Yar Aikin Hotel Hausa Novel Part 1
YAR AIKI.
0⃣1⃣
NA
ALAWIYYA ADO
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷.
Khalid ne jingine jikin kofar da zata sadashi da falon mahaifinsa, Alhaji Abbas, yakai kusan mintuna biyar yana buga kofar falon cikin nutsuwa, ganin ba à bude kofar ba yasa shi jingina da jikin kofar.
Aunty salma ce ta fito ta bude kofar falon, ganin khalid à tsaye jikin kofa shine yasata sakin fuska, cikin fara à ta bude masa kofar sosai yasa kai ya shiga.
“yarona sannu da zuwa yau kaine da wuri Haka ?
Ina kabar min surukata ?
Cikin fara à take masa wadan nan tambayoyin.
” ko zama banyi ba Aunty kike tsareni da tambayar ina surukarki, surukarki na gida, KO tashi batayi ba ma na fito “.
Tab ! Kace ko sallama ba kayi mata ba ka fito ?
Inafatan dai lfy ?
” lafiya lau Aunty sammako nayo muku Alhaji nakesan gani kafin ya fita shiyasa nayo sammako dan ko gun Hajiya ban Shiga ba ”
Ai kuwa ka daki gurbi dan wallahi Alaji yayi sammako sunje gidan Alhaji Bukar, jiya cikin dare akayo masa waya yana gida ciwan ciki ya murdeshi cikin dare, toh Sun kaishi asibiti cikin daren Amma basu kwana ba suka koma gida, shine yayi sammako yaje yaga jikin nasa “.
Ya Salam !
Aikuwa bari intashi inbisu inga jikin nasa.
bari in leka mu gaisa da Hajiya sai in wuce daga nan.
Aunty Natafi, cikin sauri ya tashi ya fice daga falon .
kai tsaye bangaren mahaifiyarsa y dosa Hajiya jiddah, à gurguje suka gaisa ya fito ya doshi gidan Aminin mahaifinsa Alhaji Bukar dake unguwar farawa.
Karfe goma Sha daya na safe agogon dake manne à babban dakin ya buga, bugawarsa yayi daidai da farkawar SUHAIMA daga baccin da ta kwanta tun jiya, idanuwanta ta daga takai dubanta kan agogo ganin da tayi lokaci ya ja, shine ta tashi cikin sauri ta fada bandakin dake makale à cikin dakin barcin maigidan ta.
Wanka tayi, sannan ta sanya doguwar riga ta gabatar da sallar asubahi ,bata tsaya yin doguwar addua ba tafada dakin girki dan samun Abinda zata Sanyawa cikinta, sabida azababbiyar yunwar da takeji.
Ruwan shayi ta tafasa ta sanya cikin fulas, ta soya wainar kwai ta debo kayan shayi ta nufi falonta dan ta karya kumallo.
Kusan karfe d’aya na rana taji ana kwankwasa kofar falonta, Dan kwalli tayafa akanta, ta je
domin ta bude kofar, tana budewa idanuwanta suka sauka kan aminiyarta, wata wawar runguma tayi mata suka shigo falon suna dariya.
“kai kawata baki da kirki kiri kiri kinki zuwa gidana sai da à waya ko muyi chart ” ?
cikin dariya Nabila tace “Amma dai kya barni in zauna kafin ki fara yin mitar” yauma sa a kikaci nazo miki kema Ai ba kirkin gareki ba daga ke har khalid din.
Wallahi kawata KO jiya mun dade muna hirarki.
Hmm !
Ku kuka sani dai.
Tashi ki samo min abinci yunwa nakeji.
yunwa ?
Aikuwa sai dai kisha shayi nima daxu shi na gama sha ,ko kuma ki shiga madafin ki dafa Ai kema nan gidanki ne kawata.
Nabila kuwa kasake tayi tana kallanta, cikin mamaki, toh yanzu daga zuwa na gidan mutane ina bakuwa sai à tura ni kichin yin girki, wato Suhaima kiwar nan taki har yanzu baki daina ba duk fadan da akai miki bakiji ba ko !!
“yanzu mijin nakima ruwan shayin kika bashi yasha da zai fita ?
kinji ki ko da wani zance, idan baisha ruwan tea ba me zan bashi ?
ni yauma ina bacci ya fita, Ban saniba ko ya karya ko bai karya ba ya fita.
wani wawan kallo Nabila ta jefa mata, Amma kedai kin zama shashasha wallahi ace mijinka shine zai fita kana kwance kana baccin asara, ki tunafa ke amarya ce ko wata guda baku rufe ba,, baxaki tsaya ki kula da rayuwar mijinki ba, sai ki zama shasha cikin gidan Aurenki.
nikam kin bani mamaki wallahi karatunki ya zama na banza da wofi ma.
ke ke ke dakata !
Suhaima ta daga mata hannu cikin bacin rai take magana ai gara muyi dama mun dade bamu kwafsa ba, dan nayi Aure kuma shikenan baxan huta ba menene amfanin auren Ai Nayi Aure ne dan muji dadi mu huta amma Sam bazan iya yin aikin gida ba kin san ko mumy ba sani takeyi ba.
Nabila dai, takaici ya cikata ko magana taki yi, mayafinta ta cire ta shiga kichin din, tana shiga tafara cin karo da kayan wanke wanke jibgi guda, kichin din yayi gaja gaja, omo ta dauka tayi wanke wanken ta gyara ko ina à kichin din yayi fes.
sannan ta dora musu abincin da zasuci.
Bayan tagama girkin ta zubo musu suka zauna sukaci suna hirarsu ta sun dade basu hadu ba, sai kusan karfe biyar na yamma sannan Nabila ta tafi gida.
wannan kenan
[10/7, 17:11] +234 706 738 2588: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷
‘YAR AIKI
0⃣2⃣
Na
ALAWIYYA ADO
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Bayan tafiyar Nabila, suhaima komawa tayi tayi kwanciyarta, bayan wani lokaci bacci yayi gaba da ita.
