Yar maye Hausa Novel Complete

Yar maye Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*’YAR MAYE*

 

 

 

*Mallakar*

 

 

 

*Zainab Muhammad*

 

*(Indian Girl)*

 

 

 

 

 

*Wannan littafina kuɗine 300 kacal zaki biya ki karanta cikin farin ciki da annushuwa a tuntuɓeni ta wannan number dan biya 07063452697 ko jin ƙarin bayani*

 

 

 

 

 

 

 

*Bunus page*

 

 

 

*1*

 

 

 

Wani ƙaton mashaya ne na masu kuɗi wanda ya gaji da haɗu manyan mutane suke ziyartar wajan domin ba kayan ƙaramin kuɗi a wajan sai masu tsada.

 

Wata ash ɗin motace ta danno kai cikin mashayar a haukace,motar ta gaji da haɗuwa ba kaɗan ba saboda ta tsaru.

 

Cikin motar kuwa wata haɗaɗɗiyar big lady ce wacce ta gaji da haɗuwa ga kyau ga diri a uwa uba nera wanda daka ganta kasan nera ta gaji da kuka a tare da ita.

 

Tsayawa faɗar tsantsar kyanta da dirinta ma ɓata lokacine dimin ka daɗe baka gama ba.

 

Kyakykyawar ƙafarta fara wadda take tamkar ta jaririrai tsaɓar kyau da shaini tayi jan ƙunshi wanda ya sake haska ƙafar,daga can kuma ta sako gaba ɗaya jikinta ta fito.

 

Tana sanye cikin wasu arnan riga da wanda masu kyau da tsada hannunta riƙe da pos da wayoyi guda biyu, rigar ta matuƙar kama jikinta wanda hakan ya fito da ilahirin siffar ƙirjinta koma ya bayyana,wandan ma ya kamata sosai.

 

Kai tsaye cikin mashayar ta nufa wanda wasu ado ki walwali da sheƙi a wajan,tana shiga ta sami kujera ta zauna tare da ɗora jakar akan table ɗin dake gabanta.

 

Ma’aikacin wajan ya iso wajanta da sauri yana tambaya.

 

“Hajiya sannu da zuwa me za’a kawo maki”

 

“Ka kawo min duk wani nauyin abun maye wanda zai fitar dani daga hayyacina”

 

Ta faɗi haka tare da dafe kanta da hannunta.

 

Ya amsa da “An gama Hajiya”

 

Ya koma inda ya fito inda,bai jima ba sai gashi ya dawo da kwando a hannunsa ɗauke da kayan maye kala-kala.

 

Yace”Hajiya gashi”

 

Tace”Nawa ne duka kuɗin?”

 

Ya zaro ido da,Cewa”Hajiya duka da tsada fa?”

 

Cikin ɗan ɗaga murya Tace”Na tambayeka tsadar su? Kuɗin su na tambaya”

 

Ya ɗan sosa kai,Yace”Dubu hamsin 50 Hajiya”

 

Taja wani dogon tsaki tare da zuge jakarta ta bashi kuɗin.

 

Ya ƙarɓa ya wuce yana wai wayenta.

 

Haka ta dinga ɗaukan kowacce kwalba tana ɗiɗɗikewa kamar mara hankaki har sai da ta sha kwalba biyar kuma gasu masu ƙarfin gaske.

 

Kanta taji ya sara idanunta sun fara ganin dishi-dishi take duk ta sauya ta koma *YAR MAYE* miƙewa tai ba tare da ta ɗau sauran ba ta ɗauki jakarta ta fice daga wajan.

 

Motar ta ta nufa ta shiga tare da fafararta ta bar wajan.

 

Gudu take kamar ta tashi sama da taimakon Allah ta isa gida.

 

Ƙaton gidane bani da gida ba ya gaji da haɗuwa da tsaruwa tsabar girmansa ka yini kana tafi baka ga ƙarshensa ba saboda girma.

 

Horn tayi mai gadi ya buɗe mata get bata jira ya gama buɗewa ba ta afka ciki da sauri mai gadin ya matsa.

 

Tana yin paking ta fito ta nufi cikin gidan tana layi da tangaɗi.

