Hausa Novels

Yar Gan Gan Hausa Novel Complete

Yar Gan Gan Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tags: yar gan gan

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM(da sunan mai rahma mai jinƙa)

 

 

1&2

 

 

“”””””””””””kuttt,lalle kai wannan dan iska ne,har mu zaka zo ka biyo hanyar da muka biyo , bayan yau kaga mune a layi,ina kallon ka har wani yana cema kasake hanya amma kaƙi, yau to inaga ajalinka ke kiranka, tunda kai dan yawa be ne,yanzu kaima zama yawwa”.

 

ya faɗa yana zaro sharɓeɓiya wukar dake kugunshi, wadda ake kira da (ƴar gindi).

 

shiko bawan Allah sai zazzare ido yake yana kifi-kifi dasu, ga zura ta wanke mishi fuska ganin basa da alamar rahma akan fuskar su.

 

 

juyawa nayi ina kare ma yan tsurarun mutane dake gurin kallo, wanda da alama duk cikin dabar tasu suke.domin dukkan su babu mai wata shigar Arziki.

 

idona ne ya sauka kan wata ƴar matashiyar budurwa wanda kallo daya zakayi mata kasan ba karamar mai kyau bace ajin farko dandai ta ɓata kanta da bin ƴan daba.

 

 

wani mugun kallo naga ta jefeni dashi ganin ina kallon ta ta,take na saukar da idona da sauri kasa gani wani mugun kwarjini da tayimin sosai fuskarta tayi kama da ta masu muggan aiki.

 

dauke idonta tayi daga kaina tana kallon wanda ke rike da wannan mutumin, wanda tun zaman ta gurin bata dago ta kalli kowa ba sai yazu.

 

 

suna hada ido da wanda ya rike wannan mutumin, take ya zuɓe kasa yana yi mata kirara, da alama itace Ogan su,

 

 

 

“kyeleshi ya tafi Arne”, abinda baji ta faɗa kennan tana mikewa daga inda take,

 

 

taku ta fara cikin tafiyarsu ta gayu, wani layi tabi take shima naga mutane na komawa gidaje da gudu,kara leka fuskar tan nayi, gain ta kara haɗe fuska ne ba bu zance mutumci , hakan yasa nima na kama kaina tun kafin tayi min rashin M.

 

wata mota ce naga ta biyo layin a dari uku da sittin (360) sosai gudun ya hadarma mutane unguwar ga gudun ƳAN GAN-GAN ga kuma na motar data kunno kai Unguwar.

 

 

wata ƴar Yarinya naga tana kiciniyar tsalaka ti-tin Unguwar ,tazo dai-dai tsakiyar titin sannan ta lura da motar da ta shararo da gudu, karin tayi wani yunƙuri ji kake.

 

 

kiiiiiiiiiiii,kuuuuuuu kichaaaaa kake ji

motar tayi sama da Yarinyar ta tular da ita chen gefe sosai hankalin mutane Unguwar ya yi kan Yarinyar, da gudu sukayi kan Yarinyar , mai motar kuwa ko niyyar tsayawa ma baiyi ba, gudu kawai yake tsulawa, sosai ran ƳAR-GAN-GAN ya ɓaci wani huci ta fara fitarwa mai zafin gaske kallon Arne naga tayi, ganin ya fige wani mashin dake kusa dasu yabi bayan motar da gudun bala’i shima, sosai abin ya bani mamaki, gani batace dashi komai ba amma yabi bayan motar.

 

sosai na lura da cewa bata cika yawa magana ba , amma daga ta kallesu sunsan mai take nufi.

 

 

kan Yarinyar da aka banke tayi, darewa naga mutanen gurin sunyi sun bata guri, isa muka karasayi gurin Yarinyar gani ko numfashi batayi sosai ne yasa ƳAR-GAN-GAN,daukarta da sauri tayi gurin wata mota data gani.an parker ta a gefen titin sosai motar ta tafi dani

ganin azababben kyau da take dashi.

