Hausa Novels

Yar Gudullen Sarki Hausa Novel

Yar Gudullen Sarki Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Page = 1

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Ajiyar Zuciya Mai martaba sarki Oumar yaja yana me kallon fuskar matarsa Da take zaune akusa dashi wacce ta dire zancenta tana fargabar Amsar da Sarkin Zai bata

 

a hankali Takawa ya bude baki cikin Maganarsa ta Nutsuwa yace mata”Fulani ZINARU kinfi kowa sanin Halina kuma kinsanni sosai akan magana Daya danake bana canxawa idan nayita,dan haka inaso murufe wannan zance haka kafin wani yashigo yajita.

 

Fulani Zinaru ta gyara zama tana murmusawa tace”Ranka ya dade bawai nayi ja akan batunka bane,ina ganin tunda acikin mu ba yara, kuma munada hangen nesa sannan muna da tunani me zai hana bazamu bi maganar farko ba wacce na kawo ta a farkon Zuwan yarinyar nan gidan nan,banyi tunanin zaka iya canza wannan batun ba,to amma kuma tunda yanxun kace ba haka ba walh nafara zargin ka fara son yarinyar nan ne tunda har bazaka yarda ayi nesa da ita agidannan ba sbd gudun matsala nan gaba.

 

girgixa kai sarki yahauyi kana yace”Kiyi Hkr Zinaru bawai naqi ta taki ba ne, Ba kuma wai nafara son yarinyar bane, A,A ina hangen aje a bata ashirin ne azo goma bata gyaru ba,abinda yafi ma ki taimaka ki daure kibani kwana guda nayi shawara Inba haka ba zuciya ta zata shiga damuwa akan wannan batun kema kinsani.

 

ita dai Fulani shiru tayi tanajinsa da Alamun ranta bai mata dadi ba na rashin amincewa da shawararta da yayi.

 

lura da hakan da Takawa yayi sai ya gyara xama Ya jingina bayansa da jikin bango ya dora hannunsa na hagu akan Babban Tuntun dake kusa dashi kana hannunsa na Dama ya dorasu akan hannayen Gimbiyar Tasa yana mata wani kallo me wahalar fassaruwa kallo na Na Rarrashi da banbaki fuskarsa dauke da fara,a yace” Zinaru kece ni, nine ke, munyi Aure tun bamusan meye Auren ba,iyayen mu Aminan juna ne,Munso juna kamar mu hadiye juna har kawo yau da muke zaunen anan dake bazan taba cewa ga ranar da muka sami sab’ani dake ko akaji kanmu ba ko Abokiyar zama danai miki ni kika taya murna kuma kika mana Nasihar xaman Aure nida ita, to nikuwa me zan ce dake,haba kincancanta a zaman uwargida a gidana bana haufi ina Alfahari dake Fulani,gashi kin haifa min Yaron da nake Alfahari dashi Yarima D’ane daya gaji Mahaifiyarsa a kyawawan halaye To nikuwa me zance dake akowane fanni kina kyautatamin kina zama Lfy da abokiyar zamanki duk Munanan Halayenta kin iya zama da Ita wallahi Zinaru banajin akwai abinda zaki nema agareni inqi yi miki saidai kawai inaso kizama me yimin Uzuri sannan ki zamo me yafiya agareni Nasan a wannan karon daurewa zuciyarki kawai kikai na Gagarumin Laifin Dana Tafka miki Na Auro karamar yarinyar cikina, Amma kika Qi nunan Damuwarki kuma nasan kin shiga Damuwar hakan, Abin farin cikinma kin riqemin Sirrin daya zamto shine mafi kyawu a zamantakewar mu Sannan….. dakatar dashi din da Gimbiya tayi shiya bashi damar Gimtse bakinsa tare da zuba mata Manyan idanuwansa yana jiran tacewarta.

 

A hankali ta furta” To wai duk wannan Yabo da kakemin da kambama maganganun na Meye ne,?

 

Murmushi yasakeyi yana fadin” Najin dadin zama dake ne, dole ne na yabeki akoina Gimbiya,’Yar Sarki Jikar Sarki matar Sarki kuma wataran mahaifiyar Sarki.

 

tayi murmushi ta sadda kanta kasa tana murza zoben gwal din dake yatsanta.

