Yaji ta mata Hausa Novel complete
Da gudu ta fado parlourn gidan tana fadin umma ki taimaka na hadaki da Allah kice ya sakeni wallahi bazan iya zama dashi ba zai kashe ni.
Salati umma ta rafka tana tafa hannu tace ludu ? Ludu kaide kayi asara yanzu da kayi zaman aure ka gwammaci kayi ta zuba yayanka a shaddar kasuwa ? Yanzu Mata ta 10 kenan fa. Toh saketa nace ka saketa banza mugu kawai!
Tunda mahaifiyar tasa ta soma zance fito yake abinsa yana saisaita gilashin dake idonsa ya zazzago da ita tare da gyara sarkokin dake wuyarsa yace hey look mom! Kuna sa min ciwon kai fa kunsan banason stress ko kadan.
Jin hayani da tada zaune tsaye a parlourn yasa budurwar dake rolling gyalen abayanta sauko wa da gudu domin jin kwakwaf takalmar ma a hannu ta rikosu tana mai sakala jakarta.
Da gani bazata wuce shekaru 20 ba ta sauko tana fadin banyi mamaki ba tunda na jiyo ana hayaniya da hauma hauma nasan bazai wuce ludu wando a kasa ba amma nayi tsammani ko sati za’a Dan kai ai.
Hayaiyakowa yayi yana fadin ke marakisiyya in baki fita harkata ba zan daddanna miki ashar fa naga kin Rena ni, kanki rawa yake toh wallahi ki kiyaye ni ko na balla yarinya!
Marakisiyya ta tabe baki tace ashar ai ba kalar wacce banji ba a bakinka harda Wanda bangane ma’anars iya kaci ka zageni na Rama ne Dan na gaji da hakuri da kai ina anfanin GIRMAMA wanda ya kasa kula da zip din wandonsa?
Warbota yayi zai dauketa da Mari umma tace wallahi ludu kana Marin marakisiyya babu ni babu kai. Ba dole yarinya ta rainaka ba? Ace bakada aiki sai cutar da yayan mutane ? Ka wani sabule wando yama sunan Dan iskan abin ? ta tambayi marakisiyya…
Murkuda Baki tayi tace ass down umma tace yauwa ass dawun to fice min daga gida kuma ka bawa yar mutane sakinta sannan ka jira sammaci daga mahaifinta tunda kai bakasan mutunci ba.
Wata file ya ciro a mota ya shigo yana kara sabule wando Wanda gaba daya ba a kunkuminsa take ba dangwalarta kawai zakayi ta fadi. Yace dama da takaddu na nake yawo kuma a rubuce yake printed ma kuwa sunan ta kawai zansa da adadin saki.
Kallon yarinyar dake makale jikin umma tana tsittsilla ido yayi yace young chick yama sunan ki? Baki na rawa tace bara’atu yace yeah haka ne fa ni na dauka binta ne ma.
Marakisiyya da ta kame haba ne tace jar ub* ! Yasin ludu bakada mutunci ko kadan wai baka ma San sunan matar ka ba? Ince kwananku 6 da auren? Kamata yayi ace kuna shauki da kaunar juna kuje honeymoon shine har ka fice Mata aka? Gira ya daga Mata yana cije lebe irin na yan iska yace toh bata iya kure bulalata ne ai.
Mari umma ta sauke mai tana fadin Weldon uban marasa tarbiyya chief of yan iska a idon uwarka da kanwarka kake zancen batsa?
Kallon marakisiyya tayi tace ke kuma yar jakan uba nasan zancen yana miki dadi toh wuce munafukar banza ki tafi jami’a kuma dama idan gp dinki bai canja ba wannan semester keda babanku.
Ciki ciki marakisiyya tace ai in canji ne zaku samu in na kwaso carry overs tunda bazaku iya yaba min ba. Umma ko fadi take kundai San halinsa! Wallahi sai ya hanaki pocket money baki daya.
Buga kafa marakisiyya tayi tace haba umma duk kokarin da nake fisabililla kuma AI da gaskiya ta ya za’ayi ayita ma wannan halittar aure kamar siyar yar tsana amma ni ace sai na gama wani degree? Kuma duk kokarin da nake bakwa gani.
Umma tace dallah gafara can semester uku a jere gp dinki 3.75 bazaki canja shi ba? Toh da first class mukeso ki fito. Ko wannen asararren dan uwan naki da kike korafin ana masa aure yayi kokari bai bamu kunya ba.
Gyara zaman wandonsa yayi ya wani karkade Riga yace fada Mata dai umma kaina ba irin nata bane kamar an zuba dusa da 1st class na fita kuma gani fresh guy itama hassada take Dan tasan ba samu zatayi ba jibgata fa ta kusa shekara 20 amma a kasa kamar turmi.
Marakis tace aikin banza a economy din shi ne kake wani fariya? toh ni physics nake karantawa karka kawo min wargi ehe kuma da kake batun tsayi inada ita sosai ma kuwa Kaine de kadau dogon kafa kamar dalbato kuma kasan ance dogo da hankali dace ne.
