Yarima Abdulmalik Hausa Novel Complete
YARIMA ABDUL-MALIK
*Story & written*
*By*
*Yusrah Musa Abubakar*
*(Mrs Al’ameen Ahmed)*
*Dedicated to Zarah Musa Dan Adam*
*In the name of Allah the beneficent and the most merciful*
*Be good be helpful everybody will like � u*
*Page 1*
Abuja fct babban birnin tarayya, misalin karfe shida na safe, hadari ne sosai ya taso garin ya bada kala mai kyau. Sakamakon rana bata fito ba, gashi ana kada iska mai ni’ima.
Wani kayattaccen layi ne, yasha kwalta mai kyau, sai walwali yake, gashi an kawata shi da fitilu masu d’aukar hankali. Tun daga farkon anguwar zaka san ba anguwar masu karamin karfi bace, yadda tsarin ta yake da tafka tafkan gidaje na alfarma.
Karanta Littafin Matar Nura
Wani kyakkyawan gida ne, mai dogon gini ya gaji da kyau. Kuma ko ba’a fada maka ba kasan gidan sarauta ne, saboda yanayin zanukan jikin gidan da tambarin masarauta. Dai-dai wannan lokacin, wasu matane uku ne, ri’ke da wani mutum da kayan fadawa a jikin su. A yanayin rikon da sukai masa zasan laifi yai suka kamoshi.
A kofar tangame man get d’in gidan suka tsaya. Tare da ‘kwan’kwasawa. Ganin haka yasa nace, bari na bisu, domin naga meke faruwa fadar. Irin tsaruwar gidan bata lokacine, tafiya ce mai tsawo sukai, sannan suka tsaya a wata iriyar kofa ta glass. Da alama wani suke jira. Sun kai minti goma a gurin, kafin suka hango shi tafe ta cikin glass d’in, da sauri suka bud’e kofar, cikin girmamawa suka duka masa.
Wai wai wai, masha Allah. Zan kad’i, wani kyakkyawan saurayi ne, fari tas dashi. Ya fito sanye da kayan army, wand’an da su kai matukar bala’in yin masa kyau. Umh da gani babu tambaya, wannan shine yarima Abdul-malik. Zare glass d’in idon shi yai, tare da zuba wa wanda aka kamo ido, tabd’i. Ni dai kauda fuska ta nai, dan wadannan razanannun idon na sa bazan iya kallonsu ba, wata firgitacciyar tsawa ya daka. Wanda ba mai laifin ba, hatta fadawan sai da suka tsorata. kowa yai zaman dabas a kasa, jiki na rawa, cikin fada ya fara magana” suraj na yarda dakai, shine zaka min haka? sai ka fada min uban waye ya baka poised, yace ka zuba min cikin abin sha, ko kuma ka karasa rayuwarka a gidan yari”.
Kuka wanda aka kira da suraj keyi, amma ko kashe shi zaiyi bazai taba fada masa wanda ya bashi gubar ba. Ganin yadda jikinsa ke rawa, ya kasa mgn ya musu nuni da cewa, su tafi da shi su tambaye shi har sai ya basu amsa. Mikewa sukai, cikin girmamawa. suka tafi dashi, yana wani irin kuka. Dan yasan Allah ne ka d’ai yasan irin azabar da zai sha a gurinsu.
Gashin kansa yake shafawa cikin dunbin tunani to waye zai bada poised a bashi? waye keson ganin bayanshi? ganin ya kasa samun amsa yasa ya fito a part d’in, cikin wani irin taku ya nufi palon kakan sa, lokacin daya shiga dukkan ahlin gidan suna zaune a palon. Amma banda maman sa, dan bata wurin du’kawa yai, cikin girmamawa a gaban mai martaba. cikin tsananin so mai martaba ya riko hannun sa, yana murmushi. A duniya yana son Abdul-malik matuka a ransa. Kowa fuskarsa da walwala, banda Yahanasu da takejin duk duniya ba wanda take ‘ki kamar sa. Wani irin firgitaccen kallo take binsa da. Ganin yadda mai martaba yake lailaya shi kamar jariri. Mai martaba ne ya fara magana “Muhammad ina fatan baka da wata matsala?” murmishi yai cikin jin dadin kular da mai martaba ke bashi yace “bana bukatan komai”. kallonsa mai martaba yai “ka tabbata?” kai ya d’aga yana sakin wani kayattaccen murmishi. Ganin yadda yaha tai da fuskarta ita da mahmud kamar anyi musu mutuwa.
