Hausa Novels

Yarima Jalal Hausa Novels

Yarima Jalal Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

Yarima Jalal

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

Jalal! Jalal! Jalal! Jalal! Sai kiransa nake amma shi wanda na kira da jalal din ko motsi baiyi ba,sai da na karaso wajansa kafin yace min so nawa nake fada Miki idan zaki rinka kirana kizo inda nake kafin ba tun kina nisa ba..kallonsa naki cikin mamaki a cikin zuciya ta kuwa cewa nake wlhy dad ne ya daure masa gindin ya mana abinda yagadama a gidannan amma zan koya masa hankali.makaranta zaka kaini magana nake cikin isa da gadara idonsa a gefe yace min ina driver dinku cikin masifa nace oho watan idan nace ka kaini makaranta ko da driver bazaka kaini ba koh to ganin gida yaji..

Jalal kuwa idan you asan da wata a gun to dotse yayi magana ganin zai bata min lokaci yasa na Fara magana a sanyaye domin nasan in zamu kwana a gun bazaya tashi ba cos yana min kasheji akan idan zan masa toh insan yanda zana tauna harshena..

Ina gama masa maganan cikin natsuwa ya tashi ya nufe wajan adana motoci ya dauki mecedec,idan akwai moton da na tsana to itace amma saboda idan na tsaya masa magana bata ma kaina lokaci zanayi sai na shiga kawai. Tafiya muke babu Wanda ya kula dan uwansa kamar ance masa ya juya ya kalleni saiya ganni daga ni sai wando da riga da dan karamin gyalle wani birki yaja da har na saka wani kara daga ido nayi saina ga ashe har mun karaso. A cikin zuciyata magana nake yau kuma salon wulakancin da za’amin kenan a waje zai ajeni wani dogon tsaki nayi na budi kofar moton najita a kulle daga ido nayi ina mai kallonsa.jalal kuwa ko kallona baiyi ba sai ma kara kauda kansa dayayi yace min me nafada miki ranar nan bace miki nayi duk ranar da ya kasance ni zan fitar da ku to ku rinka saka hijab ba,ina mai tabbatar miki da cewa yanzu zamu koma gida ki saka saina dawo da ke..kamar zanayi hauka amma saboda hali irin nawa na bashi hakuri ina ganin kamar ci baya ne.haka inaji ina gani yayi reverse muka koma gida gashi sai kirana ake tayi wai za’a mana text…a gate ya tsaya da sauri na fito na shiga ciki ko minti biyar banyi ba na fita da sauri sanye da hijab toyobo mai ruwan powder (pink )..

Wow abinda yafada kenan saboda kyaun da nayi cos acewarsa yau ce rana ta farko da ya fara ganina da hijab.tafiya nake bakina a ture,sai yaga na masa kyau sosai ina karasowa ya kauda fuskarsa..yana tsayar da moton kafin ya gyara parking na fito nayi tafiyata shi kuwa bina yayi da kallo yana murmushi yarinya sai girman kai haka zana koya miki hankali.ya juya ya fice a makarantar ya huce gida..dawowa yayi ya dauko ni a makaranta amma yaita jirana banfito ba jalal kuwa idan akwai abinda ya tsana itace a bata masa lokaci shiyasa ma baya African tym saboda duk lokacinda ka fada masa abu to yana zuwa kafin lokacin tayi..yanzu dai Sun tashi da kusan minti daya kenan😏ni kuwa da gangar na masa saboda ya batamin nawa lokacinda safe..ina zuwa baya na budi na shiga ina mai murmushi ciki2 domin nasan zanja magana amma abin mamaki ko uffan baice min ba saima gyara kwanciyar da yayi a moton.gyara zama nima nayi tun ana minti talatin har an gangaru hour daya hmmm an kira asr,cewa nayi a zuciyata kila yayi sallar azahar ni kuwa banyi ba gashi har LA’asar tayi bude kofar nayi na kumo gidan gaba…leeemat kuwa cewa tayi kin ma kanki kiyamullaini ba wai sunan wani sallan dare..ina zaune na dan kalle shi ta gefen ido abin mamaki idonsa biyu, saida ya kara kusan minti talatin kafin ya ta da motar suka tafi gida yana mai dariyar keta a zuciyarsa daya fahimce inajin yunwa domin cikina har kururuwar yunwa takeyi……

 

Written

By

Leeemat💮…

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat)💮

 

 

Alhaji nasir bammali shine mahaifina, hajiya naja’atu itace mahaifiyata mu biyar ta mahaifemu  nakasance ya ta farko a gunta inda tasakamin  sunan simra ina da shekara uku ta haife jalilah sai kuma yan biyu dahir da dahira sai autan mu ummu kulsum amma ummu muke kiranta.mahaifana haifaffun garin zaria ne wato kaduna State kenan a gun suke zama har aka haife mu nayi primary har secondary dina a zaria yanzu ina University of Zaria wato Abu kenan inda nake karanta medicine and surgery jalilah ita ma tana abu inda take karanta bsc nursing yan biyu kuma na secondary ummu na playclaas..ina shekara ta biyar kenan jalilah kuma na shekara daya a university din,duk da karatun mu bai hana mu aiyukan gida ba irin su kwankeke da abinci kai har da shareshare domin mahaifiyar mu ta hana a dauko mana Mai aiki anata cewar batason a kora mata yara a gidan miji duk sanda mahaifinmu ya mata korafi abinda take cemasa kenan saiyace idan sun tafi makaranta wa zaiyi aiyukan saitace ni zanayi har su dawo saiyace in kin tsofa da aiki amarya zan kawo miki sai suyi dariya kawai.kwankin kaya da guga kuwa mahaifinmu yace bazamuyi ba jalal she ke mana da mu da mahaifinmu da mahaifiyar mu sai idi driver sa’annan baba Mai gadi.rayuwa muke cikin sakewa amma bai hanamu biyayya ga iyayenmu ba duk kayan da muka gadama muke sakawa sai zuwan jalal rayuwar mu ya hanamu sakewa,zana iyacewa ni yafi tsana saboda bana masa ta dadi haushin sa nake ji, akwai ranar da zamu tafi ziyara a gidan kakaninmu idi driver dad dinmu yayi aikansa a banki layi yayi yawa sai bai dawo da wuri ba ni kuwa na kagu na ga hajiya tsohowa mahaifiyar dad dinmu saina ce ma dad dinmu yafada ma jalal ya kaimu muna shiga cikin moton saiyace wai nafito tambayansa nayi meyasa saiyace na canja kaya ko kuma na saka hijab na duba shigarda nayi doguwar rigace da mayafinsa saidai fitted ce,dan Allah wannan rigar me yamasa da zakace na canja,ni gaskiya babu wani rigar da zan canja na gyara zama ina maijin haushin halinsa na takura tsawa ya daka min har bansan lokacinda na fita ba na shiga ciki ina kuka side na dad na nufa ina fada masa abinda jalal yamin hau ni da fada yayi na tashi na nufe wajan mom ita ma fadan taimin dakina na huce nayi kuka har na godiwa Allah tun daga wannan ranar na tsane sa bana masa kallon mutunci saboda da shi iyayena suka min fada wannan shine musabbabin rashin jituwa a tsakanin mu dukkanmu muna nuna wa juna miskilanci amma daga karshe ni nake sauke nawa na bi nasa ra’ayin saboda wani tsoronsa da nake ji amma baya hanani na masa rashin mutunci…..

 

 

Written

By

Leeemat💮….

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat)💮

 

 

 

Babu irin wulakanci da tozarcinda bana masa amma duk bandaina jin haushinsa ba.jalal kuwa duk lokacinda ya zauna saiyayi tunanin wai meyasa na tsane shi bayan ga su idi da baba maigadi mts kawai yayi ya cigaba da harkansa

Yau ya kasance graduation dinmu na gama makaranta an bani shaidar na zama cikakkiyar likita murna kuwa ba’acewa komai munyi hoto sosai domin har da jalal nayi hoton,da aka kawo mana hotonan kuwa sunyi kyau sosai saima wanda mukayi da jalal domin yana kallona ne cikin wani salo da na kasa cire idona a hoton

Anyi sha’ani lfy muka dawo gida washegari na tafi gaida dad dinmu ina gaidashi na Mike zana fita ya kira ne na dawo na zauna yafara da cewa simra nace na’am,yace duk abinda uba yake ma danshi na miki ko ban miki ba nace kayimin saina yace sauran me gabana yayi mummunan faduwa.

Aure ya fada,aure yanzu ya rage min na miki Kuma na baki daman ki fitar da mijin da kike so duk da dai ne yadace na fitar miki da miji a matsayin ki na budurwa amma kinyi wasa da damar ki dun haka ni zan fitar miki da miji nan da kwana uku idan baki fitar da wanda kike so ba,nan na mike jiki a sanyaye na huce dakina gashi bana kula samari na tuna da numbar wani da muka hadu a wajan bikin uncle dinmu da sauri na nufe jakata amma abin takaici bangani ba sa’annan na tuna a lokacinda yake bani numbar na yaga takardan domin nace masa bazan iya bashi wayata ba saiya rubutu min a paper.

Haka dai har kwana ukun yayi amma babu komai nayi kuka harna gode Allah

Da safe saboda tsoron jin mijinda dad ya zabamin ya hanani tafiya gaidashi saida ya saka a kirani,na tashi na tafi ido a kunbure saboda kuka na zauna tare da gaida shi ko amsawa baiyi ba yacemin tunda kin kasa kawo miji to na zaba miki jalal…

 

 

 

Päge 4

 

 

!.Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat)💮

 

 

 

A razane na kallesa ina kuka dad jalal fa kace,kwarai kuwa haka nace idan Kuma ban isa da ke bane saina sani koh tashuwa nayi na huce dakin mom na fadi a jikinta ina kuka tambayata take amma na kasa bata amsa sai dad da nake ta cewa mom kuwa rudewa tayi a zatonta wani abune ya same sa da sauri ta fita daga daki ta shiga side dinsa saboda akwai wani coridor da za’abi a shiga falonsa tana shigowa wani ajiyan zuciya tayi kafin ta tambaya me ya same simra,magana yake cikin bacin rai wai ace wannan yarinyar bata da sayayye ga kanwanta tana da miji jiranta akeyi amma babu, shine na zaba mata jalal a matsayin mijinta mom ita ma a razane tace wani jalal din badai na gidannan mai kwanki da guga ba. shi ya bata amsa ko kema gardaman zakimin,a’a na isa Allah ya huce zuciyar ka ta tashi ta fice abinta ta sameni inata kuka ina ganinta nace wallahi mom banasonsa dan Allah kifadama dad ni bana sonsa ya zabamin wani na yarda amma ba jalal ba.mom kuwa babu abinda take sai aikin lallashi tare da bani bakin nayi hakuri dad bazaya min zabin tumun dare ba amma na ki sai kuka nake

Mom kuwa irin matan nan ne masu bin maganan mazajansu idan yace ga abinda yake so to haka zatayi ko da kuwa batason abin Allah yasa muma muyi kuyi da wannaan halin ameen

 

 

Päge 5

 

 

Written

 

By

 

Leeemat💮….

 

..

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: Y@RIM@ J@L@L

 

Nah halima musa akano (leeemat )💮

 

 

Yau ya kasance weekend babu makaranta inason na dan fita shopping na saya abubuwanda bandashi amma babu idi driver tsaki nayi saboda na tuna da jalal dan girman kai bansan yaya zan masa magana ya kaini ba side din mom na huce na tarar tana gyare2 dakin ta na fara tayata tare da mata maganan inason taima jalal magana ya kaini shopping bude bakinta tacemin daga yau shine yau idan kina da bukatar tafiya wani gu karki sake ki zo wajena saboda ni ba sa’arki bace sai girman kan tsiya kinason ki fita amma girman kai ya hanaki masa magana,na marairaice fuska sa’annan nace mata wallhi mom dan rashin mutunci ne wai inzaka masa magana kuma saika tausasa harshen ka nikuma gaskiya bazana tsaya ina tausasa masa harshe kamar wani mijina ba bayan kuma dan aikin mu ne,jalal na shiguwa falon mom da niyar zai kawo mata tsako a gidan hajiya tsohowa kenan yaji abinda simra ke cewa girgiza kai kawai yayi ya fice. Yana shiga dakinsa wayarsa tayi kara yana daukowa yaga abokinsa ne hello dude ya kake wallahi Kalau inson mu hadu yau ok to babu damuwa ina zowa yanzu jalal ya kashe wayarsa sai wani kirar ta shiga yana dubawa yaga mom ce da sauri ya dauka to to kawai naji yana cewa sa’an ya kimtsa jikinsa ya fita ya tarar simra na jiransa shiga moton yayi Suka tafi,suna tafiya babu abinda ke tashi a motar sai karatun alqur’ani na sheikh sudais surar AL’imran  simra kuwa sai bin karatun take a zuciyata saboda ta sauke tun tana ss1,tama mance bata fada masa inda zaya kaita ba ji kawai tayi ya sayar da moton daga ido tayi domin ta ga ina ya kawo ta saita gansu a wani gida mai bala’in a ranta cewa tayi nan kuma inane tabe baki tayi irin I dont Care din nan fita yayi ya shiga gidan ya tarar da abokinsa mai suna kamal suka bude shafin hira.