 

 

handle din motar taja ga mamakin ta itama sai taga motar ta bude, boye mamakin ta tayi kawai ta shimfidar da Yarinyar sit din baya, gaban motar ta bude ganin wani mutum matashi Yaro kyakyawa zaune yana dan daddana waya ko ɗagowa baiyi ya kalle taba.

 

sosai tayi mamakin ganin mutum cikin motar domin batayi zaton akwai mutum cikin motar ba.

 

 

dago idanunshi ya yi ya watsasu cikin nata wani banzan kallo yake watsa mata.

 

“Masha Allah”, na furta cikin zuciya ta gani zalar kyan da yake dashi, sai da naji zuciyata ta buga, sosai na dauku da ganin wannan halittar.

 

 

wani mugun tsaki naji ya buga, dago idanunta tayi ta kalleshi jin ya yi mata abinda tafi tsana a duniya , tsorata nayi ganin yarda idanunta suka rine da baƙin ciki.

 

 

kullo motar shi ya yi yana watsa mata banzan kallo, sosai ta kara kullewa.

 

daya daga cikin Yaranta na gurin ta kalla ta nuna mishi motar tare da matsawa gefe , da karfi ya bude murfin motar da bala’i ya juyo ya dauka ko itace gani gansaƙyeƙen katon mutum baƙi sama kashi , yasa ya dan razana da yake namijin duniya ne sai bai bari razanar ta fito akan fuskarshi ba.

 

kare daure fuska ya yi tamau yana kallon mutumin, dakye ya iya furta , “lafiya malam”, yana kara hade gabas da yamma kudu da arewa, .

 

shima mutumin saida yasha jinin jikinshi ganin duk yarda Ogan su take cin daci to wannan Baban tane.

 

ɓaice komai ba illa nuna mishi bayan sit din motar shi daya yi.

 

kallo daya ya yiwa Yarinya dake shimfiɗe kamar gawa, ya kauda kanshi.

 

mutumin yace “mota zaka bamu mukaita Asibiti”.

 

jin yace haka yasa mutumin dan sassauta hade fuskar amma duk da haka fuskar hade take.

 

fita ya yi daga motar tare da dauka duk wani abu da zaiyi mishi Amfani .

 

waya naji tana ringing jim kadan naga ya kara wayar a kunnenshi yana magana kamar wanda akayiwa dole.

 

chen sai baga ya ajiye wayar boot din mota ya bude wata kujera ta Alfarma wadda ake iya karyata asa a cikin mota naga ya fiddo sai kuma, ya yi kasan wata bishiya ya aje tare da zama yadan lumshe idonshi.

 

dai-dai nan kuma naga Arne da wata Yarinya sun fito daga motar da aka bige Yarinyar , sosai Yarinyar take zazzagawa Arne ruwan bala’i tana cewa.

 

“kaidin banza zaka shamin gaban mota sannan ka kawoni nan gurin, Wallahi sai nasa a kashemin kai dan karamin….”

 

bata karasa magana ba tajin taɗiyeta tayi wata irin muguwar casus a faduwa,bata tantance a ina take ba taji saukar wasu tagwayen maruka masu a zabar zafi.

 

sosai ta gigice tarasa halin da take ciki jin azabar da bata taɓa jin irinta ba.

 

tashi tayi tana tanga-tagan cikin wata katuwar kwalbatin dake kusa dasu ta faɗa jikake, tunjummmm , ta faɗa cikin kwalbatin.

 

shiko mutumin da har yanzu bansan sunanshi, zaune yake har yanzu idanunshi a lumshe saidai yana ganin abinda duk sukeyi ta wutsiyar ido.

 

fisgo gashin dokin dake kanta ƳAR GAN GAN ,tayi tana ihu da kuruwa amma dashi ta jawota daga cikin kwalbatin kan titin ta jefar da ita taci gaba dayin ball , da ita sai ihu take tana neman dauki.

 

Arne ne ya ja motar da Yarinya take ya yi wani dan madai-daicin hospital dake Unguwar da……

 

muje zuwa

 

 

 

 

 

Name: [YAR GAN GAN HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Leave a Comment

error: Content is protected !!