 

Falone guda uku zaka wuce sannan ka shiga babban falon gidan daga nan kuma sai manya-manyan ɗakuna da banɗakinsu a ciki sun zagaye fakon sai kitchen da denning abin abin sha’awa,daga nan kuma sai wata ƙofa da zata sadaka da matattakalar bene wanda idan ka hau zaka ga ƙarshen haɗuwa falone wanda yafi na ƙasahaɗuwa da ɗakuna da kitchen sai wata ƙofa da zata sadaka da ƙorido.

 

Wannan kenan.

 

Bayan ta wuce duk falukan ta shiga babban falon.

 

Wata babbar hajiyace zaune akan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun ɗakin,sanye take cikin wani dandatsetsan leshi mai matuƙar kyau da tsada.

See also  Rauf Aregbesola and Tinubu Are they fighting

 

Wayace maƙale a a kunnanta wanda alama ya nuna waya take,da sauri ta miƙe ganin shigowarta cikin wani hali.

 

“Afaf mene haka? Me yake samunki eyye”

 

Hajiya Nafisa ta faɗi haka cikin tashin hankali.

 

Afaf ta ɗan yi murmushi irin na ƴan maye cikin muryar mayen,Tace”Mammy me kika gani?”

 

Mammy Tace”Afaf me kike so ki zama eyye? Me kike so rayuwar ki ta zama kina so ki ɓata rawarki da tsalle ko?”

 

Haɗe rai Afaf tayi sannan.

 

Tace”Mammy bacci nake ji mayi magana idan na tashi”

 

Tana gama faɗar haka bata jira abin da Mammy za tace ba tai ciki abinta.

 

Mammy ta bita da ido tare da yin kalar tausayi da fuskarta,komawa tai ta zauna jabar akan kujera tare da zabga uban tagumi.

 

Ita kuwa Afaf ɗakinta wanda ya gaji da haɗuwa ta shiga,komai na ɗakin pink an red ne ya yi matuƙar kyau.

 

Faɗawa kan gadon tayi tare da lumshe kyawawan idanunta,take wani wahalallan bacci ya kwasheta.

 

Wannan kenan.

 

*Washe gari*

 

A hankali ta buɗe lumshashshun idanunta tare da bin jikinta da kallon taga shigarta ta jiyace da au bata canja ba ashe ta faɗa a ranta.

 

A hankali ta sauko daga kan gadon ta cire kayan jikinta tare da nufar toilet,ta daɗe tana wanka kafin ta fito ɗaure da tawol da wani kuma a hannunta tana tsane kyakykyawan gashinta mai tsananin shawa da baƙi.

 

Gaban mirror ta nufa ta zauna akan kujerar tana kallon kanta,itama kanta wannan shu’umin kyan nata yana bata tsoro.

 

Lation ta shafa a duk ilahirin jikinta sannan ta miƙe ta nufi wordrob ɗinta wanda yake danƙare da kaya nasu kyau da tsada.

 

Kallo ta shiga bin su da shi can ta ɗauko wasu riga da siket masu kyau rigar ta net ce sket ɗin kuma mai tsaga.

 

Ta saka ƙaf albarkatun ƙrijinta sun bayyana ta cikin rigar ba abin da ba a gani,sannan ta ɗaure kanta da ribos mai kayu da kyan gani gashinta ya zuba a bayanta ta ɗauki wayoyinta ta fito zuwa falo inda ta tabbatar Mammy na can.

 

Tafiya take cikin takunta mai ɗaukan hankali.

 

Mammy dake zaune a falon kan kujera taci ado bana wasa ba tana kallon tashar new na labarai.

 

“Hy Mammy fatan kin tashi lafiya?”

 

Afaf ta faɗa lokacin data iso tsakiyar falon inda Mammy take.

 

Mammy ta ɗaga kai ta kalleta sannan.

 

Tace”Afaf zauna za muyi magana”

 

Afaf ta kalli wayarta sannan ta kalli Mammy,Tace”Mammy lokaci fa yana ƙurewa gashi ina da lectures na safe”

 

“Maganar da za muyi fa tafi wannan lectures mayin manci”

 

Mammy ta faɗa tana kallon Afaf.