Simra kuwa tun tana zaman dadi har ta fara na wuya ana hour daya har anzo biyu uku kuma taki kiransa saboda girman kai numbarsa ma batta da shi haka ta zauna godiya Allah ac a kunne take amma fa cikinta ya gayamata saboda yunwa.jalal kuwa ganin azahar ta gabato yasa shi yin sallama da kamal ya fito ya tarar da ita ta kunbura saura kadan ta fashe yana shiga yace mata ina kike son na kaiki tundake bazaki fadamin ba ni bara na tambaye ki amma fa karkiyi tunanin tsoron ki nake a sanyaye nace masa shopping zanaje,muka tafi mun dawo gida kusan karfe biyu ina shiga mom na tambayata meyasa muka dade haka na zayyana mata abinda ya faru ina hawaye,cewa tayi maganinki kenan amma fa na gode masa domin ya kuya miki hankali hucewata daki nayi na cigaba da kukata….

 

 

 

Päge 3

 

 

Written

 

By

Leeemat 💮….

.

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat)💮

 

 

 

Tun daga wannan ranar na tsiro da ma jalal wulakanci, aika duk da dai nasan idi driver ake aikan sa amma saina bawa jalal amma abin mamaki zaya harma yamin abinda nace ya kawo min wanki kuwa ya kwanke kayan akwatina Sun fi so goma anawa tunanin wai saboda yace ya fasa aure na

Bangaran Iyayena kuwa sunyi fadan sunyi nasiha amma na kiya jalilah itama tamin nata maganan amma na zagzageta nace mata kar ta karamin maganan jalal,har da wani cewa yana da kyau ga aji da miskilance mts idan yana da kyau ke ki aure sa mana na fada raina a bace ita ko tacemim Allah ya baki hakuri ta fice abinta domin jamal yazo mijin da zata aura banker ne sa’annan shima a Zaria yake Sun hadu a lokacinda ta tafi bank bude account dinta amma saboda bata sa akeyi ba domin na bani hakuri akan na rakata naki shine ta tafi da kanta,jamal ya taimaka bata da sauran prossesses da akeyi harta gama ganin taimakonda ya mata ya saka ta karba numbarsa domin su rinka gaisawa har zumunci ya zama soyayya,haka dai rayuwa ya cigaba da tafiya,dad dinmu dayaga abin nawa gaba yake yi ya saka  mana ranar auranmu a ranar kuwa har nayi zazzabi saboda kuka..

IV aka kawo mana saboda biki ya rage sati biyu kannena nata yabun iv din amma ko kallonsa banyi ba har cewa suke lah har da rubutun India a ciki a raina kuwa cewa nake a ina wannan dan rigimar ya saka an mishi iv har da wani India a ciki wa ya iya India da za’a karanta bangama maganan zuci ba naji dahir nacewa ai uncle jalal ya iya India ai inajinsa yana waya da wani wai abokinsa ne ya koya masa a raina kuwa cewa nayi makaryacin banza a ina yaga aboki da har zayace abokinsa ne ya kuya masa kila ma a kauyansu ko radio basu da shi…

 

 

Päge 6

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )💮

 

Saita raba iv jalilah take amma ko kallon nawa banyi ba saboda a cewata abin kunya ne ace wai zan aure jalal da jalilah taga ban da iya in zata fito zaita dauko har da nawa sa’annan ta dauko wayata ta rubuta sms na gayyatar auran ta sending ma all contact dina bansani ba har satin auran yayi an tambaya me zana yi nace mata babu abinda zanayi haka jalilah sunyi kamu da friends day nima nayi bikin amma in ba an fada maka bane bazaka gane nima amarya bace domin ankon da akayi shine na saka kyau kuwa ba’a cewa komai saidan ramar da nai dama ba kiba ce dani ba jalilah ce dai mai kiba kadan gobe za’a daura aure dad dinmu ya kirani yamin nasiha sosai simra wato dai kin nunamin ban isa dake ba tunda na miki miji shikenan kin hana wa kanki sukuni bayan kinsan ko wani uba bazaya zaba wa dan sa zabin da baida kyau ba amma babu komai inhar ban isa dake ba gobe idan a kaiki ki saka shi ya sake ki ki dawo gida magana yake rai a bace babu abinda nake yi sai kuka yana gama ya fita abinsa a ranar akayi walimah WA’azi akayi Wanda naji kamar da ni ake nayi kuka har a ranar da zazzabi da kwana na kwana

Washegari ya kasance dauren aure jama’a kuwa kamar ana hawan sallah kai da yan kasashen waje da ma sarakuna na gari daban daban irin su isa mustapha agwai na daya sarkin lafia nasarawa state da sarkin Zaria da sunusi lamido sunusi sarkin kano kenan dama wanda baxana iya lissafa ba an daura aure da gwalagulai da ba’asan nawa ne kudin su ba na simra kenan yanda Kuma na jalilah kudi aka bayar,

Mahaifinmu baiso haka ba amma babu yanda ya iya domin yace albarkar aure ake so..

Ana daura kuwa magana yazo har gida an daura mana aure wani kuka na sake dama banda lfy sai jikin ya karatashi mom dinmu ta shiga ta sameni tamin nasiha tare da cewa bamusan abinda yasaka dad dinmu bawa jalal ke ba amma munafatan Allah yasa alkhairi ne domin nasan insha Allah zakiyi alfahari da zabinda dad dunku ya miki sa’annan naji dan sauki cewa tayi na tashi na shiga nayi wanka ina gama na saka wani shadda a cikin kayan dad da daddare aka zo daukan amarya jalilah domin ance ni sai gobe garin su jalal da nesa baza’a kaini yau ba sai gobe muka tafi kai jalilah gidanta dake g.r.a da zamu dawo kuwa munyi kukan rabuwa domin nima gobe zan tafi yafeyar ta na nima saboda bansan wani irin rayuwa zanyi a can ba…

 

Written

By

Leeemat 💮

…..

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )??

 

 

Washegari aka kawo min kaya kamar na sarauta na saka sa’annan na dura da alkyabba kamar wata sarauniya na ce a raina motoci kuwa Sun kai goma,ni duk abin mamaki yake da ban domin har na kasa cewa komai aka kaine wajan mom tamin nasiha mai rasa jiki na kuka sosai na rumgumeta ina cewa umma ki gafarceni nasan na muku gardama da dad inason ki yafemin kuka nake kamar za’a kaini gidan ajalina,domin har na saka mutanin falon kuka mom ta kasa daurewa ita ma sai kuka takeyi tare da cewa nayafe miki simra dama bakimin komai ba da kyar aka babbare daga jikinta domin inaga kamar bazana sake ganinta kuma ba side din dad aka nufu dani dad shima yamin nasiha tare da cewa yasan bazan bashi kunya ba domin yasan sainayi alfahari da zabinda yaymin wata rana,nima na masa alkawarin insha Allah zanyi biyayya ga jalal bazan bashi kunya ba natashi muka fita a gidan sai kuka nake tare da ma gidan mu kallon karshe,mota na biyar aka saka ni ina shiga muka tafi ina kuka tare da kallon gidanmu, munyi tafiya mai dan tsaho sainaga mum tsaya saboda tsakani na da driver akwai wani abinda ya rabamu maganan zuce nake wai har mun iso kenan amma kuwa garin babu nesa kofar aka bude min na fito gabana yayi mummunan faduwa sakamakon abinda nagani…..

 

 

Päge 8

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )??

 

Me zan gani,ganinmu nayi a gidan sarkin Zaria me muka zo yi anan nayi tambaya a raina amma babu amsa wani bamgarin cemin yayi kila kunzo gaisuwa ne ko kin mance sarkin Zaria aminin dad dinki ne,gimbiya mutafi naji muryar wata na mace namin magana tafiya take ina binta a baya har muka iso wani side muna shigowa muka tarar da wata mata daga ganinta kaga Mace mai sarauta saboda yanayin zamanta cikin kasaita fuskar ta a daure yanda naga matan sukayi haka nima nayi muka gaida ita amsawa take kamar dole nan da nan haushi ya kamani Allah yasa nima ba talaka bace da za’a raina min wayo muna zauni kusan minti talatin amma batace mana komai ba ni kuwa na kumbura saura kadan yarage na fashe ina shirin zan mike kenan sainga wacce muka shigo da ita tace uwargijiya samu shiga can,ban ma tsaya sauraron abinda zatace ba na fita muka danyi yin tafiya sosai sa’annan muka shiga Wow abinda na fada kenan sakamakon daular da nagani a falon sai kamshin turare ke tashi a falon muka zauna saiga wata mace kyakyawa ta fito daga wani daki da Fara’ar ta ta karaso sannu da zuwa tashi tashi ki zauna a kujera tacemin amma nace mata a’a nan ma ya isa kaina a kasa cikin jin kunya,ai nan gidan ku ne kar kiji kunya kinji murmushi kawai nayi aka kawomin kayan shaye2 da na ciye2 ruwa kawai na sha,muka cigaba da hira da ita inda take tambayata ance nagama karatu koh eh nace mata sa’annan tace ai munso muzo amma fu’ad ya kiya a raina nace waye mai wannan sunan kuma har wajan karfe 8na dare ina wajan sa’an muka nufe wani gu nisa da gidan sarkin ko Kuma nace a baya gidan yake katoton gida aka shigar dani sa’an matar tace min nan ne gidanki na daga ido ina mai kallonta saitace sunan indo amma anfi sanina da jakadiya duk abinda kike da bukata zaki iya aikowa a kirani ta fice ta barni a gun da tambayoyi a zuciyata…

 

 

Päge 9

 

Written

By

Leeemat??…..

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

Na shiga toilet nayi wanka ina fitowa na sauna a kan stool na dressing mirror ina shafa mai domin komai yana gun abin mamaki duk maiyukanda nake anfani da shi ina gama shafawa na zauna inata tunani bangane abinda ke faruwa ba jiran jalal kawai nakeyi yazo yamin bayanin mekefaruwa  ina cikin tunani naji an budi kofa gashi Kuma banda komai a jikina na mike da niyyar dauko wani abu na rufe jikina amma is too late me kikeyi haka kamar wacce bata da gaskiya naji yafada na juya da niyyar masa rashin mutunci amma saina tuna da alkawarinda nama dad dinmu sainayi shuru matsowa yayi kusa dani najada baya ya kamamin baki ya murda kara na saka domin wani azama naji rashin kunyan da kika saba zakimin?kin dai san da da yanzu ba daya bane yanzu sai abinda nace Kuma sai abinda naso,banason gardama idan nayi magana sa’annan idan na kiraki kar ki bata min lokaci ko me kikeyi ki barshi kizo inba abinci kike kikedafawa ki barta kizo inya so ya kune zaiki dafa wani tunda dai abinci na ne kindai ji abinda na fadamiki koh? Daga masa kai nayi ya kara matse min baki da baki na miki magana ko da kai kara na sake saboda yanda yake min da bakin hawaye na bin kunci na sa’annan ya sake min bakin saina ce masa babu yanda zana amsa maka bane ai saboda hannun ka na baki na juyawa yayi ya fice abinsa jalal nace masa ya juya yana zuwa inaja da baya hannuna ya kama ya saka farcinsa a fatar hannunta kara na sake sa’annan yace baki da kunya koh?jalal kika kirani yanzu mijinki nake ba mai kwanki da guga ba ki san sunanda zakina kirana ba jalal ba,me ke tafe dake na sassauta muryata sa’annan nace kaya nake son na saka ya nufe drower ya cire min night gown mai kyaun gaske ya bani yayi yafiyar sa yana kaiwa bakin kofa ya cemin daga yau abincina ya dawo hannun ki kai har dama wanki na yayi tafiyarsa,zaunawa nayi a bakin gado na sake kuka mai tsuma rai oh ni simra na shiga uku meke shirin faruwa dani ne kar dai ace  Y@RIM@ J@L@L na aura? Ku biyone domin jin wanine jalal….