Khalid kuwa yana fita ya dauki hanyar farawa gidan Aminin mahaifinsa, Alhaji Bukar, da yake ya saba da masu gadin gidan yana zuwa suka bude masa tangamemen gate din shiga gidan ya sanya hancin motarsa ciki, kai tsaye cikin gidan ya shiga dan dan gidan ba bakunsa ba Ne bayan yaje Sun gaisa da mumy, bangaren Alhajin ya nufa ,à zaune ya samesu shida mahaifin nasa, Bayan ya shiga ya sami guri ya zauna har kasa yaje ya gaida mahaifinsa sannan aminin mahaifin nasa yayi masa sannu da jiki.
“sannu yaran kirki wanene ya sanar maka bani da lfy ne ?
Alhaji Bukar ya tambaya.
Abba naje gida ne gun Alhaji shine Aunty take fadamin baka da lfy, Alhajin ma yana nan gidan” Shine na taho dan inga jikin naka.
Ka kyauta kuwa, Nagode maka ai naji sauki aussi, jiya ban zaci zan kwana a duniya ba sabida azabar ciwo.
Ayya sannu Abba, Ai jiki yayi kyau.
Allah ya kara afuwa.
Amen y Allah yarona.
Shikam Alhaji yana zaune yana jinsu, sai da suka gama sannan yakai dubansa ga Khalid yace .
“ince ko lafiya na ganka da wuri haka ?
lafiya lau, Alhaji dama gaisheka naxoyi.
À à babban mutum ban sanka da karya ba lallai akwai magana à bakinka, cewar mahaifin khalid.
shikam dariya yayi yace Alhaji ,da gaske babu komai, tafiya ma zanyi tunda naga jikin Abban yy sauki.
Ai jiki yayi sauki sosai nima tafiya nake sanyi, tunda ya warware.
Karfe Bakwai na dare, khalid ya dawo gidansa, gimbiyar tasa tana kwance kan doguwar kujerar dake kewaye da falon,, Jin bude gate din gidan shine yasata tashi da sauri dan tasan maigidan Ne ya dawo, kafin ya shigo taje dakinta ta kara gyara fuskarta da powder, ta feshe jiki da turare.
sallamarsa ce tasa ta fitowa da sauri daga cikin dakin, da dan gudunta tazo ta rungumeshi, tanai masa sannu da zuwa, shi kam kamshin turarenta da yabugeshi shine ya cenza masa komai.
Baby na yau fa nayi fushi da kai, ta dan tureshi daga jikinta tana turo masa baki na shagwaba.
Haba matata laifin me kuma nayi miki akai fushi dani ?
Bacin kaine tunda ka fita tun safe baka dawo ba sai yanxu kuma ko ka kirani a waya kaji yaya ma nake.
tasake turo baki tana shagwaba.
Yi Hakuri matata, yau aiki ne yayi min yawa amma bazan karaba, ya kama kunnensa Alamar yanaja kamar wani yaro, Hakan da yayi kuwa abin dariya ya Bata.
toh, Baby na hakura.
Yauwa matata, ya fada cikin dariya.
wanka yaje yayi a bandakinsa, daga baya ya dawo ya sameta zaune à kan kujera tana ta chart, kusa da ita yazo ya zauna ya karbe wayar dake hannunta ya ajiyeta gefe, wato ke dai bakya gajiya da chart kullum ?
tashi tayi ta zauna daf da shi har takan jiyo bugun ziciyarshi, toh Baby na yaya zanyi, kullum ina zaune ni kadai daga kallo saï chart sune abokan hirar tawa.
kada kansa yayi to shikenan, me kika dafa min yunwa nakeji.
ta ware idanuwanta dara dara, wai gashi banyi girki ba, dazu ma Nabila ce tazo shine ta dafa mana Amman akwai ragowa ko in debo maka zakaci ?
gyada kansa yayi kawai, yace to jeki ki kawo min.
mekewa tayi taje kichin din ta dakko filet taje ta bude tukunya ta zubo masa, ganin taliyar bata da yawa kamar bazata ishe shiba har kanzo kanzon ta kwasu masa.
yana zaune yana kallo ta shigo ta ajiye masa akan dan karamin teburin dake gabansa.
Gefen sa ta dawo ta zauna, lomar farko yakai bakinsa yaji kanzo à bakinsa da sauri y furzar da ragowar dake cikin bakinsa.
lafiya baby na ?
kai kawai ya daga mata alamar ehhh lafiya nake.
kawo min ruwa shine abin da yace mata.
na urar sanyaya ruwa ta bude ta dakko masa ruwa roba daya, ko kufi Bata dora akai ba haka ya balle murfin ya kwankwadi ruwan, saï da ya kusa shanye ruwan sannan ya ajiye sauran.
SUHAIMA, ya kira sunan ta, ita kanta ji tayi banbara kwai sabida bai saba fadar sunanta kai tsaye ba.
cikin sanyin jiki ta dago da kanta takai dubanta gareshi.
kina jina ko ?
ya kuma magana a karo na biyu.
“ehhh, ina jinka.
ta fada jikinta a sanyaye.
[10/7, 17:12] +234 706 738 2588: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
‘YAR AIKI 🙆
Page 0⃣3⃣
NA
ALAWIYYA ADO
SUHAIMA, kina ganin haka ya dace ace muna gudanar da rayuwar Auren mû ?
Ki sanar dani menene matsalarki à gun girki da gyaran gidan nan ?
Baki iya ba ne ?
Inje in kirawa maryam kanwata ta koya miki.
Suhaima tunda mukayi Aure yau kusan sati uku kenan, bakya girkan abinci, sai dai muje gidan cin abinci na siyo mana, ko inje gida inci acen, kina ganin haka kowanne magidanci yakeyi à gidansa ?
Idan akwai matsala kiyi kokarin sanar dani matata, ya fada muryarsa cikin rauni.
Tunda ya fara maganar nan, ita kam hawaye ne yake sassarfa zuba akan kumatunta, bata da Katar Da shi ba sai da ya gama maganarsa.
Cikin kuka ta fara da cewa.
