsaye yana nuna Kunun da hannu yana tab’e baki.

 

 

Sakin baki Kunu ya yi yana kallon shi kafin cikin k’uluwa da fusata yace.

 

 

“A hakan dai kuma aka ga damar bani ita ko ma a yaya nake, ai naga bani na halicci kaina ba Allah ne ya halicce ni ko?”.

 

 

“Eh daman bance wani ne ya halicce ka ba ai, Allah ne amma kuma daya halicce kan ai baka gyara kan ka kuma ai MANZON ALLAH (s.a.w) da kansa cewa ya yi a cikin wani hadith da wani malamin mu ya tab’a yi mana tun muna yara a islamiyya manzo da kansa yace ” *Annazafatu minal iman* ma’ana ita tsafta cikon imani ce, to amma kai fa ka gan ka dan Allah ina tsafta a tare da kai?, nifa in gaya maka tun da na ji wannan hadisin na rik’e shi har yanzu ban manta da shiba shi yasa kaga kaf cikin abokan mu na fiku gayu sabida ni bana wasa da maganar MANZO”.

 

 

Kunu yana jin maganar da Ma’aikin Allah yayi akan tsafta dan da nan jikin shi ya yi sanyi da haka cikin rawar murya ya amsa da cewa “(S.A.W)”.

 

 

Sannan cikin sanyin jiki dana murya yace.

 

See also  Bariki Gadona Hausa Novel Complete

“Aboki na daga yau zan ke gyara jiki na duk da bani da kayan ‘yan gayu wallahi kasa jiki na duk ya mutu da na d’au zafi sosai amma tunda ka ambaci Manzon Allah shi kenan ka gama magana, amma dan Allah ka taya ni da addu’a Allah ya mallaka min KALISA”.

 

 

“Shi kenan kar ka damu Allah ya baka” ya fad’i hakan yana mai mik’a masa hannu alamar yin musabaha.

 

 

Shima kunun mik’a masa yayi sukai musabahar sannan Iro ya masa sai an jima ya wuce.

 

 

Shikam Kunu komawa yayi ya zauna yana ta tariyo maganganun Iro.

 

 

 

_ASTAGFIRULLAH WA’ATUBU ILAIHI_.

[16/12, 4:12 pm] +234 810 533 7469: *’YA ‘YA MATA*

 

( *Kyautar Ubangiji* )

 

“`MALLAKIN“`

 

*Fad’imatu Musa Usman*

( _Mmn Khairi And Muslim_ )

 

 

3&4

 

لبسم الله الر حمن الر حيم

“`Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangiji mad’aukakin sarki me kowa da komai wanda ya ba ni iko da damar rubuta wannan littafi, dan haka ina k’ara mik’a godiya ta a gare shi“`.

 

“`Ya ubangiji na ka k’ara tsira ga MUHAMMADIRRASULULLAH da zuri’ar sa da Sahabban sa baki d’aya“`.

 

*TSOKACI*

*Ban rubuta littafin nan dan wani ko wata ba idan kuka ci karo da wani abu da yayi dai-dai da na ku labarin to a rashi ne, dan Allah a kiyaye zargi*.

 

 

 

___________Kalisa tana kuka ta dirzar kayan wanki, ta na cikin hakan ne kuma ta saki wanki ta sa hannu biyu ta dafe hab’a ta tafi tunanin tarihin rayuwar su.

 

*ASALINSU*

‘Yan jahar yobe state ne amma su na zaune a cikin garin potoskum, Sunan mahaifin su malam Ayuba Allah ya yiwa mahaifin su na su rasuwa tun Kalisa na ajin k’arshe na primary, ya mutu yabar su su goma cif a duniya, Maman Kalisa na da yara biyar dukan su mata Kalisa ita ce babba a gurin Maman su sai mai bin bayan ta Nihla,sai Anisa,sai Yusra, sai autar su Yesmin.

 

Sai kishiyar Maman su wacce ita ce uwar gida itama tana da yara biyar amma ita duk maza ne kuma yaran ta sune manya dan autan ta ma shi ne sa’an Kalisa amma Kalisa ta girme shi da watanni 7 a duniya, Babban yaron ta sunan shi Isya suna kiran shi da Yaya ita kuma uwar tana ce masa wannan yaron ko wannan d’an duk sunan dai da yazo bakin ta sabida bata iya kiran sunan shi tana masa kara a matsayin shi na d’an farko, sai mai bi masa shi kuma sunan shi Idris, sai Aliyu sai, Ilya sai autan ta Jafar.

 

Suna rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali kafin mahaifin su ya mutu domin mutum ne jajirtacce duk da bamai kud’i bane amma yana k’ok’arin wadata su.

 

Tunda ya fad’i ya mutu shi kenan komai na su na farin cikin su Kalisat ya rushe domi kuwa KULUWA uwar gidan Baban su tuni ta rusa komai domin kuwa bata bari yaran ta su kyautata musu a matsayin su na ‘yan uwan su kuma Mata masu rauni, tun ranar arba’in d’in mahaifin su tasa aka raba gado aka bawa kowa nasa, hatta gidan da suke ciki taso a sashi a cikin rabon gadon sabida tasan ita zata mallake shi amma dangin mahaifin Kalisa suka k’in amincewa duba da yanayin d’an uwan na su ba wasu kadarori ya bari wad’an da su ma su Kalisa da mahaifiyar su za su samu matsuguni ba ga shi kuma ba ta da kowa domin marainiya ce a hannun Yayan ta taso kuma shima tun bayan auren ta ya rasu dan haka bata da wani tudun dafawa,shiyasa dangi sukai ruwa da tsaki wajen hana sa gidan a cikin rabon gado aka bar shi akan cewa har sai ABU mahaifiyar su Kalisa ta gama aurar da yaran ta kaf sannan a raba sabida idan aka raba ba’asan ya zata yi da yaran ba gashi dangin Baban su Kalisan ba mai k’arfin da zai iya d’aukar d’awainiyar su.

