YANDA ZAKI GYARA NONON KI A SATI DAYA
Ingantaccciyar hanyar da zakibi wurin gyaran nononki.Wannan hadin yana karawa mace girman nono kuma sam ba ya faduwa.
Ko da a ce tana shayarwa ne idan har tana amfani da wannan hadin sai dai mu ce Allah san barka.
ABUBUWAN DA ZAA NEMA
1). Farar shinkafa
2). Garin Alkama
3). Garin habbatus sauda
4). Garin Ayaba (Plantain).
5). Gyada mai malfa (mai zabo)
6). Aya
7). Madarar gari.
8). Zuma
YADDA ZA’A HADA
Za ku bare bayan plantain sai a yanka shi, a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai a hada aya da gyadar a markada a tace ruwan.
Bayan nan, sai a dora kan wuta a zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hade a guri daya, sai kuma ku zuba garin madara da zuma, ku dama ya yi kauri sai a rika sha safe da yamma.
Hadin Kaddara Hausa Novel Complete
Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa. Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar Allah za ki samu biyan bukata. Allah ya tamake mu.
Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin da na ambata to kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan.
Ko kuma ki sami garin hulba, ki tafasa ki rika gasa nonon da shi, sai kuma a shafa man hulban a kan nonon a ga abin mamaki sannan kuma a fasa kwan salwa a shafawa nonon, kuma a fasa guda uku a sha su danye.
Insha Allahu za a dace.
[…] Karanta Yadda Zaki Gyara Nonon Ki A Sati Daya […]
[…] Gyaran Nono a Sati Daya […]
[…] Gyaran Nono a Sati Daya […]