Hausa Novels

Yankan Baya Hausa Novels Complete

Yankan Baya Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Yankan baya

GARGAƊI

Ban yadda wani ko wata su juyamin labari ba, kuma ban yadda ayi min editing ba ko a karamin wani abu ba sannan ban yarda a doramin shi a YouTube ba sai da izinina, dan Allah a kiyaye

 

Page 1&2

 

Zaune nake hannuna riƙe da littafin addu’o’i na Hisnul Muslim ina azkar ɗin maraice, Yaron maƙotan mu Amir ne yayi sallama, cikin sakin fuska na amsa masa, shigowa yayi muka gaisa sannan ya ce Aunty Nana wai kizo inji wani a waje! Tuni fara’ar kan fuskata ta gushe na ce kace bananan dan Allah, sai da ya ɗanyi jim kafin ya juya ya fice, hararar hanyar wajen nayi tare da sakin tsaki…

Umma ce ta fito daga kitchen, ƙarasowa tayi ta zauna a kusa dani, dafa kafaɗata tayi ta na faɗin anya rayuwa zata tafi a haka kuwa Mamana? Ya kamata ki dinga saurarar manemanki har Allah ya haɗaki da nagari kiyi aure amma zaman haka ai bashi da fa’ida!

Tuni hawaye suka wanke fuskata cikin kuka nake faɗin Umma da bakinki kike faɗin na kara bawa wani damar shiga rayuwata, har kin manta *YANKAN BAYAN* da ɗa namiji ya min kin manta tashin hankalin da namiji ya jefani ni da ku wanda ta sanadiyar hakan kika kamu da hawan jini! Kuma ta dalilin hakan na rasa mahaifina!! Kuka ne yaci ƙarfina dole nai shiru, Murmishi mai ciwo Umma ta yi tana faɗin ina zan manta Mamana, ai ya barmana abun da har abada zai dunga tuna mana da shi a rayuwa, amma hakan ba yana nufin za ki hakura da komai ba ne ya kamata zuwa yanzu ki nutsu ki samu abokin rayuwa kina da kuruciyarki, kar abun daya faru a baya yazama sanadiyar rugujewar farin cikin ki, hakan zai zama tamkar ƙin amsar ƙaddara ne, kuma duk wani mumini na ƙwarai ansan shi da yadda da ƙaddara mai kyau da akasin haka, kuma yin hakan imani ne, dan haka ina so ki zama ɗaya daga cikin masu ɗaukar ƙaddarar data afka musu.

 

“Insha Allah Umma”, haka kawai na iya faɗa mata na tashi na shige ɗakinmu, ina shiga na kife akan gado ina sakin kuka mai ta6a zuciyar mai sauraro, na kai kusan 30 minutes ina kuka, ni kaɗai nasan ƙuncin da zuciyata ta ke shiga duk lokacin da aka ambata min kalmar SOYAYYA ko AURE, a da bani da abu mafi soyuwa a raina kamar kalmar SO tana sa ni nishaɗi, lokaci na musamman na ware don hidima a gareta amma a yanzu nafi tsanarta fiye da mutuwata. A hankali na fara sassauta kukan jin kaina yana sara min, tashi nayi na ɗauro alola jin ana ta kiran sallah wasu masallatan ma har sun shiga, na daɗe zaune ina addu’o’i har aka kira sallar isha’i kafin na tashi na ba da farali.

 

 

NASARAWA GRA

Tafiya ya ke a slow cikin rashin kuzari, a hankali ya kai hannunsa ya kunna karatun al’ƙur’ani cikin ƙira’ar *Sheik Abdullahi Abba Zaria* a hankali ya fara bin karatun yana tuƙin cikin nutsuwa da sanin ƙa’idar tuƙi, dai-dai wani madai-daicin get ya yi parking, kashe motar ya yi ya ɗauki wayarsa da key ɗin motar ya fito, kira ya danna minti kaɗan aka ɗauka, yana amsa sallamar bai bari sun gaisa ba ya ce “kana gida ne?” OK kawai haka ya ce ya sauƙe wayar yana ƙarasawa gaban get ɗin, ƙwanƙwasawa yayi, wani ɗan dattijo ne ya leƙo yana ganinsa ya washe baki alamar cewar yasan shi sosai, gaisawa sukai cikin girmama juna, sannan ya ciro kuɗi ya bashi, godiya yai ta zuba masa tare dasa masa albarka, shikam tuni yayi gaba ya shige cikin gidan, yana zuwa ya ƙwanƙwasa ƙofar baifi two mint ba aka zo aka buɗe masa.

 

Murmishi ya sakar masa yana faɗin ka ce dama kana kusa, hannunsa ya kama suka ƙarasa cikin falon, har suka zauna hannunsu yana cikin na juna gaisawa sukai cikin barkwanci, tambayarsa yayi ina madam, kallon corridor yayi ya ce yanzu zaka ganta ta fito ai na sanar da ita zuwan ka, bai ƙara magana ba, nan dai suka fara firar duniya.