 

 

Haka su ka ci gaba da rayuwa a gidan a hannun ‘yan uba masu tsananin nuna musu ‘yan ubanci bisa koyarwar uwar su domin kuwa tsana suke nuna musu me tsananin gaske gashi kullum cikin yi musu gori suke a matsayin su na ‘YA ‘YA MATA sai kace su suka halicci kan su a hakan ko abu yaran Kulu suka shigo da shi sai sun ci sun rage sannan ake ba su Kalisa shima sai sun taki sa’a, Mahaifiyar su Allah ya yita mace mai hak’urin gaske duk tsangwamar da ake mata ko yaran ta bata bud’e ido ta kalla bare ta tanka kuma ko yaran ta za suyi magana hana su take domin kuwa kaf yaran ta Masifaffu ne na ajin k’arshe basa barin ta kwana Albasa ce wacce bata yi halin ruwa ba, kaf d’in su Kalisa ce me d’an dama-dama, k’arshen Bala’i kuwa Nihlah kenan dan ita bata jin magana ko kad’an domin kuwa indai an mata sai ta tanka ko da uwar ta hana ta bata bari,amma ita Kalisa ko ta taso zata tanka indai uwar ta kalle ta shi kenan ta bar abun haka zata bari ko da bata so ba.

See also  Bazawara ce Hausa Novels Doc Download

 

 

Haka suke rayuwa cikin rashi ‘yanci wata ran ma abunda za su ci gagarar su yake, sabida suna gani za’ayi a hana su ga mahaifiyar su bata da k’wakk’warar sana’a da ta fara Kulu zata rushe ta sabida Kulu Allah ya yi ta macece mai bak’in ciki da hassada ta tsani ta ga wani ya ci gaba a rayuwa inba ita ko yaran ta ba, dan haka bata barin Abu da sana’a da Abun ta fara zata rusa ta ita yaran ta da ta dena sai ita kuma ta ci gaba da yin sana’ar da Abun ta bari, ga yaran ta gaba d’aya ta koya musu bak’in halin ta, Aliyu ne kawai me d’an dama-dama .

 

Haka rayuwar su Kalisa ta kasance har Allah ya sa Kalisa ta kammala secandry ita ma secandry d’in wani mak’ocin su ne ya sa su ita da Nihlan amma da ta yayyayen su ne saidai suyi ta zama a haka hatta islamiyya mak’ota ke sa su sabida ba wanda be san halin da suke ciki a gidan ba, bayan ta kammala makarantar gaba da primary Babban yayan su Isya ya bujiro mata da maganar aure wai zai had’a ta da Kunu wani mai saida rake a bakin layin su wanda tun tuni yake nunawa Kalisa so amma bata tab’a ko da kallon shi ba bare tasan yana yi sabida sam-sam Kunu bashi da wani tsari wanda za’ace mace kyakkyawa ajin farko irin Kalisa ta saurare shi sabida mugun K’azami ne na tashin hankali kullum da kaya d’aya yake yawo ga hak’ora a dafe duk sun yi gansai sabida rashin yin burush ko yaya ya bud’e baki zai magana ji zakai tamkar an bud’e shaddar da ta wuni a rufe wai amma shi za’a bata duk mane man auren ta a rasa wa za’a bata wai sai Kunu kuma ba tare da anyi shawara da ita ba kawai aka ce mata shi zata aura ita da ko soyayya bata tab’a yi ba domin kaf masu son ta ba wanda ta tab’a bawa damar yin soyayya da shi, sabida ita ta tsara cewa ba za ta yi aure ba har sai tayi karatu me zurfi ta zama cikakkiyar lawyer me k’watowa ‘YA’YA MATA hakk’in su amma wai kawai a zo a bujuro mata da maganar aure auren ma da Kunu dan haka ba tare da shayin komai ba ta sanar da Yayan nata ita fa bata son Kunu karatu kawai take so ta cigaba da yi, ai kuwa nan da Yayan da Uwar sa da sauran k’annan sa suka mata caaaah a ka , da taga da gaske ba makawa auren za’a mata shine ta amince amma tace su barta ta samu wanda take so amma ko kashe ta za suyi wallahi ba zata auri Kunu ba, jin hakan yasa kuwa suka sake rufar mata, takura ta yau daban ta gobe da ban ga shi Uwar ta bata magana komai za su yi mata kuma idan Kalisa tace zata yi uwar ta hana ta, ba bu irin wahalar da basa gana mata akan auren Kunu amma k’ememe ta k’i amincewa, a cikin kalolin wahalar da suke mata shi ne fa yau ma Kulu ta jibgo mata wanki sannan ta hana ta zuwa islamiyya.…

 

 

“Ke!! Kalisa dan Uwar ki wankin da na saki kenan!!, shine zaki saki wanki ki kama tunanin banza ko?, to wallahi yau sai kin gane kuskuran ki “.

 

 

Fir gigit Kalisa ta dawo daga tunanin tarihin rayuwar ta a loacin da Kulu ta fito d’auke da buta daga ban d’aki shi ne take surfa mata ruwan masifa…..

 

 

 

“`ASTAGFIRULLAH WA’ATUBU ILAIHI“`



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Ya ya mata Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top