Girke-Girke

Yanda ake hada Kalolin drinks na Zamani

 

CUCUMBER AND APPLE

INGREDIENTS:

1.Coconut
2. Cucumber
3.Apple
4.Sugar
5. Milk water
6.Flavour

PROCEDURE:

Da farko za ki wanke Cucumber Apple, sai ki yanka su gaba daya sannan kiyi Blending nasu. Idan kin gama sai ki tace ki sa Milk Sugar and Flavour sannan ki juya sosai, sai ki sa Jug ki kai Fridge ya yi sanyi.

MINT LEAF JUICE

INGREDIENTS:

1.Mint leaves
2.Tamarind
3.Flavour
4.Sugar

PROCEDURE:

Da farko zaki wanke Tamarind ki dora wuta ya tafasa, sai ki wanke ganyan na’a-na’a sannan kiyi Blending nashi, sai ki dauko Tamarind idan ya tafasa sai ki tace tare da Na’a-na’an, sai kisa Sugar and Flavour sai ki juya sosai, kisa Fridge yayi sanyi.

DRINKS MANGO

INGREDIENTS:

1. Mango
2.Lemon
3.Flavour
4.Sugar

PROCEDURE:

Da farko za ki samu Mango me kyau ki wanke shi sai ki fere bayan ki yanka, zuba Blanda kiyi Blending na shi ki juye a Jug, sai ki matse Lemon ki tace tare da Mango sai kisa Sugar and Flavour, ki juya sosai da haka sai ki sa Fridge.

DRINKS PINEAPPLE

INGREDIENTS:

1.Pineapple
2.Milk water
Sugar
Flavour

PROCEDURE:

Da farko zaki fere Pineapple, ki yanka sannan kiyi blending, idan kin gama sai ki tace, ki zuba a cikin Jug naki sai kisa Milk water Sugar and Flavour, sai ki juya sosai daga nan sai ki kai Fridge yayi sanyi.

TAMAREND JUICE

INGREDIENTS:

1.Tamarind
2.Ginger
3.Kanunfari
4.Sugar

PROCEDURE,:

Da farko za ki wanke Tamarind ki sa tukunya ki daka Ginger Kanunfari, ki hada su gaba daya ki dora wuta.
Idan ya tafasa sai ki tace idan ya huce sai ki zuba Sugar ki juya daga nan sai ki sa Fridge…….

Biskit din Oreo packet daya
Madarar peak powder cokali goma
Whipping cream rabin kofi
Suga da dan ruwa

OREO MILK SHAKE

INGREDIENTS:

1.Biskit din Oreo packet
2.Peak milk powder
3.Whipping cream
4.Sugar and water

PROCEDURE:

Da farko dai zaki hade wadan nan kayan gaba daya , ki zuba kiyi blending idan kin gama sai ki sa Fridge yayi sanyi k’arara sannan ki karairaya biskit din kisa akai.

BANANA PUDDING

INGREDIENTS:

1.Banana
2.Egg
3.Lemon
4.Sugar
5.Flavour

PROCEDURE:

Da farko za ki bare bawon Banana ki tsaga tsakiyan, ki cire bakin tsakiyan, sai ki yanka ki sa a blender.
Sai ki fasa Egg ki matse ruwan lemun tsaminki, sai ki kada sosai ya kadu, sai ki zuba shi a kan Banana, ki zuba Sugar sannan kiyi Blending, idan kin karasa sai ki juye a Jug ko Cup kyau ki sa Flavor sai ki kara juya shi sosai, sai ki sa a cikin Oven ki sa wuta kadan, ya samu kamar 5Minutes sannan ki cire, Shikenan kin hada Banana pudding.

KUNUN MADARA

INGREDIENTS:

1.Couscous
2.Madarar gari
3.Coconut
4.Flour
5.Sugar
6.Ruwa

PROCEDURE:

Da farko zaki samu tukunya ki dora akan wuta ki sa ruwa ba dayawa ba sai ki zuba Sugar, idan ruwan ya yi zafi sai ki sa Couscous din, ki bashi kamar 8minutes kada ki bari ya fara fashewa. Ki samu roba ki sa Milk kina damawa da ruwan, ki sa Coconut milk and Coconut water ki juya su hade sai ki sa 2½ cup na ruwa ki sake mixing, bayan 8Minutes sai ki zuba mixture na ki a cikin tukunyar ki juya ki bari ya tashi kaman sau biyu, sai ki samu karamin roba ki sa Flour sai ruwa kadan ki dama ki tace, sai ki sa akan kunun don ya danyi kauri, bayan nan zaki sauke bayan 1mint.

Zaki iya sha da zafin sa idan kina bukatar sanyi zaki iya sakawa Fridge.

KUNUN COUS-COUS

INGREDIENTS:

1.Cous-cous
2.Sugar
3.Madara
5.Banana
6.Flavour

PROCEDURE:

Da farko zaki samu Madara gari ki kwaba ta da ruwa ta yi tsululu sai ki dora akan wuta, idan ta tafaso sai ki kawo Cous-cous kina zubawa a ciki, ki ringa juyawa domin ka da ya dunkule, idan kin zuba iya yawan da ki ke so sai ki cigaba da juyawa har zuwa 5minutes kafin nan zaki ga ya dahu yayi kauri sai ki sauke daga kan wuta kisa Sugar ki yanka Banana ki saka a ciki, sannan zaki kara Madara sai ki zuba Flavour me kamshin Vanilla ki juya ya hadu daidai……

KUNUN GYADA AND BANANA

INGREDIENTS:

1.Gyada
2.Banana
3.Gero
4.Sugar
5.Madara

PROCEDURE:

Da farko dai zaki gyara gyada ki soyata sama-sama sai ki wanke, ki samu Banana me kyau kiyi Blending sai ki dora akan wuta ki bari ta dahu har sai kin ga ta fara fitar da kumfa sai ki dauko garin nikakkiyar gyadar ki zuba 2tbspn a cikin kunun gyadar ki kawo kullun kamu na gero kamar 3spn ki damashi da ruwa ki zuba akai zaki ga ya hade jikinshi ya danyi kauri sai ki sauke idan zaki sha ki zuba Sugar and Madara……

Alhamdullah Alhamdullyah, Alhamdullahi Alah kulli halin

Leave a Comment

error: Content is protected !!