Sirrin Rike Miji

Yanda zaki gane kina da aljani da addu’o’in da ya kamata ki yi

ALJANI NE A JIKINKI LITTAFI NA DAYA ZUWA NA BIYAR

 

ALJANI NE A JIKINKI 01

Duk da dai ni ba mai bada magani bace, kada mace ko namiji su karanta rubutun nan su zo fada mun in basu magani, kawai dai zan wayar wa mutane da kai ne saboda su san suna da matsala kuma su nemi magani. In shaa Allahu wannan taqaitaccen rubutun zai kawo wasu daga cikin abubuwan da suka shafi jinnu.

Mafiya yawan mata zaka ji suna tambayoyi kala-kala iri-iri, wanda mafiya yawan matsalolin su aljanu ne amma su basu fahimci hakan ba.

MAFARKI

Aljani yakan bayyana kansa ta mafarki, wanda idan mace ba ta sani bane sai ta dauka ko wani abu ne daban. Zaka ji mace tana cewa ina yawan mafarkin kura, kare, raqumi na bi na aguje wani lokacin ma har su cije ni duka a cikin mafarki.

Ko tayi mafarkin an jefa ta cikin wani babban ruwa, ko kuma ruwan sama yayi ta dukanta, ko kuma tayi mafarkin an jefo ta daga wani wuri mai nisa, ko tayi mafarkin namiji yana zuwa mata yana kwanciya da ita ko yana son kwanciya da ita, ko tayi mafarkin mace ‘yar’uwarta tana nemanta kamar yanda namiji yake nemanta.

Ko tayi mafarkin Makabarta ko mafarkin matattu. Ko ta rinka mafarki mai masifar tsoro na wasu irin halittu da bata taba ganin irin su ba, kuma da safe ta kasa tuna mafarkin.

Ko kuma ya rinka zuwa miki a matsayin wani abu da kike mutukar tsoro a rayuwarki, sai ya zama har kina tsoron ki kwanta bacci.

Kuma abun mamaki koda kin yi addu’a sai kin yi shi. Duka wainnan kodai aljani na son shiga jikinki ko kuma already yana jikinki.

ALJANI NE A JIKINKI 02

ALAMOMIN ALJANI NA ZAHIRI

Wainnan dama wasu suna daga cikin Alamomin da Aljani zai iya nuna kansa amma sai wanda ya san su ne zai fahimtar da ke. Aljani mugu shine wanda baya bayyana kansa balle a masa magani, wanda zai fadar da ke ya tashi, ai ya nuna a masa magani kenan tun da an san da shi, mugun kuwa baya tashi sai dai ya rinka azabtar da ke ta fanni iri iri. Aljani ya kan sa mutum ya rinka jin wainnan dama wainda basu ba saboda kowa akwai irin nasa Alamomin, gasu kamar haka:

1.Yawan ciwon kai mai tsanani da jiri.

2.Ciwon Mara, baya da kuma kwankwaso.

3.Jin motsi a gabanki kamar tana, ko kiji motsi a cikinki yana zuwa bangare bangare.

4.Jin abu kamar kiyashi na bin jikinki, ko kamar tsutsa, haka nan zaki rinka jin motsi a kanki kamar wani abu na tafiya.

5.Jin wani abu mai dan nauyi ya kwanta a wani bangaren jikinki, wani lokacin ya tashi daga wannan wurin ya koma wani wurin.

6.Jin zafi ko sanyi a tafin kafarki, ko kiji wannan wurin yayi dumi kamar an sa wuta, can kuma sai ya matsa ya koma wani wurin.

7.Jin wani abu kamar yana hadiye ki.

8.Rashin son kitso ko wani abu da zai taba kanki, zubewar gashi dss.

9.Rashin barci da daddare.

10.Yawan faduwar gaba da tsorata da abu qanqani.

11.Rashin son mutane da gudun mutane, da tsoron mutane in ta shiga wurin da akwai mutane da yawa kamar kasuwa, da rashin son magana da mutane.

12.Yawan fushi da tsiya, kiji kowa ma haushi yake baki haka nan kiji kin tsani mutane.

13.Qin aure, da rashin son maza, mace taji bata son namiji yace yana sonta, ko yace zai turo gidan su, wata ma gaba daya zata ga babu mai kulata, babu mai cewa yana son ta. Ko kuma idan wani ya fito neman auren sai zancen ya lalace saurayin yace ya fasa, in shi kuma yake so sai taji ita kuma bata son shi.

14.Zaki rinka ji kamar ana miki magana, ana cewa ki aikata wani mugun abu, ko idan kina kallon wuqa sai kiji kamar ana cewa ki coka ma wane, ya zamana dai ba a rabaki da mugun tunani.

15.Yawan jin zafin jiki, kasala da kuma ciwo na rashin dalili, wato ba a rabaki da zazzabi jikinki yayi zafi, kuma ko kin sha magani baya bari.

16.Yawan son kade kade da raye raye, wato aljani zai rinka saki yin wasu abubuwan da da can ba halinki bane, lokaci daya sai aga kin canza kin tashi daga mutumiyar kirkin da aka sanki.

17.Yawan kallon madubi da yawaita kallon jikinki tsirara a madubi.

18.Son dare, ya zama kin fi son dare akan rana, haka nan da son zama a cikin duhu.

