Yar Mulki Complete Hausa Novels

Yar Mulki Complete Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Cikin nutswa drivers din suke tukin,gudun kar ran Amal ya baci,motoci ne guda biyar ajere,gabadayansu bakakene,motar tsakiya itace wadda Amal ke ciki,akwai biyu agaba biyu a baya wadanda duk body guards din Amal ne aciki.

 

 

 

 

 

Haka suka cigaba da tafiya,tana faman basu umarnin yadda take son tukin yakasance cikin tsiwa,da kuma mulki,suna xuwa kofar gidan,mai gadin yayi xumbur ya mike ya bude gate din tacewa drivern kai tsaya cikin tsiwa,ta xuge glass ta kalli mai gadin a wulakance,tace,banace maka idan na dawo kadaina batamin lokaci wajen bude gate ba?? Ya tsugunna yace kiyi hakuri ranki ya dade,baxan sake ba,Amal tace idan ka bari na kara maka magana a karo na biyu a ranar xakabar gidannan.ta bada umarni drivern yaja motar xuwa harabar gidan.

Motar da Amal ke ciki na tsayawa,bayin ta guda biyu suka fito,kowacce a gefen ta guda daya,suna ta faman gyara mata riga wadda ke jan kasa,suka shiga cikin gida.

 

 

 

 

ILHAM HAUSA NOVELS

Bangaren momy ta nufa,tana shiga momy tace my Amal kindawo?,Amal ta karasa ta kwanta a cinyar momy tace ehh,momy ta shafa kanta,tace Amal meya faru ne? Naga duk ranki a bace,yau kuma waya taba min ke? idon Amal ya ciko da kwalla tace momy nifa vanason mai gadin nan wlh,duk sai ya batawa mutane lokaci kafin ya bude gate,momy tace akan wannan kawai kike nema kiyi kuka? So kike ki tayarmin hankali,kawai dan kuka baya miki wahala? Kinga kiyi shiru xansa mai martaba,ya canja masa aiki acikin gidannan.

 

Salon So Hausa Novel Complete

 

 

momy ta kalli jakadiya dake gefenta tace kawowa Amal ice cream,jakadiya tace to rankiya dade,ta fita cikin hanxari,,sannan momy ta mai da idanun ta kan Amal tace,nasa akawo miki abinda kike so,ki daina bata ranki kinji.Amal tayi shiru alamar ta gamsu da rarrashin da momy tayi mata.

Amal kyakykyawace,farace tass, gashinta har gadon baya,hakoranta ajere suke wadanda suma farare tasss,tana da diri mai kyau,Amal akwai mulki dasan nuna ita ‘yar sarki ce, babu dama mutum yayi wani abu ba dai-dai ba sai ta nuna masa isa,da nuna sai abinda take so,akwai son hutu da kuma shanawa,wannan kadan kenan daga cikin halayyar Amal.

 

 

 

Amal tace momy bari naje na kwanta bacci nake nakeji,ta kaimin ice cream din daki,momy tace to,ki turomin haneefa,Amal tace to.

Amal na shiga daki ta tarar da haneefa a xaune akan sallaya tana karatun Alkur’ani,tacewa haneefa kije inji momy,yadda Amal tayiwa haneefa maganar kamar bataso,haneefa na karasa shafin da take karantawa tasa alamar tsayawa,ta tashi dan xuwa kiran da momy tayi mata,saboda tasan tana kara mintina dayawa xata sha fada awajen momy.

 

 

 

 

Tana xuwa momy tace da haneefa kije cikin abin kayan wankin dakina ki debo duk ilahirin inner wears din dake ciki maxa-maxa ki wanke min su,wannan kan bashine na farko ba,haneefa ta saba tunda ta taso ita take wa hajiya fateema wankin inner wears,haka ta wuce ta debo kayan.

Tana fitowa falon Abdul ya jijjiga kai aransa yace ina matukar tausayin yarinyar nan,haneefa tace yaya Abdul ina wuni ya ansa,lfy kalau haneefa ya karatu tace lfy kalau,ta wuce toilet don wanke kayan da momy ta bata. Karasa littafin a kasa.

‚Äč

 

 

Name: [ Yar Mulki Hausa Novel ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2021

 


 

 

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published.