Sannan da kake batun wani fresh guy ina kyau anan ? Mutum jikinsa duk tattoo nifa ganin Dan kwaya nake ma, kodan menene marabar taku tunda kai har giya ma sha kake kaga kafi kamasho a fadar oga shaidan ko? bata ankare ba taji an jefeta da takalmi tace Allah ya isa na tana mai fita a guje ta shige motanta tana zumburo baki.
Lekowa tayi ta window tace andai yi asara su dogo har yau ba’a girma ba! kuma babu abinda zanyi da tsiya irinka ni ko me irin halinka yace yana so na ya cuce ni ka duba ka fa jiki duk tatoo ga wani Dan iskan Dan kunne ga abin hanci da kake makalawa ka lafta sarkoki a waya sai kace hanjin Dan taure.
Fitowa farfajiyan gidan yayi yana hargagi lokacin motanta na shirin fita yace yarinya karya kike indai girma ne kinsan an girma saide kice an girma ba hankali.
Tace kanka akeji dadin abin kaida bakinka ka fada. daidai lokacin mai gadi ya rufe gate shigowa yayi kamar wani zaki yana huci Yace wallahi mom zan karya kafar yarinyar nan!
Umma tace fadamin waje daya Wanda yake karya ne a cikin zancenta. Mikewa yayi ya nufi hanyar fita yana fadin haba common on mom nifa harda laifin ki yarinyar nan ke rainani. Sai ta kafto min rashin mutunci kawai saiki wani daure Mata baya?
Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta
-
Hausa Novel AppApp
-
Hariji By oum Apnan
-
Bariki na Fito
-
Nakasa ba Kasawa ba ce
-
Siradin Rayuwa
-
Bororoji Hausa novel
-
Life Partner Hausa Novel
-
Heedayah Hausa Novel Complete
-
Duniya ta Amna
-
Zaman Hostel Complete
-
Mahabeer Hausa Novel
-
Matar Makaho
-
Banida Gata
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
-
Kyawuna Jarabta ta
-
Jiddatul khair
-
Wacece Ni Hausa Novel
-
Ahali Daya Hausa Novel
-
Abraham Hausa Novel
Umma tace jeka de Allah ya shirya kuma yaune rana na karshe idan ka sake shigo min parlour da takalmi babu kai babu gidannan. Sannan da kake batun ta rainaka ka gyara hali tayi respecting dinka tunda kaima ai ka rena uwarka, ubannaka ma Dan kana samun kudi wajensa yasa kuke dasawa.
Ficewa yayi bai karashe jin zancen mahaifiyar tasa ba yana fito Dan ba karamin kular dashi marakis keyi ba duk yadda bayason magana ko ya shiga harkarta yar iskan kanwar tasa sai ta tsokalo shi.
Mota ya shiga ya bude gwangwanin beer dinshi ya soma sha yana fadin kai bakina har ya fara ciwo tsabar surutun da nayi yana mai nufin hotel kamar yadda ya Saba.
Marakis tana isowa makaranta ta fito sidif sidif ta shige aji Dan ba abinda bataso kamar popularity ita dai burinta daya kuma bai wuce tayi aure ba. Don tasan kanta da halittar da Allah ya Mata ko zama tayi a gefen namiji a aji sai ta bata jikinta koda kuwa magana ma bata hadasu ba.
Kamar kullum zama tayi a tsakiyar kawayenta kuma aminanta guda biyu mansura da habiba wadda suke ce ma Beeba.
Mansura cikin jin dadi tace hehe kawas yau zaki sha mama ki! Marakis da son jin gulma tace menene? Beeba tace yanzu tunda saura 15 mins a shiga darasi mai zai hana ki rabani na siyo abinci ? Dan banci abincin Rana ba na fito.
Mikewa sukayi suka fice daga slt din suka nufi school market, marakis na hadasu da Allah su fada Mata surprise din su kuwa sai ja Mata aji suke suna dariya. Fuskar abin tausayi tasa bayan sun siyo abinda zasu siya suna dawowa ita coke kawai ta siya.
Kallon kasa take tana tafe tana musu kukan karya bata ankare ba taji suna marakis gabanki kalli gabanki kamin ta iya dago kanta sukayi wani wawan karo dashi wadda ya haddasa komai na hannunshi zubewa tare da fadawa cikin ruwan da ya hadu a gefe ita ma ta fada jikinsa.
A tunaninta yan iskan ajinsu ne hakan yasa ta saki Goran hannuta Wanda dama already ta kwada masa ita goshi ya bata masa farar shaddar sa da lemo tana mai fadin sannu hanshaki uban marasa mutunci ai sai….
Zaro ido tayi kamar mujiya ganin Wanda tayi wa aika aikar ba kowa bane sai…….


Name: | [Yaji ta mata Hausa Novel complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi

Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram

Leave a Comment