 

Mai martaba Oumar yaci gaba da cewa”Nauyinki nakeji a yau kin bukaci abu agurina ban amince miki da yinsa ba,inaso ne nayi wani Nazari akai duk da bakya bani shawarar banza Amma kiyimin Uzuri Gimbiya Nasan ba kin kawo shawara akan Yarinyar nan ne dan bakya son ta ba Nasan akwai abinda kike hange kamar yanda nima akwai abinda nake hange agaba inhar Muka sake aka fitar da yarinyar nan Agidan nan duk da ba kowa yasan Matsayinta ba sai ni saike Sai Danginta dana rabota dasu.

 

A sanyaye ta daqo kanta ashe hawaye take zubdawa tahau gogesu da bayan hannayenta.

 

da saurinsa ya miko mata tissue yana rawar jiki yana goge mata yana fadin “Hankalina yatashi kicire damuwa aranki gimbiya banyi Tunanin Ranki ya baci haka ba.na Aminta da abinda kikazo min Dashi ko banason abu zanyi bana son tashin hankalinki Zinaru bantaba ganin hawayenki na tsartuwa ba sai yau akan abinda baikai yakawo ba to kiyi hkr Zan rabu da JIDDAH Rabuwa ta har abada, ba ma Nesa da ita zanyi kamar yanda kike bukata ba A’A Rabuwar Aure yakamata nayi da ita ko don na faranta miki rai Matata….

 

da sauri ta katseshi da cewa”A’a Ranka ya dade karkayi haka, kar kaja min laifi gurin ubangiji Ka janye maganar Rabuwa nan kada Allah ya tuhumeni aran lahira,Nikam na janye batun da naxo maka dashi, Yarinyar nan Amana take agunka Hannunka da Nata na a cikin na Mahaifinta yana baka amanarta ya koma ga Mahaliccinsa baikamata kuma ace ka karya alqawari tunkafin Tafiya tayi Nisa ba,Ni dai dama shawarar dana kawo ayi nesa da ita akaita ajiya wani wajen ko akaita karatu nesa sbd mutanen kusa damu ‘Yan tsegumi da kuma masu surutu shiyasa na Kawo maka tawa shawarar da kake ganin kamar na takuraka ne….dakatar ta yayi da sauri yana fadin”Ba takura a duk maganar da zakizo min da Ita Gimbiya na Amince Zanyi abinda kikace Amma kibani kwana biyu inyi shawarar yanda zan da ita karatun ko Inkaita ajiya wani wajen kafin zuwa lokacin da zata girman yayi hakan? Kin bani Lokacin?

 

tahau gyada masa kai Tana kokarin Mikewa zata fita

 

ya kamo hannayenta yadawo da ita ta zauna Dab dashi ya kalleta ido cikin ido yace”Baki yarda dani bane Gimbiya,?

 

tace”Na dade da yarda dakai,indai kace zakayi abu to zakayin.

 

ya gyada kai yana fadin”to banga alamar a yau kinyi amanna da zancena ba ko Rantse miki zanyi?

 

tayi saurin girgiza kanta

 

yace”To so nake ki saki Ranki bana so agane akwai damuwa atare dake.

 

ta murmusa kana ta ja hancinsa tana goga nata akan hancin nasa tana murmushi.

 

yaji dadin hakan har cikin ransa dama wannan Al’adar tace indai tana cikin farin ciki ko tana jin shauki akansa saitayi masa hakan

 

shikuma hannu bibbiyu yake sawa ya rungume kayarsa.

 

******

Fitar Fulani Zinaru a Dakin Takawa da kamar Mintina goma yasaka waya ya kira nambar Galadima yace masa Yana nemansa da Gaggawa a yanxun.

 

Tagumi Ya zuba yana sakawa da Kwancewa akan wannan batu tabbas tunda ya furtawa Gimbiyarsa Maganar Fita da Jiddah daga gidan to dole ne yacika mata wannan Alqawarin to amma yasan akwai matsala akwai kuma cutuwa ga Yarinyar gashi tafara sabo dashi wannan shi ake kira Rana zafi Inuwa quna domin dole zaiwa zuciyarsa bawai dan yaso ba kam.

 

Sallamar Galadima a lokacin shiya katse masa zuzzurfan Tunanin Daya lula.

 

Galadima yashigo yasami guri ya zauna kana ya mika Gaisuwarsa ga Takawa kana yace”Ranka ya dade gani nazo fatan lafiya?

