Abubuwan hadawa:
-Shinkafa.
-Zogale.
-Nama.
-Albasa mai ganye.
-Mangyada.
–Kayan miya.
-Maggi.
-Kori (Curry).
-Gishiri.
-Cittah da tafarnuwa.
Yanda ake hadawa:
Ki gyara shinkafarki ki wanketa ki tsane
A barzo miki shi a inji sai ki ajiye a gefe
Sai ki wanke namanki kidora awuta. Ki sa maggi, da gishiri, da tafarnuwa, da citta, da albasa
A gefe guda kuma ki tankade barzazzen shinkafarki, domin da tsakin za ki yi amfani
Sai ki sa ruwa ki wanke tsakin ki tsane shi, sai ki zuba shi a madambaci ki dora a wuta.
Sai kuma ki gyara zogalenki, ki wanke, ki hada da tsakin sai ki rufe.
Ki tsame namanki, sai ki yanka kayan miyanki ki ajiye a gefe.
Uwargida sai ki duba tsakinki idan yayi za ki ji yana kamshi kuma tsakin ya dahu
Sai ki sauke ki zuba a roba mai fadi, sai ki zuba soyayyen manki, da albasa, da sauran kayan miya: maggi, da gishiri, da kori, da tafarnuwa, kuma ki juya ki daddanna sosai sai kin fahimci komai ya yi dai-dai
Sai ki zuba dan ruwan tafasashen naman ki juye atukunya ki maida shi wuta ki bashi kamar minti sha biyar, za ki ji gida yadau kamshin girkinki.
Leave a Comment