Yar Goni Hausa Novel Complete
ƳAR GONI
*FREE BOOK*
Na fara wannan Book
10 ga watan December
ƙarfe 3:00pm.
Ya Allah kasa yanda na fara lafiya kasa na gama lafiya, Ya Allah ka dafamin ta hanyar isar da saƙona zuwaga inda nake so yaje Ameen🤲
*Gajeran Labari ne*
STORY AND WRITTEN
BY
MRS IBRAHIM
Marubuciyar
Rayuwar Mariya:Free Book
Mugun Aboki:Free Book
Maryama:Free Book
Uban Mijina Zan Aura: Paid Book 200
AYISH YAR HAJIYA:Paid Book 300
AND NOW
YAR GONI
📚
*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
بسم للله الرحمن الرحيم
Page 37&38
………Bayan Sude’s ya koma gida Aliyu ya samu yana zaman jiransa, shima da sauri ya shirya kana suka nufi gidansu Asiya.
Ɓangaran Abba daga wajan Shopping ɗin Direct gida ya wuce yana zuwa ya shirya yayi wanka, ya zauna zaman jiransu Sude’s, Asiya kuwa tana ɗaki anci kwalliya kamar za’aje gasar kyau sosai ta haɗu tasha doguwar riga na Shadda wanda tasha zubi kayan sun mata kyau sosai kamar ban ita ba.
Hon ɗin Motar su Sude’s ne yasa Asiya fitowa daga ɗaki shima Abba jin hon ɗin da sauri ya tura Saleem akan ya tarosu ya kaiku ɗakin baƙi, da sauri Saleem ya fita bayan sun shigo ya ƙarasa wajansu suka gaisa rakiya ya musu zuwa ɗakin baƙin Abba wow zo kuga Sude’s yanda yasha manya kaya tamkar mutumim kirki haka shima Aliyu sunyi kyau sosai, zama sukayi kana Saleem ya bar wajan, daga Sude’s har Aliyu sunyi mamakin ganin gidansu Asiya domin yanda suke tunani har ya wuce haka, Kalle-Kallen da Sude’s yake a ɗakinne ya hango ƙatan Hoton Abba Asiya dake manne a wajan”Na Shiga Uku Aliyu mai zan gani haka?kardai wannan shine Mahaifin Asiya?” Ya faɗa yana cire hular kansa “Lafiya Sude’s kake tambayar ko shine ma Mahaifinta?kuma ni da kake tambayana ba yanzu muka zo gidan da kaiba taya zan san shine ko ba Shiba” “to lalle akwai matsala dole mubar wajan nan yanzu” cewar Sude’s “ban gane mubar wajan nan ba taya kake tunani zamu tafi, nifa ban gane abinda kake nufi ba ya kamata kamin bayani?” cewar Aliyu nan Sudes ya kwashe labarin abinda ya faru ya faɗawa Aliyu “Innalillahi Sude’s ashe har yanzu baka daina wannan ɗan iskan halin naka ba?Ace Babban mutum kamar wannan ka bugeshi sanna kace masa Sorry ba tare da magana mai daɗi ba? ko da ace ba shiba bai kamata kayi hakanba, amma yanzu aiga irin abinda ka kajo, kuma wallahi ya Tabbat daga yau babu kai babu Asiya” “Ah Haba Aliyu daina wannan maganar, wallahi Asiya kamar na sameta, dan haka kota halin yaya wallahi saina cimma burina akanta, kuma nasan cewa ba wani ganeni zaiyi ba tunda bai kalleni sosai ba” ya faɗa yana share gumin dake zubowa daga fuskansa “to wallahi ni baza’ayi wannan abun kurya dani ba dan haka mu haɗu agida” cewar Aliyu dake maganar yana shirin fita, da sauri Sude’s ya jawo shi kana Yace”dan girman Allah ka tsaya ayi komai da kai wallahi idan kamin haka ba kamin adalci ba” cewar Sude’s dake maganar kamar zaiyi kuka.
Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta
-
Hausa Novel AppApp
-
Hariji By oum Apnan
-
Bariki na Fito
-
Nakasa ba Kasawa ba ce
-
Siradin Rayuwa
-
Bororoji Hausa novel
-
Life Partner Hausa Novel
-
Heedayah Hausa Novel Complete
-
Duniya ta Amna
-
Zaman Hostel Complete
-
Mahabeer Hausa Novel
-
Matar Makaho
-
Banida Gata
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
-
Kyawuna Jarabta ta
-
Jiddatul khair
-
Wacece Ni Hausa Novel
-
Ahali Daya Hausa Novel
-
Abraham Hausa Novel