“Haba Baby na, kasan inayin aikin gidan nan dai dai kokarina, kasan kuma abubuwan sai a hankali tunda ba sabawa nayi da yi ba bayan haka kuma ga wasu hidin dimun sun kara hawa kaina wadan da ban saba da su ba.
Kaga dazu ma da kyar na iya tashi nayi sallar asubah sabida gajiyar da nayi duk jikina ciwo yake, ta karashe maganar cikin shagwaba, hmm toh yaya kakiso inyi ?
Shiru yayi, yana jinjina magan ganunta, ya kuma gasgata abun data fada masa, musamman ganin hawaye akan kyakykyar fuskar tata.
kamo hannunta yayi Ya sanya cikin nasa, ya tallafota yana rarrashinta, nan da nan ta sake ranta suka fada cikin nishadi.
Karfe goma, na safe, khalid Ne rike da bakar jakarsa, wadda yake tafiya kasuwa da ita, gefansa kuwa suhaima ce ta rakoshi bakin motarsa.
Baby na, cikin wata sigar Jan hankali ta kirashi, cikin kasalalliyar murya ya amsa mata.
yaya akayi ne madam ?
“Dama cewa nayi ko inzo mutafi tare ka sauke ni agun mumy na, kaga tunda makayi Aure bata zo gidan nan ba, nima kuma banje ba ”
Tabb !
Ai ke da ki fara fita sai bayan wata shida.
Ya fada yana dariya.
itama dariyar takeyi.
Haba dai dan Allah ka barni inje.
toh ki bari idan Allah ya kaimu gobé idan zan fita saï mutafi taré in saukeki agidan naku.
Murna tayi sossi har da rungumarsa, motarsa ya bude ya shiga,mai gadi ya bude masa gate din ya fita.
Suhaima kuwa ciki ta koma da tsananin murnarta, wayarta ta dauka tayiwa mumy Albishir din zuwanta à gobe, itama mumy taji dadin ziyarar ta ‘yar tata zata kawo mata.
Tunda Ta kwanta à kan doguwar kujerar falon, data ta bude ta fara sana ar tata ta chart, sallah ce kawai take tashinta ita ma ba akan lokaci ake yinta ba.
washe gari tun da sassafe suhaima ta tashi ta shirya sabida murnar zuwa gida, karfe goma da rabi, ya sauketa a kofar gidan su, tare da bata sakon ta isar masa da gaisuwarsa à gun mumy, kafin yazo da daddre.
da gudu ta tusa kanta cikin dakin mumy din ta tana kwance taji suhaima a kanta tana ihun murna.
tashi tayi ta zauna tana fadin ohhh, suhaima ko yaushe zakiyi hankali ?
Ki dubi yadda kika fadomin aka ko sallama babu, Dan Allah ki dinga nutsuwa.
yi hakuri mumy murnar ganinki ce ta mantar dani komai.
Gefen kujerar da take taje ta zauna ,mumy dady kuwa yana nan ?
Sabida inganshi nayi sammakon nan.
” Aikuwa kinyi sa a yana kusa bai fita ba”
Da gudu ta tashi zata tafi gun dady, ke dakata cewar mumy ai baya gidan dan gidan mlm mude ne ya rasu sunje gun jana iza amma zai dawo dan ko karyawa baiyi ba”
Jiki à sanyaye suhaima ta dawo ta zauna, mumy wanne daga cikin yaran gidan ?
Wannan mara lafiyar kwakwslwar ne ya rasu.
Allah sarki Allah ya jikansa ai ya hutama wallahi.
Ke yaya maigidan naki, ince ko kuna zaune lafiya babu wata matsala ko ?
Mumy bubu wata matsala,, sai dai gidan ne yayimin girma bana juré shareshi gaba daya, mumy ga wanke wanke ga girki, sune kawai suke bani wahala mumy.
Shine matsalata kawai.
Ai shiyasa nake fada miki ki koyi aikin Gida sabida duk macen data iya komai kafin tayi aure ta huta komai zaizo mata da sauki.
Ni wallahi mumy bazan iya ba.
kawai ki bani mu ifa in tafi da ita ta dinga tayani aikin.
kema kin san wasane wannan, ta yaya zan dauki ‘yar data ragemin in baki ita, Ai ko dadynku bazai yarda ba, shi khalid din ba yanada kanne ba abaki guda daya mana a cikinsu, sai ta dinga taimaka miki.
Ni wallahi mumy bana san kannensa suzo gidan nan koda da yini ne bare su dawo gidan da zama.
” ke SUHAIMa kada fa kizama irin matan nan da basa son dangin mijinsu su rabesu, kiyi kokari ki dinga jan ‘yan uwansa à jikinki hakan zai kara bashi dama akan ya kara kyautata miki ”
Zumburo baki tayi Tom mumy zanyi tunda kince ayi din.
ranar dai yini sukayi suna hira da mumy da kannenta, har dady shima ya jima ana hirar da shi daga bisani kuma ya shirya ya fice kasuwa.
Kusan karfe takwas, saura Khalid ya shigo gidan, dukkansu à falo ya samesu, har da dady din.
Bayan ya tsuguna ya gaida surukan nasa, ya jiyo kan kannen matar tasa, Suhail da Na ifa, manyan gari sannunku.
Suhail ne ya fara gaida Shi sannan Na ifa, gaisuwa sosai sukayi da wasa da dariya.
mukullin motarsa khalil, ya mikawa Suhail.
“jeka cikin mota ka dakko muku alawa à bayan mota ”
Cikin girmamawa ya karba ya tafi aiken da mijin yayar tasa yayi masa.
Suhaima na kwance jikin mumynta koda khalili ya shigo hakan baisata ta Mike ba daga kwancen tayi masa sannu da zuwa.
Suhail ne ya shigo da mayan ledoji guda biyu kowacce shake da kayan kwalama yaje gaban mumy ya dire mata .
cikin murna mumy tayiwa surukin nata godiya, da fatan samun zaman lafiya cikin Auren nasu.
shikam dady fada yayi akan kashe kudin da khalil yayi gun siye siyen da Yayo.
sannan yakara da yimusu nasiha, akan wasu nauyin da Allah ya dora musu akan junan su.
sai kusan karfe goma na dare sannan suka koma gida cikin farin ciki bama kamar Suhaila dataje taga mumy da kannenta.
wannan kenan
[10/7, 17:12] +234 706 738 2588: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
‘YAR AIKI.