 

Afaf ta nemi hannun kujera ta zauna sannan.

 

Tace”Is ok Mammy ina sauraranki”

 

Mammy ta sauke ajiyar zuciya,Tace”Hmmm! Afaf abu na farko da zan fara tambayarki shine da wannan kayan zaki fita yanzu?”

 

Ɗan yatsina fuska Afaf tayi tana kallon jikinta kafin,Tace”Me ya sami kayan jikin nawa kuma Mammy?”

 

Mammy ta dafe kanta,Tace”Ok ke baki ganin tsirara kike kenan to wallahi idan har ni na haifeki ba zaki fita da waɗan nan kayan ba,sannan kuma da wannan mummunar ɗabi’ar da kika ɗaukarwa kanki kika zama *YAR MAYE*”

 

Ta ɗaga kai ta kalli Mammy ita ba ma kalmar da Mammy ta faɗa na ƴ*YAR MAYE* ne ya dameta ba illah da Mammy ta rantse kan ba zata fita da kayan jikinta ba to ai ita bata ga aibunsu ba.

 

“Ki tashi kije ki canza kuma atamfa zaki sa ba ƙananan kaya ba”

 

Taji muryar Mammy a tsawace ta faɗi haka.

 

Miƴewa tai ta tafi tana bubbuga ƙafa ta koma ɗakinta,sai da ta ɗan jima kafin ta ɗauko wata atamfa riga da sket suma dai ga su nan dai ɗinki tamkar tsirarar amma yafi wan can.

 

Sawa tayi cikin naƙin ciki ta ɗauko wani yalolan mayafi ta ɗora akan gashinta ta fito,ko kallon inda Mammy take bata sake yi ba ta fice.

 

See also  Bakar Sakayya Hausa novel complete

Wajan in da motocinta suke ta nufa ta shiga wadda da alama sabuwace kyakykyawa da ita,kunnawa tai tare da bata wuta ta fice daga get ɗin.

 

Shi kuwa mai gadi dama tuni ya wangale get ya matsa,tana fita ya rufe ya koma yana mata fatan shiriya.

 

Bata tsaya a ko ina ba sai babbar university ɗin dake garin abuja ta ƴaƴan manya,inda ta saba yin paking ta nufa tai paking motar ta sannan ta fito.

 

Duk mutanan dake wajan suka bita da kallon mamaƙi ganin yai wai Afaf ce ta saka atamfa wasu har da ma magana ƙasa-ƙasa dan suna shakkarta.

 

“Se babbar yarinya ƴar gidan babban mutum”

 

Wata budurwa wacce kamaninta sun nuna itama ƴar hannuce a ɓangaran shaye-sheye da kuma wasu ɓoyayyun sirri wanda ban san mene ba.

 

Rungeme Afaf tayi tana daɗa mannewa a jikinta sakamakon jin tausasan ƙirjin Afaf ɗin a jikinta.

 

Dariya Afaf ta ɗanyi da,Cewa”Suby ya gida”

 

Suby Tace”Lafiya ya yaufa kin matuƙar burgeni ba ƙarya”

 

Afaf ta ya tsina fuska Tace”Mtsssss wallahi yawane ai wai Mammy ta tilasta na saka bayan ta san bana ra’ayin waɗannan kayan”

 

Feedy ce ta karasu ta katse masu maganar tana mai yiwa Afaf kirari.

 

Afaf tai juyi tana fari da ido.

 

Feedy Tace”To mu sami wajan zama ko”

 

Ba musu suka ƙarasa wajan wasu kujerun roba suka zauna suna cigaba da hirar su.

 

Suby ta kai hannu kan ƙirjin Afaf kafin,Tace”Gaskiya waɗannan suna tsonan ido fa”

 

Afaf ta harareta da,Cewa”Kuma sun fi ƙarfinki wallahi”

 

Fedy tai dariya,Tace”Au Afaf har da saurin shiga masallaci,to nima fa sun daɗe suna tsone nawa ido”

 

Wani dogwan tsaki Afaf taja sannan.

