Littafin Yar hisba Hausa Novel
Littafin Yar hisba Hausa Novel
9/7/2021
FREE PAGE1
Tana sauka daga Adaidaita sahu ta nufi ofishin Hizba na ƙaramar hukumar TSOKUMBO da ke jahar KADABO, Fuskarta lilliɓe take da niƙafi ko ƙwayar idanunta ba’a gani.
Kai tsaye ta wuce ciki, mai gadi da hankalinsa baya wajen ya fara kiranta “Ke! Ke!!” Amma ko juyowa ba ta yi ba tayi gaba. Jin takun sahunsa a bayanta yasa ta cake, kafin ya furta komai ta ɗage niƙaf ɗin fuskarta, Suna haɗa ido ya haɗiyi wani busasshen yawu yace “Jeki” Kai tsaye ta shige ciki, kan bencin da masu ƙara ko ƙorafi suke ta zauna, tana ƙara nazartar yanayin wajen a gabanta Shugaban ya shiga ofishinsa ya zauna.
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels Pdf
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
Masinjansa ne ya shiga da sauri riƙe da wasu takardu, a ƙalla sai da ya kwashe kusan minti goma sannan ya fito, Matar da ke gefenta yace “Ku shiga” da sauri kuwa suka shige ciki ita da wata matashiyar yarinya mai goyo, basu wani jima ba suka fito, ɗan jim ta yi ko za a ce ta shiga ta ji shiru, kawai sai ta miƙe ta nufi bakin ofishin.
Cikin siririyar muryarta tayi sallama “Assalamu Alaikum” da sauri Kwamanda da ke waya ya juyo, da hannu ya nuna mata Kujerar zama, ta zauna sannan ta buɗe jakarta ta zaro wasu takardu ta ɗorasu a kan teburin da ke gaban Kwamanda, sannan ta koma inda ta taso ta zauna.
Hakan yayi daidai da kammala wayarshi, “Wa’alaikumussalam mene ne ya ke tafe dake?” Takardun gabansa ta nuna masa sannan tace “Allah ya gafarta Malam aiki na zo nema.”
“Wa yace miki muna ɗaukar sababbon ma’aikata?”
Cikin sassanyar muryarta tace “Ba wanda ya faɗa min, na zo a ɗaukeni aikin sakai ne bana buƙatar wani albashi ko wani tagomashi, zan yi domin Allah.”
Fuskarshi ya ƙara ɗaurewa kamar ko yaushe sannan yace “To dama mu ai aikin Allah muke yi, ko ana bamu wani abu to ihsani ne, sannan mudai ba mu da buƙata a halin yanzu, sai ki tara gaba, ko ki nemi wani aikin ina ganin zaifi.
Niƙaf ɗinta ta ɗage fuskarta ta bayyana, kyakkyawace ajin farko kuma fara tas, tanada manyan ido mai ɗauke da dogon baƙin gashi, tana do dogon hanci mai tudu da ya dace da fuskarta mai matsakaicin faɗi.
Ɗago idon da Kwamanda zai yi suka haɗa ido, bai son lokacin da wayar hannunshi ta zame ba, “Lahaula wala ƙuwwata illa billah” ya furta a fili, a zuciyarsa kuwa cewa ya ke ta yaya ma zan yarda mu ɗau wannan aiki anan, ai barin irin waɗannan matan a wuri haɗari ne mai girman gaske…
Miƙewa tsaye tayi ta tattara takardunta ta tura jaka, ssnnan tace “Akaramakallah zan wuce yanzu sai haɗuwa ta biyu, tunda na biyo ta ƙa’ida ban sami fa’ida ba Insha Allahu zan karya ƙa’idar kuma na sami fa’idar, mu haɗu a babban hedkwata.”
