Hausa Novels

Ya zan yi da Raina Hausa Novel

Ya zan yi da Raina Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

YA ZANYI DA RAINA

 

 

By

 

 

Hanyluv

 

 

 

 

 

 

Free page

 

 

 

 

Page 1️

 

 

…….Motoci ne wajan guda biyar suke sharara gudu akan titi kae kana ganin irin gudun da suke yi xaka san sauri suke sakamakon hadarin da suka ga ya taso gadan², kana ganin motocin nan kasan wani mashahurin me kudi aka ɗakko, wata shigiyar haɗaɗɗiyar baƙar mota ce a tsakiyar su Bugatti Divo a ƙalla zata kae $5.8 Million kudin Amurika se ɗaukar ido take yi motoci biyu ne a gaban ta biyu a bayan ta masu ƙirar Mercedes- AMG Project one suma baƙaƙe, tapiya suke yi a gaggauce basa so ruwan nan ya riske su a hanya saboda sun san wanda suka ɗauko yana jin tsoron ruwan sama

 

 

Wata anguwa suka shigo me masifar kyau kae kace ba a Nigeria suke ba a hankali suka fara horn a wani katafaran gida kaman gidan shugaban qasa daga waje gidan ya tsaru iya tsaruwa securities ne a bakin gate din gidan, me gadi ne ya ƙaraso da sauri ya bude musu Gate din, sae da suka fara shiga gidan naga ashe ba komai nagani a waje ba, fadin girman gidan da tsaruwar shi ma ɓata lokaci ne, gida me shegen kyau fatin gidan ya kasan ce white and ash part hudu ne a gidan daya ya kasance madaidaici me kyau sauran ukun kuma masu girma ne sae dae daya daga cikin su haduwar shi kuma ya fi dukkan su, kowanne ya kasance anyi mae ado da flowers masu matukar kyau, a parking space suka yi parking motocin, duk inda na kae da son irga motocin gidan kasawa nayi, motoci ne haɗaɗɗo a gurin…

 

Suna gama daidaita parking suka yi saurin fitowa.. ɗaya daga cikin bodyguard dinne yayi saurin bude motar dake tsakiyar su, sun kae 5min kafin wanda ke ciki ya pito, kafar shi ya zuro daga cikin motan sanye da Black cover shoe👞 , fitowa yayi gaba daya kasancewa ya juya baya ban samu ganin face din shi ba amma Black suit ne a jikin shi ya kasan ce irin zaratan dogayen mazan nan ne wa ƴanda suka amsa sunan su maza, gashin kanshi ya kasance baƙi me santsi yasha gyara se shining yake yi, tapiya ya fara cikin sassarfa ya nupi part din da yapi kowanne haduwa yana isa ya bude door din ya shiga.

 

Dakin Duplex ne, painting shi white ne komae na dakin mint green and up white ne daga gepen stairs din dinning area ne suma mint green and up white dinne da console gepen dinning din, 2 bedrooms ne se kitchen a ƙasa a sama kuma wani parlorn ne se 2 bedrooms acikin shi, parlorn ya hadu iya haduwa se wani daddaɗan kamshi ne ke tashi a ciki, direct sama ya nufa yana shiga parlorn be tsaya ba ya wuce bedroom dinshi daya ke right side ya buɗe ya shiga,

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Kyaun bedroom din kuwa koh na shugaban ƙasa albarka, komae na dakin white nd golding ne, yana shiga ya fara rage kayan jikin shi, daga shi sae boxer ya shige toilet, 30min after ya buɗo kofan ya pito tun daga fararen santala²n kafafun sa na fara kallo masu ɗauke da kwantancan baƙin gashi har na iso xuwa faffaɗan ƙirjin me yalwan baƙin gashi a kwance, face din shi na kalla, yana da manyan idanu masu ɗauke da zara²n eyelashes, yana da cikan gashin gira , hancin shi dogo ne, pink lips dinshi sae shining yake yi ga beard din shi shima ya kwanta, Masha Allah kyakykyawa ne ajin farko kae kace balarabe ne, irin shi ake kira da Mijin Novel, sae faman lumshe lulu eyes dinshi yake yi kaman me jin bacci, baze wuce 30yrs ba, ƙarasawa yayi gaban dressing mirror dake dauke da mayuka da perfumes da dae sauran su, shafe² ya fara bayan ya gama ya feshe jikin shi da perfumes kala², gaban closet ya je ya buɗe ya ciro top red color me gajeren hannu da trouser three-quarter black color yasa sannan ya qara ya feshe jikin shi da perfumes ya gyare gashin kanshi sannan ya pito, Daya daga cikin manyan part din ya nupa yana xuwa ya bude door din tare da shigewa, shima haɗaɗɗan plat ne duplex amma shi ya kasance purple and up white ne komae na dakin, painting dakin kuma up white shima dakuna uku ne sae kitchen a ƙasa a sama kuma akwai wani parlorn da kitchen se 3 bedrooms