Abban mahmud shima dake kallon Yariman cikin kauna yace “idan akwai matsala ka fada min baba na, kasan ban san ganin ka cikin damuwa” tun kafin yai mgn yaha ta tare shi da fadin “haba mai sai kace wani yaro, sai tambayar sa kake, ai yana da hankali idan yana da matsalar zai fada. Idan adalci ne, ai ga mahmud meyasa shi baka tambaye shi ko yana da matsala ba?”
Murmishi abban mahmud yai yana kallonta, yace “ai in dai lamarin baba na ne, ni yafi gold a gurina. Ina ji dashi, ina ririta shi tamkar raina”. Cikin bacin rai, yaha ke duban yarima kamar ana ‘kara hura mata wutar ‘kiyayyar sa a ranta. Kallon mahmud tai “tashi mu tafi” mi’kewa su kai, suka fita a dakin. Da kallo abba ya bisu yana mamakin wacce irin mace yake aure kamar yaha mara tunani haka Allah ya sau wa’ke. Duk ranar data kai shi bango zata sha mamakinsa.
Mi’kewa Yarima yai yana musu sallama ya fita, suna sa mai albarka. Part d’in maama d’in sa ya shiga, don kwata kwata idan bai ganta ba baya samun nutsuwa, yana shiga palon ya hangota kishingide, ganin sa da tai yasa ta mi’kewa zaune, tana tarar sa da murmushin kauna. Bako kunya yana zuwa ya kwanta a jikin ta. Hannu tasa a suman kansa tana shafawa, cikin murya mai sanayi tace “baby baka rabo da rigima har yanzun jinka kake yaro, kafa girma kosai ka fara ganin naka yaran zaka san ka girma?” mi’kewa zaune yai yana rike mata hannu a hankali yace “I love u my sweet momy fatan kin tashi lafiya? kuma ba wata matsala?” dariya tambayar ta bata tace “wato baby na fahimce ka, tambayar dasu mai martaba suke maka yau kuma ni ka kewa?” ‘Kara rike hannunta yai cikin shagwaba yace “haba mama, kin san yadda nake jinki a raina ke d’aya ce tamkar da dubu. Dukkan wata soyayya da kulawata a gareki take ina matukar son ki my mah”.
Murmushi tai cikin jin dad’i tace “na sani ba wanda kake so sama dani Allah yama albarka, sannan kuma kaci abinci? abinda baka so nace dagowa yai yana ganin ta kureshi da kallo yasa yace ” eh zanci idan na koma” har lokacin kallonsa take tace “oh da gaske? toni ban yarda ba tashi muje ga abinci can kaci kada ulcer ta kama min kai”.
Bata fuska yai irin baya so d’innan, mama tace “bazan barka ka tafi ba sai kaci ko kad’an ne,” shiru yai yana karya wuya ya koma kalar tausayi dan ta barshi ya tafi. kiran sa akai a waya ya d’aga yana son kwacewa daga rikon datai masa amma taki sakin sa baiwace ta shigo da abincin ta ajiye sauke wayan yai yana kallon abincin ya dauke kai daukan spoon in tayi tana dibowa takai saitin bakinsa. Yai saurin rufe ido ganin idan ta biyeshi ba ci zaiyi ba ta aje spoon in tamai durar karfi da yaji.