 

 

Written

By

Leeemat ??..

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

Päge 1⃣1⃣

 

Na kasa bacci sai juye juye nake tayi ga yanayin garin Zaria da sanyi ni kuma ban iya kwanciya ni daya ba tare da naji dumin jikin wani ba,ko a gida haka nake manne wa jalilah saboda banason sanyi ga kuma tunanin auran da nayi bansan a zahiri jalal mai wanki da gugan gidan mu na aura ko kuma yarima jalal dan sarki na aura ba,haka dai tunani yamin yawa ga sanyi ya daman kamar nayi kuka bani dayin bacci ba sai da asubah(kunsan dai shaidan babu abinda bazaya iya ba sai lokacin sallah na samu Mai dadin gaskiya).ban tashi ba saida naji saukan ruwan zafi a jikina kuma kunsan Allah inaga tafashashshan ruwa ya xuba min domin naji xafin ruwan har zuciyata dama ga jikina baida kyau nan da nan wajan ya tasa kamar wuta ya kuna ni a gun,maganan da yake yi yadawo dani maganan zuci da nakiyi,haka aka kuya miki a gidan ku da safe bazaki gaida mijinki ki hada masa karin kumallo ba,wai ma tsaya kinma yi sallah kuwa domin nasan a gida bakya sallah da wuri wai ke sanyi ko rau rau da ido nayi nace masa wlhy sanyi yayi yawa banyi sallah ba fincikoni yayi ya fitar da ni waje na dibo ruwa a wani randar da ake sallah a masallacin da ke gefen gidan ya zaunar dani oya Fara alwala mugani ina taba ruwan hannuna yayi wani shocking na yarfa hannuna ina mai bashi hakuri ya barni na shiga ciki nayi In kuma bai yarda ba na dibo ruwan zafi nayi dashi,ga jikina duk a jike sakamakon ruwanda ya zuba min a jiki,haka nake alwalar ina kyarma jikina sai rawa yake kamar wacce ake kada da ruwan bazari ina gama nakasa tashi saboda yanda jikina ke rawa dibo wani ruwan yayi yace tunda sanyi bai isheki ba bari ba karo miki a guje na shiga ciki ina idar da sallah kichen na nufa na masa breakfast mai sauki na kawo masa da ruwan zafi a flask ina ajiyewa yace nashiga kichen In bude kichen cabinet zanaga garin coffee na kawo masa,ina kawo masa na juya zan tafi yace daga yau abinda zaki rinka kawo min kenan in kin kawo min breakfast to kawai nace na juya na shiga ciki wanka na fada ina fita na saka leshi mai ruwan pauda da ruwan kwai sai da ratsin purple gaskiya favourite colour dina kenan(pink yellow and purple ) ina gama na fita na tarar da bayanan na dan leko waje na aika a kirawomin jakadiya na komu ciki na tarar da abinci a kan dining table na zauna sainaga note a gefen cooler din ina budewa sainaga a rubuta abinci ne daga gun hajiya ina budewa naga su kayan mu da gargajiya ne naci sosai na kai saura kichen na zauna a falo ina jiran jakadiya ta karaso banfi minti biyar da zama a falon ba sainaji salama na bada umurnin a shigo tana shigowa tafara kwasar gaisuwa na amsa sa’ananan na gaida ita tare da fada mata bukatata nason ta fadamin labarin jalal murmusawa tayi sa’annan tace tohhh..

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

Päge 1⃣2⃣

 

 

 

Sarki jalaludden muhammad shine mahaifin yarima yana da mata biyu sarauniya amina itace uwargida kuma matarsa ta farko auran gida aka musu inda sarki bayasonta itace ke so asiri suka mar har ya aure ta anyi aure shekara daya ta haife masa na mace yayi murna sosai ta biyu ma haka mace bai damu ba saboda masanin adini ne sosai, ta uku ma mace duk bai damu ba mutanin fada suka bashi shawara akan ya kara aure mana murmushi yayi sa’annan yace mu kara hakuri mana dodo yaran nawa ne uku fa insha Allah mu tsaya muga abinda Allah zayayi nan gaba mana  sarauniya amina kuwa magana yazo kunnin ta akan ana shirin sarki ya kara aure idan bata haife magajin sarki ba hankalinta ya tashi ta fara shige shige domin ta samu na miji har Allah ya bata wani cikin murna ba’acewa komai domin wani malami yace mata zata haife na miji haka dai kowa a masarautar yana jira sammanin na miji zata haifa haka dai ranar da zata haihu gidan sarki ko ina shuru kake ji domin kowa ya kasa kunne domin yaji me za’a fada haka dai ta haihu lafiya anata sanarwa ni kuwa leeemat na kagu naji me aka samu abinda kunnuwa na suka jiyu ya saka wayata faduwa….

 

 

Written

By

Leeemat💮….

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

Päge 1⃣3⃣

 

 

 

Kunnuwa suka jiyu min Allah ya raya mana gimbiya yar sarki bari mu leka dakin mai jego sarauniya amina kuwa babu abinda take sai kuka tana Allah ya isa wa malamin da yace mata na miji zata haifi saboda ba’udan kudin da ta bashi babu yanda aka iya anyi suna amma ba’a dadin rai ba bayan sati biyu an hadu a pada waziri ya fada ma sarki akwai wata yarinyar da ya yaba da hankalin ta a gidan wani makocina ko za’a daura muku aure da ita insha Allah za’a samu abinda ake so,sarki yace za’ayi haka waziri yace babu abinda baza’ayi ba yallabai sarki yace to amma zanji mu dan gana da ita,waziri yace babu damuwa basai ka tafi ba sarki yace a’a zan tafi kar ka damu haka dai sarki ya shirya suka tafi saiga sarki a gaban budurwa ana hira abin gwanin sha’awa,sarki ya kasa kwanciya sai tunanin fa’iza haka dai ba’a dauki wani lokaci ba aka daura aure amarya fa’iza ta tare a gidan mijinta saidai wani abun mamaki tunda aka kawo ta bata kara ganin angonnata ba kusan wata daya kenan ta rame saboda damuwa sallah kuwa babu dare babu rana tana kai kukanta ga rabbin izzati ya karkato mata da kan mijinta kareta saboda tanajin lbr uwargidan ta da biye biye gefen sarauniya amina kuwa tunda taji lbrn sarki na tafiya hira da tashi tsaye da shige shige har Allah ya bata sa’a asirin ya kamashi a ranar da aka kawo amarya,fa’iza kuwa babu irin abinda bata gani da dare intana barci amma sakamakon adu’a datakeyi  aka dai take ta fama wulakancin Kala kala babu wanda bata gani daga gun sarauniya har kuyanganta haka dai take hakuri har Allah ya amshi adu’ar ta…..

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

Päge 1⃣4⃣

 

Ranar AL’amis da dare ta idar da sallah isha’i kenan tana adu’a saitaji anyi salama har tsoro ya kamota tana tunanin waye kenan da Daren nan ta mike ta budi kofar wa zata gani sarki tayi wani ajiyar zuciya sa’annan ta mashi gu ya shiga ciki ya zauna ta kulle kofar ta kawo masa ruwa da abinci domin bata rasa da abinci a gidanta yayi murmushi yace amarya bakya laifi kamar ko kinsan banci abinci ba murmushi tayi ta gaidashi ya amsa yana mai kallonta tare dacin abinci yana santi ita ku mezatayi sai dariya ya gamaci ta Karo masa ya cinye ya karace a karo masa binsa kawai tayi da ido ta tashi da kawo masa yankakkyan kayan marmari yasha sosai sa’annan ya dan kishingide,yallabai yallabai tashi ka tafi dare yayi fa sosai domin har ya Fara bacci lumshe idonsa yayi yace korata kike tace waneni yayi murmushi yace to yau a anan zan kwana zuciyarta yayi fari tare da godiwa Allah daya amsa mata adu’ar ta,cikin damuwa tace anty amina fa yace tana bangaranta mana ai tasan inada amarya ai murmushi nayi cikin jin dadi nace to tashi kayi wanka yallabai na hada masa ruwa yayi kwanka kafin ya gama kwankan na fitar masa da rigar bacci na ajiye masa a kan gado yana fita ya ganni a kwance cewa yayi har zaki kwanta eh kawai nace masa ya gama saka kayansa ya kwanta kusa dani,inda yafara sarrafani nikuwa mezanyi sai adu’ar mijina ya dawo gareni har yana niman hakkinsa kayana ya fara cirewa sa’annan tsoro ya dirar min amma ban nuna masa ba saboda inajiran ranar da zaidawo gareni kuma ace ban kwata ma kaina yanci ba haka dai na daure ya kawar da budurcina kuka nake na farin ciki domin adu’a nake wa iyayena da suka bani tarbiya mai kyau har na kawo abinda kowacce mace take burin kawowa gidan mijinta,sarki kuwa sai hakuri yake bani tare da lallashina a daran ya min wanka yayi nasa muka sake kwanta bacci har washegari sa’annan na tashi na hada masa kari yace ya huce pada……

 

 

Written

By

Leeemat ??

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

Päge1⃣5⃣

 

Haka dai sarki ke zowa gidan har sahon sati daya kafin ya koma bangaren sarauniya,haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya wani rana fari wani baki,yau da gobe babu wuya a gun Allah na waye gari da son cin goroba a rana daya sainaci guda goma ko fin haka sa’annan Allah ya taimakeni babu wani rashin lafiya ko Kuma wani laulayi shiyasa ma cikin ya haura wata bakwai babu wanda ya sani sai sarki haka dai muke rainon cikin har ya kai watan haihuwa sarki yace bazan haihu a Nigeria ba aka mana shirye2 tafiya India kafin sarauniya amina tasan ina da ciki nan da nan ta huce gidan malaminta inda take fada masa abinda yafaro murmushi kawai yayi yace mata yanzo me kike so tace masa ita tanason indan suka tafi kar su dawo su mutu daga ita har abinda yake cikinta,malamin dariya yayi yace bazayaji ba saboda matan tana da kariya sosai amma abinda zan iya miki shine idan ta haihu saimu karkata hankalin mijinki ya dawo gareki bakince tare zasu tafi ba ta daga masa kai yace to zaki iya tafiya ta danka masa kudi masu yawa tayi tafiyar ta.kafin ta dawo amarya fa’iza Sun tafi tana dawowa ta kira wayan sarki take fada masa akan mamanta ne bata da lfy ta tafi gaida ita to kawai yace tare da cewa Allah shi bata lfy tace ameen.

Sun sauka garin India inda suka tafi masaukinsu saboda sarki yana da gida a gun haka dai suka cigaba da rainon cikin har ranar haihuwar ta yayi ta haife yaron ta na miji mai kama da ita murna kuwa ba’a cewa komai ya kira waziri yafada masa abinda aka samu masarautar kowa na cikin farinciki inda sarauniya amina na cikin bakin ciki har kuka sanda tayi…

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

Päge1⃣6⃣

 

Sarki ya masa huduba da fu’adudden inda suke kiransa da fu’ad bayan sati daya suna shirin dawowa domin ayi suna amma fu’ad ya tashi da masakaicin ciwo suka dakatar da tafiyan su aka kaishi asibiti yayi kusan wata daya a asibiti yana warkewa doctors din suka basu shawara Akan su guje abinda zai saka shi kwanciya wai da sunan baida lafiya saboda shi irin mutaninda in rashin lfy ya kwantar da su sai Sun kasance a kwance na sahon wani lokaci kafin su farfadu suka dawo gida,haka dai suke kula dashi har ya kai shekara uku suka saka shi a makaranta a Indian tare da saka shi a islamiyya.sarki kuwa anata kiransa a gida akan ya dawo kan milkinsa yanajin su saida yaga idan ya musu haka bai kyauta WA kansa ba sa’annan ya fara shirin bar  India a ranar da zaya dawo ya fadawa amarya fa’iza akan da zarar ya kammala primary dinsa itama ta dawo gida ta barshi ya cigaba da karatun sa ta masa korafi akan lafiyansa yace mata akwai wanda zasuna kula dashi Kuma bayason tayi nisa da shi haka dai ta hakura tacigaba da zama da danta har ya gama primary an masa komai na secondary sa’annan tayi shirin dawowa gida Nigeria inda sunyi kukan rabuwa,fu’ad kuwa yayi kuka sosai saida ta hanashi kafin yayi shiru tana tsoron kar kukanda yayi ya saka masa wani rashin lafiya,haka dai ta tafi ta barsa dashi da masu zama da shi.