 

tashi takawa yayi daga kishingidar da yake kana ya hau gyada kansa yana fadin”Galadima lafiya ba lafiya ba, domin wani gagarumin Abune ya tasomin wanda narigada na Gudanar dashi atun farko bansamu na sanar maka da maganar ba ina kallonta a sirrin da ni kadai zan shanyeshi sai matata da nake ganin itace babban sirrina ta wannan bangaren tunda itace zata rikemin ajiyar da nazo mata da ita cikin kwanciyar hankali sai gashi ansamu sabani ta Nan.

 

Sarki Oumar yayi shiru na ‘yan mintina kana yaci gaba da fadin”Wato labari zan baka takaitacce wanda nasan kasan da tsohuwar amintarmu da margayi Kwamared Mamuda Marafa na Can Jahar Kaduna ko?

 

Galadima yahau gyada kai yana fadin “Nasani sosai,ban manta ba, Allah dai yajikansa da Gafara.

 

“Amin, cewar sarki Oumar kana yaci gaba da cewa”Abinda ban sanar maka ba shine a ranar da zai Rasun nan ina tare dashi kansa na kan cinyata yana makyarkyatar nan yana cikin wani hali na rashin lafiya rai kwakwai mutu kwakai Yarinyarsa Daya jal na kusa damu tana kuka na ganin halin da mahaifinta ke ciki margayi ya kamo hannayenta ya kamo nawa ya hadesu guri daya yace min yana so intaimaka in Auri Jiddah ‘yarsa sbd wasu kyawawan Manufofin dake ransa akan hakan tuntuni yaso ace Yarona Yarima ya baiwa Aurenta to amma sai yafasa a ranar ya canza tunani da hangen nine magidancin da zanfi rike masa Yarinya da amana, adan hakan aranar ya danqamin amanarta yace kuma yana so intaimaka masa inkuma taimaki tsohuwar amintarmu insa adaura min Aure da Jiddah aranar Sadakar ukunsa ko bakwansa dan yana ji ajikinsa bazai tashi ba.

 

Ina kuka yarinyar nan na kuka haka na Aminta da maganarsa nayi masa wannan Alqawarin sannan yabarwa Dan’uwansa da suke uba daya wasiccin a cika masa wannan Alqawarin.

 

hakan kuwa akai aranar bai kara kwana a duniyar ba yace ga garin kunan.

 

dama ban bar garin ba munsauka a masauki nida me dakina da mukaje dubiyar tashi tare Munshiga tashin hankali kuwa sosai na rashin mutumin kwarai.

 

kwana biyu da maganarsa kuwa wannan Dan uwa nashi yatada min maganar da akai agabansa na Auren jiddah da Mahaifinta yabar wasicci.

 

na nuna masa tsoron hakan kada yin hakan ya haifar da samun matsala agaba saboda karancin shekarun yarinyar Bata kai shekara goma ba sannan gata da wayon tsiya agabanta akai maganar bana so ayi kuma azo mutunci na ya zube a idon Al’umar garina.

 

Malam Labaran Dan,uwan Mahaifin nata shiya kara karfafamin guiwa da bani shawarar in amince kawai ayi sai arufe maganar kada inbari kowa yasan wacece agurin sai matsayin ‘Yar riko ko da Matana kada in nunawa shima yai Alqawarin zai rike amanar sirrin nan.

 

haka na Aminta da wannan magana ba wai don raina yaso ba.

 

aka daura wannan Aure a lokacin da aka gama yin sadakar Uku na Kwamared Mamuda wanda hankalina yai mugun tashi bayan gama daurin Aure domin wani abu ne ya faru da aka kira min Jiddah yayan Mahaifin nata ya kawota guna da muka kadaita ni dashi yakawota har gabana ya nuna mata ni amatsayin wanda zai tafi da ita yace mata tasa aranta tayi sabon Baba komai take so ta tambayeni zan mata kada ta damu nima zan dauketa amatsayin ‘Yar cikina don ni Dan uwan babanta ne.

 

budar bakin yarinyar shine”to ai banaji babana yace masa ya Aureni ba kafin ya mutu,to kuma ya fasa Auren nawa ne da zai zama sabon Babana,? ai naga dai baba ba,a taba hadashi da miji ko?