Batun yaha kuwa suna komawa part d’ita ita da mahmud ta soma zagaya palor cikin taikaici zama Mahmud yai cikin jan tsuka yace wai dan Allah umma me yasa abbana yake min haka kamar ba shine ya haifeni ba gabadaya ya tattare soyayyar sa ya dorata akan Abdul-malik kafin ya kira sunana sau daya ya kira nasa sau goma gaskiya na gaji yaha ce ta juyo tare da cewa af kwantar da hankalinka mahmud na kusa daukar mataki kowama ya huta amma kafin nan sai munsan yadda zamuyi mu shiga jikinsa kaga daga nan hakanmu yacimma ruwa sai mu kasheshi ta ruwan sauki batare da an zarge muba shine aure zanje gaban mai martaba nace ya kawo lokacin daya kamata ace ya aje iyali idan har mai martaba ya yarda zan fadi yarinyar daya kamata ace ya aura
Mahmud da hankalinsa yadan tashi yace to wacce zaki zaba masa idan mai martaba ya amince zama tai tana kallnsa tace ina nufin hajara yar gidan yaya kasan ta kusa zuwa mikewa mahmud yai what umma hajara fa aa da sake abinda na dade ina mafarkin samu yaha tace kamarya yace haba amma ai kinsan nike son wannan yarinyar gky ban amince a bashi ita ba
Dafa shi yaha tai tace karka damu mahmud zanyi maka bayani ba kanason ganin bayan Abdul-malik ba to ai dole sai ta wannan hanyarce kadai zamubi mu samu nasara yanzu idan mukace zamu kasheshi ba wani dalili hakan zaiyi mana wuya amma idan ya auri hajara zata sheke mana shi ba tare da munsha wahala ba kuma bamai zarginmu kaga zamu dawo mune da fada a gurin mai martaba idan ya zama babu shi kayi tunani ta wanna hanya ce kadai zamu iya shafe shi mu batar da tarihinsa har abada
Cikin gamsuwa mahmud yace kima haka ne fa kinga riba biyu zan samu an kashe shi kuma na auri wacce nake so cikin jin dadi yaha tace shiyasa nake yinka akwai fahimta yanzu kaje ka tafi hospital kada lokaci ya kure ma kuma ka sake tunani akan abin dana fada maka tana kaiwa nan ta wuce shima mikewa yai ya fita
Kano farawa wata budurwace tafe a wannan anguwa ita kadai kyakkyawa ce ta ajin farko kuma yanayin kayan dake jikinta bazai nuna maka cewa yar talakawa bace sai dai ba haka abin yake ba muje zuwa mahaukaci yahau kura
Wani gida ta buda ta shiga amma iya yanayinsa zai nuna maka cewa gidan hayane da wata tsohuwa suka hadu zata fita a gidan cikn tausayawa ta kalleta tana cewa sannu kinji zainab ki kara hakuri komai mai wucewa ne ki daina sa tunani a ranki in Allah ya yarda wata rana zakiga ribar hakurin ki murmushin karfin hali zainab tai tana daga mata kai tace ngd da kulawarki inna sai kin dawo Allah ya tsare amin inna tace tana ficewa ita kuma ta shiga gidan bangare biyu na inna da nasu
Da sallama ta shiga tanaiwa matar dake zaune a gaban kuloli sannu da gida ko cira kai batai ba balle ta sa ran zata bata amsa wucewa tai ta shiga dakinta tana tunanin yaushe ne zata samu canjin rayuwa rashin iyaye baiyi ba gashi batasan kowa nata ba balle ta koma wurinsu mahaifanta sun rasu batasan danginta ba sai hjy bilki kishiyar mamanta wannan wacce irin rayuwa ce ta tsinci kanta a ciki goge hawayen fuskarta tai jin bilki na kwalla mata kira cikin sauri ta fito tana cewa gani umma
Tsaki taja wato zainab wuyanki ya fara kwari ko sbd ke tinkiya ce kullum sai nayi da baki na akan fita da abinci shago saboda kin gado bakin halin uwarki to wallahi wuya zaki sha a gurina kuka zainab keyi dan idan akwai abin data tsana a duniya shine ka zagar mata mahaifa
Bilki tace inye hamshakiya danna zaki uwarki kike kura to ko tana raye zan zageta balle tana bayan kasa ke dalla tashi ki fitamin da kayan sana’a ta dan wallahi kikamin kwashe duka zaki mikewa tai ta f
ara diban kulolin tana fita dasu tana shago taga tanimu ya sauke hindu a mota dan girgiza kai tai cikin takaici sai bayan la’asar ta koma cikin gida dukda abincin ya kare tun wuri zamanta a wajen yafi mata alkairi bata kudin tai daidai hindu ta shiga da bakar leda a hannunta ta mikawa bilki tana cewa wanka zanyi in anjima tanimu zaizo kallon Zainab tai ke jeki debo mata ruwa zatai bako ba irinki bace mai bakin jini kuma ki dawo ki dafa mata wannan kazar
Kala zainab batace ba ta dau bokiti tana fita a gidan bayan ta debo tana shigowa gidan a zaure suka hadu da bashir yana ganinta cikin murna yace masoyiyata dama ke nazo nema ya gida kallonsa tai cikin takaici taja tsuka zata wuce ya jawo hijab inta bokitn ya fado ya fashe
WASH ALLAH GASKIYA KUNA KOKARI
YARIMA ABDUL-MALIK
*ANNURI WRITER’S ASSOCIATION*
By
YUSRAHMS ABUBAKAR
#YMA
Dedicated to Maman khaleel
Safiyya Aliyu
Ina matukar godiya da nuna kaunarki a gareni MY FEEDOH may Allah bless you and your household wannan page din naki ke daya har zuwa page 20 mallakar kine.