 

 

Wata farar babbar kamilalliyar mace ce kyakkyawa me kama da wannan saurayin zaune akan daya daga kujerun parlorn hannun ta rike da remote tana kallon tashan NTA News, aƙalla baxa ta wuce 50yrs ba, Sanye take da atampa anyi mata design da purple and black color anyi dinkin A-line gown anyi wa atampa stonework wuyanta sanye da sarƙar gold da earrings dinta, Murshimushi yayi wanda yasa dimples dinshi lotsawa karasowa wajan matan ya fara yi “MOMMA NA” ya fada da cool voice din shi, waigowa matar daya kira da Momma tayi tana faɗaɗa murmushin ta kallon shi har ya qaraso inda matan take zama yayi a kusa da ita tare da kwantawa yana daura kanshi akan cinyar ta yana lumshe lulu eyes dinshi, ajiyar zuciya Momma ta sauke tana shafa kwantacciyar sumar shi

 

“Mage uwar son jiki ya akayi ne?” Momma ta fada tana murmushi shagwaɓe fuska yayi yana faɗin “Momma na gaji Twiny is wicked baki ga aikin da ya tara mun ba”, Momma ta tunsire da dariya tana fadin “habawa ai ni AYMAN ya kyauta mun da yayi maka haka yayi magani uban ƴan son jiki” turo baki yayi yana shagwaɓe fuska, Shafa kanshi ta qarayi tana faɗin “oya my lazy boy tashi go and perform your ablution naji an fara kiran magbri….” Kafin ta qarasa aka turo ƙopan, wani babban mutum ne ke karasowa parlorn ya sha mulum² din farar shadda Gezna se sheƙi take yi taku naji a bayan shi na kalla naga wani me kama da wanda yake kwance a cinyar Momma cikin shiga ta suit, ƙara waigowa nayi ina kallon guy din da yake kwance a cinyar Momma naga kaman tasu ta ban mamaki, kana ganin su kasan twins ne masu matuƙar kama, “Sannu da hanya ABBAN su” naji Momma ta faɗa tana me yi ma mutumin da suke shigowa fara’a, wanda aka kira da Abba shima murmushin yayi tare da cewa “yawwa sannu da gida Wifey”, saurin ta shi yayi daga cinyar Momma yana bawa Abba waje tare da fadin “welcome back Abba”, “Thank you son”, Abba ya faɗa yana zama, “Momma barka da gida, Twiny har ka dawo?” saurayin da suka shigo da Abba ya fada, “yawwa sannun ku da dawowa” Momma tace, shi kuma harara ya galla mai ba tare da yace komae ba, miƙewa Abba yayi da hanzari yana fadin “kuje ku ɗauro alwala muje Masallaci naji an fara kiran sallah”, wucewa sama Abba yayi dan ɗauro alwala su kuma suka wuce dakunan dake ƙasa donyi.

 

suna pitowa suka wuce Masallaci basu samu Momma a parlorn ba dan itama ta tapi yin sallahr, Masallacin dake jikin gidansu suka shiga don gabatar da Sallah, basu suka pito ba se da suka yi sallahn isha’i sannan suka dawo, dayan saurayin da suka dawo tare da Abba part dinsu ya wuce don yana so yayi wanka su kuma suka wuce part din su Abba, suna shiga suka samu Momma tana qara setting dinning qarasowa parlorn suka yi tana sakar musu murmushi Abba yace ni bari na ɗan watsa ruwa na dawo,

 

“A sakko lapia” Momma ta fada tana jan kujera ta ƙara da cewa “Ayaan xo ka xauna, dan nasan yanda kake cemun ka gajin nan kiris ya rage ka fara mun kukan yunwa” , wanda aka kira da Ayaan ne ya dago yana qara marairaice fuska tare da tasowa yana tahowa dinning arean, tapiya yake yi cikin ƙasaita har ya ƙaraso dinning ɗin tare da xama a kujeran data ja mishi, food flasks ne wajan kala 5 ne na farko food flask ne me dauke da White basmati rice dayan kuma Couscous ne anyi jolop din shi da vegetable da hanta da aka yanka qanana se daya food flask din farfesun kayan ciki ne dayan kuma egg source dayan kuma farfesun ne na swordfish yasha Onion… Bayan Momma ta gama buɗewa