 

Tace”Daɗina daku duk ƴan iskane ku to ni dai kwalelan ku”

 

Suby Tace”Ai wallahi Feedy Afaf tawace ni kaɗai bakya da kaso a wajanta”

 

Feedy Tace”A ina ta zama taki to ai Afaf tana dina ce wallahi kuma ni zan mora”

 

Nan suka fara ca-car baki wanda hakan yasa Afaf ta miƙe tsam ta bar musu wajan,kai tsaye ajin da suke ɗaukan lecures ta nufa.

 

Yadda taji ajin ya yi tsit ya tabbatar mata da akwai malami bata tsaya kallin ko waye ba tai cikin ajin kai tsaye.

 

“Keee!”

 

Taji muryar malamin ta doki dodon kunnanta,bata juyo ba taci gaba da tafi dan samin wajan jama.

 

Ya sake Cewa”Ke ba dake nake ba”

 

Da sauri wata ta taɓata,Tace”Babbar yarinya dake fa yake”

 

A hankali Afaf ta tsaya tare da ɗan juyowa,Tace”My name is Rahma Abdullahi Mai duniya amma ana kirana Afaf ko Babbar yarinya”

 

Malamin duk da ya san wane Abdullahi mai duniya,sai ya kalleta cike da izza shima.

 

Yace”Ban tambayeki wacece keba domin ba ruwana da wane ubanki,wayace ki shigon aji bayan na fara lectute?”

 

Afaf taji zafin maganarsa sosai,sanna ko ba komai ai ya dizgata a gana studient.

 

Ita ta kalleshi cikin izzar,Tace”Ohooo! ya yi,yo tsaya kaji Afaf bata tambayar izinin shigowa lectures idan har tai rayin saurara”

 

Tana gama faɗar haka ta nemi waje ta zauna bata ko sake kallonsa ba.

 

Zuciyar malamin tayi zafi sosai dan haka bai sake tanka mata ba ya ɗauki kayan aikinsa ya fice.

 

Nan ƴan class suka dinga kallon Afaf a ran su suna cewa ai ita ta cuce su,amma basa da damar faɗa dan haka duk suka miƙe suka fice.

 

Tana zaune tana danne-danne a waya sai ga su Suby sun shigo sau ɗaya ta kalle su ta ɗauke kai ta mayar kan wayarta.

 

“Babbar yarinya me ya faru naga ƴan class sun fita suna ta surutu?”

 

Feedy ce ta faɗi haka.

 

Ba tai magana ba sannan bata ɗago kai ba.

 

Suby Tace”Feedy kema fa kin san Babbar yarinya bata bada labari kuma bata mai-mai cen magana”

 

Feedy Tace”Hakane kuma fa”

 

“Mai abin sha a jakarsa ya ban”

 

Suja ji Afaf ta faɗi haka.

 

Suby Tace”Ni dai wallahi babu”

 

Ita kuma Feedy ta zuge jakarta ta fito da ita kwalba guda ta miƙa mata.

 

Ɗaga kai tai ta fara kwankwaɗa ba tare da ta tsaya ba har sai da ta shanye tass.

See also  Raina kama hausa novel complete

 

Bata sake komawa ta kan su ba ta ɗauki jakarta ta fice daga class ɗin,kai tsaye motarta ta shiga ta kunna ta bar makaranta gaba ɗaya ta nufi gida.

 

 

 

 

 

 

 

 

**

 

Kai tsaye yana fita daga class ɗin office ya nufa ya ajiye kayan hannunsa ya nemi kujera ya zauna yana tunanin wannan fitsararriyar yarinyar wani har da faɗar ko ita wacece,ga shi tayi shiga ta marasa kunya.

 

“Zan yi maganin fitsararki Afaf”

 

Ya faɗa yana mai buga benci.

