Yar Gidan Deelu Hausa Novel Complete

Yar Gidan Deelu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Alhamdulillah Allah ya sake dawo dani ɗauke da sabon novel, a wannan karon nazo maku da sabon salo, dafatan zaku ƙarbesa kamar ko wane novel nawa, nagode*

 

*Allah kajiƙan iyaye na ka gafar ta masu ya Allah kayi masu rahma ka saka su a aljannar ka ta firdausi dasu da ‘yan uwa musulmi baki ɗaya amin ya Allah*

Shara rowa tayi da mugun gudun ta, kamar wata Balbela, ta faɗo cikin gidan kamar wata kububuwa, mutanen dake zazzaune a tsakiyar gidan suna a yukan su, suka ranta a cikin na kare, duk suka watse, suka shige a cikin ɗakunan dake a cikin gidan suka rurrufe ji kake gara ram.. Gam fam! duk ana rige_rigen rufewa, ita kuwa faɗar takeyi “kowa yayi ta kan sa jama’a babu lafiya! ”

 

 

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Duk wannan guje_gujen da akeyi ana neman gurin ɓoyo, mace, ɗaya ce, Zaune riƙe da baki tana bin kowa da ido ita batada alamar tashi tsaye ma, sai ma kallon ta da ta maida akan yarinyar data shigo cikin gidan a har gitse.

 

 

Ita kuwa yarinyar da gudu ta nufi gurin da wata mata ta yarda buta ta nemi gurin ɓuya, taje da mugun gudu ta ɗauki butar ta nufi rijiyar dake tsakiyar gidan ta janyo ruwa ta cika butatar ta afka a cikin bayi da gudu ta rufo ƙofar jin kake garam, ta rufo, sai kawai kaji fessss….. Fessss…. Ɓurrrrr….. Ɓurrr…. sai uban nishin ta ke tashi, tana faɗar “wai.. Wayyo kaka ta, Delu, kiya feni zan mutu ciki na zai fashe wayyo ni kai na, wai.. Wai.. “.

 

 

Kusan mintina biyar sai gata ta fito tana uwar zufa tayi dur ƙushe a ƙasa tana dafe da cikin ta, duk tabi ta jiƙe da zufa, sai zarar ido takeyi, can ta ɗago ido tana kallon faɗin gidan kawai ta tashi tsaye tayi jifa da butar, ganin duk yawan mutanen gidan babu kowa sai mace, ɗaya kawai ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya harda dafe ciki, dariyar taci gaba dayi ganin wasu na leƙowa ta jikin window da ‘yar kusuwar ƙofa gurin da ake saka key, aikuwa ta ƙarawa dariya yawa harda su faɗuwa ƙasa tana mulmula a ƙasa, harda hawaye,

 

 

 

Ta ce, “yeho..! Ni ‘Yarr gidan kaka ta..! Sai ni ‘yar gidan kaka Delu! Yarinya ‘yar amanar Delu! A taɓani Delu ta zaune mutum hahahhh, oh Allah! Naso a ce nima ina da ƙiba yau da na riƙa zaune mutane idan sun yi mani iskan ci! “.

See also  Naga ta kaina Hausa Novel Complete

 

 

Dafe kai tayi taci gaba da ɓaɓɓakar dariyar ta,. Sai kuma ta maida kallon ta akan wannan matar ta ce, “kai! Ni dama na sani, ke Kaka kowa zaiyi gudun ceton rayuwar sa, amman banda ke, ke ala dole ga jaruma, mai jarumta yo ko Kawu Ali fa yake ciwon ƙafa, yau yayi ta kan sa, har ya manta da cewar baya iya tashi ballema yayi tafiya, amman ya ɓuya amman ke kina nan zaune, to bari kiji garin nan dai babu lafiya dan yau hari aka kawo muna ruwan boma_bomai ne ke tashi, dan haka kema kiyi ta kanki”.