*If you go to the river dont swim it can carry you away.
Page 2
Da gudu Bilki ta fito ganin abinda daya faru yasa tace kan ubancan amma Zainab anyi muguwar yarinya sbd bakin hali saida kika karasa min bokiti to wallahi baki isa ba saikin biyani mayya kawai mitsiyaciya ta karasa maganar tana janta ciki hakuri Zainab ke bata amma wani irin gigitaccen Mari ta sauke mata saida ta durkusa har kasa bisa kafafunta saboda azaba wanda hakan yai daidai da shigowar Inna da sauri ta karaso tana dago Zainab din dake kuka fuskarta tayi ja wani irin kallo taima Bilki mai nuna cewa wata rana zaki nadama tace amma wallah Bilki baki da da’a sau nawa zan fada miki ki daina dora hannunki akan yarinyar nan rashin iyaye fa ba hauka bane kinsan irin bala’in da kike kwasarma kanki kinsan hukuncin mai zaluntar maraya me yasa baki da tunani ko kadan ina tsorace miki ranar da zaki kuka da idanunki Zainab ba yarinyar da za’a wulakanta bace duk abinda ya sameki ki kuka da kanki na fada miki.
Kallon sama da kasa Bilki ke mata tunda ta fara magana sannan tace ahayye nanaye kaji mace da kwarton munafirci meye ruwanki a ciki amma ba laifinki bane da alama yunwa kike ji ga dusa can idan kin gama ci kije ki sha ruwa munafikar tsohuwa kawai tana kaiwa nan ta wuce ta koma ciki.
Da kallon suka bita inda sabo kuma Inna ta saba da wulakancin Bilki ba tun yauba hannun Zainab ta rike tace muje dakina Zainaba ki huta kinji ki ta hakuri komai mai wucewa ne Allah ya jikan Umar da Khadija ameen Zainab ta furta cikin damuwa amma ko babu komai tana samun sauki idan Inna ta wuni a gida.
Yau Yarima ke shirin zuwa kano gurin kakarsa zaune suke a palor mama ta kalleshi tace gaskiya babyna kana da kyau kamar balarabe “harka shirya kenan”? Da kai ya bata amsa taci gaba da cewa Allah ya kare min kai baby inaji a jikina kamar zuwanka gurin ammi alkairi ne tamkar zaka hadu da wani abu dazai saka farin ciki kuma ya zamo maka garkuwa a rayuwarka.
Ido ya zuba mata bayan ya gama jin jawabinta yai murmushi har dimple dinsa na lotsawa amma baiyi magana ba mikewa mama
tai tana kire hannunsa suka fita har mota tai masa rakiya kafin ta koma.
Lokacin daya dayai perking da mota a harabar gidan da mamaki Mustapha dake tsaye kafar shiga palor yake kallon motar da tunanin waye a ciki bai kare mamaki ba Yarima ya fito yana gyara agogon hannunshi domin shi kadai ya bata shi mutum ne wanda baya bukatar takurar wasu fadawa ko bayi duk inda zaije shi kadai yake zuwa ko driver baya bukata.
Dagowa yai sukai ido biyu da Mustapha wani ihu yai yana rungumeshi cikin nuna tsantsar murna yace abokina kaine dama zan ganka kwana kusa gaskiya nayi kewarka yaushe raban da mu hadu kusan shekara biyu fa murmushi Yarima yai yana kallon shi yace sorry ba gani yau nazo muje ciki na gaji inason na huta shiga sukai wata farar mace ta dago tana kallonsu tace dama saida tunani na ya bani tunda naji Mustapha na ihu yana cewa abokina nace nasan kaine ba wanda zaizo yayi wannan haukan sai kai ta karasa maganar da murmushi.
Rungumeta Yarima yai a rayuwarsa yana matukar son ammi Mustapha ne ya fara dariya yana cewa wato Abdul-malik har yanzu baka janye wannan dabi’ar taka ba yanzu runguma ce gaisuwa dagowa yarima yai yana kallon ammi alamar ta tanka Musty yace malam bafa zakazo ka sanya tsohuwata magana ba ka baro taka acan tana hutawa zaka wani takura min tawa harararsa Yarima yai kafin ya mike yana cewa muje na gaji inason na huta bani da lokacin ka wucewa sukai yana cewa ammi bari ya dan huta.
Zainab ce zaune a tsakar gida tana hada kunun aya Bilki ta fito a daki tana cewa Zainab me kikeyi anan? dagowa ta tana kallonta tace kunun aya nake hadawa