19.Jin kamar ana kiran sunanki ko firgita yayin da kike ke kadai a wuri, koma ki rinka ji kamar ana biyoki in kina tafiya, ko kamar wani abu na bin qafarki.

20.Yawaita kuka na rashin dalili ko rashin kuka, wasu sun ce yana daga cikin alamun aljani.

21.Qin karatun Qur’ani, da kasa karanta Qur’ani koma daukansa, kiji rabin kanki na miki ciwo ko wani bangare na kanki kamar zai tsage saboda tsananin ciwo, ko kuma jin bacci da kasala, kiji kamar an cire miki karfin jikinki, kuma kiyi ta hamma kina jin bacci. Ko kuma ana fara karanta Qur’ani gabanki yayi mugun fadi, kuma ki rinka ji a ranki baki so, ko kiji kamar ana tsira miki allura a kunni.

22.Jin kamar ana tsira miki allura a jikinki, duk da wasu sun ce alamun sihiri ne to amma aljani ma yana sawa kiji kina zaune an tsikara miki abu kamar allura har sai kin yi zunbur kin tashi.

23.Rashin jin dadin saduwa da tsanar miji yayin da ya nuna alamar yana son saduwa da ita, ko kuma koda yayi zata ji ita bata ji komai ba, wato dai an dauke mata sha’awa. Da kuma jin zafi yayin jima’i.

24.Aljani zai iya sanyawa mace mugun infection ta yi ta fama yaqi warkewa.

25.Jin kamar kin aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba, wato kamar kina bacci kamar kina farke.

26.Ganin inuwa kamar na wani, ko kiji an danneki baki numfashi, sai kin yi addu’a sannan a tashi kanki.

27.Yanke jiki ki fadi baki san in da kanki yake ba har aljani yayi magana, ko ki fadi ba tare da yayi magana ba, amma dai kin san baki san abun da ya faru ba.

28.Jin kamar an daura miki dutse a zuciyar ki, wato ki ji nauyi a ranki, ko kiji an matse miki numfashin ki, ko in kin kwanta ki kasa numfashi da kyau.

29.Samun ciwukan da da can baki da su, aljani yana sawa mutum ciwo a jikinsa wanda likita zai duba ya gani wata rana kuma ace ba a gani ba, sai ka ga mace tana ta yawon neman magani bata san aljani bane ke wahalar da ita.

30.Yawan waswasi musamman a ibada. Da rashin son yi ibadan na gaba daya.

31.Rikitar miki da al’ada, yanzu zaki ganki ba jini ya dauke, sai kin yi tsarki kinyi sallah sai kawai ki sake ganin jini haka zai ta miki wasa.

32.Hana haihuwa, aljani yakan hana mace haihuwa, ko kuma in ta tashi haihuwa sai an tsaya a kanta saboda zasu azabtar da ita.

33.Zama da datti da qazanta, aljani ya kan hana mutum tsafta da zama cikinsa idan yana jikinsa, musamman idan aljanin arne ne.

34.Sumbatu da firgici a cikin baccin ki, za a ga kina maganganu marasa kan gado koma kiyi ta firgita kina ajiyar zuciya kuma duk bacci kike.

35.Lalacewar jiki ko ciwo a wani sassa da aljani ke zama.

Wainnan dama wasunsu da yawa suna daga cikin alamar akwai aljani a tare dake. In kuma namiji ne shima zai iya experiencing problems dinnan ba wai dole sai mace ba. Kamar rashin son aure, rashin sha’awa gaba daya, mafarkin suna soyayya da wata mace har sun yi aure duk a mafarki, da tsanar matar sa haka nan ya ji ya tsani matar sa. Allay Ya tsare daga sharrin su.

ALJANI NE A JIKINKI 03

DAGA CIKIN ABIN DA KE SA ALJANI SHIGA JIKIN DAN ADAM

Yana da kyau mutane su kiyaye wainnan abubuwan dama wasun su, don ganin sun kubuta daga ko wane irin Aljani da shaidani. Akwai hanyoyi da yawa da aljani ya kan bi ya shiga jikin mutum kamar:

1.Yawan gafala, ya hada da qin yin addu’oi, qin tsayar da ibadodi da qin karatun qur’ani, da shagala sosai da rayuwar duniya.

2.Lokacin da mutum yake cikin tsananin fushi, aljani ya kan samu daman shiga jikin mutum a lokacin da yake tsananin fushi.

3.Zama wurin da aka tabbatar Aljanu na zama wurin, kamar wurin qazanta, wuri mai danshi, bola, maqabarta dama sauransu.

4.Idan mutum yana kallon fina-finan batsa ko hotunan batsa ko yawan tunanin da dulmaya a cikin sha’awa, kina yawan sanyawa kanki fitinar sha’awa da son saduwa.

5.Idan mutum yana da tsoro da yawan firgita ya kan ba aljani daman shiga jikinsa.

6.Zubar da ruwan zafi a Qasa, idan mutum yana haka to zai iya watsa ma aljani ya qona sa, a bari ya huce ko a sirka kafin a zubar.

7.Kwanciya ba addu’ah, ya zama mace bata damu da kwanciya da addu’a ba, shima ya kan ba aljani daman shiga jikin mutum.