Page 0⃣4⃣
NA
ALAWIYYA ADO.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌐HAJOW📝🌐
👩👧👧👩👧👧👩👧👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾
Rayuwa tana ta tafiya a tsakanin, Khalil da Suhaima a yanzu haka suna cikin watanni hudu da Auren su sai dai babu abinda ya cenza, sai ma karuwa da wasu abubuwan sukai.
Suhaima ta samu yadda takeso a gun khalil, kudi bata da matsalarsu, kuma da yake ta kasance bamai rowa ba ce, takan yawan yin baki daga bangaren ‘yan uwanta da kawayenta, ‘yan uwan khalili kuwa basa zuwa sabida basu samu fuska agun matar gidan ba.
WACECE SUHAIMA ?
Alhaji Salisu sharif, shine cikakken sunan mahaifinta, Wanda yake zaune à unguwar NA ibawa, Alhaji salisu, dan kasuwa ne cikin kasuwar kwari, Yana sai da atamfofi cikin shagonsa, rufin asiri dai dai gwargwado Allah yayi masa, Asalinsa dan garin katsina ne cikin wani gari da ake kira da KAYAWA, kasuwanci ne ya kawoshi garin kano har Allah yasa, zamansa à kanon yake.
Bayan ya dawo kano da zama Allah ya hadashi da safiyya, kanwar Abokinsa ce Rabiu, tun ana soyayya à boye har da kowa yaji manya suka shiga maganar har Allah yasa safiyya rabansa ce akayi Aure akasha biki.
gida madaidaici ya kama musu haya à unguwar tarauni, zaman lafiya suke sosai à tsakanin su.
tunda sukayi Aure Allah ya budawa salisu harkokinsa, kasuwa ta bude masa, cikin ikon Allah yasiyi fili a unguwar Na ibawa sannu a hankakali yake ginin filin har Allah yasa ya gama.
À wannan lokacin kusan shekarsu uku da Aure Amma ko bari safiyya bata taba yiba.
ita kam Abin yana damunta, anma kullum mijinnata rarrashinta yake akan tayi hakuri, in Allah yaso zata samu rabonta itama.
Kwanci tashi babu wuya a gun Allah ,safiyya ta samu ciki, bayan dogon laulayi da tasha, watan cikin tara wata ranar lahadi nakuda ta kamata, hankallin Alhaji salisu ya tashi sosai, cikin hanzari yaje gidansu ya fada .
Tare suka taho da inna Rabi kishiyar mahaifiyarta, Asibiti suka tafi Cikin ikon Allah basu jima da zuwa ba ta sallubo jaririyarta, cikin koshin lafiya.
Kar kaso kaga murna agun Alhaji salisu da danginta, ita kam safiya ji take tamkar ta hadiye jaririyar sabida murna.
Ganin lafiyarta kalau, ita da jaririyar aka basu sallama.
Kai tsaye gidan mijinta aka wuce da maijego.
Dangi fa kowa sai murna, musamman idan anzo angajaririya kyakykyar gaske.
Dan gin Alhaji salisu duk sunzo daga garin KAYAWA.
Ranar suna jaririya ta amsa sunan AiSHA sunan mahaifiyar Alhaji salisu, Amma ana kiranta Da ( SUHAIMA)
haka dai suka cigaba da rainan jaririyarsu, cikin hakan kuma Alhaji Salisu ya karasa ginin gidansa dake NA IBAWA.
Bayan sun koma sabon gida, suka cigaba da gudanar da Al amuran su na yau da kullum.
Shekarun SUHAIMA, bakwai à duniya sannan Safiyya ta sake haihuwa.
Wannan karon namiji ta samu kar kaso kaga murna a wannan gidan.
ranar suna yaci sunan mahaifin safiyya Umar ,shima suke kiransa da (SUHAIL)
Shekarunsa hudu shima aka haifi NA IFA.
haka dai rayuwar gidan ta kasance cikin mutunci da farin ciki.
Soyayya mai karfi mumy takewa SUHAIMA, har zuwa lokacin da tafara girma, makaranta mai kyau mai tsada mahaifinta ta ya sanya ta.
yarin yace mai kwazo da kokari, ko cikin makaranta takan dauki sakamako mai kyau na jarrabawa.
wannan damar da t’a samu shine yasanya SUHAIMA sangarcewa kiwa ce da ita sosai.
hakan kuwa ya farune da laifin mahaifiyarta, domin har shekarun ta sun fara ja Amma mumy wanki take mata koda pant din ta ne, shara kuwa batayi bare wanke wanke.
wannan muguwar sangartar da mahaifiyarta tayi mata va karamin batawa dady rai yake ba.
Hakan dai yake mata fada akan lallai ta gyara tarbiyar yarinyar ta sabida diya macece wata Rana gidan wani za à kaita.
duk lokacin da dady yake wannan fadan mumy banza takeyi da shi.
SUHAIMA ta zama cikakiyar budurwa, à wannan shekarar zata gama makaranta.
Cikin wannan rugun tsumin ne samari suka fara fitowa neman Aurenta, nan fa mumy tayi mata huduba akan sai mai kudi ko dangidan masu kudi ta yadda zata samu jin dadi cikin gidan Aurenta .
wannan karatun na mahaifiyarya ta dauka, Dan haka indai baka da wani abu ko kazo bata fita, idan kuna anyi sallama da ita dady na gida hakan zai tilas ta mata akan sai ta fita din.
cikin hakan Allah ya hadata da KHALiL, tabbas Khalil shine irin mijin da take jira dan akwai kudi à kwai kyau.
Hakan ne ya bashi damar samun soyayyarta cikin ruwan sanyi tare data mahaifiyarta, tunda ya gano su ai kuwa yake musu barin kudin kamar ba yaso.