 

Amjad kenan matashin saurayi mai ji da ilmi ɗan masu kuɗi (nace tofa kenan kwaryar sama na dukan ta ƙasa) ya yi karatu mai zurfi wanda da kansa ya zaɓi zama lecturing a wannan makaranta,wannan shine ranarsa na farko a makaranta wanda kuma shine yai gamo da Afaf mara kunya.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Amjad Hafeez shine sunan sa ɗa na uku a wajan iyayensa Alhji Hafeez Faruq da Hajiya Salma,ƴaƴa biyar suka haifa a duniya Yaya Hadiza itace babba tana aure a cemaron da yaranta sannan Yaya Faruq mai sunan kakansu yana da aure da yaranshi suna zaune a london,sannan sai shi Amjad (Muhammad) yana da shekara 27 watan sa ɗaya da dawowa daga india.

 

Babanaa yana da kuɗi domin ɗan kasuwane.

 

Wannan kenan.

 

 

 

 

 

 

**

 

Tana isa gida bayan tai paking motarta ta nufi ɗakinta a sannnan ta fara jin zuciyarta ta fara washewa game da ɓacin ran da take.

 

Tan shiga tai wurgi da wayoyin da jakarta akan gado itama ta faɗa jaɓar,tunanin abin da ya faru a makarantar take kafin ta ɗau alwashi a ranta.

 

Dake ta shawu yasa tana cikin tunanin bacci ya ɗauketa mata daɗi,a cikin baccin ne tai mafarki wai gata a wani ruɓaɓɓan gida na ƙasa gidan talakawa ga wasu mutane da bata san su waye ba.

 

A firgice ta farka saboda wannan mafarki da tai ai ba abin so bane kamarta ace gata gidan ƴasa na talakawa ina.

 

Jiki a saluɓe ta miƙe ta shiga toilet tai wanka sannan ta saka wasu best da wando ta koma ta zauna bakin gado tare da kunna tv plasma ɗin dake ɗaki.

 

Kai tsaye wata tasha ta kai ana waƙa da rawar disko kiɗan yai mata daɗi tana ji tana gyaɗa kai daga haka ta miƴe itama ta fara rawar.

 

Afaf tayi nisa da rawarta Mammy ta turo ƙofa ganin Afaf tana wannan yasa taja ta tsaya tana kallon ikon Allah.

 

Ganin ba zata dena ba yasa ta ƙarsa ta kashe kayan kallon.

 

Tsayawa tai da rawar da sauri ta kalli wajan,ganin Mammy yasa.

 

Tace”Au Mammy yau she kika shigo ɗakin?”

 

Wata uwar harara Mammy ta buga mata sannan.

 

Tace”Yanzu Afaf haka rayuwa za tai miki saboda Allah? Wai du-du-du shekarunki nawa eyye 16-17 fa kike amma gaba ɗaya ba kyaji”

 

Zunɓura baki Afaf tayi.

 

Tace”To ni kuma Mammy me nayi eyy?”

 

Mammy Tace”Ubanki kike banza sha-sha-sha mara tunani”

 

Afaf ta kalli Mammy da sauri.

 

“Na faɗa ko zaki rama?”

 

Mammy ta faɗa.

 

Afaf tai shiru tare da ƙasa da kanta.

 

Nan Mammy ta ƙaraci faɗanta ta gama ta fice.

 

Afaf tai irin abin nan na ko a jikina bayan fitar Mammy.

 

Wayarta dake kan gado ta fara ruri ƙarasawa tai ta ɗauka tare da kallon screen ɗin wayar Hassy taga an sa.

 

Ta amsa tare da ƙarawa a kunne ba tai magana ba.

 

Daga can ɓangaran Hassy Tace”Babbar yarinya yau fa da Dinner”

 

“Dinner wa a ina?”

 

Afaf ta tambaya.

 

Hassy Tace”Dinner birthday ɗin Hussy”

 

Afaf ta ya tsina fuska kafin,Tace”Amma shine dan rai nin hankali sai yau za a gaya min to ba zan zo ba”

 

Cikin muryar lallashi Hassy,Tace”Haba Babbar yarinya afuwa wallahi sai yau aka tsara amma ai kin sa shagali babu ke ba shagali bane”

 

Afaf ta ɗanyi fari da ido sannan.

 

Tace”Nace ba zan zo ba domin ai ne ba shara bace da kowace bola a zuwa a kaina”

 

Tana gama faɗar haka ta katswe wayar.

 

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top