Genaral info

Yadda Yan Nigeria Suke Matukar Son Fim Din Squid Game

Yadda Yan Nigeria Suke Matukar Son Fim Din Squid Game

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SU ma ‘yan Nijeriya ba a bar su a baya ba wajen kallon wani fim mai dogon zango da ya shahara a duniya a ‘yan watannin nan, wato ‘Squid Game’.

 

‘Yan Nijeriya sun karaɗe soshiyal midiya da muhawara kan fim ɗin, kamar yadda takwarorin su a sauran ƙasashe ke yi.

 

A Facebook a Nijeriya bayanai sun nuna an yi maganar fim ɗin sau kusan 150,000 a ‘yan kwanakin nan, sai kuma Instagram inda aka tattauna maudu’in #squidgame sau kusan 732,183.

 

Takaitaccen Tarihin Zainab ta shirin labarina

Duk da yake an san da fitowar fim ɗin, amma a yanzu ya tabbata a hukumance ‘Squid Game’ ya zama shi ne gagarumin fim mai dogon zango da Netflix ya taɓa samarwa. An kalli diramar a ƙasar Koriya sau miliyan 111 a kwanaki 28 na farko inda ya doke shirin ‘Bridgerton’ da a da ya ke kan gaba da miliyan 82.

 

 

Ana lissafa yawan waɗanda su ka kalli fim ɗin ne ga duk wanda ya kalli minti biyun farko.

 

 

Kamfanin Netflix ne dai ya samar da fim ɗin.

 

Mataimakin shugaban Netflix na Koriya ta Kudu, maso gabashin Asiya da Australiya da New Zealand, Minyoung Kim, ya ce, “Shirin ya samu gagarumar nasara fiye da zaton mu.”

 

Ya shaida wa CNN cewa, “A lokacin da mu ka fara zuba jari a shirye-shirye da finafinan Koriya a 2015, mun san cewa so mu ke mu yi abin da zai jawo hankalin mutane a yankin Koriya da Asiya da ma duniya baki ɗaya.

 

“A yau, fim ɗin ‘Squid Game’ ya zama gagara gasa fiye da mafarkin mu.”

 

Shirin, mai zango tara, wanda aka fara a watan Satumba, ya na bada labarin wata ƙungiyar wasu matasa ‘yan bana bakwai ne da su ke yin wasannin yara, wato ‘games’.

 

Kusan kowa magana ya ke a kan ‘Squid Game’, kama daga kan fitattun mutane zuwa mashahuran ‘yan ƙwallo.

 

Taurarin fim ɗin sun yi suna a duniya. Jung Ho-yeon, wanda ya fito a matsayin Sae-byeok, ya samu mabiya miliyan 14 a Instagram tun bayan da aka ƙaddamar da shirin a ranar 17 ga Satumba, kamar yadda mujallar ‘Forbes’ ta wallafa.

Leave a Comment

error: Content is protected !!