Cikin kankanin lokaci maganar Aure tayi karfi, aka tsaida maganar Aure bayan tayi candy da wata guda za a sha biki.
Komai yayiwa mumy yadda takeso, lefe na gani na fada Aka kawo daga gidansu khalili.
kar kiga murna da zakwadi agun uwar da ‘yar.
Ansha biki na kece raini, indai raina tayi kuka ta kowanne bangare.
ranar lahadi akaje aka mika amarya gidan Angonta khalili, gida na kece raini da burgewa nan aka saka Suhaima.
Ku biyoni muje zuwa.
[10/7, 17:13] +234 706 738 2588: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
‘YAR AIKI.
Page 0⃣5⃣
NA
ALAWIYYA ADO (Teeyma phaty)
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🔰 HAJOW ✏🔰
👩👩👧👩👩👦👩👩👦 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏼
Cikin kwanakin amarcin su ba karamar kulawa suke da junan su ba, shi kam Khalil ganin yadda rayuwa tayi masa dadi da amaryarsa da take tararairayarsa, bashi da wata matsala.
Kusan sati guda ya kwashe a gida ko kasuwa baya fita, suna dirzar Amarci, da gimbiyar tasa.
Wani lokaci suna zaune da Suhaima suna hira ga dukkan alamu hirar tana kayatar da su, dan Suhaima ce kwance akan doguwar kujerar falon, kanta gaba daya yana jikin Khalil.
“”Baby na ”
Ta kirashi cikin murya mai taushi da daukar hankali.
” yaya akayi ne madam “?
“kaga yau sati guda dayin bikin mu, Amma Hajiya batazo gidan nan ba sai su Aunty Salam ne sukazo, me zai hana yau ka kaini inje in gaisheta”
“madam kenan, ke bakisan kunyar Hajiya bane “?
“Ai bazata iya zuwa gidan nan yanzu ba, sai dai Muje mugaisheta, ko anjima da daddare ne”
Hmmmm !
“Hajiya kenan ”
Cikin, dariya Suhaima, take magana.
” mudai babu ruwan mu da wani Jin kunyar dan fari idan mun haihu ko ” ?
kunnenta ya kamo yanaja da karfi, Jin zafin da tayi ne ya sa ta tashi da gudu tabar masa falon.
Bayan an idar da sallar isha i, suka dauki hanyar zuwa gidan su Khalid, kwalliya sosai Suhaima ta caba, abinka da kyakykyawar mace haka ta fito fes da ita.
shi kansa Khalil ya yaba mata wannan kwalliyar da ta yi, less ne blue mai adon Pink, mai manyan flawers à jikinsa, kayan Adon da ta sanya komai Pink ne, dangin kayan kwalliyar mata, Sarka da awarwaro da tarkacen kayan kawa.
Suna tafe suna hirar masoya irin masoyan da suka shagaltu gurin kaunar ju nan su.
Bayan yayi parking din motarsa à harabar gate din gidan nasu, da kansa ya zagayo ya budewa Suhaima kofar motar, santala santalan kafufuwanta ta zuro, ta fara takawa cikin tafiyar yanga da jan hankali.
À babban falon gidan suka yada zanzo, domin duk yaran gidan suna cikin falon suna hira.
matan gidan ne babu su a cikin falon.
Zulaikha ce ta fara tasuwa da murnar ta ta tari Auntyn nata.
“Oyoyo ga Aunty mu ”
Abin da take ta maimaitawa kenan tun lokacin da ta hangi shigowar Khalid da Amaryar tasa.
saurin kanin nasa ma tasowa sukayi gaba dayansu suka rungumeta.
“Aunty Suhaima sannu da zuwa ”
“yaya Khalid meyasa baka fada mana zakuzo ba ? ”
“kai Ku kyaleta haka mana kada kuji mata ciwo mana, sai kace wasu yara kanana, Ku bata guri ta zauna tukuna ina su Hajiyar ne ? ”
Faiza ce ta dago ta bashi amsa da cewa.
“tana daki sallah takeyi ”
“0k, bari inje inga ko ta idar.
kallansa ya kai inda Jalila take zaune, wata muguwar harara ya zabga mata.
“Ke bakiga baki bane ? ”
“yi hakuri yaya ina chart ne banji shigowarku ba ”
Gyada kai kawai yayi, ya fice yabar falon.
Cikin sallama ya tusa kai ya shiga dakin mahaifiyar tasa, shigarsa tayi daidai da shafa adduoin da takeyi.
“Amen wa alaikassalam, Khalid kaine tafe da daddaren nan ?
“Hajiya bani kadai bane tare muke da Suhaima tazo ta gaisheki ne ”
Ohhhh Ikon Allah !
“sati guda dayin Auren shine har aka fara fita yawo ? ”
Allah dai ya shiryeku !
“toh ina ka barta kuma”?
tana falo gun su Zulaikha.
jeka shigo da ita mana.
amma kafin nan Ku fara shiga gun Aunty yara ta gaisheta.
“Tom Hajiya bari muje mu dawo din”
Bangaren Aunty Salma sukaje suka gaida ta. “Amarya sannu da zuwa, yau kece bakuwar mu, zuwa bako waya bare mu taryeki “?
“Khalil baka kyauta min ba ai ko ni kasanarwa zuwan naku.
“Aunty kiyi hakuri, yanzu muka shirya zuwan shiyasa ban sanar miki ba, kuma naga zuwan namu na dare ne ba rana ba”
“Ai ko dare ne ka fada”
“kaina bisa wuyana baza a kuma ba Aunty na”
Firinjin dake dakin ta taje ta bude, ta dakko ruwa da lemo ta kawo musu.
kememe Suhaima taki sakin jiki tayi hira da Aunty Salma ganin haka ne yasa suka taho bangaren Hajiya.
sanda suka shigo bangaren Hajiyar ta fito daga cikin dakin ta a falo suka sameta ita da yaran suna hira.
tunda Suhaima ta shigo, ta nemi guri daya ta zauna,shi kam Khalil bayan Sun gaisa da Hajiyar ficewa yayi ya tafi gun Alhajinsa.
duk yadda suka so yin hira da ita taki magana saï dai ta danyi murmushi idan anyi abin dariyar.