A lokacin sarki ya dawo gida kuwa sarauniya ta rinka murna ita a nata tunanin maganin da aka masa ne bata kuwa san saboda mutaninsa ya dawo ba…

 

 

 

Written

By

Leeemat 💮……

.

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

Päge 1⃣7⃣

 

 

Amarya fa’iza kuwa tundaga kan fu’ad bata kara koda batan wata ba,bata nuna damuwanta ba saima godiwa Allah tayi tunda har ya bata fu’ad,inda kuwa a bangaren sarauniya taci alwashin sai ta halaka fu’ad ko badade ko bajima toh yaya kenan za’ayi mundai ji furucin sarauniya amina,bari mu leka India.

India kuwa fu’ad tun yana damuwa har ya dawo ya daina damun kansa inda ya mayar da hankalinsa  kan karatun sa yana gama jss three sai aka applying masa school of army dake New Delhi saboda fu’ad akwai son soja ya fara daga ss1 har Allah ya taimaka ya gama sa’annan yacigaba daga inda ya tsaya yayi karatunsa har ya gama lafiya sukayi passing out parred ya fita da second leutinant suka dauke sa aiki inda suke zama a barriki,aiki yake cikin gaskiya da rikon amana inzasu tafi yaki kuwa a koda yaushe suna cikin nasara idan wayansun su Sun samu rauni shi yake musu treatment saboda Allah ya bashi wannan baiwar….

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

Päge 1⃣8⃣

 

 

Akwai wani yakin da suka tafi duk da dai su sukayi nasara amma mutaninsu sunji rauni sosai bayan fu’ad ya gama treating dinsu sai major dinsu yayi kiransa a office dinsa yanatafi ya sara masa yanda dai munsan sojoji ke yi yace masa ya zauna yana zaunawa saiya fara da cewa dama wani sharawa na kawo amma bansan ya zaka dauke a abinba murmushi fu’ad yayi yace sir ai shawara kace ai nasan mai kyau ce fada min ina saurarunka sai yace masa naga kana da baiwar treating mutani to me zaisa bazaka tafi course na likitanci ba iyaso dai idan ka dawo sai ka cigaba da aikin ka anan kana duba mana marasa lafiya,fu’ad kuwa ya amince suka turashi course na shekara hudu a California yaso ya tafi Nigeria ya sallame ma’a dinsa amma amarya fa’iza tace ita tafi son idan zaya taho ya taho gabadaya haka dai ya hakura tare da missing dinta…..

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

Päge1⃣9⃣

 

 

Ya tafi California tare da samun nasarar karatunsa har ya gaima saidai karatun yaso yadan bashi wuya kadan amma da taimakon Allah da ta adu’a ya gama ya dawo India na nasarori sosai inda yayi kudi sosai abin sai wanda kagani kawai,yayi aiki a India saida ya kai matsayin major kafin ya dawo Nigeria inda aka hada masa liyafa ta ban girma saboda tunda amarya fa’iza ta tafi India da cikinsa sai a ranar aka Fara ganinsa amma a garin Zaria babu wanda baisan labarin dan sarki ba duk da ba wanda ya taba ganinsa haka dai a ranar da ya sauka garin Zaria cewa zakiyi shugaban kasa ne yazo haka dai suka masa liyafa akaci aka sha,inda mata kuwa sai kawo kansu suke amma duk sonda suke ikirarin suke masa na karya ne wasu saboda kudinsa wasu Kuma saboda mulki,haka dai ya tayi har ya auro ki amma bansan ya akayi har ya yarda an muku aure ba saigashi kina tambayata labarinsa nasan duk yanda akayi bakisan waye yarima dan sarki ba.daga mata kai nayi tare da cewa tabbas bansan shi ba amma jakadiya meyasa ake kiransa da jalal bayan sunan sa fu’ad toh me karatu ku biyomu domin jin meyasa ake kiransa da jalal taku mai son nishadantar da ku leeemat

 

Written

By

Leeemat💮…..

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

2⃣0⃣

 

 

Yarima fu’ad Wanda akafi sani da yarima jalal duk da dai ban zauna da shi a lokacinda yake India ba amma yarone mai hankali ya tashi da taimakon na kasa da shi,ko a makarantar su in zasu zana jarabawa yakan taimake wanda basu sani ba duk da yana fuskance matsala saboda ana hukuntashi amma bai hanashi taimako ba sa’annan tun bai mallake hankalin kansa ba yake bayar da zakkah saboda malaminsu yamusu WA’azi akan idan mutun yana da arziki da kudi sosai to Allah yace ya bayar da zakkah tun daga lokacin ya fara zakkah saboda anasa tunanin shima yana da kudin da zaya iya baida zakkah,da azimi kuwa abin ba’acewa komai saboda yana saka a dafa abinci kullum ana kaiwa masallatai tare da gidan marayu da yamma kuwa idan za’ayi breakfast watan lokacin sha ruwa kenan tea ake da bread a bawa basu bukata,yayi gidan marayun da bazana iya lissafa miki ba da yake daukan nauyin komai nasu cin su da shan su duk tare masallatai,lokacinda ya dawo Nigeria kuwa abinda yake a masarautar nan sai san barka saboda duk wani abinda mai martaba sarki keyi haka yarima yakeyi kamar yanda bayi sa’annan ya hada musu aure da mazajansu bayi yantattu sa’annan shi yake komai na auran ya kuma bawa mazajan aikin yi.

Saboda hali irin na yarima fu’ad babu abinda bai dauka ba a hali irin na mahaifinsa shiyasa muka lankaya masa ko kuma nace muna kiransa da sunan mahaifinsa wato ❗Y@RIM@ J@L@L❗…….

 

 

Written

By

Leeemat??

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

2⃣1⃣

 

 

A ranar na dafa masa abincin da ni kaina bansan na iya dafa abinci mai dadi sosai haka ba,ina kammalawa wanka na fada nayi sallar asr na fito falo na zauna ina kallo domin inada tabbacin zaya shigo idan ya dawo daga gun aiki saboda duk da dai ban zauna da shi sosai ba amma irin mutanin nan ne da idan nauyi na kansu suna kokarin saukewa ban idar da tunanin da nake ba na jiyu sallamar sa na amsa ya shigo na gaida shi ya amsa sa’annan na kawo mar abincin sa ina ajewa na shige daki mintina kadan naji yakirani (R@NI S@HIB@)a raina nace na yau kuma kenan na gobe saiyafi haka yau kuma sunan da za’a kirani dashi kenan a gidan mu SONI@ yake kirana oho ai na ma mance dan India ne jin wani kiran nayi da sauri na fito gani wai ke wacce irin mara hankali ce ke sau nawa na fada miki akan a duk lokacin da zaki kawo min abinci inason ki kawo da coffee ya hakuri na mance ne shiyasa kafansa ya dura akan kafata ya matse wani kara na saka sa’annan yace kinga wannan zaya tunatar dake a duk lokacin da zaki kawo min abinci kichen na huce na kawo masa zan huce daki yace dawo nan ki zauna haka kike ganin mom keyi a duk lokacin da ta kawo ma dad abinci?na dawo na zauna a kujeran da ke fuskartansa ina mai kallon irin halittar da Allah ya masa…..

 

 

 

 

!Y@RIM@  J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

2⃣2⃣

 

 

Fu’ad dogo ne  sosai na nuna wa sa’a fari ne shi irin dai fatar indiyawa sa’annan ga sumar sa inda dai kuka ga na India a raina nace dole komai naka ya fita irin tasu ko saboda komai naka da rayuwan ka a garin kayi shi Wow beauty point dinsa kuwa ba’a magana saboda duk abinda yake ko magana yake ko karatu zakaga ya lutsa baton idanunsaa kuwa sleeping eyes gareshi ga idon manyan2 dasu kamar an masa gorin idon shiyasa idan ya daga ido ya kalleka duk fitsarancinka sai ka natsu saboda yanda idon keyi like magic,fatar jikinsa kuwa kina ganinsa kawai kinsan dan hoto ne saboda yanda skin dinshi yake fresh ga wani sheki da yake yi kamar ba soja ba,kirjinsa kuwa a bude yake tafiya yake a baude kamar dai soja.idan an zo batun magana kuwa kamar ana saka shi dole ne kafin yayi wani magana mai tsayi sai da wani kwararrar dalili sa’annan yana maganar tare da lumshe ido kamar mai shirin bacci kai dole ne ma idan yana magana ya bake sha’awa.mari na ji amma hannun nasa kamar auduga naji a firgice na kallesa yace me haka da wani kallo kamar tsohowar mayya kallonsa kawai baki a budi saboda yanda idonsa keyi a raina nace maiyasa ban taba lura da fu’ad kyakyawa bane sai yau……

Leeemat ??

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat)💮

 

2⃣3⃣

Inma maitar kika ci to kurwata kur yafada, bude bakina nace masa ai haka mom takewa dad in yana cin abinci ko ba kai kace min inyi abinda mom ke ma dad ba nayi maganan cikin shagwaba kamar zanayi kuka kallo yake saboda yanda na masa kyau tashuwa nayi nace masa nima kurwata kur yanda yafada da hausansa kamar na makoya amma fa idan kaji zakayi zaton slangs na hausa yakeyi amma hausan ne bai tsaya masa a baki sosai ba Cup ya dauka ya jefeni dashi kafin na shiga daki Cup din ya saman a kafa faduwa nayi a gun ina mai yarfar da hannu na alamar zafi nan da nan jini ya fara gangarowa.fu’ad kuwa ko a jikinsa saima kama gabansa da yayi a haka na shiga bayi na wanke ina saka ruwan dettol ina ihu kamar wanda aka sakani dole saboda zafi.haka dai nayi jinyar kafata har ya warke fu’ad kuwa ko sannu bai taba hadani da shi ba a cewar sa ai nima likitace zana iya kula da kaina basai an kula dani ba.

 

 

 

 

 

!Y@RIM@  J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

2⃣4⃣

 

 

 

 

Tashuwar asuba kuwa babu abinda ya janza domin kuwa kullum shi yake tashina nayi sallah sa’annan da ruwan zafi haka dai har na saba tashuwa da ruwan zafi a jikina ni kuwa wai na irin tashi wani rana kafin yazo din nan bana iyawa saboda sanyi masarautar ko ina bishiya kamar wani dauji.nayi wata daya chaf kafin na fita a gidan muka nufa fadan sarki jalal muhammad mulki akwai wahala sannan akwai dadi tafiya muke cikin kaya ta alfarma duk inda muka huce gaisuwa ake mana fu’ad kuwa sai amsawa kawai yake cikin Fara’a da kamala kawai sainaji sonsa ya kara tasiri a cikin zuciyata muna isa fada muka tarar babu kowa sai sarki yana jiran mu muna shiguwa da murmushi a fuskarsa yace yau na bawa kowa hutu ya zauna da iyalansa inason na gana da ya ta murmushi kawai nayi muka gaida shi cikin girmamawa yace ma fu’ad babu ruwana da kai fu’aduddeen tunda kanamin rauwar yata sai yau kaga damar kawo min ita susa keya yayi alamar kunya ni kuwa kamar na nitse a kasa saboda kunya ya juya ya fuskanceni bari muyi maganan da da mahaifi fu’ad yawani tura baki kamar wani karamin yaro Papa wato anyi sabuwar ya shine kuka manta dani daga kai har ma’a ko to shikenan babu damuwa kowa da ranar shi,sarki kuwa ko sauraransa baiyi ba yace min ya ta nace na’am babu wani matsala ba ko na juya na kalle fu’ad yanda yamin da idonsa ya saka ni saurin kawar da fuskata.sarki yace min kar kiji tsoro ki fadamin idan da wani abu budi bakina sainace…….