 

kowannenmu saida ya girgiza da kalamin yarinyar sbd indai ta fahimta to zancen ayi abu a sirri ya rushe.

 

take Malam Labaran yace mata “Ke ai an fasa daura miki auren dashi shawara kawai aka yanke akan kibishi ku zauna tare amatsayin uba da ‘ya kinga tunda Sarki ne shi ba saikawai kema kidawo ‘Yar Sarki ba.😃 Take kuwa Yarinyar taita murna harda tsallenta tana fadin “Yeeehhh Shikenan Nazama Jiddah Yar Sarki..

 

ta fita aguje tana fadin ta zama ‘Yar sarki dolene ma ta bini masarauta

 

saida mukai dariya da kalaminta

 

kawun nata yace” Yaro yaro ne kaji fa shirmenta ta ma mance da mutuwar mahaifinta ita yanzun kuma murnarta zata zamo ‘Yar sarki lallai dole ne ka zamo me kaffa kaffa da wannan magana ka boyeta sosai acikin Ranka don kada wataran ta gano

 

Na gyada masa kai ina amanna da maganarsa

 

kuma ko da Na koma masauki da yarinyar bayan tayi sallama da kowa nata nazowa da Gimbiya Zinaru da ita suna hada idanu jininsu ya hadu ta fada jikinta tana murnar ganinta wai ita a murnarta fa tayi sabuwar uwa don dama tana cikin Maraicin Mahaifiyarta ne.

 

Ita Zinaru ma Tausayin yarinyar ne yakamata take tajata jikinta ta rumgume tana gaya mata ita ma tasamu ‘ya zata riketa amana.

 

to bayan mun kebe da zinaru adaren da zamu wayi gari mutaho sai nake gaya mata komai na abinda ya faru tsakanina da Yarinyar da yanda akai komai.

 

ba qaramin girgiza tayi ba jikinta yai sanyi takasa cewa komai.

 

dakyar ta magantu tace min kawai”ina tsoron wani abu.

 

Nayi nayi ta gayamin me take tsoro taqi gayamin tace dai agaba zan gane.

 

da kanta tacemin tana so aboye wannan maganar bata so kowa yaji.

 

nayi murmushi nace mata”Nafita muradin hakan.

 

to tunda muka dawo gidannan Jiddah na Hannun Zinaru tana mata rikon Amana da son juna da sukeyi amma fa zinaru na cikin tsoron wani abu da har kawo yanzun da mukai wata guda da zama da yarinyar nan zinaru taqi gayamin wane abune wannan da take tsoronsa agaba kawai dai yau ta tashi da dagamin hankalin wai lallai tana son infita da Jiddah inkaita wani waje,har yanxun jikinta na bata wani abu agaba tana tsoron abinda takeji ya faru acikin gidan tana gudun tashin hankalin da Ba,asaka masa Rana tafison wai in kaita karatu nesa na tsayin wasu shekaru ko inkaita ajiya ta zauna agabansu wasu can nesa da garinnan a cikin mutanen arzikina nikuma Galadima nakasa aminta da wannan batu da taxo min dashi shine kaima nakeso kazo kaji sannan kabani taka shawarar inji sbd kaina a kulle yake.

 

 

shiru na tsahon lokaci galadima yayi yana ta jinjina wannan labari kana ya gyara zama yana fadin”Zancen gaskiya Ranka ya dade banga laifinka ba sam,ka zama jajirtacce akan maganar nan dai na kuma tausayawa yarinyar domin a yanxun rayuwarta na kan digirgire bata san komai akan zancen ba duk ba zata sami wani zunubi na Aure ba inta karya dokarsa,tunda akwai yarinta sosai atare da ita,saidai fa a yanzun tarbiyyarku kadai ita take bukata ba ta wani waje ba,domin inhar tayi nesa dakai za.a sami matsala zata iya yin soyayya da wani baka sani ba,kuma idan ta riqa bata kusa dakai nan ma za.a sami matsaltsalu na abubuwa da dama domin zancen akaita karatu ma waje bata taso ba me hankali ma ya yakare a kasar waje,bare mara aure hhhuumm ina ganin ayi hakuri dai abarta a nan din kaci gaba da lallaba me dakin naka har ta sakko ta barta anan din ka bata baki sosai inma Alqawarin bazaka taba kebewa da yarinyar ba ma zakai mata daidai ne dan asami masalaha ne Allah bazai kamaka da laifin komai ba,kuma nima in Allah ya yarda bazan taba daga maganar nan ga kowa ba.