 

“Ayaan me xan zuba maka” ta tambaye shi, “just white rice and egg source is enough Momma” ya fada yana yatsine face, fara zuba mishi ta yi yayi saurin dakatar da ita “Momma ya isa”, kallon shi tayi tana ɓata fuska “wae meyasa kwata² baka son cin abinci ne” marairaice fuska yayi kaman wanda yake shirin yin kuka tura mishi abincin tayi itama ta zuba wanda take so tare da jan kujera ta zauna.

 

Suna cikin cin abincin ne Abba ya sakko sanye da jallabiya fara shima ya zauna, saving dinshi Momma tayi sannan ta koma kafin ta fara cin abinci, bude ƙofan akayi dayan ne ya shigo shima ya sauya shiganshi irin na Ayaan amma shi top din shi is yellow shima ƙarasowa yayi ya zauna, “oya yi saving din kanka tunda kayi late ni na gaji da tashi” Momma ta fada tana cin abincinta, ɓata fuska yayi kaman ze yi kuka yana fadin “haba Momma ni bakya sona kinyi saving Twiny amma ni kice ba xaki yi saving dina ba”, Momma tace “ae tun ɗaxu muke jiran ka kae sarkin wanka kaman xaka canxa fata kaki fitowa”, Ayaan ne tunsire da dariya harda buga cinya yana fadin “gaskiyan ki ne Momma na cigaba da cin abincin ki”, “Ayman kyalesu kaji yi saving din kanka ae Allah yaso kana da hannun ka” Abba ne ya fada cikin sigan lallashi, tashi yayi yana kumbure² yayi saving kanshi sannan ya fara ci.. Ayaan kam ci yake yi kaman baya son ci while Ayman sae buga loma yake yi, they are really resemble to each other se ka kalle su da kyau ne xaka gane banbancin su Ayaan yana da dimples da wushirya, shi kuma Ayman bashi da dimples se wushirya amma se ka lurane xaka gane hakan.

 

 

Ayaan ne ya fara tashi, “Goodnight” yace yana shirin tapiya se kuma ya juyo yana fadin “Momma ina HASEENA banji ta ba tunda na shigo”, “tana part din HAJJO tace acan xata kwana”, gyaɗa kanshi yayi tare da juyawa ya wuce part dinsu

 

Yana shiga ya cire kayan jikin shi ya canxa ixuwa pijamas milk color masu bala’in kyau da santsi, zama yayi akan resting chair dake bedroom din ya janyo laptop din shi ya fara dube², ringing wayar shi ta fara ƙirar iPhone 14 Promax daukan wayan yayi yana duba waye yake kiranshi IMRAN ne,

 

sae da ja ɗan ƙaramin tsaki sannan ya ɗaga tare da faɗin “mallam lapia kake damuna da kira a wannan time ɗin?”, daga dayan ɓangaren ji nayi yana cewa “amma lallae Ayaan ka cika ɗan iska ina cikin duba patient ka dame ni da kira in same ka a company bayan naxo ace mun wae ka tapi kaga hadari ya taso saboda ubanka hadarin ze maka”, ya ƙarasa fada cikin ɓacin rai, murmushi yayi dan yasan gaskiya ne ya kunnashi da yawa”, “aw dariya ma kake yi shikenan ba laipin ka bane laipina ne dana ke biyema shirmen ka dama dae Ayman ne”, cikin murmushin shi yace “yi haƙuri aboki na kasan yanda bana son ruwan saman ya taɓani ka bari gobe ka dawo ka same ni”, “uban kane xe dawo ya same ka” Imran ya ƙara faɗa a zafafe, Ayaan kuwa tunsirewa yayi da dariyar da be cika yi ba se ya ga abun mugunta cikin jin haushi Imran ya katse kiran kittt.. murmushi ya qara yi tare da ajiye wayan a gefe yana fadin “ae nasan fada kawae kake yi koh yanxu na kira ka nace kazo zuwa zakayi ”.