 

Da fara’a ɗauke a fuskarta tayi musu sallama, zuwa tayi ta ajiye tiran dake hannunta sannan taje ta zauna a kujera tana faɗin Yayah ahmad barka da yamma, murmushi yayi ya ce yauwa hasanarmu ya gida, naga da alama abokina yana samun kulawa ta musamman dan naga har wani fresh yayi, bata iya bashi amsa ba sai tambayarsa da tayi “Yayah Ahmad ina twin ɗita, wallahi na zata tare kuka zo!”

Cup ɗin hannunsa ya ajiye yana faɗin! Matsalar ta ce ma ta kawoni wajenki wallahi duk hanyar da nasan zanbi dan na samu kusanci da ita nabi amma babu wani cigaba sai ma ganin da nake kamar a yanzu gani ta ke bata da maƙiyi kamar ni, na samu ƙanin mahaifinta ya bani izinin naje mu dai-daita kanmu, amma a kullum na nemi hanyar kusanta kaina gareta ita kuma zata ƙara nisanta kanta da ni, zuwa yanzu ba wanda bai aminta da ni ba a familynta sai ita kadai tsawon wata shida(six months) ina jelen zuwa wajenta amma bata ta6a yadda mu haɗu, duk ranar da naci sa a ta fito to babu kalma mai daɗi tsakaninmu sai na maimaicin irin tsanar da tamin da kuma roƙon na rabu da rayuwarta, tabbas Maryam da zan iya da tuni na daɗe da rabuwa da Khadija ko dan yadda nake ganin zallar tsanata a cikin ƙwayar idonta amma bazan iya ba! Ba zan iya ba Maryam!! *I’m in love for her too much* wallahi, ki bani shawara Maryam me ya kamata nayi! Shin wai wacce irin cin amana namiji yayiwa Khadija da har ta kasa mancewa.?

 

 

Ɗagowa yayi yana kallon Maryam cikin tashin hankali ya ce “Maryam kuka! Na faɗi wata magana ne da ta 6ata miki rai? Duk ya ruɗe yana jero mata tambayoyi, juyawa yayi yana kallon mijin Maryam ɗin, haɗa hannayensa yayi alamar roƙo ya ce dan Allah aboki ka rarrasheta wallahi bansan me na faɗa ba da har ya 6ata mata rai ba.

Sai a lokacin Aliyu ya tashi ya koma hannu kujerar da Maryam ɗin ta ke, rarrashinta ya ke yana faɗin haba Maryam bai kamata mutum yana cikin damuwa yazo ya sanar da ke dan ki bashi shawara kuma ki kara masa damuwa ba. A hankali ta fara rage kukan nata tare da goge fuskarta, magana ta fara cikin rawar murya ta ce “dan Allah Yayah Ahmad kayi haƙuri wallahi tausayinka ne yasani kuka domin kuwa na tabbata kai alkhairi ne ga Bestie ina roƙon Allah da ya nunamin ranar aurenku, sannan dan Allah kaci gaba da haƙuri a kan wanda kake yi insha Allah da sannu komai zai zama labari”

 

Gyara zamansa yayi ya ce insha Allah ina fatan hakan, baya ga soyayyar Khadija da ƙaunarta har da tarin tausayinta ma a raina, ina fatan Allah yasa na zama sanadiyar walwala da farin cikin ta,

Maryam ta ce amin Yayah Ahmad, a kullum burina kenan ƴar uwata kuma aminiyata ta koma rayuwarta kamar ta baya.

Insha Allah zan cika miki burin ki amma sai da taimakonki komai zai tafi, yanzu dai ki sanar dani *WACCE IRIN CIN AMANA NAMIJI YA YIWA ƘAWARKI!?* sannan a yanzu me zan mata ta saurareni?.

 

Tashi Maryam tayi saboda taji kiran sallah ta ce nasan ƙawata sosai nasan abun da ta ke so da wanda bata so a da, amma gaskiya yanzu ta chanza amma ka bani kwana biyu zan binciko maka, sannan maganar cin amana yafi dacewa kaji a bakinta, amma tabbas anci amanarta sai da ta gama yadda da shi da dukkan zuciyarta, ta jingina dukkan wani farin cikinta a gare shi, ranar ɗaurin aure yazo mana da maganar da ta *gigita tunanin mu…*

 

Tana gama faɗin haka ta nufi hanyar corridor, ɗakinta ta shige dan yin alola.

Su ma tashi sukai suka nufi masallaci…

 

 

Bayan sun fito daga masallaci Ahmad ya dubi Aliyu ya ce.

 

Aboki nifa gida zan wuce, kallonsa Aliyu yayi ya ce “ba zaka tsaya muyi dinner ba”? A’a kawai ka cewa Maryam na wuce sai weekend zan shigo.

Ba dan Aliyu ya so ba ya rakashi har wajen motar sukai sallama.

Sai da yabar layin sannan ya wuce gida cike da tausayin abokin nasa.