 

Sarki Oumar yahau gyada kai yana fadin”To Nagode Sosai Galadima zanyi kuma abinda kace sbd nima abinda kake hange shi nahango shiyasa nayi mata tirjiya amma nasan yanda zan shawo kan Gimbiya harta hkr din nagode.

 

nan sukai sallama da Galadima yatafi yabar Maimartaba Yasake shiga wani tunanin.

 

********

Zaune take a kan kujera 3siter da kuyangu guda uku akusa da ita kowanne da aikin da yake mata

 

daya kuyangar tana mata firfita dayar kuma tana bare mata ayaba tana miko mata dayar kuma yankan Qumba(farce) take mata.

 

A guje Jiddah ta shigo tana fadin”Ummah! Ummanah!!

 

murmushi Gimbiya Zinaru tayi tana kallon shigowar Jiddah a sukwane ta fada kanta tana fadin “wayyo Ummana ashe kina nan inata nemanki tundazu nazaci ma kina gurin Abbana.

 

Gimbiya Zinaru tace mata”Kai, Jiddahna karki Karyamin Cinya mana.

 

Dariya Jiddah tayi tace”To Umma bani kadai gareki ba inma na karya ai babu me hawanta dai dama nice ai.

 

Gimbiya Zinaru ta zuba mata ido tana Qaunar yarinyar sbd wayonta da kaifiyyarta ga kyau kamar balarabiya ga farin jini har ji take aranta inama itace mahaifiyarta amma ta gefe guda fa shaidan na son ya ribaceta akan jiddah so take tayi nesa da Ita sbd kada suzo su shaqu da juna gaba kuma ta zama abokiyar kishinta inta girma ta zama cikakkiyar mace da sarki zai mayarta matar Aurensa ta Hakika.

 

“Ummah kinsan me? Jiddah ta katseta da fadin hakan

 

G.Zinaru tace”Saikin fada zan sani Jiddah ta.

 

Gyara zama jiddah tayi tana fadin”Walh yau Abbana ya Canzamin Suna me Dadi,kinsan wane Suna ne,?

 

G.Zinaru ta girgiza kanta

 

Jiddah taci gaba da fadin”yace daga Yau Nakoma GUDALIYARSA….

 

gaban Umman saida ya fadi to me Takawa yake nufi da radawa Jiddah Sunan nan.? jitayi jiddahr tace “Umma na Abbana fa yace Gudaliya yana Nufin Daya tilo tal dayake ji da ita,kinga Kenan nazama ‘Yar GUDULLEN SARKI. tunda Gudaliyar sace.

 

umman ta kalli Kuyangin gurin da suke mata hidima ta dakatar dasu tareda basu izinin fita

 

dukkansu suka fice amma fa kowacce suna maimaita sunan GUDULLEN SARKI a cikin Ransu,mamaki sukeyi da har yarinyar da akace ‘yar Dan uwansace ta sami shiga haka agun sarkin da har wai yau tasami canjin suna agunsa sun san dai yana da Yaro daya jal daya haifa aduniya amma shi bai saka masa wannan suna ba sai ‘Yar Riko.

 

Gyara zama Umman Tayi tace”To My Dota Nima daga Yau zan ringa gaya miki sunan ‘Yar Gudullen sarki tunda naga kina so ko.

 

Da fara’arta tace”To Umma ba Dole in so ba,Abba nane fa ya saka min sunan dan Allah kici gaba da gaya min zanji dadi.

 

dariya Umman tayi kana tace”To yayi, amma yakamata kije sashin Auntynki Iyami itama kisanar mata wannan suna me dadi da Abban naki yasaka miki itama ta ringa gaya mk.

 

maqe kafada Jiddah tayi ta sauya fuska tana fadin”tab nidai bazanje inda take ba walh bata da kirki ba sona take ba,nima kuma walh batayimin ba kawai ki kyaleta idan Takawa yasa akayi shela aka sanar zataji acan.

 

kama baki Umman tayi tace”Au ashe abin babba ne kenan har shela zai saka ayi a gari kowa yasan cewar kin zama Gudaliyarsa kenan.