 

 

Buɗe kofan akayi Ayman ne ya shigo, dagowa yayi yana kallon shi, karasowa yayi yana cewa “Ayaanu ya dae”, idan yana son tsokanan shi haka yake kiranshi da sunan da Hajjo take ce mai dan yasan baya son tana kiranshi da haka, harara ya balla mai yana qara daure fuska, “haba Twiny na meye na ɓata fuska kaima kasan in banda Abba yace na rakashi ae kasan baxan barka ka tapi Company kae kadae ba” Ayman ya fada yana qarasowa kusa da shi ya zauna, “walhy baka ga yanda nasha aiki ba yau da nasan haka xanje na samu aiki a gurin nan da sae dae na barshi gobe muje tare muyi” Ayaan ya faɗa yana ya tsine face, “toh yanxu dae tunda na dawo kawo aikin nan na taya ka” Ayman ya faɗa yana amsan laptop din hannun shi, bashi yayi yana yi mae bayanin abubuwan da akayi yau a Companyn, duddubawa yayi bayan ya gama ya mike yana fadin “komae yayi daedae” ya juya ze pita Ayaan yayi saurin cewa “oh na manta ban fada maka ba” Ayman juyowa yayi tare da fadin “meya faru?”, “DADDY yace wae next week xamu je Zaria xa’a buɗe sabon restorant din da aka gina na snacks da coffee and so on”, Ayaan ya fada tare da rupe laptop din shi yana qoqarin kwanciya a makeken bed🛏️ din shi , kaɗa kai Ayman yayi yana fadin “Allah ya kaimu” tare da ficewa ya nupa shima bedroom din shi.

 

Ayaan yana shirin kwanciya ya fasa yana daukan wayan shi tare da nemo numbern Haseena yayi dialing 2× ba a dauka ba se ana ukun kafin ayi magana yace “ki kawo mun coffee yanxun nan”

 

Muryan wata Dittijuwa naji tana bambami tana faɗin baxa ta hado ta kawo ba ɗin idan kaji haushi kaje ubanka ya daura maka aure a yau matar ka taxo ta hada maka, dan itama bacci take tana hutawa, “mtwsss wae ke matan nan ina ruwa na da ke da xaki dunga shiga harka ta ne, aure ne kuma baza ayi ba din”

 

kittt… Ya kashe wayan yana jefa ta kan bed ya pita tare da sau ka kitchen yana xuwa ya dauki cup tare da fara hada coffee din,

 

Bayan ya gama ya koma sama, a parlorn ya zauna tare da kunna makekiyar plasman dake parlorn yana sipping coffee yana kallo se da ya gama ya kashe ya tapi bedroom ya kwanta tare da yin addu’a.

 

 

Washegari da wurwuri suka fita Company saboda aikin da suke so suyi.

 

 

 

__________________________

 

 

KAIRAH!!!!! KHAIRAH!!!!!! Wae ina kike ne kizo ki amso mana kamun gidan Laraba mana, wata mata take fada, dan ƙaramin tsakar gidane, wanda gidan yake sasa² ne gidan irin family house din nan na talakawa ne, zaune matar take a kan irin karamar kujeran nan ta tsakar gida, bazata wuce 39yrs ba black beauty ce tana da manyan idanu ga pointed nose kana ganin ta kasan lokacin da take budurwa anyi kyau, riga da zani ne a jikinta kayan sun dan sha jiki…. Labulen dakin nasu ta daga tare da pitowa, wata kyakkyawar yarinya ce me kama da matar dake tsakar gidan sak, kalar fatan jikinta ita ake kira da brown skin din nan se sheƙi take kaman ba ƴar talaka ba, tana da matsakaicin tsaho, tana da manyan idanuwa, eyelashes dinta zara² tana da yalwar gashin gira ga goshin gashi ya kwanta ga hanci dogo bakin nan ɗan ƙarami pink lips zarrr, tana da boobs daidai jikin ta cikin ta a shape kaman bata taɓa cin abinci ba, tana hips irin na manyan mata sae ka dauka ta kae 20yrs din nan ne, nan koh 17yrs take ba dankwali a kanta gashi ne baƙiƙƙirin me santsi se sheƙi yake yi har gadon bayan ta, yarinyar ta hadu ajin farko.

 

 

“MAMI gani”, “ungo kije gidan laraba ki amso mana kamu da ragowar canjin mu na jiya, wannan kuma daga nan ki biya shagon adnanu ki siyo mana sugar ta hamsin”, amsa tayi ta koma ɗaki tasa hijab tare da fita.

 

A kofar gidan taci karo da wani babban mutum, durƙusawa tayi tare da fadin “kawu ina kwana”.