Basu bar gidan ba saï da sukaje bangaren Alhaji, Aunty Salma ce tayi mata jagorar zuwa gun Alhajin, yayi musu nasiha sosai akan su zauna lafiya da kiyaye hakkokin da suka hau kan ko wannensu. kyautar kudi masu yawa Alhaji yayi mata à lokacin da sukai masa sallamar komawa gida.
itama Hajiya tayi mata tata kyautar ta turare masu kamshi.
Aunty Amarya ma haka, kannen Khalili kuwa har bakin mota saï da suka rakata amma banda Jalila, shi kansa Khalili yaji dadin yadda aka karrama amaryar tasa à gidan su.
saï dai abin da ya daurewa Khalili kai bai wuce yadda yaga Suhaima taki sakin jikinta à gidan na su.
KO bata saké tayi hira da su Hajiya ba ai ta saki jiki da kannen nasa suyi hira.
tun à mota yake ta tunanin dalilin da yasa suhaima yin hakan.
sai kusan karfe sha daya suka koma gida, bayan Sun koma gida, nan suka baje à falo suna hira tana yabawa da halin kirki irin na Hajiyarsa.
Har cikin ransa yaji dadin yabon da tayiwa iyalan gidan su.
✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷
‘YAR AIKI
Page 6⃣ to 1⃣0⃣
Na
ALAWIYYA ADO (Teeyma phaty)
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🔰HAJOW 🔰
👩👩👦👩👩👦👩👩👦JURIYA DA HAKURI ONLINE WRITERS✍🏼
Godiya mara adadi ga masoyan wannan labarin nawa, Allah yasa sakon dake cikin sa yaje ga al ummar mu masu hali irin na Suhaima.
WANENE KHALIL ?
KHAlili Bukar Hashim shine cikakken sunan Sa.
Mahaifin Khalil hamshakin mai kudi ne cikin kewayen unguwarsu, asalinsa haifaffan cikin garin kano ne Wanda yake à unguwar yakasai cikin karamar hukumar birni da kewaye.
mahaifinsa shine mai unguwar yakasai, Alh sani, yana da matan Aure guda biyu Zainab ita ce uwar gida tana da yara shida, Hafiz shine babba, saï mu azzam,San nan Sadiya da Aisha sai karimatu, sai kuma dan karamin su shine Abubakar Wanda suke kira da( Bukar) kasan cewar sunan ka kansa yaci Wanda ya haifi mahaifiyar sa Zainab .
A bangaren Harira kuwa, amaryar Alh sani tana da yara guda Biyu mata, Sakina da zulaiha.
zaman lafiya da kaunar juna shine abin da yake wanzuwa cikin gidan Alh sani mai unguwa.
Alh Sani mutum ne adali cikin iyalan sa domin baya tauye wa kawa hakkinsa tsakanin zaman
matan nasa, wannan ce tasa yaran gidan suka taso kansu à hade tamkar duk ciki daya suka fito.
Hakan ma ya samo asali ne gurin hakuri da kawaici irin na inna Zainab, haka dai yaran suka taso cikin girmama iyayensu da junan su.
Bayan Sun girma, kowanne Allah ya rufa masa asiri duk Sun fara kasuwanci, kuma cikin ikon Allah suna da Nasibi.
manyan maxan gidan duk sunyi Aure, matan ma duk an aurar da su, Bukar ne kawai Baiyi Aure ba a cikinsu sabida yana karatun digiri din sa a jami ar bayaro ta kano.
Bayan kammala karatunsa ya hadu da uwargidan sa, Hajja Maryam, ‘yar unguwarsu ce gidan su babu nisa da gidan mai unguwa, cikin kan-kanin lokaci maganar Aure ta taso, biki anyishi cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Gida ne mai kyau flat suka taré ango da amaryarsa, Haka dai rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin nuna kauna da kulawa da juna.
kwanci tashi babu wuya à gun Allah Hajja maryam ta samu cikin dan ta na fari, murna kamar Sa goya cikin haka suka dinga yi ita da mai gidanta Bukar.
Kasuwancin sa kullum habaka ya keyi yana sai da kayan abinci cikin babbar kasuwar singa ta cikin garin kanon dabo.
À kwana à tashi babu wuya agun Allah ciki ya shiga watannin haihuwa, duk wani tanadi Babu Wanda Bukar baiyiwa maijego da jaririnta ba.
Ranar wata litinin, cikin dare nakuda ta kamata, ya sanyata à mota sai asibiti, bayan doguwar nakuda ta sallubo jaririnta santalele kyakykyawan gaske, murna sosai kowa ya nuna da godiya à gun Allah da ya basu wannan kyautar.
Dangin kam sunyi rawar gani dan yaro ya zama dan lele gun dangin uwa da uba, Ranar suna yaro yaci suna Ibrahim sunan wan mahaifinsa da yake duk sauran Yayye Sun rigaya Sun sanya sunan Alh Sani.
dan haka tun ranar suna dangi suka fara kiransa da Khalil.
tunda Khalil yazo duniya Al amura suka kara war warewa Bukar, kudi ya nunku komai ya yalwata, gashi ta ko ina yana yawan taimakawa ‘yan uwa da abokan arziki.
Bayan shekara uku, Hajja maryam ta sake haihuwa, wannan karan santaleliyar budurwa ta sullubo, nan fa murna da farin ciki suka kara yalwatuwa.
Ranar suna aka sanya mata suna Zulaikha, dg nan fa haihuwa ta ballewa Hajja maryam yanzu haka tana da yara Bakwai, Shamsiya, Rukaiyya, Nasir da Jalila, saï karamin su shine Mus Ab…
Bayan shekaru da Auren Hajja maryam, Alh Bukar ya tanfatsa gidansa na gani na fada a unguwar N’ai bawa ‘yan lemo, gida ne na kece raini na nunawa sa à.
iyalan sa Sun koma gidan cikin farin ciki da murna.