Suna cikin maganar saiga Sallamar Saleem ya kawo musu abin taɓaw, da sauri suka zauna suna Murmushi, yana ajewa ya fita kana Abba ya shigo sallama yayi suka amsa amma gaba ɗaya kansu yana ƙasa, gaisawa sukayi nan Abba ya fara tambayar waje Sude’s ɗin da sauri Aliyu ya nunashi, Alokacin Sude’s ji yayi kamar yayi ihu domin yau kashinsa ya bushe, ɗagowa kansa yayi kana sukayi ido huɗu da Abba, kallonsa Abba ya fara yi domin Tabbas ya gane shi amma nuna masa yayi kamar bai gane shiba, Murmushi Abba yayi kana shima yayi murmushi nan dai suka fara magana Abba yace ya bashi Number Mahaifin sana domin za suyi magana, da sauri Sude’s ya haɗa number Aliyu ya bashi, nan suka yi Sallama da Abba yace zai turo musu Asiyan.
Yana fita Sude’s yasa dariya”Haba Aliyu dama na faɗa maka wallahi bazai gane niba, yanzu Shikenan an wuce matsalar” ya faɗa suna tafawa.
Abba yana barin wajan ya shiga palounr ya zauna domin ya rasa mai yake masa daɗi “Yanzu wannan ɗan iskan Yaron shi Asiya take so?” ya faɗa cikin damuwa, nan ya fara ƙwalawa Ammi kira da sauri ta fito “Abban Asiya baƙin har sun tafi ne?” “je ki ƙira Asiya zasu gaisa kafin su tafi” shine iya abinda Abba ya faɗa kana ya wuce ɗaki, Ammi kuwa ɗakin Asiya taje kana ta sameta kwance saman gado”kije baƙin naki zasu tafi” daga haka Ammi ba tace komai ba ta fita, Asiya kuwa cikin farin ciki ta ɗauki Hijab ɗinta har ƙasa ta feshe jikinta da turare kana ta fito, tana fitowa sukayi karo da Ya Saleem ƙamshin turaren jikinta saida yasa ya lumshe ido”Am dan Allah Ya Saleem kayi haƙuri wallahi ban kula da kai a wajan ba” ta faɗa kanta aƙasa Murmushi yayi kana yace”taya zaki kula dani a wajan bayan kina sauri kije ki ga Sudes” kallon sa tayi tace” Haba Ya Saleem banda zolaya Allah ba haka bane, yanzu dai bari naje idan na dawo mayi magana”, ta faɗa tana barin wajan, da kallo Saleem ya bita domin harga Allah soyayyar Asiya kullum ƙaruwa take aransa.
Asiya kuwa da sallama ta shigar wajan su Sude’s yana ganin shigowarta aa tashi da sauri yaje ya rumgumeta, ita ma rumgumarshi tayi domin ko kunyar Aliyu basu jiba, zama sukayi waje ɗaya kana suka gaisa da Aliyu bayan sun gaisa ya fita ya basu waje, Sude’s kwa da kallo yake bin Asiya kana ya janyota ya fara kissing ɗinta, ganin yana wuce gona da irin yasa ta masa magana suka kama wata firar.
“Abban Asiya wai maike faruwane dan Allah ka faɗamin koda wata matsala ne?” cewar Ammi dake magana cikin damuwa nan Abba ya kwashe labarin yanda sukayi da Sude’s a wajan Shopping ya faɗa mata aƙarshe Yace”Hajiya ban nuna masa na gane shiba sannan ban nuna masa bazan bashi auran Ƴata ba amma tabbas Asiya bata dace da wannan Yaron ba, domin tarbiyansu ba ɗaya bane”
numfashi Ammi taja kana tace” Gaskiya Abban Asiya ya kamata a ɗauki mataki amma yanzu ka bari zanyi magana da Asiyan naji mai zata ce” haka dai suka tsaida magana akan za tayiwa Asiya magana.
Asiya kuwa Ita da Sude’s gaba ɗaya sun shagala ganin sun jima yasa Aliyu ya ƙirashi awaya akan ya zo su tafi”Baby zan tafi badan na gaji da ganinki ba sai dan babu yanda na iya gaskiya zanyi kewarki zan tafi da tunani falll raina” ya faɗa yana shafa kanta.
Asiya kuwa dake kwance akan kafaɗarsa tace”nima haka Sude’s zanyi kewarka amma yanzu ai komai ya kusa zama dai-dai tunda maganar aure ta shigo danni gaskiya na fiso ayi auran nan cikin ƙanƙanin lokaci” haka da sukai ta maganar kana Sude’s ya bata tsaraban da ya kawo mata na kayan lashe-lashe harda na maye, bayan ta amsa suka fito daga ɗakin rakiya ta musu har wajan mota kana suka shiga saida suka fita daga gate ɗin kana ta shigo ciki, tana Shiga ɗakinta ta wuce kana ta cire Hijab ɗin ta zauna tana duba abinda ya kawo mata……..✍🏻
Kuyi haƙuri fan’s kwana biyu bakwa jina wallahi mun ɗan samu matsalan rashin mutane amma in sha Allah yanzu zaku dinga jina😍.
Comment And share👏🏻
Mrs Ibrahim ce😍


Name: | [Yar Goni Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi

Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram

Leave a Comment