8.Mace mai cire dan kwalinta, wata har bayi tana shiga ba dankwali.

9.Yawan aikata sabo, ya zama mutum baya rabuwa da munanan halaye da dabi’u, idan aljani yaga zuciyar ki babu Allah sam a cikinsa to sai yayi maki kaka gida a jikinki.

10.Yawan sauraron waqe waqe da kade-kade, ya zama kullum kunnin mutum babu karatun qur’ani sai waka da kida, yana mutuqar lalata zuciya da kashe zuciya.

11.Shiga cikin damuwa, ya zama mutum baya raba kansa da damuwa, kullum ya na cikin bacin rai da damuwa wannan ma yakan ba aljani daman shiga jikin mutum.

12.Fita cikin tsakar dare, ya zama mutum ya na fita da tsakar dare ba tare da wani dalili ba, wani a haka yakan yi gamo da aljani.

13.Amfani da layu da wasu abubuwan da boka ko malami ya baki, yana mutuqar budewa aljani kofa zuwa jikinki ko ma ‘ya’yanki. Saboda yawancin layun in kin bude sunayen aljanu ne suke hadawa su yi shirkan dashi.

14.Nuna tsiraici da shigan banza, domin yawanci zaka ji aljani ya shige ta ne saboda irin shigan da take yi da bayyana kwalliyarta.

15.Kwance kai da daddare, akwai aljanin da yace saboda tana tsifar dare ne yasa ya shige ta, kenan yana da kyau a rufe kai da daddare a daina budewa.

16.Da qoqarin addu’a koda baki da tsarki, wato kada kice don baki da tsarki zaki zauna har sai jini ya dauke kin yi tsarki. Duk safe kiyi azkar haka ma da yamma.

Sannan aljani ya kan shiga jikin mace idan an turo shi, wato in an miki sihiri kenan, wata kuma duka bashi bane jarabawa ne irin na Ubangiji, tana kiyayewa kuma sai ka ga kuma tana fama da jinnu. Muna roqon Allah ya kiyaye mu kuma ya tsare mu daga sharrin su.

ALJANI NE A JIKINKI 04

SHAWARWARI GA MASU JINNU

Duk wanda yake fuskantar matsalolin na jinnu akwai abubuwan da ya kamata ya fahimta kuma ya kiyaye.

1.Mafiya yawan mutane basa ganin tasirin magani ne saboda a zuciyar su suna kokwanto, duk kuma abin da kake kokwantonsa to abu mai wuya ne ka ga tasirin sa. Idan Annabi ya ce wannan addu’ar zata kare mutum daga dukkan wani abun cutar wa daga safe zuwa yamma, ko daga dare zuwa wayewar gari to kiyi Imani 100% cewa Allah zai baki kariya. Annabi shine mai gaskiya abin gasgatawa da ya ce Habbatus sauda tana maganin dukkan cuta ban da mutuwa to sai kiyi imani cewa idan ina amfani da ita zaki warke daga dukkan cuta. Sai ki ga cikin yardan Allah kin nemi matsalarki wata rana ki ga bashi.

2.Hakuri da gujewa gaggawa, idan an baki addu’a ko magani kada ki ďauka yanzu yanzu ko gobe ne zaki warke a’a, ki yi ta addu’a kina magani a kwana a tashi za ki nemi matsalarki ki rasa, domin Allah yana amsa addu’a mutuqar bawa bai yi gaggawa ba. Zaka ga mace tayi shekara tana abu, ta samu saukin wasu abun amma bata warke duka ba sai ta ce ita ta gaji da wahala wannan maganin baya mata komai sai ta dai na.

3.Kiyaye dukkan abin da akace ki kiyaye da aikata dukkan abun da aka ce ki aikata da kuma jajircewa, kada ki fara amfani da magani ko ki fara yin addu’a ki ji sauki bayan kwana biyu ki watsar da komai ki koma rayuwar ki ta da, idan baki wasa ba in ya tashi dawo miki sai yayi har da gayya, domin aljani in shi kadai ya shige ki in ya ji dadin wuri sai yayi ta miki gayyan wasu.

4.Kiyaye neman magani ta hanyar zuwa wurin malamin duba ko boka, hakika haramun ne wannan, kada kije wurin wani mai aiki da aljanu kice ya rabaki da naki, in bai rabaki ba ya qara miki wasu. Kuma abun da za su yi shine wai sulhu, aljani ya fadi me za’a masa sai a masa ya bar jikinki. Zai iya yi kamar ya tafi, in aure ya hanaki to zaki ga kin samu kin yi amma yana nan bai tafi ba, iyaka ya dai na azabtar dake ne saboda ki aminta da boka da kuma aikinsa, kin gane hikimar da suka yi amfani da ita? Ana nan kuma wata rana komai zai dawo sabo, sai ki sake rugawa wurin boka sai ya ce ai wannan asiri aka miki ba waccen matsalar bace, a haka zasu yi ta dulmiyar dake. Boka ba zai iya baki tsari ba Allah ne mai tsarewa, asaran kudin ki kawai kike yi kina sake jawo ma kanki masifa. Don haka shine your eyes sister.

