Yadda Ake Korar Shaidanun Aljanu Daga Gida Ko Gona Ko Fili :
Tag: Yadda Ake Korar Shaidanun Aljanu Daga Gida Ko Gona Ko Fili
TAMBAYA TA 3006
*******************
Assalamualaikum mallam Allah ya saka da alkhairi Allah yaji kan mahaifa, mallam tambaya nake dashi ran jumu’a mai zuwan nan idan Allah ya kaimu inshallahu zanyi aure, to gidan da zan zauna sai wasu su daga cikin yan’uwa na suke ta kiraye kirayen naje na karbo taimako wai na binne a gidan, Ni kuma naki , shine nakeson mallam ya taimaka abani shawara maiya kamata nayi dangane da shiga sabon gida a tafarkin sunna. Daga dalibin a zauren fiqhu nagode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Yadda kayi din nan shine mataki mafi dacewa domin ta irin wadannan hanyoyin ne sai ajefaka cikin shirka ba tare da ka sani ba.
Ga wasu matakai sahihai ingantattu da zaka iya bi domin tsarkake gidanka daga shaidanun aljanu da kuma samun tsaro daga kowanne sharri :
1. Ka rika karanta suratul Baqarah duk bayan kwanaki biyu agidanka. Idan baka samu damar karantawa ba, koda a na’urar MP3 PLAYER ka sanya, muryar karatun ta kewaya ko ina acikin gidan.
Yazo acikin hadisi Manzon Allah ﷺ yace “SHAIDANU BASU ZAMA ADUK GIDAN DA AKE KARANTA SURATUL BAQARAH”.
2. Ka nemi ganyen magarya guda bakwai ka dakasu atsakanin duwatsu guda biyu (ma’ana kayi amfani da duwatsu biyu daya bisa daya) sannan ka zuba acikin ruwa mai tsarki, ka tsoma babban yatsanka na hannun dama acikin ruwan, ka kisanto da bokitin dap da bakinka sannan ka karanta Ayatur Ruqyah gaba dayansu, sai kuma Suratul isra’i da suratu Yaseen, Sannan ka yayyafa ruwan ko ina cikin gidan nan. Har jikin bangon.
To in sha Allahu komai yawan Aljanun dake gidan zasu fita da izinin Allah. Koda suna bayyana afili ana ganinsu, to in sha Allahu daga rannan ba za’a sake ganinsu ba.
3. Lubban Zakar da Mustakha, idan aka samesu ahadasu waje guda arika turarawa acikin gidan, in sha Allahu shaidanu basu zama a inda zasu ji Qamshin wadannan turaren.
4. Kullum kafin ka kwanta barci ka rika karanta fatiha, ayoyi hudu na farkon baqara, ayatul kursiyyi da ayoyi biyu na gabanta, sai kuma ayoyi uku na karshen Suratul baqarah. In sha Allahu Allah zai kiyayeka dakai da gidanka da iyalanka har makobtanka ma daga sharrin barayi ko ‘yan fashi ko matsafa da duk wani mai mugun nufi.
5. Duk cikin dare kafin ka kwanta ka rika yin wannan addu’ar Qafa daya :
أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لَا يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولَا فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وَذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ، وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فِيهَا، ومِنْ شَرِّ مَا ذَرَأَ فِي الأَرْضِ، ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طَارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بْخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ
‘A’udhu bikalimaatil Laahit-taammaatil Allatee laa yujaawizuhunna barrun wa laa faajirin min sharri maa khalaqa, wa bara’a wa dhara’a, wa min sharri maa yanzilu minas samaa’i, wa min sharri maa ya’ruju feehaa, wa min sharri maa dhara’a fil-‘ardhi, wa min sharri ma yakhruju minhaa, wa min sharri fitanil-layli wan nahaari, wa min sharri kulli taariqin ‘illaa taariqan yatruqu bikhayrin yaa Rahmaan.
Imamu Ahmad da Ibnus Sunniy ne suka ruwaito hadisin addu’ar.
In sha Allahu babu wani mummunan abinda zai sameka daga sharrin barayi ko ‘yan fashi ko ‘yan daba ko matsafa ko mahassada. Addu’a takobin mumini ce.
WALLAHU A’ALAM.
- DAGA ZAUREN FIQHU 07064212990 (07/01/1444 05/08/2022).
Agaskiya kuna kokari dan muna ilmintuwa,ni shadantunwa,da fadakartuwa.Allah ya kara basira.
Tnx