 

 

 

Written

By

Leeemat💮….

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

2⃣5⃣

 

 

 

Babu komai fu’ad ya sauke wani ajiyan zuciya sa’annan yayi murmushi yace Papa kana shakku da irin rikonda nake mata ne sarki yace a’a bada kai nake ba kamin shuru amma ya ta kamar da magana a bakinki amma kin kasa fada min nayi murmushin da bai kai zuci ba na rasa wani karya zana masa sai wani dabara ya fadu min sainace masa dama so nake na ga mom da dad amma yace ba yanzu ba nan da nan fuskar sarki ya sauya ya fara fada amma fu’ad ka ban kunya ace yarinya nason ganin iyayenta amma ka kasa kaita su gana ina kai kullum saikaga naka iyayen amma kar ka sake yin haka Kuma ko kullu yaumin take son ganinsu to ka tabbata ka gaita.kai daga yau na kafa doka duk ranar jumma’a a kaita itama ta gaida iyayenta godiya mukayi sa’annan muka nufa bangaran  sarauniya amina,sallama mukayi fu’ad ya zauna tare da cewa mamuji ganinta mukayi ta fito a daki cikin shiga ta alfarma tana ganinmu da Fara’arta ta karaso tana fadin a’a yata tashi ki zauna a kujera mana saboda a kasa na zauna tun farkon zowana a kasan ma naga irin tarbar da ta min ballatana zowana ta biyu amma mamaki ya hanani rufe baki.cikin mamaki nace a’a nan ma ya isa ta hada fuska tare da cewa nace miki ki tashi ki zauna sa’annnan na tashi na zauna ta saka aka kawo mana abin mutsa baki dukkan mu mukace mun koshi saita ce oho my son yau Kuma baza’a ci abinci a gidana bako saboda an taho da amarya ko Kuma dai kana tsoron karta xane ka inkun koma gida ne dariya kawai mukayi muka sallameta sai gidan mahaifiyansa muna shigowa na cire rigarda ke cikina saboda zafi na kwanta a three seater…..

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

2⃣6⃣

 

 

 

 

Muna komawa gida yana bude kofa na shiga daki a guje domin nasan nayi laifi amma me kafin na kulle kofata ya shiga dakin ya cafkoni ya jani zuwa bangon dakin yana kokarin sunbatata ina kokarin kwace kaina hannunsa ya tallafe kaina ya fara kissing dina,naji dadi amma sai zafi nake ji kamar labban bakina zai fito saboda zafi yana gama yace ki kara saka papa yamin fada saboda ke sa’annan karki san irin maganan da zaki rinka fada masa wannan kadan na miki yafice a dakin hannu na saka a labbana ina taba saboda zafin da nakeji.washegari na kai masa abin kari tare da coffee dinsa na mance da kashejin da yake min na gaisuwa bugu naji a bakina wani kara na sake saboda zafin da ya ziyarce ni da sauri na gaida shi sa’annan na saka hannuna a baki naga jini da sauri na shiga daki na nufe gaban mirror ina duba bakina sainaga ya kumbura a raina nace me ya saka bakina yin haka ba zanace dai bugun bakina da yayi ne ya saka bakina haka ba,ok ko dai kiss da yamin jiya ne yasaka bakina yin haka amma kuwa Allah ya isa na fada tare da cire anpiclox na sha,

Ina zaune a falo da kumburarran bakina yace min yau jumma’a amma bazaki tafi gida ba sai bakinki ya warke saboda kar suce ban iya riko ba a raina nace dama ka iya ne,amma fili sai nace masa to Allah ya kaimu ya kalle ni cikin mamaki yace hmm baki ya mutu ko da kuwa na nuna miki ko ni waye da kin min wani rashin kunya….

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

 

2⃣7⃣

 

 

 

 

Cikin ikon Allah har bakina ya samu sauki jumma’a ta kewayo ya kaini gidan mu na shiga da ihu ina mom domin nasan tana gida saboda ranar jumma ‘a bata dadewa a office bayan mun gaisa nake fada mata abin AL’ajabi jalal yaron aminin dad ne sarkin Zaria mom itama kanta tayi mamaki domin yan uwanta babu wanda ya fada mata murmushi tayi cikin cin dadi tare da cewa kai amma nagode wa Allah amma dad dinku bai taba cin min komai ba kullum ina cikin damuwa ya tura ko su hassan da hussaini ne su duba ke amma saiyace lafiyan ki kalau amma meyasa kika rame haka nasan ki da rashin cin abinci ko Kuma dai kina da wani matsala ne ki sanar dani murmushi nayi nace mata wlhy babu komai mom komai lfy kalau kinsan yau da gobe sai Allah bare ni da na tsince kaina a cikin sarauta kinga kuwa sai a hankali zana saba muka hira kafin na ce mata zani gidan jalilah tacemin abincin fa nacemata in na tafi gidan jalilah zanace mom tace da take fama da rashin lfy shine zaki sakata wani aikin ko domin nasanki da Sun jikin babu gara babu dalili a raina nace da kuwa kinsan irin aikin da nakeyi yanzu da baki cemin mai son jiki ba ina shiguwa gidan sainaga jalilah a jikin mijinta saina koma baya nayi sallama ganin jalilah nayi tana oyoyo sis simra cikin dariya nace ya akayi kika gane muryata tace amma ai ko a cikin magagin bacci ne san gane muryanki,mijinta kuwa ya gaida ni sa’annan yace hmm yau anga yaya simra na huta da kuka kullum waini inkai gun ki batasan a wani hali kike ciki ba dukkan mu mukayi dariya sa’annan ya fice a gidan to ni bari na fita tunda ga yayanmu ta zo ko cikin shagwaba tace masa yaushe zaka dawo cikin lallashi yace nan bada jimawa ba,kallon such as nake  cikin sha’awa saboda yanda suke tafiya da rayuwansu ta birgeni sosai……

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat)💮

 

 

 

 

 

2⃣8⃣

 

 

 

 

 

Sis simra ina magana kinyi shuru na juya ina kallonta ina mai murmushi rayuwanku ne abin sha’awa jalilah tace yaya simra mu bar wannanan maganan yaya gidan yake ko kuma nace kauyan yake cikin murmushi tace jalilah a garin nan muke gidan ma a gidan sarki aminin dad jalilah cikin cikin mamaki tace kina kardai nace jalal shima yana daga  cikin bayin gidan ne amma yantacce simra tace ko daya jalilah ina munajin labarin yarima jalal a lokacin da muke gida da har kike damuna da kinason kuwa ki ganshi saboda irin labarin da ake bayarwa akansa to ba wani bane yarima jalal sai jalal mai mana kwanke da guga.cikin kaduwa jalilah tace kina nufin jalal shine yarima jalal dan sarki jalaluddeen muhammad! Murmushi nayi na tace mata kwarai da gaske kina mamaki ko sa’annan na fara bata labarin shi amma bansan ya akayi  har yazo gidan mu ba sa’annan na fada mata irin abinda yake min saboda bama boyewa junan mu sirrin mu ina kuka har na gama fada mata tare da cewa kinga abinda na masa Allah ya juya lamarin ya zama mijina kuma walhy tunda an daura mana aure nayi alkawarin masa biyayya amma shi babu irin wulakancinda bayamin hakuri jalilah ta rinka bani tare da cewa kar ki damu wata rana sai labari saikinyi alfahari da auran sa godiya na mata muka shigaba da hiranmu wanda duk nasa ne da tuna irin abubuwanda yake mana lokacinda muke gida amma bamu taba lura da irin abubuwanda yake yi kamar na jinin sarauta  amma bamu taba gane ba har kusan magriba kafin na bar gidan ina shiguwa gida na tarar da  fu’ad na jirana gabana sai faduwa yake tayi kichen na nufa na kawo masa abinci ina ajewa ya kama hannuna ya matse da farcansa nayi kaman banji ba saboda mom na gun amma fa ina shiga kichen na duba hannuna naga har yana jini ina shiga falo na tarar ko taba abincin baiyi ba haka muka tafi gida gabana sai faduwa yake saboda fargaban abinda zan Tarar…..

 

Written

By

Leeemat 💮

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ Y@RIM@!

 

Nah halima musa akano (leeemat )??

 

 

 

 

2⃣9⃣

 

 

 

 

Muna isa gida yace na dafa masa abinci yunwa yake ji cikin mamaki nace masa amma na kawo maka abinci kace bazakaci ba ka koshi saiyace to yanzu zanci ko kuma ban isa na sakaki bane Allah ya baka hakuri na shiga kichen na masa indomie na kawo masa yauwa wa ya baki izinin tafiya gidan jalilah cikin inna inna nace masa babu kowa oho saboda kin rainani shine kika tafi ba Tare da izinina ba koh to yau zana hukunta ke dai dai da laifin ki cikin kuka nace dan Allah ka yahakuri bazan sake ba ko ta kaina baiyi ba ya huce side dinsa ya kawo kayansa ya watsa min a jiki tare da cewa yanzu nake son ki wanke sa’annan ki goga saboda gobe zana fita radin suna cikin hawaye na mike tare da kwashe kayan na nufa toilet na fara wanke kayan har hannuna na jini saboda alkyabba ce akwai karfe2 a ciki amma haka na wanke ga idona kamar zaya fada a kasa saboda baccinda nake ji ban gama wankin ba sai sha biyu na dare saboda tsoro ban iya fita waje na shanya kayan ba a toilet na shanya nayi zaman hour biyu amma kayan kamar yanzu na shanyata ganin karfe biyu ya huce har da kwata ya sakani kwanciya nayi bacci da niyar da safe zan tashi na goga kafin ya shigo. amma me cikin barci naji kamar ana zuba min ruwan zafi da sauri na mike tare da bude ido amma hasken ranar da ya kashe min ido ya sakani rufe idona cikin sauri, cikin fada yace har na fita suna na dawo amma baki tashi daga bacci ba ina kayanda na sakaki wanki da guga cikin sauri na nuna masa hannuna daya tashi saboda wanki nace masa wlhy na wanke amma ban guge ba fincikoni yayi muka fita falo yace oya maza dauko ki taho nan ki goga yanzunnan ina shiguwa daki kuwa alwala nayi na yi sallah da sauri sa’annan na fito da kayan na saka iron na Fara guga amma kamar banayi fu’ad cikin sauri yace min ki danna hannunki sosai ko bakisan wannan alkyabba bace cikin hawaye nace wlhy ina dannawa hannuna zafi yake min, nuna min hannunsa yayi yace kinga kayanki abinda yamin?tun ban iya guga ba har na iya duk da dai wani lokaci ina badawa a wanke tare da goga amma saida na kune saboda jaraba irin nake cikin kuka na cigaba da gugan har na gama……

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ Y@RIM@!

 

Nah halima musa akano (leeemat )??

 

3⃣0⃣

 

Amma duk da irin cin mutuncin da fu’ad ke min bai taba zagen iyayena ba shiyasa ma ban taba nuna damuwata ba saboda nasan ni na masa laifi ba su ba kuma yana hukuntani ba tare da su a ciki ba haka dai na cigaba da rayuwa a gidan fu’ad babu abinda na nima na rasa ta fannin abinci har ma sitira sa’annan ko wani jumma’a ina tafiya gaida iyayena abu daya ko kuma nace biyu shine kawai damuwata amma ni daya yafi damuna wai ace ina matsayin matarsa amma ban taba tafiya side dinsa wai da sunan gyarawa ba sai na biyu wani abu bai taba hadani da shi ba wai da sunan tarayyar aure saboda yace saiya gyara min zama sa’annan zayayi zaman aure dani ni wannan bayama damuna kamar hanani gyara masa makwancinsa sai bayin gidan su suke gyara masa ni kuwa abin haushi yake ban amma babu yanda na iya saboda ya ce a duk ranar da ya tarar dani a side dinsa ko kuma an fada masa saiya karairaya min kafata kamar na muciyan nan shiyasa nake wa kaina kiyamallaini…..