5.Abu na gaba shine yaqi da zuciyar ki, ‘yar’uwa suna yaqin kine kema kina yaqar su da ayoyi, addu’oi da ingatattun magungunan Manzon Allah. Kada idan suna nuna basa so ki biye ki dai na, a’a kiyi yaqi, idan kin yi amfani da wannan kin sha baqar wuya gobe ma haka zaki sake yi ba fashi. A haka haka tun kina yi kina shan wuya har wata rana zaki wayi gari baki jin komai har kiyi ki gama.

6.Kokarin tsananta addu’a da roqo. Idan an miki ruqya aljani zai iya ya gama ihunsa ya jigata ya gudu, wani dan gatan ma ana kawo ki gaban mai ruqya zai fice, ayi karatun a gama duk bashi ma abin sa, bayan kun gama kuma sai ya dawo, haka nan in magani ne, zai yi nesa dake ya qi shigowa jikinki ko ya fita a jikinki in mazauni jikinki ne, saboda maganinki na azabtar da shi, to amma yana nan yana jiran ran da zaki dai na, sai ki ga komai ya dawo miki sabo, sai kuma a sake komawa wurin mai ruqya? Amma in ke ce kullum kike addu’an ki babu fashi fa bayan an cire? Har abada shi da ke, saboda ba zai taba samun daman shigowa ba don kullum cikin kariyan Allah kike. Ki zama mai ruqyan kanki.

7.Shawarar qarshe ita ce koyon adduoi, musamman na safiya da maraice, babban sakaci ne ace babu wasu addu’oi da kika iya a kanki wanda ko baki duba littafi ba zaki karanta don neman kariya ba, duk addu’ar da aka baki aka ce na kariya ne daga shaidanu haddace shi ya kamata kiyi. Duk lokacin da kika ji alamar aljani zai shigo jikinki ko kika ji wani iri fara addu’oi kada ki dai na har sai kin dai na ji. Ba wai kawai ki zauna komai sai kin duba paper ba yanda in baki tare da paper shikenan zaki zauna ba addu’a saboda baki iya ko daya ba.

Ina roqon Allah ya kare mu daga sharrin shaidanu.

ALJANI NE A JIKIN KI 05

GUDUNMUWAR DA ZAN IYA BAKU NA MAGANI DA ADDU’OI

Kamar yanda na fada a farko cewa dalilin yin taqaitaccen rubutun nan shine saboda yawan tambayoyi da muke samu akan matsalolin mata wanda aljanu ne amma sun kasa fahimtar haka. Rubutun don in kin san kina da aljani ne kije ki nemi magani amma ba wai ki nema a social media ba. Ban san komai game da bada maganin aljani ba, don wasu suna ta tambayar magani, ko likita ne baya bada magani a social media zai ce kije asibiti ne, saboda wata kila akwai abun da ido da ido ne zai fahimta, don haka a nemi magani na zahiri, ba wai ayi ta boye ciwo ana tambaya a nan ba.

Amma dai zan bada abin da na bawa mutane da dama kuma sun ga amfanin sa, shima din wani mai ruqya ne ya taba fada mun, sannan zan qara muku da addu’oi, gasu kamar haka:

1.Habbatus sauda na gari

2.Habbatus sauda oil

3.Musk ja

3.Garlic oil

4.Zaitun

Zaki mayar da garin habbatus sauda kamar komai naki, kullum ki cire kayan ki duka, sai ki samu abu babba ki lullube, sannan ki zuba garin Habbatus sauda, har sai hayakin ya kare tsaf a jikinki.

Sannan idan zaki yi wanka ki debi garin dan dai-dai shima ki zuba kiyi wanka dashi.

Idan zaki ci breakfast ki zuba kadan a tea ko kunu, haka nan a cikin kosai ko egg. Haka ma da rana, ki barbada a cikn abincin ki, haka nan ma a ruwan shan ki, ya zamana kina amfani da habbatus sauda sau hudu kenan.

A abinci, a abin sha, ruwan wanka, hayaki. Ya zamana koda baki ci a ko wane abinci ba, kada ki bari dai gari ya waye har ki yammatu baki yi amfani dashi ba, don ni wani lokacin haka nan ina ďiban garin in saka a baki na, saboda ba tsami, ba bauri, kuma ba wari, sannan ina enjoying shansa a cikin tea, kuma nakan zuba shi a cikin abin da nake yawaita ci ko sha haka, yanda mutum ba zai manta ba. Habbatus sauda magani ne ko kina da matsala ko baki dashi, wasu har a abinci suna hadashi a cikin spices.

Sannan zaki iya sawa a cikin man kitson ki, ko garin ko oil duk wanda ya samu a rinka miki kitso dashi.

Bayan nan, sai ki hada zaitun, habbatus sauda, da kuma man tafarnuwa, ki rinka shan rabin tea spoon safe da yamma, dan kadan in dai ya shiga cikin ki shikenan, shima magani ne sosai, kuma yana gyarawa mace hailarta, yana hana ciwon cikin during menstruation, yana saukarwa mace da ni’ima kuma yana kashe infection in kina dashi. Sannan idan kin gama jini kafin kiyi tsarki ki shafa shi a farin auduga wato musk kenan ki saka a gabanki.

Kuma zaki lakata habbatus sauda a hancinki kija ya shiga kanki zaki ji shi har maqoshinki, shima yana hana aljani zama jikin mutum.

