Yar fillo complete Hausa Novel

Yar fillo complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Yar fillo complete Hausa Novel

Hankalinta kwance take damun furarta tana “yan wakokinta ckn harshen fillanci

 

 

Saiji tayi Anrufe mata idanu ta baya

 

Ta tsaya cak! Da damun tana shakar kamshin turarenshi a tafin hannun nashi

 

Tasan ko waye ta haddace kamshinsa Abokin tane wato Abdul hamid wanda take kiransa da Abokin birni

 

 

Murmushi tayi tareda cewa “walh naganeka Abokin birni ne…

 

 

Yacire hannunsa daga fuskarta ahankali yana fara,a yadawo gabanta ya durkusa yana kallon kyakykyawar fuskarta

 

Ta ajiye kwanan shan robar datake damun takalleshi da mamaki tace “abokin birni yaushe ka dawo?

 

 

Yace yana dry “Yanxu yanxu muka shigo kauyen naku jaka kawai na jiye agidan gona nataho gunki.

 

 

“Amma dai kai kadai kazo ko???

 

Ya girgixa kansa ya nuna bayanta yana fadin “kalli can kiga ‘

 

ta juya ahankali tana dora idonta akansa take taji wani k’ululu aranta ranta yai mugun b’aci da wannan bak’in toxali da tayi wannan shi ake kira da mugun gamo ………

 

 

 

 

_Coming Soon_

 

 

 

Hankalinta kwance take damun furarta tana “yan wakokinta ckn harshen fillanci

 

 

Saiji tayi Anrufe mata idanu ta baya

 

Ta tsaya cak! Da damun tana shakar kamshin turarenshi a tafin hannun nashi

 

Tasan ko waye ta haddace kamshinsa Abokin tane wato Abdul hamid wanda take kiransa da Abokin birni

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
 

Murmushi tayi tareda cewa “walh naganeka Abokin birni ne…

 

 

Yacire hannunsa daga fuskarta ahankali yana fara,a yadawo gabanta ya durkusa yana kallon kyakykyawar fuskarta

 

Ta ajiye kwanan shan robar datake damun takalleshi da mamaki tace “abokin birni yaushe ka dawo?

 

 

Yace yana dry “Yanxu yanxu muka shigo kauyen naku jaka kawai na jiye agidan gona nataho gunki.

See also  Hotunan Jaruma Maryam Yahaya

 

 

“Amma dai kai kadai kazo ko???

 

Ya girgixa kansa ya nuna bayanta yana fadin “kalli can kiga ‘

 

ta juya ahankali tana dora idonta akansa take taji wani k’ululu aranta ranta yai mugun b’aci da wannan bak’in toxali da tayi wannan shi ake kira da mugun gamo taki jinin

Taganshi takuma tsaneshi kamar yadda shima yatsaneta

 

 

 

Abdallah kenan yaro matashi dan kwalisa me ji da kansa me takama da arxikin da Allah yabaiwa ubansa gashi shi mutum ne marason son talaka akusa dashi yanada shariya gashi miskilin gaske

 

Cousing ne ga Abdulhakim wanda jininsu ya matukar haduwa very close suke tun suna yara suke kwana daki guda har yanzun da suka girma basu raba dakiba Halayyarsu ta bambanta don kuwa shi Abdulhakim mutum ne meson mutane bashida wata matsala ga wasa da dariya baida wulakanta jama.a

 

Abdallah yanada boyayyen halin da bai taba bari Abdul hakim ya ganoshiba wato shan giya wanda tun suna malesia yakoyi sha shida abokansa na sheke aya harda neman mata wanda aboye yakeyi bai taba bari Abdul din yaganeba don sigari kawai daya kamashi yanasha saida yayi wata uku bai masa magana ba shima dan Abdallan yayi kwantan bauna ya nuna masa cewar yadaina shane shiyasa ya sauko daga fushin dayai dashi

 

 

Abdul hakim yatsani mutum mai halin banxa balle me shaye shaye shiyasa bai taba yin abokiba sbd baya son tension

 

 

 

Dije ta hade girar sama data kasa takalli Abdul hakim tace “abokin birni me yasa kaxo min gunnan da wannan me bakin halin?

 

Abdul hakim yayi dry yace “haba khadija yaxakicewa d’an uwana me bakin hali dan Allah kada kisake aibata masa suna kinji.

 

 

Tace “amma kasan dai jinin mu bai haduba ko? Kasan baya sona yatsaneni gaskiya bana son nasake ganinsa..,Abdallah daya karaso gun yatseta da sauri “ke kaxamar yar kauye ba gunki naxoba kuma nima ba qaunar ganinki nake ba gun dan,uwana naxo

 

Ya nuna Abdul hakim “kai kuma ko kataso kazo muwuce muyi abinda yakawomu kokuma walh indauki mataki dan yanzu zanyiwa dadi waya inshirya maka sharri walh.

 

 

Abdallah yahade rai “kaga mallam banason rashin mutumci kabar gunnan ko muyi fada

 

 

“Mun dade bamuyiba dama gara muyin indai akan wannan bakauyiyar ce kuma kasani ba inda zan motsa walh kafara kafarka banza mara aji.