 

********

 

Ahmad yana zuwa gida yai parking ya fito gaisawa sukai da masu gadinsu sannan ya nufi part ɗin su, yana shiga ɗakinsa ya ajiye wayarsa da mukullin motar a durowar, toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fito a gurguje ya goge jikinsa jallabiya ya ɗauko fara ya saka tare da fesa turare me daɗin ƙamshi sannan ya rufe ɗakin ya nufi massalacin gidan.

 

Sai wajen 8:30pm ya fito a masallacin hanyar 6angaren iyayensu ya nufa, da sallama ya shiga parlour ba kowa sai TV da ta ke ta aiki ita kaɗai, dining ya nufa ya zauna, yana zama sai ga Shareefa tana saukowa, wajensa ta nufa tana faɗin lah Yayah yaushe ka dawo, ɗazu na leƙa ɗakinka baka nan, kallonta yayi ya ce ban jima da shigowa ba naje masallaci.

Gai dashi tayi sannan ta zuba masa abincin, yana kallonta har ta gama ta tura masa gabanshi, murmishi yayi ya ce “nagode little, Allah ya baki miji nagari”.

 

“Amin” Yayah, kaima Allah ya baka mata ta gari, kafin ya amsata sai ga iyayensu sun sauko, risinawa Ahmad ya yi ya gai da iyayen nasa cikin girmamawa.

Duk Shareefah ce ta zuba musu abincin sannan ta zuba nata, sai ga Shareef ya shigo, gai da iyayen nasu yayi sannan ya juya ya gai da Yayah Ahmad.

duk dare haka suke haɗuwa suyi dinner tare.

 

Zama Shareef yayi yana kallon Shareefah, ɗauke kanta tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da cin abincinta, wai me yasa kika rainani ne yarinyar nan? Murmishi ta yi bata tanka shi ba, tunda yaga bata kulashi ba yasan yau an tsokanar tata ba sa kusa abincin ya zuba ya fara ci.

 

Duk Shareefah ta rigasu gamawa tashi tayi tai musu sai da safe ta nufi ɗakin ta saboda tana da exam gobe.

Daddy ne ya miƙe ya kalli Ahmad ya ce “idan ka gama ka sa meni a parlour”.

Parlourn sa ya nufa wanda ya ƙawatu da wasu royal chairs haɗaɗɗu masu kyau da tsari sai wani tamkamemen plasma,daya kusa cinye rabin bangon parlourn, zama yayi ya kunna labarai.

 

 

Bayan kamar minti goma Ahmad ya tura ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama sai da ya mishi izini sannan ya ƙarasa ya zauna a ƙasa, duk mai da hankalinsu sukai ga TV suna kallo.

Sai da aka gama labarai sannan Daddy ya jiyo ya ce “ina maganarmu ta kwana? Ka sa magana Ahmad yayi, tashi tsaye Daddy ya yi ya ce Ahmad! Ahmad!! Ahmad!!! Sau nawa na kira ka?

Kansa yana ƙasa ya ce “sau uku Daddy”

 

 

Toh na baka sati biyu ka fito da matar da zaka aura ko kuma na aura maka *Aziza!!.*

Yana gama faɗin haka ya fi ce ya barshi a durƙushe…

 

 

*******

Ina idar da sallar isha’i nayi shafa’i ta wutiri a daddafe saboda zazza6in da yake neman sauko min, ko takan abinci ban bi ba na kwanta tare da addu’a, amma me! Gaba ɗaya baccin yaƙi zuwa da na rufe ido sai hoton fuskarsa na ke gani, tunani ta farayi yau tsawon watanmu shida da kwanaki ni da Ahmad duk wani nau’in rashin kunya da baƙar magana na faɗa masa dan ya rabu dani amma duk da haka yana haƙuri dani, shin ko dai zan bashi dama ne!? Da sauri na miƙe tsaye ina faɗin inaa!! Bazan ta6a son ka ba Ahmad duk halinku ɗaya ne.

ɗakin na shiga zagayewa ina tuna abubuwan da suka faru shekaru uku baya…tsawon wannan Shekarun dai-dai da rana ɗaya ban ta6a barin Abun yafita a raina ba, barci nake, cin abinci,wanka, idan tafiya na ke, komai idan ina yi sai abun ya faɗo min, zuciyata taƙi barina nayi sukuni.

Numfashina naji yana barazanar ɗaukewa, jan ƙafata nayi na ƙarasa bakin gado na zauna ina fisgo numfashina da ƙar, har na samu ya dai-daita, ina zaune Umma ta turo ƙofar ta shigo, zama tayi tana faɗin “har yanzu kukan ki ke yi ko”? Kai kawai na girgiza mata. Ta ce

 

“To tashi muje ki ci abinci” kallon ta nayi na ce “wallahi Umma bazan iya cin komai ba yanzu” kai ta kaɗa sannan ta juya ta fi ce.

 

Haka na kwanta ina ta juyi har zuwa lokacin da bacci marar daɗi ya dauke ni.

 

 

*Ya ku ka ji salon my fans???*

*Comments ɗin ku shine kaɗai zai tabbatar min da kun amshi book ɗin*

 

 

 

 

Leave a Comment