Shi kuma musk din, abin da zaki yi dashi shine, zaki lakato da abun goge kunni, saboda a daskare yake, ki shafa a gaban kumban ki, wato in da kike sa reza kike yankewa a duka yatsun ashirin, kafa da hannu kenan.

Sannan ki shafa a gaban ki, da anus dinki, da cibiyar ki, da nipples dinki, da kunnuwanki, da hancin ki, da bakin ki, duka hujin jikin ki kenan 32. Wannan shi zaki yi ne kullum in zaki kwanta.

Wainnan ayoyin da surorin su kuma kullum zaki samu lokaci ne ki karanta su duka lokaci daya ban da tsallaken rana, kullum kiyi.

Suratul Buruj (Wassama’i zatul buruj) sau 3.
Suratul Yasin sau 1.
Suratul Mulk.
Ayoyi biyun karshen suratul Qalam.
Sannan sai Suratul Mu’minun aya ta 97 da 98, su kuma zaki karanta sama da sau 11.
Suratul Furqan Aya ta 23 ki karanta sau ba adadi.
Idan kin yi sati biyu ko uku kina karanta su sai ki koma karanta suratul Buruj sau uku da safe, uku da rana uku da yamma.

Sannan da qoqarin kwanciya da alwala, da kuma yin adduo’in bacci, in kika duba hisnul muslim zaki gansu. In kuma ba zaki iya ba sun miki tsaho to kada ki kwanta ba tare da kin yi wainnan ba, Falaq, Nasi, da Qulhullahu sannan da ayatul kursiyyu da mulk ki shafe jikinki dashi.

Da karanta Falaq nasi suratul Ikhlas Ayatul Kursiyyu bayan ko wani sallah.

Sannan kuma ki kula da wainnan adduo’in:

 

Auzu bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli aay-nin lammah. Safe da yamma. [Bukhari].

 

Bismil-lahil-lazee la-yadur-ru ma’aas-mihi shay-un fil-ardi wala fis-sama-i wahuwas-sameeul-aa’leem. Safe da yamma. [Tirmizi da Abu Dawud].

 

Bismillahi arqik, min kulli sha’yin u’zik, min sharri kulli nafsin au anin hasd Allahu yashfik. [Muslim]

Da wannan ma roqon Allah samun sauki daga ciwon.

 

Azhibil-ba’-sa rabban-naasi washfi aan-tash-shafee la shifa-aah illah shifa-uoka shifa-uon laa yu-gaa dee-ru sa-qaa-maa. [Bukhari da Muslim]

Idan kuma kika ji wani wuri yana miki ciwo sai ki yi bismillah sau 3 sannan ki karanta wannan:

 

Auzubillahi wa qudratihi min sharri maa ajidu wa uhazir.(Sau bakwai). [Muslim].

Sannan in kin ji suna miki motsi a gabanki ko a jikinki kamar tsutsa ko kiyashi kiyi ta karanta wainnan Nur aya ta 45 da kuma mulk aya ta 22:

´Ù’ﺘَﻘِﻴﻢ)). [الملك ٢٢].

DA YIN WANNAN KODA SAU ‘DAYA NE A WATA

Zai kare mutum daga sharrin Aljani kuma in akwai sihiri a jikin mutum ma zai iya karyewa.

Ki samu ganyen magarya guda 7, ki dan jajjaga shi yanda zai farfashe sai ki saka a kwano ko gora, sai ki karanta wainnan.

Cikin Suratul A’araf aya ta 117 zuwa 121.

Sannan sai kuma Suratul Yunus aya ta 81 da 82:

 

Idan kin karanta sai ki yi wanka dashi duka jikinki, amma wurin yin wankan ya zama kin sa towel ko zani a qasa yanda ruwan ba zai rinqa sauka a qasa ba saboda karatun da ke cikinsa. In kin gama sai ki shanya ya bushe, ba wai cika ruwa zaki yi ba ďan dai-dai zaki sa wanda zai isheki.

Sannan kowa akwai irin nasa wasu ma suna karanta baqara a ciki, da wasu ayoyi wainda suka fi wainnan yawa, sannan akwai wani mai ruqyan da yace za’a iya karanta baqara ko ki sa a karanta miki a ruwa ki rinka sha, ya zama ruwan shanki, in ya kusa qarewa ki sake cika goran ba wai sai an ta sake maimaitawa karatun ba.

Sannan da sauraron baqara da Al-Imran, Mulk, Buruj da yasin dama Qur’ani gaba daya, ko kisa a kunni ko kisa a gida gaba daya, yana koron Aljanu da shaidanu.

Zaki ce abun sun yi yawa ko? Ba su yi yawa ba muddin ciwon kike yi, babu abin da ya kai lafiya dadi, sai kina da lafiya zaki yi komai. ‘Yar’ uwa ki gujewa duk wani kade kade da raye raye, ya zama Qurani kullum kike ji, da yawan ambaton Allah.

Wannan shine rubutu na qarshe a wannan rubutun ALJANI NE A JIKINKI In da nayi kuskure ina roqon Allah ya gafarta mun, in da nayi dai-dai kuma in roqonsa ya bani lada.

Duk wacce take fama da matsalar nan Allah ka yaye mata, Allah kasa ta rabu dasu, Allah kasa ta koma kamar yanda take da.

Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar.

WANE MUTUM BARE ALJAN!