 

 

Abdulhakim yadawo da kallonsa gun dije da take hada kayanta zata bar gurin yahau bata hakuri dan yaga kuka takeyi

 

 

“Dakata khadija kiji nawane duka furar zanbiya ki koma gida ki huta kawai.

 

 

Tace ckn kuka “kabarshi kawai nagode ko iya cin zarafin dan,uwanka ya isheni ayau.

 

“Oh my god khadija banso ranki yabaci akan wannan inda sabofa yaci ace kinsaba,

 

 

Ta rike kugu takalli gefe tace “abokin birni yakamata kaima kabarni kamar yadda dan,uwanka yabukata tunda mutumci ne ajunanmu ba soyayyaba.

 

 

Yace “”naji amma kinsan Allah ne yahadamu bashi ba ballan tana yarabu kuma kinsan nayi sabo da shan furarki duk sanda naxo kauyen nan dan haka kizubomin aleda natafi da ita kokuma walh inkai kararki gun Addaji ince yau kinmin rowar furarki me ddi.

 

 

See also  Bafulatana Hausa Novel

Ta duka ahankali ta juye masa furar data gama damun aleda takulle tabashi

 

Yakarba yana cewa “nagode ga kudin.

 

 

Ta sunkuci kayanta tayi gaba bata kulashiba shida kudin nasa

 

 

Tsaki Abdallah yaja yace “banxa kaxami meshan kayan kaxamai kai dai walh kalar zaren ba kalar yadin bane.

 

 

Harara ya maka masa “kashiga hankalinka zan b’atar maka walh ina ruwanka cikinka ko nawa?

 

 

 

Abdallah yai gaba yana masa dryr mugunta

 

shikuma Abdulhakim yabi bayansa yanata yi masa mitar abinda yayiwa di

Koda suka isa Gidan gonar dadyn nasu kowa safgarsa yashiga ran Abdulhakim abace yake kokula Abdallah baiyiba na tsahon wasu awanni yana fushi dashi

 

Shiko Abdallan

Yanuna ko ajikinsa hakan saida yaga da gaske Abdul din yake kana yaje yasameshi awata yar rumfar shakatawa yaxauna akusa dashi yace “Abokina har yanzun fushi kake dani ko?

 

 

Abdul hakim yai biris dashi yaci gabama da karatun news paper dinsa

 

 

Abdallah yakwace news paper din yace “kai dan iska nizaka juyawa baya akan waccen yarinyar da bata kai takawo ba kana nufin har anxo lokacin da wata zata shiga tsakaninmu lallai kuma nan gaba bansan yazakaimin ba inkanunata amatsayin wacce zaka aura inna hana.

 

 

murmishi Abdulhakim yayi yace “kana bani mamaki Abdallah kanayin abinda bai cancantaba kuma ba halin gidanmu bane wannan wulakanta dan adam din da kakeyi sam momy da dady basu koyarmu hakanba sunbamu tarbiyya kuma sun nusarmu da gane cewa talaka da me kudi da dan kauye da dan burni duk daya yake agun ubangiji.

 

 

“Amma ai ba matsayinsu daya aduniya ba. Abdallah yafada da zafin rai da daga murya

 

 

“Kai kake ganin hakan kuma lamarin Allah baida wuya xai iya maida me kudi yadawo talaka haka zai maida talaka yadawo me kudi kokuma dan kauye ya dawo dan burni harma yafi dan burnin bude ido da iya mu,amula ta wayewa

 

 

 

“Walh karya kake duk inda dan kauye yaje baxai taba wayewa ba dole saiya xauna amatsayinsa kaidai kawai sbd yarinyar can nne yau kaxama me wa,azi

 

 

Dariyar maganar Abdallah taso sille masa amma saiya dake yace “to kaima fa asalinka dan kauyenne koka manta anan aka haifi mahaifin dady nan ne asalinmu dan dai duk mun rasa kakannin namune da sun rikeka agunsu.

 

 

Wani naushi yakawo masa dan jin haushin lafazinsa

 

Abdul hakim yagoce da sauri yana dariya

 

 

Shikenan suka shirya

 

 

aka shiga hira amma saida yatursasa Abdallah akan wai saisunje yabaiwa dije hakuri na yanda yasata kuka

 

 

Abdallah yaja tsaki yace “Allah yakiyaye inbaiwa sa,ar kanwata ta biyu hkr haba aiwalh ko za.a kasheni baka isa ba bakuma ta isaba sbd kana sonta saika bakanta min.

 

 

Abdallah yace “nifa babu soyayya atsakaninmu kawai amintace da haduwar jini.

 

 

 

Tsaki Abdallah yakara ja yace “hhhmmm kaji dashi duk yaran cikin gidanmu bakai aminta dasuba sai na kauye haba mutumina nafi kowa sanin halinka.

 

 

Abdulhakim yace “Amma dai kasan inada tunani bakamarka nakeba

 

 

Abdallah ya mike yabashi guri yana zaginsa “aikin banxa akwai mara hankali irinka dan,iskan kauye.