Cikin sassarfa ta fice daga ofis ɗin, idanunta na tsiyayar da hawaye, da yake da niƙaf bata damu da share hawayenba, tana samun adaidaita sahu ta haye ba tare da ta faɗa masa inda za ta je ba. Allah ya gani ina son aikin HIZBAR nan ba don komai ba, sai don na bawa addinina gudummawa da ƙarfina da aljihuna, amma sai gashi ana neman yi min sakiyar da ba ruwa, a fili tace “Yaya Falmata” murmushi ta saki tunowa da ƴar uwarta mai ƙaunarta… Mai adaidaita ne ya katse mata tunani yace “Hajiya ina muka nufa ne?” “Zoo road” kai tsaye ya juya kan babur ɗin suka ɗau hanya.
Da ƙafa ta ƙarasa gidan, mukulli ta fitar ta buɗe ta shiga, tun daga tsakar gida ta zare niƙab, hijabinta da ƙatuwar doguwar rigar da ke jikinta. Sanye take da riga mara hannu sai wando iya ƙauri(3 quater)
masha Allah kamar yanda take a fuska kyakkyawa, haka mafa a zubi da halittar jiki sai son barka.
Tana shiga ɗakin ta zare ribon ɗin da ta ɗaure gashinta da shi, zubowa yayi har kan kafaɗarta, ta cire kayan ta shiga wanka.
Tana fitowa ta zura riga mara nauyi ta tada sallah, sai da ta idar da sallah ta nufi kicin, tsaki ta ja ganin ba wani abinci. Kawai sai ta haɗa shayi ta ɗau biredi a kicin ɗin ta sha, sannan ta miƙe ta koma ɗakinta ta ɗau wayarta ta kira Yayarta Falmata, tana ɗagawa tace “Assalamu Alaikum Yayata”
“Wa’alaikumussalam ƳAR HIZBA kin yini lafiya ya su Baba?” Cikin shagwaɓa tace “Haba Yaya kema tsokanar tawa za ki yi, mu bar wannan ɗazu naje ofishin ƙaramar hukumar Tsokumbo amma wai suka koroni wai basa buƙatar Ma’aikata ko da na sa kai ne. Ni gaskiya Yaya…”
Katseta ta yi tace “A’a bana son rigima Baby kefa har yanzu jinki ki ke kamar ta goye ko? Duk ke kika jawo komai tun farko sai da nace miki zan yiwa Yayanki magana ya sama miki aiki, amma ki kayi kunnen uwar shegu ke a’a sai aikin Hizba. Amma ba komai Insha Allahu zuwa sati mai zuwa kin zama cikakkiyar Ƴar Hizba.”
Cikin zaƙuwa tace “Alhamdulillali! wayyo daɗi, na gode Yayata Allah ya barki da Yayana.” Murmushi Yaya Falmata ta yi tace “Kinfi ƙarfin haka ƴar uwata, na so ace kina kusa dani a ganina za ki fi samun kulawa, ina tausayinki Baby amma kin dage kinfi son zama a Kadabo, Allah ya kare mini ke a duk inda kike.”
Ba ta jira amsar Baby ba ta katse kiran hawaye na bin kuncinta, a ɓangaren Baby ma hawayen take, na tausayin Yayarta babu irin masifar da Yaya Falmata ba ta sha ba don kawai ta inganta rayuwarta, me za tayi ta biyata “Addu’a” ta furta a fili, lokaci guda ta miƙe don ɗora girki kafin Mahaifinta ya dawo.
BAYAN SATI ƊAYA
A cikin sati ɗaya a ka samawa Baby aikin Hizba, har yunifom (unifoam) ta ɗinka, wani irin shauƙi ta ke ji tamkar duk wani burinta ya cika, tsabar ɗoki gani tayi Litinin ta ƙi saurin zuwa.
Ranar Litin tun asiba ta tashi, sai da tayi musu abin kari ta gyare gidan sannan taci abinci ta shiga wanka.