 

“Da ban kwana ba xaki ganni ne eh ye, nace xaki ganni ne”, Kawu ya fada yana huci, “tashi ki bani waje kapin na mangareki makirar yarinya kawae”, tashi tayi da sauri ta fara tapiya ya rakata da faɗin “shegen iyayi Uwar ki ta koya miki girman kai tunda nace ta dunga yi miki awara da dankali yanda Uwani take wa Mariya amma ta kafe wae ke karatu xaki yi, toh ba se ki yi ba daga nan ki kawo mata babban karatu gida”, ya karashe a zafafe, ita dae girgiza kae tayi tana faɗin “fatan ka ya tsari ɗanyen tutu” kasa², tayi wucewan ta, shi kuma gidan ya shige yana ci gaba da fadan da yake yi yana xuwa daman sasan su Khairah ne na farko nan ya faɗa bako sallama a tsakar gidan ya sami Mami rupe ta da fada yayi, “wato kin daurewa yarinyar nan gindi har zuwa take gaba na ta nuna mun ita ban isa da ita ba, toh wlhy daga ke har ita ku pita a ido na kuma karatun ma na kusa katse shi aure xan hada su da JAZULI tunda ta kae munzali”, yana gama fadin haka ya fice rai a ɓace, ita dae Mami tunda ya fara faɗansa kanta na ƙasa bata ce kanzil ba har ya gama ya fice daga sasan.

 

 

Tapiya take yi kaman tana tausayim kasa da kamu a hannunta wani shago ta shiga tare da mika kuɗin hannun ta tana cewa “Adnanu abani sugar ta hamsin”, amsan kudin yayi a zuciyarshi yana cewa yarinyar na burge shi ko kaɗan bata da hayaniya ga ta kyakkyawa da ita chocolate colour, miƙa mata sugarn yayi sannan ya bata chanjin, amsa tayi ta fara tapiya, “Khairaaah” taji an ƙwalla mata kira, waigawa tayi tana murmushi dan tasan koh wacece, wata farar yarinya ce kyakkyawa jikinta da uniform me kaman shekarunta ta ƙaraso tana faɗin “ohh ko shiryawa ma bakiyi ba kenan”, “Haba SARAH kin san ina da sauri yanxu dae mu qarasa gida nayi wanka kaya kawae xan saka” Khairah ta bata amsa, suna tape suna hira har suka qarasa gida.

 

shiga sukayi suka yi suka samu Mmai tayi tagumi tana tunani, “Mami gashi na siyo” Khairah ta fada tana ajiye mata kayan, Mami ta karɓa tana amsa gaisuwan da Sarah ke yi mata tare da shiga dan qaramin kitchen dinsu, ita kuma ɗaki ta wuce tana qoqarin canza kaya,

 

Fitowa tayi sanye da Uniform da school bag dinta, Mami miqo mata kokon tayi tana fadin “gashi yi sauri ki sha na bama Sarah taqi sha”, karba tayi tana faɗin “Mami ae Sarah yar gayu ce bata shan koko”, duka Sarah ta kai mata tana cewa “inji qaryar ki ba”, kaucewa tayi tana xama akan kujeran tsakar gidan ta fara shan kokon, tashi tayi tana cewa “Mami mun tapi” , “har ya ishe ki?” Mami ta faɗa, “eh Mami se mun dawo”, A dawo lapia ta yi musu suka tapi tana mamakin yanda sam Khairah bata son cin abincin.

 

Kasancewar makarantar bata da nisa suna tape suna hira har suka isa makarantar..

 

 

 

 

________________________

 

 

Zaune yake a office yana danna laptop din dake gaban sa, Talephone din dake kan table ya dauka ya danna numbers sannan ya kara a kunne, bayan an ɗauka yace “bring coffee” be jira me za a ce ba maida ya ajiye, after 5min wata budurwa ta shigo ta ajiye masa tare da fadin “the coffee is ready Sir”, da hannu yayi mata alama, juyawa tayi ta pita, aikin shi ya ci gaba da yi yana sipping coffee, nocking kofa aka fara yi, sae da ya jima kapin yace “yess come in”, turo ƙopan akayi, dago idanuwan shi masu kama dana me jin bacci yayi yana kallon me shigowa office din……..

 

 

 

 

 

 

 

Wannan littafin ₦200 ne ki biya kafin free pages ya qare

Send via

1467362098

Muhammad Hanifa

Access bank

Idan kuma katin waya ne na MTN ₦300 seki ɗauka ki turo

evidence of payment through 09129251300 WhatsApp number

 

 

 

 

 

 

 

 

 Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Ya zan yi da Raina Hausa Novel ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!