 

Daga mata gira tayi tana dariya kana tace”kin manta Umma Gudullen sarki fa nace miki ba Gudaliya ba.

 

umman tace”To ai duk Daya ne suna sunan da aka kira mutum dashi wanda ake so kenan daya tamkar da dubu.

 

Jiddah tace”Eh mana,to Amma umma wai yaushe Yaya Yariman zai dawo ne,nifa na matsu naganshi saboda bai sanniba nima sai a hoto kinga nake ganinsa.

 

Umman tace”ai yasan da labarinki yana yawan cewa agaidaki idan yayo waya.

 

Ta kama baki tace”oh amma umma baki taba gaya min ba ko ki hadamu awayar.

 

Umman tace”aduk lokacin daya bugo bakya kusa ne kina dakinki ko kina gun Abbanki.

 

Jiddah tace”To wai Umma Yaya yarima yana da Fara,a a zahiri a gaske,kamar yanda nake ganin yana dariya da murmushi a wasu hotunan nashi?

 

Umman ta gaji da surutun nata saita daga mata kai kawai.

 

nan ma gyara zama ta sakeyi tace”Umma dan Allah kibani labari akan halayen yaya sbd insan abinda yakeso da wanda baya so sbd kada idan ya dawo in kuskure inbata masa rai ya dakeni.

 

dariya Umman tayi tace”Ai yayanki bazai taba dukan ki ba shi din me sanyin haline nasan idan yadawo jininku zai hadu sosai

 

“to yaushe zai dawo ne wai,ni walh nagaji aita magana daya taki karewa.

 

dariya Umman tasakeyi tace “kwantar da hankalinki yakusa gama karatun yadawo saura shekara daya da rabi.

 

kama baki Jiddah tayi tace”Huuu tab amma fa za.a dade kenan bai dawo ba tab ainima karatun zanyi me tsayi irin nashi Likita yake karanta ko umma?

 

zaune ta tashi daga kishingidar da tayi ta qura mata idanu kana tace”Yarinyata kina son kiyi karatu me tsayi kema?

 

ta gyada ma umman kai

 

Umman tace”Kinason kiyi karatu a kasar waje tare da Jajayen fata ?

 

nan ma gyada kai tayi tana fara,a

 

Gimbiya Zinaru tahau gyada kai tace”to tashi kije abinki zanje yanzun nasami takawa nagaya masa gara akaiki kiyi secondry da ta gaba da secondryn acan ki kwashi kamar shekaru goma sha biyar acan abinki kina karatu ko,?

 

A maimakon ta amsa mata sai tahau murna da tsalle abinta dan umman ta faranta mata rai,itama tana son zuwa kasar wajen nan dai so take taji me akeji amma saidai kuma ai bata son rabuwa da Abba da umman.

 

ta gimtse murnar tana fadin “to saidai kuma umman idan natafi ai zamu rabu bazamu ringa ganin juna akai akai ba gashi yayana zai dawo ya kenan.?

 

umman tace”indai kin aminta zakije to ni zan ringa zuwar miki akusa zankuma saka yaya Yariman naki yaringa ziyartarki indai kin amince da tafiyar bakida matsala zakiyta ganinmu kinji.

 

saita saki ranta tace”to na amince zanje,kuma in Abban yaqi bari ki kirani inje in masa kuka zaifi bari inyaga hawaye na.

 

To kawai umman tace

 

Jiddah ta gama surutun ta ta tashi ta tafi tabar Umman da zancen zuci

 

lallai dole ne ma ta sami me martaba ta taka masa burki akan yanda yake samun dama yake sakewa yai hira da yarinyar nan Any how,akwai abubuwan da take hange tabbas saitasaka ido sosai bazataso aji kunya ba.

 

murmushi tayi tuna yanda lokaci kalilan taga burinta zai cika na nesanta juna da zasui da jiddah tabbas mafitar data kawo ko bai aminta ba tasan yarinyar tunda tanaso zata iya masa bore don yabarta gashi kuma yana mugun sonta Yar lele ce kuma ta dawo ‘Yar Gudulle wato Gudaliyarsa kenan…..

 

 

muje zuwa fans wannan na Musamman ne Kuma na Dabanne acikin Buks dina zaku nishadantu zaku fadakantu Sai naga comment dinku.

 

luv you all my fans💋

Leave a Comment