Tana fitowa ta ɗau mayukanta ta shafa, ta goga turaren hammata kaɗan sannan ta saka rigarta mara hannu (armless) da wando iya ƙauri sannan ta ɗora doguwar rigarta a kai. Ribon tasa ta ɗaure dogon gashinta da ya sauka har kafaɗarta, zare ribom ɗin tayi tace “Dole sai da basaja da iya taku”
a gefe kusa da kunnen damanta ta ɗaure gashin , sannan ta fice zuwa ɗakin Mahaifinsu.
Sai da tayi sallama ya amsa, sannan ta shiga ta zauna a gefe ɗaya tace “Baba ina kwana? Ya jikin naka” murmushi yayi yace “Lafiya ƙalau Uwata ba za ki bari na fara amsa gaisuwar ba, ko duk ɗokin fara aiki ne?”
Kanta a ƙasa tace “Baba ka samin albarka, a yau zan fara aiki.” A take idanunshi suka kaɗa suka yi ja, sai da ya mayar da ƙwallarshi sannan yace “A kullum albarka na biye da ke Uwata, ina roƙon Allah yasa ki fara wannan aikin a sa’a, Allah ya tsareki ya kare ki daga dukkan abinƙi, sharrin mutum sharrin aljan sharrin ƙarfe Allah ya tsareki ya baki nasara ya ɗora ki a kan maƙiya.” Cikin sanyin jiki tace “Amin Babana na gode Allah ya ja kwana.” “Ameen” ya furta yana goge hawayen daya zubo masa don kar ta gani.
Da sauri ta fice daga gidan bayan ta sanya tabarau da takunkumin hanci da baki, sannan tasa niƙaf ɗinta a jaka ta fice da sauri. Tana fita ta sami Adaidaita sahu ta hau suka nufi Babbar Hedikwatar Hizba da ke ƙaramar hukumar NIRBI, tana bashi kuɗin ta nufi gate ɗin.
Ganin Mai gadin tsoho ne ya sa ta ɗan russuna tace “Baba ina kwana?” “Lafiya ƙalau ƴata ina katin shedarki(ID Card)?”
“Baba ai ni sabuwar ɗauka ce yau zan karɓa.” Bai tsawaita magana ba yace “Shige” Cike da ƙarfin gwiwa ta nufi ciki ranta ƙal kamar farar takarda.
Tana zuwa ofishin Babban Kwamanda na Jihar ta tambaya, ana nuna mata ta nufi can.
Bayan ta gaisheshi tace “Akaramakallah Yayana ne ya turoni.” Da sauri ya ɗago yace “Ok kece Honourable ya turo, ai munyi magana da shi ta waya.” Ɗan dube dube yayi sannan ya zaro ƙaramin kati ya bata yace “Ga katin shaidar aikinki nan, sai kisa hoto kiyi laminashan, Allah yasa ki fara a sa’a.” “Ameen” ta amsa kanta a ƙasa, “Ki tashi ki tafi ofishin Mata ƴan uwanki, haƙiƙa kin zo a sa’a don anjima kaɗan ƙarfe goma na safe 10:00am muna da taron tattaunawa.” Godiya ta masa ta miƙe ta fita cike da jin daɗi.
A bakin ƙofa suka kusa yin karo da wani mutum, haƙuri ta bashi ta tsugunna don ta ɗauko masa bironsa da ya faɗi, sai tabaran idonta ya faɗi , bata mayar ba ta miƙe tace “Kayi haƙuri ga bironka…” ganin bai karɓa ba yasa ta ɗago kanta, wa zata gani Ƙaramin Kwamandar Ofishin TSAKUMBO da ta fara neman aiki a gunsa. Bakinsa har rawa yake yace “Ke…ke..”
YES MY FANS KU NUNA MIN ƘAUNAR DA KUKE MIN TA YIN TURURUWA WAJEN BIYAN KUƊIN KARATUN WANNAN LITTAFI NA GODE
ALLAH YA GAFARTAWA IYAYENMU
MUM AMNASH
Name: | [Littafin Yar hisba Hausa Novel] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Leave a Comment