Bayan tatewarsu da Shekara daya ya nemo Auren Aunty Salma A matsayin Amaryarsa.
Zaman lfy sosai ake cikin gidan Alh Bukar, duk da yake Hajja maryam macace mai kishi amma tana guje duk wani abu da zai kawo musu sabani da abokiyar zamanta.
À bangaren Amarya Salma itama tana mutun ta Hajja maryam dan haka zaman gidan yake gwanin dadi.
Aunty Salma tana da yara guda biyu na farko Habib mai shekaru shida sai kuma muhsina mai shekaru uku.
wannan kenan.
Khalil ya samu karatun addini dana boko inda ya sauke Alqur ani tun yana shekarun sa na kuruciya .
Haka ma a bangaren boko, ya hada digiri din sa a bangaren Business administration, sauran kanin sa ma duk suna karatun su, zulaikha tana jami à tana karantar low, Jalila tagama skul tana jiran fitar result din ta.
dukka dai yaran gidan suna samun ilimin addini dana zamani.
Tun lokacin da Khalil yazo musu da zancen ya samu yarinyar da yakeso ya Aura, kar kuso kuga murna agun iyalan gidan.
shi kansa Alh yayi murna sosai ko ba komai yana San yaga gudan jinin nasa ya zama magidanci.
Itama Hajja tayi murna sosai dan tana San ganin surukarta, lokaci kankani Alh ya siyi filoti babba a unguwar Sharada, ya fara ginawa dan nasa muhallin zama, gini na gani na fada ake kankarawa..
Bawani lokaci mai tsawo aka dauka ba aka kammala ginin katafaren gidan Khalil din, Nan fa ‘yan uwa suka hau farin ciki da murna duk wanda yaje yaga gida San barka yakeyi da adduar Allah ya rika masa.
Alh da kansa shida Aminin sa suka shirya duk wasu abubuwan da akeyi gun hudimar biki.
tsoho mai dogon zamani Mai unguwa shima sai da yaxo yaga gidan da aka dan dasawa jikan nasa, yaron Kirki.
CIKIN GIDAN KHALIL.
Suhaima tana zaune, tana kallo à babban falonta ta Wanda ya kayatu da kayan kawa na daki, hannuta rike da remot, tana, cenza tasha Arewa 24 zuwa mbc 2
Kwakwaso kofar falon akeyi da karfi, da sauri ta tashi ta nufi gun dan ganin wanene yake mata wannan bugun kofar.
cikin fushi ta ke tambayar.
“waye ne ”
Jin muryar mumy din ta à bakin kofar ta amsa mata da cewa.
“Suhaima mune”
da murnar ta ta bude ki .
“mumy sannu da zuwa ”
cikin falon suka shigo dukkanin su, saï dai yadda taga falon kaca – kaca Shine ya tsorata.
“Suhaima me yasame ki haka ne”?
“mumy me kika gani “?
“Au ke bakiga yadda dakin naki yake ba ko ina kace _kace, sai kace kuturwa”?
“Bakya yin shara ne Suhaima “?
Girgiza kai tayi, mumy nifa wallahi gidan nan yayi min girma bazan iya aikin gidan ba.
mumy dai gurin zama ta samu ta zauna, cikin bacin rai take magana a yanzu.
Haba SUhaima !!
yanzu wannan abin da kike ai bai kamata ba da ranki da lafiyar ki ace gari ya waye kafin mijinki ya fita, bazaki gyara jikin kiba ki gyara gidanki, shi kansa ya fita cikin murna da farin ciki ?
Kiduba yadda kike fa”
ace yarin yar mace kamar ki, karfe kusan uku na rana, Amma ko wankan safe bakiyi ba ”
Nikam banji dadin yadda naxo na ganki ba, gaskiya.
“Na ifa”
“Na am mumy ”
tashi kije ki dau tsintsiya ki gyara mata gidan ”
À gyara KO ina da ina.
cikin awowi uku suka hadu suka gyara gidan tsaf gwanin sha awa.
komai ya dawo kal.
sai bayan sallar magariba mumy suka tafi gida, kafin tafiyarsu gidan mumy ta sanarwa Suhaima cewar za a samo mata.
*’YAR AIKI*
wannan kenan.
✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*’YAR AIKI*
Page 1⃣0⃣ to 1⃣5⃣
NA
*ALAWIYYA* ADO (Teeyma Phaty)
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🔰HAJOW🔰
👩👩👧👩👩👧👩👩👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS✍🏼
Bayan mumy ta koma gida, waya ta dauka ta kira, Kawarta Hajiya Asma à, bayan Sun gaisa kamar yadda suka saba à duk lokacin da sukayi waya ko suka hadu à matsayin su na Aminan juna.
“Hajiya yaya akayi ne naji Kiran wayarki da daddaren nan “?
Hmm !!!
“kedai bari kawai kawata, daga gidan ‘yarki nake, kinganni duk raina a bace yake “.
Hajiya lafiya dai KO !?
Toh lafiyar kenan, Zuwa nayi gidan na tarar da ita duk tayi kaca -kace da gida, hatta jikinta babu gyara ”
Ace yarinya daga yin Aure ko wata shida Bata kwashe à gidan miji ba amma komai yayi daidai à gidan ”
Ai kam dolé ranki ya baci, cewar Hajiya Asma à.
Duk irin dukiyar da muka labta à cikin gidan nan ace baza a gyara guri ba, lallai da saké.
“toh shine dalilin da yasa na kiraki, tunda dama Delu tana kawo masu *AIKI* daga garin su, shine na keson asamo mata kinga ta dinga gyara mata gidan”?
“wannan shine mafita Hajiya bari in kirata in fada mata, in yaso ko jibi ne saï ta tafi ta samo mata a cen garin nasu”
“toh Hajiya Asma à Nagode sosai ”
haka dai sukayi sallama kowa ya ajiye waya.
*KHALIL*tunda ya shigo falon gidan nasa ya tabbatar da cewar yau Suhaimà baki tayi, dan tun daga shigowarsa yaji kamshin turaren wuta mai dadin shaka, Wanda idan zai tuna raban da yaji hakan a gidan sa tun satin farko na Amarcin Suhaima.