Haqiqa duk wanda ya kasance yana wayen gari har ya yammatu, babu wata addu’a na kariya daga sharrin mutum da Aljan.To lallai yana cikin hatsari mai girma. Domin duniya yanzu ya zama abun da ya zama. Kuma addu’a makamin mumini ce. In har ana yi ba a san adadin abun da Allah ke kare mutum daga shi ba.

‘Daya daga cikin manyan malamai Shaikh Waleed Basyouni sun dauki lokaci suna yiwa wani dan’uwa da aljani ya shige shi Ruqya. Cikin ikon Allah Aljanin ya fita jikinsa. Sai sheikh din da shi da wanda jinnun ya kama da wani, suna tafiya. Kawai sai Sheikh Waleed ya ji wani irin qara, kamar an zabga ma wani bulala da qarfin gaske. Sai wanda Aljanin ya buge yayi tsalle kamar an tunkuďa shi gaba, saboda qarfin wannan dukan. Sai Sheikh din ya je wurin sa da sauri ya bude bayansa. Kawai sai ga shaidan bulala radau a bayansa sanadiyyar wannan qara. Wanda sai da sheikh din yayi hour ashirin da hudu da mutumin ya tabbatar lallai duka ne. Sai malamin ya fahimci cewa lallai wannan Aljanin yayi mutuqar hasala saboda an fitar da shi. Sai malamin ya cigaba da masa Ruqya, sai ya tambaye su in sune suka masa wannan dukan. Sai yace eh shi ne, ya ce me yasa? Sai jinnun ya fadi cikin fushi da qara, cewa ya tsani mutumin kuma ransa ya ‘baci. Sai ya ce to me yasa ni da abokina da muke tare baka buge mu ba? Sai ya ce yayi burin, kuma ya so yin hakan, amma sun karanta wata addu’a yasa ya kasa. Wanda wannan addu’ar ita ce:

 

 

Bismillaahil-lazi laa yadhurru ma’as-mihi shay’un fil-‘ardi wa laa fis-samaa’i wa Huwas-Samee ‘ul- ‘Aleem. [Abu Dawud 4/323, At-Tirmidhi 5/465, Ibn Majah 2/332].

Safe da yamma ake karanta ta kullum sau uku. Musamman maza masu fita kullum, baku san da wa kuke hada-hada ba. Sannan ko sabon gida mutum yayi, ya je tsakiyar gidan ya karanta wannan addu’ar sau 7 da qarfi. To ko da akwai jinnu zasu tattare yanasu-yanasu su fita. In basu tafi ba kuma, to ba zasu taba cutar da wani ba da yardan Allah. Sannan a koya ma yara har su iya kullum kafin su tafi makaranta su yi. Haka in yamma ta yi. Sannan kun san akwai kambun baka, da evil eye, mayu, yan secret cult dss. Don haka ga azkar mai sauki yan’uwa, in ma za ayi printing ne a yi, ko a rubuta kullum a karanta:

 

1.“Au’zubillahis Salimi’ul-Aleem, minash shaydanir rajim, min hamzihi wa nafkhihi wa nafthih”. X1

2.Fatiha x1

 

3.Ayatul Kursiyyu x1

 

4.Amanar-Rasulu x1

 

7.Suratul Nas 3x

بِسۡمِ ٱللهِ ٱلرَّحۡمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ۝ قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ۝ مَلِكِ النَّاسِ ۝ إِلَـٰهِ النَّاسِ ۝ مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ ۝ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ ۝ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ.

بِسْمِ اللهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ.

8.Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma’as-mihi shay’un fil-‘ardhi wa laa fis-samaa’i wa Huwas-Samee ‘ul- ‘Aleem. X3

حَسْبِيَ اللَّهُ لَآ إِلَهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ.

9.Hasbiyallaahu laa ‘ilaaha ‘illaa huwa ‘alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Adheem. X7

أعوذ بكلمات الله التآمّة، من كل شيطان و هاَمّة، و من كل عين لاَمّة.

10.“A’ozu bikalimatillahi taam’mah, min kulli shaytani wa haa’mah, wa min kulli aynin laa’mah”.X1

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ.

11.Aa’uzu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaqa. X3.

لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.

12.Laa ‘ilaaha ‘illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa Huwa ‘alaa kulli shay’in Qadeer. X10.

 

13.La’ilaha illah anta subhaka innee kuntu minaz zalimen. X7

 

14.Bismillahi sau uku, Auzu bi’izzatillahi wa qudratihi min sharri maa ajidu wa uhaziru 7x. Wannan Addu’ar yawanci sai in mutum bashi da lafiya ne yake karantawa, amma believe me tana rugurguza jinnu. In fact addu’a ce mai mutuqar qarfi.

Wadannan sune addu’a na tsari, marasa tsayi ga qarfin gaske. Cikin qanqanin lokaci mutum zai haddace in yana yi kullum. Kuma nan da nan ka karanta ka tafi in da zaka. Haka nan ka yi printing ka bawa iyali ta yi ta koyawa yara har su haddace. Kuskure ne zama babu addu’oin tsari. Kuma a yi downloading Muslim Pro App domin komai akwai addu’arsa. Allah Ya kare mu da kariyar Sa.

Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar.

MATA SAI FA MUN GYARA!