 

 

Tana ajiye aya. Kawai mutanen gidan duk suka fir fito tsakiyar gidan suna fasa uban ihu da kuwwa ce_kuwwace, tare da fara kwasar kaya masu goyo suna goye yaran su, masu ɗora Hannuwan su akan su, suna ɗorawa suna kuka, duk a firgice suke, sai sharce hawaye da majina suke, ita kuwa dariya take ka in da na in, babu ƙaƙƙautawa, kamar wata zarar riya.

 

 

Ai kuwa matar itama miye zatayi, ai sai dariya tana kallon mutanen gidan mazan su da mata yara da manya tana tafa hannu,

 

ta ce, “ikon Allah! Yau ni Delu ni kuwa nake kallon Ikon Allah ” ta riƙe haɓa tana dariya taci gaba da faɗar, “haba Al’jimma haba Ali haba Salisu, miye yasaka ne kuma han kalin ku yake dai_dai dana Ema ne wai? Yo ai kune mahaukatan ba ita ba, yo dan kunji tana doka maku uwar haukar ta, sai ku taya ta haukar harma kufita iya hauka cewar? Kaf duk faɗin ƙauyen nan kune mafi kusa da ita, yaci a ce halin ta cikin sa da bayan sa, duk kun san dashi, ba sai an baku tarihin halin ta ba, kaf ƙauyen nan waye bai san halin ta ba ne? To lallai kam kumfi mahaukaci iya hauka”.

 

 

Kaka Delu ta ci gaba da faɗar, “shegiyar gorar nan fa, a kullum da kalar tsiyar da take shukawa a garin nan ita da Indo da Meri waye zai ce bai san halin su ba, ai idan da ma karatu ne yaci a ce kun haddace, halinta, dan haka babu wani harin da aka kawo dan uban ki, Ima mike faruwa ne, ai ina ganin kamar kashi ne ya koro ki ko !? ”

 

 

Wata uwar dariyar ce ta sake bushewa da ita, ta , taso ta baro gurin da take wannan dariyar ta dawo a kusa da Kaka Delu ta zauna ta tsigare ɗan kwalin ta, ta turo shi gaban goshi ta ce, “eh! Zawo ne ya koro ni, kin fa san ance kowa ye yace duhu to baiji zawo ba, wallahi ai zawon nan shine harin da aka kawo domin kuwa bakiji yanda ciki na ke uban ƙugi, ba sai murɗawa yakeyi wallahi kin san tun daga gonar Mamman naje shan rake, aka fara wannan yaƙin da ruwan boma_bomai, a cikin ciki na, ji kike rugudu gududu, ram ram dage dagee, to tun daga can nake wannan gudun dan saura kaɗan na sake sa a wando hahhha,

See also  Prince Sapwan Hausa Novel

 

 

Kina jina ko Kaka, to shine fa mutane yan gulmar mugun abu masu baƙin bin kwa_kwaf ɗin tsiya suke tambaya ta, miye nake yiwa gudu, shine naga idan na tsaya basu amsa zan sake sa kawai na ke cewa dasu hari aka kawo kamar yanda na cewa mutanen gidan nan, gashi nasan a gidan nan a kwai magajiyar bayi, wadda koda yaushe tana bayi, safe da rana da dare, tana maya goma ko ishirin kullum, ni kuwa nasan idan na sami wani a cikin bayin nasan bazan iya zaman jira ba, dan zawon zai iya kubce mani a wando a sakani wahalar wankin kashi ban shirya ba, to shine nayi mata dubara irin ta *’YAR GIDAN Kaka DELU* to kunji yan abun yake”.

 

 

Kowa cike yake da haushin ta kamar su kashe ta sukeji, ita kuwa dariyar ta take yi ta ce, “Alhamdulillah idan zawo ya matse ka kayosa hankalin ka sai ya kwanta to kowa dai yaji duk abunda yake faruwa “.