 

 

Da yammaci sakaliya Abdulhakim yashirya tsaf yatafi gidansu dije yadade akofar gidan kafin yasami dan Aike yaturashi gidan yayo masa sallama da ita

See also  Ni da Dalibata Hausa Novels 1 & 2

 

 

Bata d’au lokaciba tafito tana ganinshi ta hau dariya tana fadin “walh nadauka ko baxaka biyo bayaba dana kara fushi akan wanda nayi.

 

 

Abdulhakim yayi dry yace “au dama fushi kk da abokinki bai saniba?

 

 

Ta murguda baki tace “eh mana bayan agabanka dan shigegen can yagama cimin zarafi amma baka dake shiba koka rama min koda da wata kalma ne me zafi dashima zaiji haushi

 

 

Abdulhakim yace mata “khadija kinga narasa yadda zanyi da Abdallah akan yadaina mk hakan amma abinda naga yafi kawai inhar yaimin kiringa ramawa kada kidubeni kawai nina saki domin innafiye shigar mk zamu ringa samun sabani dashi

 

 

Ta gyada kanta tace “to shikenan aiko walh baxan taba raga masaba dama albarkacinka yakeci

 

Abdulhakim yace mata “shigarni cikin gidan ingaida Addaji.

 

 

Tace ” to muje.

 

 

 

har cikin dakin addaji takaishi suka gaisa ckn mutumci da Addajin sannan suka fito kofar gidan

 

 

Sunyi hirarsu ckn raha yabata janta da wasa da dari

 

Lallai wannan haduwar jini tanada ban mamaki

 

 

Zakuyi mamakin jin cewar sbd dije kawai Abdulhakim yake zuwa gidan gonar tasu

 

 

Toshi kuma Abdallah sbd wa yake xuwa knn?

 

 

Alh Mustafha hamshakin me kudine yana zaune da matarsa a unguwar shagari kwatas dake Zoo road

 

Matarsa daya mesuna hjy Samira mace me kirki da son jama.a kamar dai mijinta ga alkairi

 

 

Yaransu biyar aduniya banda uku da suka rasu

 

Aunty Maryam itace babba tana Auran wani tsohon dan,majalisa a jam,iyyar APC me kudine shima

 

Abdallah shine me binta shekararsa talatin da biyu Bashir shine na uku yana karatunsa a KUT wudil bording shi ba.a futarsa wajeba Shida kannansa mata Zannurat da Mubina ” yammatane kusan sa,annin juna shekara biyune tsiransu zannurace babba tana Nouthwest sai mubina data gama secondry dinta yanzun zata fara karatun gaba da sec.din

 

 

Mahaifin Abdulhakim shine Alh Mahmud kanin Alh mustafha ne Allah yai masa rasuwa tun Abdulhakim na yaro sukayi accident shida matarsa hjy shafa,atu suka rasu dama shikadai ne dasu daganan bayan rasuwarsu rikonsa yadawo hannun dan uwan baban nasa

 

 

Rikon tsakani da Allah yasamu agidan basa nuna bambanci akansa duk abinda akaiwa Abdallah shi xa.ai masa wani xubinma har nashi gatan yanafin na Abdallah dayake akwai dukiyarsa ma agun Alhajin gadonsa knn.

 

 

Abdulhakim yabaiwa Abdallah shekara uku Amma sai anfada dan Abdallah yafishi bargon jiki yanayinsu ba daya bane Abdulhakim dan jikine dashi shiko Abdallah kakkaurane

 

 

Abdallah da Abdulhakim kud da kud suke basu taba fda ba inba na wasaba kuma Abdallah yana bashi girmansa suna mutumta juna sosai wani baya zartas da wani abun saida shawarar dayansu

 

 

Zannurat tana matuqar son Abdulhakim Amma takasa gaya masa saidai alamu da take nuna masa amma yakasa fahimtarta

 

 

~~~~~

dijen kauye marainiyace Asalin iyayanta sun rasu itanma tun mahaifiyarta na haifarta ta rasu aranar mahaifinta kuma saida ta fara girma yarasu Rikonta na hannun yayarsa da suke uba daya dan baida kowa sai yaruwarsa da kaninsa akauye su biyu ciki daya shikuma uwarsa da ban amma sai in anfada kansu ahade yake

 

 

Addaji itace marikiyarta tanason dije sosai bata taba haihuwaba shiyasa tamaisheta tamkar ta cikinta fulanine su usul ma kuwa

 

 

 

Dije yarinyace me karancin shekaru amma tanada girman jiki shekararta goma sha shida amma saika zaci tayi 20

 

 

Sai intabuga sokonci zakagane yarinta natare da ita

 

 

Kyakykyawa sosai gashi har baya saidai ba gyara gata dason tayi gayun kuma akullum tanaso taga mutum dan gayu shiyasa Abdulhakim yake burgeta gashi tana burin taga taje birni tayi rayuwa acan saidai kuma batada kowa acan ta yaya knn zataje birnin ???

Yaushe burinki zai cika……?

 

 



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Yar fillo complete Hausa Novel]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

4 thoughts on “Yar fillo complete Hausa Novel”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top