Wasu daga cikin dalilan da ke sanya jinnu shiga jikin mu fiye da maza. Duk wanda ya san matarsa ko ‘yarsa na yi ku gyara musu:

1.Zama a bakin qofa, ko bakin windo da sauran hanyoyin wucewa.

2.Fesa turare mai qarfi yayin fita, ko kuma fesa turare lokacin kwanciya bacci mai qarfi kuma ba addu’a.

3.Yawan yin zanen lalle mai fulawa a madadin asalin na gargajiya. Wanda aljani da kanshi ya fad’i cewa kwalliyar su ne a jikin wata.

4.Zama babu ďankwali a cikin gida, da kwanciya babu shi. Ko bayyana gashin a fita waje.

5.Yawan zama ba tsarki, kamar in an yi an gama da dare kawai ta kwanta babu tsarki cikin qazanta. Kuma babu ko alwala har gari ya waye tangararan.

6.Rashin yin alwala a lokacin jinin al’ada da barin yin dukkan addu’o’i. Mafiya yawa in tana jini sai ta yanke dukka komai har sai ta yi tsarki. Wanda hatsari ne sosai.

7.Yawaita fushi da sanya damuwa a rai koda yaushe. Domin wata da aljanar ta shige ta cewa ta yi kullum in ta zo wuce wa zata ga tana bakin ciki da damuwa. To wai ita ma aljanar irin halin da take ciki kenan sai ta shigeta. Idan ta na magana ita kaďai na baqin ciki sai aljanar ta rinqa amsa mata tana rarrashinta. Daga karshe dai ta shigeta, in aljanar na baqin ciki sai ta rinqa yanka jikinta da wuka. Wanda matar ma haka ta koma yi.

8.Caba ado na gani na fada a fita musamman ga wacce bata yin azkar. Da gyara adon in an samu wuri a waje ko a cikin mota. Domin ita ma wata a nan jinnun ya shige ta. Yace ta tsaya a titi ta fito da powder ta qara shafawa ta gyaggyara. Shi ya zo wucewa sai ya ga gaskiya yana sonta.

9.Zama a wuraren da aka san suna zama. Kamar wuri da koda yaushe ke da danshi, zama tsakanin inuwa da rana (rabinki a rana rabi a inuwa). Qin shiga bandaki da addu’a ko dankwali. Ko yin waqe waqe a banďaki.

10.Shagala da duniya da yawa. Bana manta wani Ruqya da na kalla na wani bature ďan America. Aljanu ne a jikinsa sun kai 10 wanda a dalilin badala ya samo su. Sai suka sa ya zama mutumin banza sosai. Wani daga cikin aljanin da ya shigo jikinsa aka ce shi kuma me yake sanya shi? Ya ce party 😂. Duk in da aka ce za a yi party to aljanin zai takura sa har sai ya je wurin sun gwangwaje. To kana iya gamuwa da jinnu mai irin zunubinka ko dabi’unka na sa’bo sai ya shiga, ya sanya ka yin fiye da abun da ya same ka a kai.

11.Shiga kasuwa babu addu’a. Ko shiga daji ko wani wuri da babu mutane sosai ba tare da addu’a ba. Akwai wani jinnun da ake magana da shi a jikin wata yarinya akan irin halittun da yake zama. Sai yace har da kare, kadangare, maciji, da jemage. Ya ce ya taba zama kare ne ya ci ji wani mutumi bayan ya shiga daji ya taka shi. Shi kuma in an ta’ba shi baya yafiya. Aka ce ina mutumin yanzu, ya ce yana can yana wahala da ciwonsa na sa masa ciwo. Kenan in zaki shiga irin wadannan wurin sai a yi addu’a a nemi tsari daga su.

12.Yawon dare, fitan magriba, sharan magriba, wankan magrib. Dauko ayyuka a magriba. Domin Annabi (SAW) ya fada mana a lokacin suke barbazuwa. To in so samu ne a dan bari magriban ya gitta sai a yi. Kuma ki rinqa qoqarin kammala ayyukan ki kafin nan. Da nutsa yara.

13.Zubar da ruwa mai zafin gaske. In kin wanke shinkafa ko kin yi per boiling ki yi banza da shi har ya huce sai ki nemi tsari (Auzu billaahi minash shaydanir rajim) ki zubar. Saboda wurin kwata da wanke-wanke suna da danshi da qazanta. Haka nan da zubar da bola da tsakar rana musamman in akwai wani abu na glass da ya fashe a ciki. Wanda in kin watsa in akwai wani abu zai iya jin masu ciwo. Haka nan zubarwa da Magriba.

14.Kashe wasu halittu a gida ba tare da kin nemi tsarin Allah ba. Babu abun da basa zama duk abun da kika gani ko zaki kashe ki nemi tsarin Allah. Bana manta ina sakandiri na kwana, wata yarinya ta kashe tsaka. Wacce ta kashe tsakan hannunta ya rike, washe gari ya kumbura. Itama wacce ta share ta hannunta ya rike sai da aka mayar da su gida.

15.Yin wulakanci ga mutumin da baki sani ba a hanya. Domin wannan halin mata ne. Gashi kin fita babu azkar, ga shi kin caba ado, an tare ki kuma kin yi wulakanci. Kin ga sai ya shiga jikinki da hujjah.