 

 

Written

By

Leeemat ??…

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )??

 

 

 

3⃣1⃣

Yau ta kasance ranar juma’a mun dawo daga gidan mu kenan fu’ad na zaune a falo da kofin coffee a hannunsa na zauna a kasa a gefensa nace masa dama so nake na maka magana inajinki ya fada tare da cigaba da shan coffee dinsa dama dad ne ya min magana akan aiki wai ya samu min aiki shine yace na fada maka saika amince kafin na fara tafiya ina gama fada masa ya juya sosai yana mai kallona da sleeping eye dinsa ya lumshe su saiyace min ina miki murna da samon aiki amma inason kimin wani aiki guda daya kafin ki fara zuwa aiki sa’annan zuwanki aiki bazaya canja daga abubuwanda kike min ba cikin murna nace masa me kake son na maka ka fadamin kuma nayi alkawarin insha Allah zan maka shi,toh mai karatu saiku biyomu domin jin me yarima jalal ke son a masa taku har kullum leeemat ??.

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )??

 

 

 

 

3⃣2⃣

 

 

 

 

Kallonsa nake ina jiran ya fadamin me yake son na masa amma bai fada ba saima cigaba da shan coffee dinsa da yayi ina zaune har ya kammala shanyewa saiyace min wani baba nake son ki masa aiki a kafa ina medicine and surgery kika karanta na daga masa kai yace magana nake miki da baaki ba da kai ba eh na amsa masa,ya cigaba da cewa maciji ya sare shi babu inda ba’a kaishi ba amma idan kafar ya dauke warkewa saiya sake dawo kamar sabo kuma wata uku kawai na baki kije kiyi tunani in zaki iya to zaki fara tafiya aiki da zarar kin gama aikin amma in bazaki iya ba to kinga zaman gida ya kamaki daman inda kika fi dace kenan yana gama yace to zaki iya tafiya ina jiranki nan da two days mikewa nayi cikin kasala na huce dakina ina mai tunanin abinyi, idan na tuna da kalmar da yake cewa wai daman zaman gida ya kamace ni da gurbataccan hausa dinsa dinnan sainace raina ya kara bace (amma fa yanda yake hausan ma abin a tsaya saurarune ).kai zana maka cewa mu mata zaman gida bamu ya kamace ba ina gama tunanin abinda zana fada masa na kwanta sai barci…..hmmmmmmm ku biyomu

 

 

 

Written

By

Leeemat ??

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )💮

 

3⃣3⃣

 

Washegari na gama hada masa breakfast na kawo masa da coffee dinsa ina zaune har ya gama ya tashi ya koma falo ya zauna na bishi a falon nace masa maganan jiya ne nake son nace maka na amince, cigaba da kallonsa yayi kamar babu mutun a wajan. daga bisani yace min to Alhamdulillah gobe za’a kawo shi a dakin wajan nan zai zauna bude bakina sainace masa ah meyasa baza’a kawo shi yau kawai ba nayi maganan ne cikin gatsi har saida ya juya yayi kallona ni kuwa a raina murna nake saboda inada nawa kimar tunda har an juya anyi kallona.cemin yayi abinda yasa ban kawo shi yau ba saboda inason na gyara masa dakin ne tare da kayan aikin da zaki mishi kwabe baki nayi na tashi alamun I don’t care dinnnan na huce dakina tare da cewa Allah ya kaimu fu’ad kuwa kallona yake baki bude saboda mamakin da na bashi. Washegari abinda na saba yi kullum aka yau ma nayi ina jiran patient dina ba’a kawo shi ba sai da yamma lokacinda ma na gama komai na gida nayi wanka sallah nake yi naji sallamar fu’ad daya ga ina sallah ya fito  falo ya xauna ina idarwa na gama adu’o ina a raina nace wato ina sallahr ma bazaya jirani a daki ba sai ya bani wahalar biyosa falo bayan abinda yake nima a guna bukatarsa ne ba nawa ba.na shiga falon na xauna nesa dashi nace masa sannu da dawowa amsar da yabani wlhy haushi ya kamani cewa yayi gashi an kawo shi zaki iya zuwa kiganshi ko ya tashi ya huce, raina a jagule na tashi na bi bayansa

 

Oh ni leeemat bansan me ya same gimbiya simra ba ganinta kawai nayi tanata kwarara amai 😳 ko dai abin ne an samu 🙈

 

 

Written

By

Leeeemancy💮

 

📢👏🏽📢👏🏽🎂🍰🍦🍕🍟🍔🍺🍺🍻🍡🍗🍣🍲🍞🍘HAPPY Birthday MAMAN ALEESHA wishing you happy many many returns and may u celebrate more and more of it……..

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )💮

 

 

 

3⃣4⃣

 

 

 

Ina dosowa kofar dakin nafara jin wari  muna shiga dakin kuwa sai abinda ma ya karu cikina har wani koowa yake na dan kalle fu’ad ta gefen ido abin mamaki kamar bayajin warin ni kuwa kamar zanyi amai amma na daure saboda kar na bashi kunya ballanta da naji yana cewa baba ga mamata wacce zata kula da kai murmushi yayi yace falalu  haka yake kiransa ko kuma yace muhammadu saboda yace sunansa da wuyan fadi haba haba duk dawainiyyar da mai martaba yayi dani kaima ka gwada naka bajintar ba’ace sa’a ba da ka bari ai har Allah yayi halinsa cikin dauriya nace haba baba ai ciwo ba mutuwa bane zamu gwada wannan mugani insha Allah zaka samu lfy nayi shuru domin ina gab  dayin amai na juya gun fu’ad nace masa sai gobe kenan zan fara dubashi Baba yace Allah ya kaimu na gode sosai Allah yayi muku albarka mukace ameen.fu’ad ya mike tare da cewa to baba saida safe ko  yace Allah ya tashemu muka fita a dakin fu’ad yayi side dinshi nima nayi nawa,da gudu na karasa toilet dina saboda amai da ya tahomin nayi ta kwararan amai kamar hanjin cikina sai fito, a ranar dai baccina rabi da rabi ne saboda amai har na galaibaita da naga ban samu nayi baccin ba sainayi alwala kawai na cigaba da sallah(anan nake son ja hankalin mata a duk lokacin da kin since kanki da dare bakyajin bacci to kiyi alwala kinyi nafilfili kiyi ta rokon Allah basai kina cikin matsala kawai zaki na tashi sallah ba domin akwai wasu matan da masusan akwai Allah ba sai suna cikin matsala kafin zaku ga Suna ibada which is not ryt Allah yasa mu dace ameen.) ina idarwa na kwanta sai wani zuciyan nace min ki fasa aikin idan zaya zamu miki matsala Allah ma nacewa a cikin qur’ani akwai abinda bazakayi ba in zaya zame maka matsala ko zaya baka wahala wani zuciya kuma nace mata kiyi Allah zai baki ladah hakuri da juriya kawai zakiyi tunda ma mijinki ne ma ya sakaki kinga kuwa lada biyu kenan gana mijinki gana taimakon da kikayi ba tare da an baki ko kwandala ba kinga kuwa ladan mai yawa ne har bacci barawo ya sace ta bata sani ba

 

Toh ku biyu mu don jin yadda abinda zaya kasance tsakanin likitar da patient dinta.

 

Written

By

Leeemancy 💮

🍡Maman aleeesha happy birthday once again 🍣🍘🍞🍞🍲

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano (leeemat )??

 

 

 

3⃣5⃣

 

Washegari bayan na gama breakfast nayi wanka na saka labcoat dina da mask na huce dakin tare da kayan aikina ina shiga na gaida shi na tambaye shi ko ya ci abinci yace min eh na masa allura sa’annan na wanke masa kafar da concentrated hydrogen (wanda ba’a diluting dinshi da ruwa ba )ina gama na masa dressing din kafar na bashi magunguna nace mishi sai da yamma kuma zana sake wanke maka kafar.haka zamu rinka wanke kafar har muga inda Allah zayayi sai muyi maganan surgery ya ce to tare da saka min albarka na fita ina fita daga dakin toilet na huce nayi wanka yau ma nayi amai amma bai kai na jiya ba saboda mask dinda na saka.haka dai na shiga da attending ma patience dina alhamdullilah kafar na improving har muka shiga watan Ramadan abinda fu’ad yace min ayau har ya saka ni kuka saboda takaici…

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ Y@RIM@!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

3⃣6⃣

 

Ya kasance gobe za’a fara azimi bayan ya gama cin abincin dare ya kirani na taho na zauna nace masa gani sai yace min gobe za’a fara azimi koh nace masa eh saiyace ok dat means a daren yau kenan za’a tashi sahur koh nace eh saiyace min to zaki rinka tashuwa kina min abinci da asuba saboda bazana iya cin dumame ba na naga ido ina kallonsa nace masa nifa bana tashuwa nayi sahur kafin na gama maganata yace ni ina tashuwa da asuba don haka a rinka tashi ana dafa min abinci saikuma abu na biyu banason ready made juice inason wanda za’a min a gida ne with fresh fruits kin gane idona na zubar da hawaye nace masa eh saiyace abu na karshe kuma abokanaina anan zasu rinka zuwa sunayin breakfast don haka a kara hannun girkin I hope i made myself  clear nace masa eh na tashi na shige daki na fadi a gado kuka nake sosai saboda takaicin tashuwar asuba dafa masa abincin nayi kukana mai isata kafin na setting alarm a karfe 3 na kwanta.karfe ukun nayi na tashi na masa tuwo da miyan kuka taji man shanu na ajiye masa da coffee dinsa na huce daki na kwanta amma saida nayi sallah kafin na samu na kwanta saboda fitina irin na fu’ad,da safe na tafi gun patient dina na masa dressing kafar sa na dawo daki na kwanta domin nayi bacci kafin lokacin abinci tayi godiyar Allah a watan azimi nake da yaushe naga ta hutu har da baccin rana nasaka alarm dina a 12……

 

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L@!

 

 

Nah halima musa akano (leeemat )💮

 

 

 

3⃣8⃣

 

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har aka gama ramadan kullum banda hutu har na rame saboda aiki ga azumi ga aiki kamar na gidan biki ga kuma baba wato patience dina.bayan sallah na masa aiki inda naci nasaran aikin domin kafar tayi sauki har yana iya takawa da sanda yanzu magani kawai yake sha, kafar na warke wa nayi wani ciwon da kamar zana mutu wato da asuba na tashi sallah sainaji na kasa tashuwa jikina yayi zafi sosai da rurrufe na shiga toilet ina idar da sallah na hau gadona kwanta nida idan na tashi da asuba to babu ni babu komawa barci sai fu’ad ya fita amma yau na kasa ina kwance amma na kasa bacci saboda tunanin abin da zaya biyo baya idan ya tarar ban hada masa breakfast ba ban gama tunanin da nakeyi ba naji  kiransa (RANI SAHIBA) da kyar na iya mikewa na fito falon ina mai tafiya kamar wanda ta sha kayan maye saboda jikina babu karfi hada fuska yayi yace ina break dina nace masa wallahi bana jin dadi bane shiyasa ina jiran saukan mari sainaga yanayin fuskar sa ta sauya alamun tausayi a cikin tarihin aurena yau ne mijina ya kalle ni da fuskar tausayi saiyace ok kinsha magani nace a’a saiyace mai yasa nayi shuru ok kawo min coffee na sha nayi late sauri nake to nace kawai ina juyawa kawai sainaji wani jiri kawai ganin falo nake yana juyamin nayi suuu na fa…….