 

 

Abun duka kaka Delu ta janyo ai kuwa da gudu tabar gidan kamar wata fil filwa, kamar walƙiya tabar gidan, kawu Ali sai alokacin ya tuno da ciwon ƙafar sa, a take ya zauna ya buɗe baki ya ce, “shigiyar yarinyar nan idan na kamata sai na ci uban ta wallahi shigiya mai suffar mayu! “.

 

 

Kowa sai da ya saki uwar dariya dan sai a lokacin ne suke tuno da asalin halin Ima, kowa abun dariya ya dawo yana basa, Al’jimma kuwa kawu Ali take yiwa dariyar irin gudun da yayi shida yake cewa da ita ko motsin kirki baya iya yi jin yakeyi ƙafar kamar ba’a jikin sa suke ba.

 

 

Ita kuwa tana fita bata tsaya ko ina ba sai rumfar da ta baro su Meri suna zaman jiran ta, tana zuwa ta zauna tana dariya take basu labarin abun da ya faru ai kuwa suka shiga taya ta dariya, Indo ke cewa, “wayyo Allah gudun kakale naso gani tabur_taɓur ke nan hahhh”.

See also  Ni da dan Jarida Hausa Novel

 

 

Meri ta ce, “wallahi kuwa ashe da mun biyo bayan ki da mun sami gani mar yaƙi dan ni biredin Mai shayi naso mu kwaso mu haɗo da kifin Iro mai mugun uban tsadar tsiya, hahhh”.

 

 

Dariya sukeyi, Ima ta ce, “yau dai sun tsira amman a kwai gobe, yan zun ku tashi muje mu kaiwa Kaka ta markaɗen ƙosai dan yau zamu koma ne, muyo cuwa cuwa gurin Iya mai Awara, kun fa san yajin ta ne da mai ya sakani zawo wallahi, kila Allah ya isa tayi muna, wai ai wallahi sai mun koma”.

 

 

Meri ta ta ce, “wallahi ke yajin da man sun raga maki nifa tun a jiya da dare na soma gudawa, na hana goggo bacci dan cewa nakeyi su yafe ni mutuwa zanyi “.

 

 

Dariya suka saka mata harda faɗuwa, tashi sukayi sukaje suka ɗauko markaɗen ƙosain, suna ajiyewa suka baro gidan suka nufi gurin tsokana inda Allah ya haɗasu da ɗan gidan Mai gari, da sauri Ima tasha gaban sa, ta ce, “ji mana Isihu kafa san irin yanda ƙawata take bala’in son ka kamar ta mutu, dan Allah ka yarda kawai muje musha biki kasan mu aikin mu a garin nan musha biki kawai”.

 

 

Cike da haushi ya ce, “Nifa ke nake so ba Lami ba, dan haka a shirye nake muyi Aure “.

 

 

Ai Ima da wani irin bala’in gudu tabar gurin tana ihu, “wallahi niba ‘yar iska bace sai na sanar wa Kaka Delu wallahi”

 

 

Irin yanda ta faɗa cikin gidan ta afka a cikin ɗakin Kaka ta fasa uban ihu ta ɗora Hannuwan ta akai kamar wadda ta rasa uwa da uba a lokaci ɗaya a take Kaka Delu ta saki tsintsiyar dake hannun ta, ta ce, “lafiya keda waye ne a garin nan eye!? ”

 

 

Buɗe bakin da zatayi ta ce, “ɗan gidan mai gari ne, zai lalata maki ni”.

 

 

Salati Kaka Delu ta saki, ta janyo mayafin ta ta yafa ta ce, muje muje, ni za’ayi wa fitsara yau ko ni ko Umaima ko mai garin muje”

 

 

Tafe suke Kaka Delu kamar zata tashi sama, ta nufi gidan mai gari hannun ta riƙe da na Ima.

 

 

 

 

*To yan uwa nadawo maku dashi baya ne saboda nasan wasu da yawa sun manta labarin sanadiyar ajiye sa da nayi adalilin rashin lafiyar danayi*

 

 

Dafatan zaku anshi wannan gyaran da labarin yanda ya kamata

 

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top