16.Barin qashin kaza ko na wani dabba yana kwana miki a daki ba tare da kin fitar ba.

17.Shiga turken awaki da magriba ko yawan shiga babu azkar. Domin wurin akwai qazanta suna iya zama a wurin.

18.Rashin yi wa ‘ya’yan mu tofi idan sun fadi musamman da Magriba. Kada ki yarda ya fadi baki karanta falaqi, Nas, Ikhlas ba ki tofa a hannun ki. Ki shafe fuskansa sannan dukkan jikinsa. Zaki iya hadawa da sauran addu’oi ma. Wata sun shigeta ne sanadiyyar fadi da tayi a bakin qofa da ‘yarta sai kuma bata yi addu’a ba. Ashe aljani ta fada ma wa a bayansa, sai ya kama yar. Ta yi shekaru yana azabtar da mutanen gidan dukkan su, bama wai ita kadai ba.

19.Barin ‘ya’yan mu su kadai suna jarirai. Kuma ba tare da mun yi musu tofi ba. Wanda yara da yawa sun girma da jinnu ne a jikinsu. Su yi ta azabtar da iyayen basu sani ba.

20.Zuwa diban ruwa da Magriba, musamman ga masu tsohon ciki. Ko wucewa ta qarqashin bishiyoyin da aka san aljanu na zama. Da mace mai sana’ar aiken yara da Magriba.

21.Shirka da yawon gidan malamai, wanda mafiya yawan mata a nan suke debo wa. Haka nan amfani da layu, ko wasu abubuwan da aljanu suke so. Aiki da turarukan da ake kiran iska da su ko iska ke so. Kamar misalin binta Sudan. To kuwa shaidanu zasu dabaibaye miki gida da ‘ya’ya. Ga bala’in shirka, ga bala’in jinnu, ga bala’in rashin samun biyan bukata.

22.Canza launin fatarki, qara gashi da ko wane irin abu ne, ko ruwa na shiga ko baya shiga. Shafa kwatas a qumbarki, canza kalolin gashi gasu nan dai abubuwan canza halittar Allah. Suma tabbas jinnu na shiga jikin mace ta dalilin su.

23.Nisantan Allah. Yin mugunta, da zama mai baqar zuciya. Yawan jin tsoro da yawn rudewa. Yawo na rashin dalili kullum kina tafe a hanya yana sanyawa a yi gamo. Bayyana tsiraicinki a social media da zahiri. Domin ana gamo da aljani ta chatting. Yawan hira da mu’amala da maza shima zaki iya gamuwa da jinnu.

Yan’uwana aljani gaskiya ne na san kun san da haka, kuma suna shiga jikin mutum su zauna har su haifar masa da wasu dabi’u, ciwo dss. In mutum ya qaryata toh wata kila bai faru da na kusa da shi bane ya ga zahiri. Jinnu sun yi mutukar shigowa cikin mutane yanzu. Don haka kuskure ne cewa jinnu baya shiga jikin dan adam. Domin zai sanya mutane sake da addu’a da jin cewa komai lafiya.

Mu rike addu’oin safiya da maraice gasu nan a Hisnul Muslim. Domin in sun kama mutum da kansa zai kore su da addu’oi. Domin in magani ne in ya qare zasu dawo. Addu’a kuma dai baya qarewa. Mu yawaita karanta qur’ani da neman tsari da su. Ya Allah Ka bamu kariya

Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar.

GA MAI FAMA DA JINNU

Ki samu lalle gwangwani uku, gishiri gwangwani ďaya ki haďa ki juya, duk in zaki yi wanka ki debi cokali daya babba ki zuba a ruwan ki yi wanka da shi.

Ki samu lalle wanda zai isa ki yi lalle hannu da qafa, ki samu garin Habbatus-Sauda cokali biyu babba, da ďanyen tafarnuwa kamar kwaya biyar, da lemun tsami guda daya. Ki juye lallen ki zuba Habbatus-Sauda, ki daddaka tafarnuwa ko a niqa ki tace ruwan ki kwaba da shi, sai ki zuba ruwan lemun tsami guda ďaya. In kin kwaba ya kwabu sai ki samu leda ki rufe roban kwabin, ki bashi kamar awa 6 zuwa 5 kafin ki sa. In kin dauko ki jujjuya ya juyu sai ki saka duka qafa biyu da hannu ki kwana da shi.

Da ya fara goge wa ki sake yin sabo ki saka. Sannan a guji sanya cello tape mai zane plz. In baki wasa ba kina dauko wa zaki ji ranki ya fara baci, kuma zaki iya kwana kamar ana tafasa ki, amma jinnun zai ji ajikinsa da izinin Allah.

A rinqa addu’ar safiya da maraice kullum, yawaita zama da alwala, rage ayyukan sabo, yawaita ambaton Allah da istigfari, yaqar shaidanin da qarfin zuciya, kada ya rinqa sanya miki mugayen tunani kina kuma aikatawa. A rinqa yawaita sauraron Baqara, da sauran Qur’ani, a rage jin kade kade ko yin abubuwan da basu da amfani. In kina neman waraka toh yi maza ki tare a fadar Allah my sister..

Yaa Allah Ka warkar da masu wannan cuta, Ka ba su ikon cin galaba a kan ko wane irin kangararren shaidani.

4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!