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

3⃣9⃣

 

 

Suuu nayi zana fadi sainaji ni a jikin mutun yaune ta kasance rana ta farko da najini a jikin mijina nasan ma saboda rashin lafiya ne amma da babu abinda zaya kaini jikinsa bansan inda kaina yake ba.jin sanyi sanyi ajikina yasaka ni bude idona  caraf idona ya sauka a fuskar fu’ad ganin yanda duk yabi ya sukurkuce kamar ba mijina mai gayu ba saina kirkiro murmushi sainaga ya mayar min kokarin tashuwa nake son nayi na kasa saboda yanda jikina taimin nauyi kamar an dora dotse sainaga ya tashi da sauri ya taba wani guri a jikin gadon sainaga gadon yana tashuwa a hankali nikuwa sai cije baki nake saboda yanda jikina ke mikewa sai inajin zafi ya tsayar da gadon ganin yanda nake yi.ya dauka briefcase dinsa na aiki yana dubani yana gamawa ya dan gyaran min gashin kaina ya baida su baya yana shafa kaina tare da cewa every thing is ok alryt u are fyn now murmushi kawai nayi saboda mamaki wai mafarki nake ko kuma a zahiri fu’ad mijina ko kuma wani fu’ad din ne yake min haka jin yana magana yasa na dawo daga tunaninda nake yi zaki iya tashi ko kuma saina dauke ki ce masa nayi a’a zan iya tashi na yunkuro zan tashi sainaji…..

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

4⃣0⃣

 

 

Sainji ya dauko ni sai bayin gida  sakani yayi a cikin bath sai a lokacin ma na fahimce babu kaya a jikina kunya duk ya kamani na sunkuyar da kaina kasa  yace zaki yi wankan ne ko kuma na miki da sauri nace zan iya  yayi murmushi yayi yace (TA’ABANA) a raina nace wannan yare nawa ya iya ne murmushi kawai nayi na cigaba na wanka na ina gama babu abinda zan rufe jikina ina daga ido sainaganshi yana kallona sunkuyar da kainayi cikin tsananin jin kunya ya towel ya dauka ya lullube ni ya dauke ni kamar wata karamar yarinya ya zaunar da ni a kujera yace na zauna na gajina da kwanciya mai ya shafa min ya saka min kaya ya bani tea na sha ina gama sha kuwa nayi amai ya share gun ni kuwa in banda mamaki babu abinda nakeji wai yarima kenan yana abubuwan nan saboda wancce ta masa rashin mutunci yana shiga toilet wanke hannunsa na sha ruwa ina cire bakina a gorar na sake kwarara wani amai daga baya naji ance min sannu juyawan da zanyi wa zan gani…….

 

 

 

Written

By

Leeeeemat💮

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

4⃣1⃣

 

Wa zan gani mahaifiyar fu’ad nagani wato MA’A kenan kamar na nutse a gun saboda kunya rusunawa nayi ina gaida ita tashi tashi ke da baki da lfy na tashi ban iya zama  a kujera kuma ba kwanciya nayi saboda tsananin jin kunya maganan zuci nake wai yanzu ta shigo ko kuma tana cikin dakin nan bansani ba amma kuwa mun cika marasa kunya in tana cikin dakin nan ne fu’ad yamin wannan abubuwan.haka dai jikina babu sauki sai amai nake tayi na sha ruwa kuwa kamar wacce bata da ruwan a jiki,har naxo na samu lfy abin mamaki gida jiya muka sake komuwa kamar yau na masa abinci saboda yayi baki ina gama abinci na kwanta bani da tashuwa ba saida naji saukan ruwan zafi na tashi a firgice before u knw banganshi ba ya fice a dakin…..

 

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

4⃣2⃣

 

 

Yau ina zaune a falo na abin duniya duk ta isheni na rasa me yake min dadi naji sallamar sa tashuwa nayi na masa sannu da zuwa yace min ki shirya monday zaki fara zuwa aiki wani ihu na saka mai karar gaske har ya rufe kunnensa yana mai murmushi ganin yanda nake murna saiyaji dadi a ransa saboda tunda muke da shi bai taba min abinda ya saka ni farin ciki kamar yau ba bansan lokacin da na bashi tyd hug ba ina thank u very much i wil never forget dis ina gamawa na ce masa ga abincin ka a dinnin is ready murmushi kawai yayi ya tashi ya nufe table.a daran saboda murna na kasa bacci salloli na cigaba da jirowa ina rokon allah ya sa na fara aiki cikin sa’a  tare da rokon allah ya  karkato da hankalin mijina gareni domin babu abinda banyi ba tafannin jawo hankalin miji irin su dafa masa abinji,kwalliya,saftar gida babu abinda banyi ba yanzu kawai adu’a zan cigaba dayi har allah ya amsa min adu’a ta ina idarwa na fara niman kayan da zan saka na ma mance akan gobe jumma’a ne saida ina cikin duba kayan da zanasa sai tunanin labcoat ya fadumin ina tunanin ya zan fara zuwa aiki babu labcoat sai na tuna akan ai gobe friday ne saina dinka a unguwar mu idan muka tafi……

 

 

Written

By

Leeeeemat??

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

4⃣3⃣

 

 

Washegari na tafi gida aka dinko min labcoat dina na dawo gida da wuri saboda banason nayi laifi.ina dawowa na dafa masa abinci na fara shiryeshirye na, haka dai har ranar monday na fara zuwa aiki amma wani abin mamaki duk lokacin cin abincinsa sai na dawo na masa kafin na koma asibiti amma abin baya damuna tunda nasamu ina zuwa aikin,in wani lokaci ina night ne haka zana dawo na saka masa abinci saiya ci kafin na koma asibiti saboda ina kammala abinci kafin ya dawo idan ya dawo kuma saiya kirani yana kirani kawai nasan abinda yake nufi saina dawo gida na saka masa abinci kafin na koma.haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya akwai wani ranar da nake shirin tafiya aiki da safe sauri nake na saka pant da bra kenan ina gyara gashina domin na saka kaya na tsaya a bakin gado saboda kayan na zuba su a kan gado ne ban ji sallamar mutum ba kawai na ga mutum ya shigo ina daga ido sainaga fu’ad.fu’ad kuwa rikicewa yayi saboda ganin albarkatun kirjina saboda gaskiya ina da boost sosai saima na saka bra irin mai karfe dina kuma duk bra dina kanana nake sakawa wanda zaya kamani ni sosai, na kasa musawa ina tsaye a gurin kamar wata gunki saida naga ina zuwa a hankali towards me saina fara komawa da baya a hankali hankali saime?..

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

4⃣4⃣

 

 

 

Ina komawa baya a hankali hankali sainaji ni na zauna a  kan gado fu’ad da ganin haka saiya sakayani da hannunsa ya daura hannunsa a kan gado yana matsuwa ni kuwa ina komawa da jikina baya yana kan karasowa kafana a kasa yana ta matsuwa da fuskarsa a fuskata duk fadin jikinsa ta hanani motsi ina zaune yana zuwa da fuskar sa dai dan bakina kamar zaya sunbace ni labbansa yana karasowa dai dai bakina ni kuwa babu abinda nake yi sai rawar jiki gabana sai faduwa yake tayi rufe idona nayi da karfi ina jiran inji bakinsa cikin nawa sallama mukaji ta falo mikewa yayi cikin mutuwan jiki ya fita ni kuma wani mahaukacin ajiyan zuciya na sauke da sauri na saka kayana na fita wa zan gani su hassan da hussaini ne nace musu ya dai da safe haka  sai suka ce min ai jalilah ce ta haihu wani ihu na saka sai suka ce min wai anata niman ki a waya is off shiyasa mukace bara mu zo kawai mu sanar da ke nace me aka samu ne suka ce min mace nace musu to mu tafi ko saina dubata before na huce  aiki wani kallo naga fu’ad ya min sainayi shuru na huce daki domin dauko gyale na ina juyawa naga mutum a bayana na damke hannuna yayi yace bance ki tafi ko ina ba ki huce gun aikin ki kawai ya juya ya fice a dakin na fita da sauri domin na fada masu hassan wani karya saina tarar basanan nayi kuka har naji babu dadi kafin na huce gurin aiki ina office dina na kira jalilah na bata hakurin insha allah mayb gobe zana shigo aiki yamin yawa ne tace babu komai sister simra ya naji kamar muryarki ta canja ne nace mata babu kamai kinsan aiki tace to allah ya taimaka nace amin ina kashewa na sake wani kuka….

 

 

 

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

4⃣5⃣

 

 

 

Kuka na sake nayi kuka mai isata kafin nace wannan abin yafara isata wallahi har da kannuwata ma ta haihu amma saboda wulakanci amma ace ya hanani tafiya,a ranar dai nayi aiki cikin dauriya ne kawai amma duk jikina a mace yake ina gamawa gida na huce jakana da gyalle na duk na zuba su a falo na huce kichen na dafa masa abinci nayi sallar magriba nayi isha’i ina dan duba wasu takarda naji sallamarsa na daga kai na masa sannu da zowa ya fita falo na fahimce me yake nufi saina tashi nima na fita na ganshi a coshin ya zauna na nufe dining area ina shirin kawo masa abinci sai naji yace saboda kin mayar dani acici ko na saya cak saiyace ki shirya na kaiki gidan jalilah saina dawo zana ci nace masa bazana tafi ba kallona yake baki bude na huce daki na fada a gado ina kuka wato ma ni da yar uwata sai an gama min milki kafin za’a barni naji na ganta to baza’a tafi ba wata zuciya kuma tace min to shi ina ruwansa ai kece mai yar’uwan idan ma baki tafi ba duk lalurarki ne da sauri na tashi na nufe dressing mirror na dan murza powder na dan shafa lipgloss a bakina na nufe falo domin nasan akwai gyalle da jakata a falon ina fita na dauka gyalle da jaka naji an jani zuwa bango bakinsa naji cikin nawa gabana sai faduwa yake domin ina zatun amsar da na bashi dazunne zaya hukuntani yamin irin na ranar daya kumburar min da baki saboda da mugunta wani kara na sake……

 

 

 

Writtten

By

Leeemat??

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

 

4⃣6⃣

 

 

Kissing dina yake kamar ya samu sweet lips dina yake latsawa cikin kwarewa har naso na mance a wani duniya nake,naji tsoron kar yamin na ranar  ya sakani sake kara amma shi ko a jikinsa(wai an duke bango yace ko jikinsa) aikinsa yacigaba dayi dayaga basaya iya jure tsayuwan ba saiya cire bakinsa cikin nawa yayi hanyar waje,ni bansan lokacinda na zame jiki  na zauna a kasa ba ina mayar da numfashi a hankali wai haka sumbata take da dadi magana nake a zuciyata sa’annan na mike na biyo bayansa na tarar ya kishingide a gefen mai zaman banza a raina nace me wannan bawan allah yake nufi ya bude baya na zauna munkai kusan minti goma kafin yacemin ki dawo gaba ke zaki driving dinmu nayi kamar badani yake ba RANI SAHIBAH dake nake magana fa na fito na zagaya na shiga muka kama hanya muna cikin tafiya yake cemin daga yau idan zamu fita tare dake ke zaki rinka driving dinmu uffan bance ba saiya kara cewa wato zamu tafi gidan kannuwanmu shine kika saka lipgloss wa zaki nuna mawa ya dan kalle fuskata tare da cewa let me  check ko kuma har yanzu bai kare ba saina share miki kiiiiii kake ji na mutu fu’ad kuwa babu abinda yake furtawa sai innalillahi wainnahilaihirajiun….

 

 

 

Writteen.

By

Leeeemat??

 

 

!Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

4⃣7⃣

 

 

Sha biyu nayi na tashi na fira dankalin turawa zuba a kwando saboda ya tsane na saka ganda a pressure cooker saboda tayi da sauri a lokacin asr yayi na tafi nayi sallah na dawo na fara aikin fruit salad, fruit salad ya dauke ni har LA’asar ina gamawa na saka a fredge na gama miyan ganda na zuba a foodflask na saka frying pan a wuta na zuba mai na tafi sallah na dawo a lokacin mai yayi zafi na fara soya dankalin sa’annan na saka tukunyan farfesun kifi a wuta nan da nan na gama amma na saka mishi sinadarin kamshi irin su cinta da dai sauraran su saboda karni ina gamawa na zuba a flasks na fira doya na saka a wuta sa’annan nayi mango fruit juice na zuba a jug na saka a fredge already akwai ruwan zafi a flask wanda zaya so tea.har an kira sallah na shirya musu table na huce daki nayi sallah nima na ci abinci na daki inata jin hayaniyar su a falo amma ban fita ba can naji shuru da alamar Sun tafi sallar isha na koma kichen na sauke doyar da na saka a wuta na zuba a injin nika doya nan da nan na gama na mulmula masu a leda na saka a cooler na kai musu falo da miyan ganda da na musu da kuma mango juice na huce nayi sallah a gajiye ina shirin wanka saina tuna da baba yau ban masa dressing kafa ba gashi na gaji saina fara kuka kawai saboda gajiyan da nayi haka I don’t have a choice na huce ina gama masa na dawo na kwanta na saka alarm 3 saboda tashuwar asuba

Hmmm har ni kaina leeemat na gaji ina kuma gimbiya simra zataji a jikinta irin wannan aiki haka amma fa lada ne kam bamusan irin ladan da take kwasa ba saidai kawai nace Allah ya bamu juriya irin na simra muma mu rinka yiwa maigidan mu haka domin tsira daga shiga wuta ameen…..