Da sallamarsa ya shiga cikin falon, yau dai babu laifi, tayi kwalliya ba kamar kullum ba, Cikin sauri ta tashi ta taryeshi ledar hannunsa ta karba taje ta ajiyeta kan dan karamin teburin dake tsakiyar falon, sannan ta dawo inda ta barshi à tsaye, shi kam gaba daya hankalinsa yana gun falon ganin yadda gurin yy fes ga kamshi yana tashi.
rumgumar da tayi masa ita ce ta dawo dashi duniyar mu.
“lafiya kuwa naga ka tafi tunani “?
jawo shi tayi ta zaunar da shi kan daya daga ciki kujerun dake kewaye à babban falon nata.
“Sannu da zuwa Baby na ”
Ta fada cikin sigar shagwaba.
“yauwa madam ”
“ya gida yaya kika yini ina fatan komai lafiya ko ”
“lafiya lau ”
ta fada cikin dariya.
zakayi wanka ne ko kuwa ?
“A à yaufa na debo yunwa da yawa tashi ki dakko flet ki juye mana abincin à ciki. ”
Yadda ya umarce ta hakan tayi, flet ta dakko à kichin ta juye musu, farfeson naman kaxa ne à leda guda, daya ledar kuma yoghourt ne à ciki manya guda biyu.
zama sukayi suna ci suna hirar su irin ta masoya, cikin hirar tasu ne take sanar masa da zuwan mumy din ta.
Anan ya tabbatar da zargin da yake na cewar Suhaima baki tayi, shiyasa yau gidan ya dawo hayyacin sa.
Bayan Sun gama cin abincin bangaren sa ya tafi dan ya watsa ruwa à jikinsa ko yaji dadi.
tunda ya bude kofar falon nasa yaga komai ya sauya an gyara ko ina.
Suhaima ce ta taimaka masa yayi wanka, doguwar riga jallabiya ta dakko masa ya saka, bayan ya gama wankan ita da kanta ta shirya shi suka dawo falonsa suka zauna suna hira.
Bayan Sun gama wayar Hajiya Asma à ta, kira mai aikin ta Delu, bata Wani jima da Kiran nata ba Delu ta shigo cikin falon na Hajiya, cikin girma mawa ta durkusa À gabanta.
“Hajiya gani, Hydar yace inzo kina kira na ”
“Ehhhh ,nice na ce ya kira min ke ”
“Toh Allah yasa dai lafiya uwar dakina”?
“À à lafiya lau Delu, dama Hajiya ce tayo waya dazu tana san yarin ya mai *AIKI*, za a kawowa Suhaima. ”
“Ikon Allah Hajiya, à yanzu dai babu yara à kasa, sai dai ko ajira zuwa nan da dan lokaci idan ansamu sai à samo mata ”
‘À à Delu duk yadda za ayi dai à samo mata yarinyar nan sabida ana bukatar ta cikin gaggawa”
Toh fa !
“inaga Abin da za ayi Hajiya zanje gidan da Ra shida take aiki in dakkota, sai ince da uwar dakin nata agida ne ake nemanta.
Tunda dama basu San jikata ba ce, in ba haka ba kuwa Alqur an baza à samu da wuri ba ”
Cikin farin ciki Hajiya ta washe baki tana yiwa Delu godiya.
“Haba Hajiya Ai kunfi karfin haka à guna “.
Yauwa Delu, to idan Allah ya kaimu goben sai ki shirya da wuri kije ki taho da ita.
À bangaren mumy, kuwa bayan ta bugawa Aminiyaarta waya kan tana son asamawa shalelen tata mai *AIKI*
Bayan Sun gama maganar ta kashe wayar.
Number Suhaima ta kira, ringin din farko, ta daga sabida wayar tana hannunta, bayan sallama ta gaida mumy cikin fara à duk da bata ganin ta amma daga jin muryar ‘yar tata tasan tana cikin nishadi.
“mumy yaya kukaje gida”?
“munje gida lafiya lau, Suhaima “.
“Dama na kiraki ki ne dan in sanar miki, nasa Hajiya Asma à ta samo miki yarinyar da zata dinga taimaka miki da Aikin gida, dan haka ki sanarwa da Khalili, kada akawo yarinya ba tare da an sanar da shi ba.”
“yauwa mumy wallahi nagode miki naji dadi sosai, muna tarema da shi ma yanzu zan sanar masa ai nasan bazai ki ba dama”
toh shi kenan, idan ansamu zaki ganta an kawo miki ita.
nan sukayi sallama da Mumy ta kashe wayar, nan ta sanar da Khalil sakon mumy na cewa tasa a samo mata mai aiki.
Suhaima wacce irin mai *AIKI* kuma !!!?
“yanzu ke bazaki iya gyara gida da yin girki ba “?
“wai menene amfanin Auren ne”?
Ace ke bazaki iya yin komai ba sabida Allah.
Ni dai gaskiya bana so gara ki tashi ki dinga yin komai da kanki, idan ban fita ba, saï in dinga taimaka miki.
Cikin kuka ta fara yi masa magana
“Haba Khalil wai yaya ka keso inyi ne ? ”
ni dai gaskiya tinda mumy ta samo min mai aikin kawai kayi hakuri tazo kaima kaga ka huta siyo abinci kullum, saï ta dinga girkawa tana gyara gidan ”
Ke kuma ki zauna kina chart na banza da wufi KO !!?
Nidai kayi hakuri kawai chart kuma ai shine yake debemin kewar zama shiru.
sabida ta kaici baice mata komai ba ya cigaba da kallansa à babbar tv din dake jingina jikin bangon falon nasa.
ranar dai haka kowanne ya kwanta zuciyarsa babu dadi.
*WASHE GARi*
À bangaren Delu kuwa ,tun wuri ta gama
Duk wani aikin da tasan akanta ya ke , bayan ta gama ta shiga tayiwa uwar dakinta sallama dan zuwa dakko mai Aikin.
wannan somin tabi ne.
✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*’YAR AIKI*
Leave a Comment