 

 

 

Written

By

Leeeemat ??

.

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

4⃣7⃣

 

Na jin abinda ya fada sai na daga brek din moton ji kake kiiiii!fu’ad kuwa babu abinda yake sai innalillahi wainnahillaihirajiun,ni kuwa cikin sauri na share sauran wanda ya dan rage a labbata.cikin bacin rai yace wai so kike kimin asarar kanki shuru nayi ina kallonsa cikin mamaki da jin furucinsa fu’ad kuwa bansan subul da baka yayi ba sai yayi sauri ya canja maganan da cewa duk da dai banda asara idan ma mutuwar kikayi wai ma wa yasakaki kiyi wannan shirmen okey saboda nace zan share sauran?to kiyi reverse mu koma gida tunda dama kwalliyar kina ma wa mutan waje ne yau bazaki nuna musu kwalliyar ba bansani lokacinda na matsa kusa dashi na tura masa bakina tare dacewa gashi kayi duk abinda zakayi dashi amma dan allah kar ka hanani tafiya gidan jalilah,dariya na bashi amma ya daure sai kuma na banshi tausayi yace huce to mu tafi na share fuskata nayi saboda har na fara zubar da kwalla.muna isa gidan na fita a guje na shiga na tarar da yan  zuwa barka  na tafi na rungume ta sa’annan nace ina baby dina mutanin falo sukayi dariya tace tana dakin ki aka sake wani dariyar dakinta na huce na dauka babin ina kallonta cikin sha’awa naji kamar motsin na daga kaina ganin fu’ad nayi yana shigowa da kaya a leda amma bansan me yake ciki ba yana zaunawa nima zaunawan nayi na cigaba da kallon babin inda jalilah tace min sis simra ki bashi babin mana sai sa’annan na tuna dashi na tashi na mika masa ita ya mata adu’a wayar sa tayi kara ya mika min babin ya fita a waje amsa kiran yana fitowa na nufe gun ledar da ya shigo da ita na bude wani kamshi naji kaza nagani irin na mai jego dinnan da sauran abubuwan ci da shi.haka dai na shigaba da zuwa gidan in na tashi daga gun aiki har ranar suna inda aka saka sunana hmmmm fada muku abinda fu’ad yayi a ranar sunan zaku ganin kamar karya nake abin mamaki ya ban haka dai aka gama suna lafiya kowa ya tafi gidansa inda maijego ta samu abubuwa sosai da kudi domin har bude account tayi ma babin…

 

 

Written

By

Leeemat💮

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

4⃣8⃣

 

Fu’ad kwance yake a kan gadonsa wanda zana iya kiransa da royal bed saboda yanda aka kayata gadon da abubuwa mai kama da gold sai sheki gadon yake duk da dakin yana cikin duhu ne amma bazaya hanaka ganin shekin da gadon ke yi ba.doom light ya saka yana son yayi bacci amma abin ya gagara gashi yau ya gaji sosai a gun aiki sakamakon babu armies duk sun tafi yaki a wani garin da suke fuskantar azzalumai masu sace masu mata da rasa.ya kasance fu’ad bayanan a cikin masu tafiyan dan haka aiyukan suna masa yawa sosai kamar ma yau da ya gaji sosai amma ya kasa bacci.sai tunanin simra yake wanda tun ranar sunan A’shadieeyah waton yarinyar jalilah kenan takwaran simra ya kasa tsukuni tunanin ta yake saboda ta bashi tausayi mutuka saboda yanda takeyi kamar sunanta ne na yarinyar ta sa’annan duk da ba’a gida ta kwana ba tasan halin mijinnata tana tashuwa da safe ta nufe gida ta masa breakfast ta jira ya shigo ya ci kafin ta dawo gidan sunan haka da rana ta kumo gidanta ta masa abincin rana domin intace zata diba masa na gidan sunan kila kifa mata zayayi a jiki domin bazaya tabaciba yana ganin abincinda dunbin mutani sukayi sa’annan ta ce zata saka mishi yace tana gama masa abincin rana ta dawo suka cigaba da sunansu.yasan ya hukuntata daidai da laifinta amma bari ya dan bata tym kadan saboda yanzu ya shirya zaman aure da ita cikin soyayya,har bacci yayi awon gaba dashi amma tunanin simra yake da irin soyayyar da zasu kasance idan sun fara zaman aure daga karshe yayi wani mummunan mafarkin da ya firgita shi,mafarki yayi akan yana wani sahara mai girman gaske inda yake hangin simra nesa dashi tana kiran sunanshi amma ta kasa karasowa wajensa kamar ana koma da ita baya inda take ta kokarin zuwa har allah yasa ta karaso sai tana ce masa fu’ad wai meyasa bazaka yafe min laifin da na maka lokacinda nake gida bane wani yanzu na canja ba kamar da ba kuma bana wulakanta mara arziki kawai dai a lokacin jinin mu bai hadu da kai bane magana take tana kuka sosai har da majina inda take cewa dan allah ka yahakuri ka gafarceni muyi zaman mu na ma’aurata saboda makiya suna sun su rabamu tana cikin maganan taga kamar yana komawa da baya tana pls fu’ad ka tsaya mana tana kuka tare da mika hannunta amma me saitaga katon rami a bayansa tana fu’ad no fu’ad no bayanka zuwa take da gudu amma saijinsa tayi ya fadi cikin ramin wani ihu ta saka a dai dai lokacin fu’ad ya tashi zufa cabe cabe a jikinsa

 

.written

By

Leeemat💮

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)??

 

 

 

4⃣9⃣

 

 

Adu’a yafara kafin ya shiga bayi domin yajin kamar har anfara sallah a masallatai yana idarwa ya fara tunanin mafarkinda yayi yau kamar an tsikare ya tashi toilet ya shiga yayi wanka yana saka kaya tare da tunanin yaya zaya fara fuskance ta da maganan domin gaskiya yau dinnan zaya kasance da matar sa abin kaunarsa yana murmushin jin dadi yana gama ya dauke turare yana sakawa domin yasan yanzu tana kichen a cikin ransa yace abincin yau dani za’a dafa sa’annan muci tare cikin kaunar juna ya murmusa ya fita yana kai bakin kofa yaji wayar sa tana ringim kamar ma bazaya dawo ba saiya juya ya koma cikin dakin sunanda yagani ya saka shi saurin dauko wa hello yace basan me aka fada masa ba kawai ganinsa nayi ya dauka car key dinsa ya fice cikin tashin hankali.baza mu koma ta bangaran sarauniya amina idan mai karatu bai mance ba sarauniya tayi alkawarin saitaga bayan yarima fu’ad to abinda yafaru yau tana son tafiya gida gaida iyayenta domin tayi kwana biyu saita nufe padan mai martaba sarki saita juyo wani magananda ya tayar mata da hankali mai martaba taji yana cewa jibi zamu rada fu’aduddeen saboda yafara aikinsa tun yanzu duk da dai nasan yanayi amma zan rada masa ko bai zauna a pada cikin mu ba ya fara sanin matsalolin mutaninsa yana biya musu bukatansu magananda bata shiga tayi ba kenan ta huce gida suka huce gidan boka ta fada masa matsala ta yana dubawa yace gaskiya wannan yaron yana da kariya sosai akwai wasu adu’oin da yake yi idan zayayi barci kuma da addo’ar iyayensa amma yau zamu jaraba mugani ko za’a dace ba kisa kike son a masa ba? ta ce eh yace to shikenan ta bashi kudi da bazana iya san adadin su ba suka fice sai murna..

Ta gefen fu’ad kuwa gudu yake kamar zaya tashi sama ganinsa nayi ya shiga bariki dinsu na sojoji abinda nagani har ya firgitani mutani nagani a kasa wadansu a mace wadansu a raye amma sunji rauni ba kadan ba sai jujejuye suke alamun suna cikin azaba da rauni yana karasowa aka sara mashi yace ya dai wani daga cikin sojan yace munci nasara amma sun kashemu sosai sabida suna da kayan aiki.alhamdullilah yace sa’annan yace musu su kwashe su a kaisu ciki zaya duba su aka shiga dasu yafara duba su wadannan basu da rai a fitar da su wadannana suka ji mummunan rauni kuwa babu adadi aiki kawai yakeyi saidai in lokacin sallah tayi ya fita yayi ya dawo ko ruwa bai sha ba har goma na tare waninda yake tayashi aikin yace ka tafi gida haka mana gobe saika karasa ai ko murmushi yayi yace a’a duk yau zan musu aka kuwa akayi saida ya gama musu kaf kafin ya dawo a lokacin biyu ta wuce yana zuwa kuwa kwanciya kawai yayi saboda yayi kwanka a barikin bacci mai nauyin gaske ya dauke shi yana tunanin sai gobe zaya ga matanshi

 

 

Written

By

Leeemat??

 

 

[3/21, 5:45 PM] ‪+234 703 003 6037‬: !Y@RIM@ J@L@L!

 

Nah halima musa akano(leeemat)💮

 

 

 

5⃣0⃣

 

 

 

Washegari simra tashi da tunani mai yawa a kwakwalwarta tun jiya bata gan fu’ad ba gashi yanzu har goman safe bai shigo ba ko mai yafaru ita bata sani ba har shabiyu tayi kai da taga abin bana karewa bane saita tashi cikin faduwar gaba  ta nufe side dinsa tare da niyyar duk abinda zaya mata saidai ya mata amma yau zata shiga side dinsa tafiya take cikin tsoro da fargaba abinda zata ji ta tarar tana tsaye a bakin kofan kusan minti talatin sa’anan tayi adu’a ta shigo a hankali  ta bude kofar bata komai ba sai katon falo tana shiga numfashinta yan niman daukewa saboda kyau da tsaruwan falon kawai da yake ba abinda ya kawota ba kenan bata tsaya kallon yanda falon yake ba ta huce wani kofar da ta gani a gefen falon saita nufe kofar ta bude shi a hankali tare da sallamar tsoro taji shuru tayi sallama sau uku taji shuru saita shiga ganinsa tayi a kwance yana bacci ta karaso kusa da shi fu’ad fu’ad fu’ad shuru babu motsi ballantana har ya amsa sai ta shiga rudani tafara kiransa cikin tsoro domin yanayin kwanciyar sa ma da tambaya bude bargo tayi hau kan gadon ta tabashi taji kamar babu rai a  tare da shi ta fara bubbuga shi tana kiran sunansa tana hawaye  fu’ad pls wake up banason irin bacci dinnan fa shuru babu magana saita fara kuka a jikinsa ta kwanta tana kuka kamar ance ta daga kanta saitaga hawaye na fita a gefen idonsa sai a lokacin tunanin kira likita ya zo mata minti kadan sai kuwa gashi yana mata korafin gidan da kyar aka barshi ya shiga bayan ya gama dubashi yace mata nidai ban fahimce komai ba amma gaskiya jikinsa is weak baxaya iya komai ba in ba abinci yace ba kafin zamu san me ke damunsa godiya na masa kafin na dawo na cigaba da kuka fu’ad tell me wat is happening to u pls tell if u dont my heart will be shatered pls fu’ad

Wani tunani yazo min kuka na ya tsananta dana tuna da labarin da jakadiya ta bani akan ba’ason fu’ad yayi ciwo saboda yana iya daukansa wata ko shekara kafin ya samu lafiya idan kuma wannan ya kasance yaya kenan zanayi ban gama da damuwan aure ba ga ciwo wayyo allah na…

 

Written

By

LeeematMuna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [ Yarima Jalal Hausa Novels]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

47 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!