Hausa Novels

Yaya Mustapha Hausa Novel A Romantic Love Story

Yaya Mustapha Hausa Novel A Romantic Love Story

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

YAYA MUSTPHA

 

 

A ROMANTIC LOVE STORY💏

 

Mallakan Dr.Hanan Al’ameen

 

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

 

Free page 🤸🏻

 

 

Page one -1

 

 

………Gudu kawai yake a titi ko kallon gabansa ba yayi burinshi kawai ya ganshi a gaban Seema, ya sa ke kallon agogon hannunsa a karo na uku ƙarfe shida saura ya nuna, ransa ne ya ƙara ɓaci ganin yanda yake gudu, amma har yanzu bai ƙarasa in da yake son zuwa ba, zuciyarsa sai tafasa take adaidai wata Center ya hangota tana ƙoƙarin tsaida adaidaitar da ta shigo center’r cikin sauri ya ƙarasa fitowa daga motar ya iso gabanta fuskarshi kamar mai shirin kuka yace “please Seema kar ki min haka I really need you dan girman Allah kizo mu shiga mota wallahi goslow ne ya tsaida ni but sorry tun da gani na ƙaraso” wani kallon ku saura kwata ta mishi tare da furta “please Fahad sakar min hannu wallahi bazan bika ba sai wani lokacin kuma ina da appointment da Gaye yanzu tana ƙoƙarin zagayeshi ta shiga napep ɗin da ta tsaida, hannunta ya riƙe tare da kallon mai adaidaitar ya daka mishi tsawa yace, kaga malam maza ka wuce anan tun kafin in ɓallaka wallahi ta ƙarasa maganar yana ƙara zare masa idanunsa da suka ƙanƙance tsabar sha:awar da ke damunshi, da sauri ya tadda a daidaitar sa ya wuce ganin yanda yake a buge ya tabbata zai iya masa komai kuma ga shi babu kowa a center.

 

Kallonsa ya mai da ga Seema wacce ta saki baki tana kallon ikon Allah ya buɗe bakinsa dake tashin warin giya da wiwi zae mata magana, hannu ta daga mishi tace nace dai ka sakar min hannu ko? Fuska ya ƙara narke mata yace “haba Seema mi yayi zafi haka kiyi haƙuri please wallahi cinkoson ababan hawa ne ya hanani ƙarasowa da wuri yana maganar ne tare da murza tafin hannunta daya rike.

“Bazanjeba nace ko dole sai nice zan iya sauke buƙatarka, yace “haba Seema ya za ki min haka kinsanfa dake kaɗai nake harka ƴanmatan club sam basa birgeni wallahi domin basa gamsar dani yacce nake so sai ke kiyi haƙuri indai dan na ɓata miki lokaci ne kar ki damu ko wane mini zan ƴara miki kuɗi fiye da yanda kike buƙata indai kuɗine baki da matsala zan baki yau fiye da yacce nake baki, shiru ta kuma mishi bata dai ce komai ba sai fuskarta data maeɓida a laya side lin,

 

Ganin tana neman ɓata mishi lokaci ne kawai

Yasa ya ɗauketa ya saka a motar duk da son kwace kanta da take a hanunshi, kuɗi ya ɗora mata a cinya bayan ya tada motar ta kalleshi ta sake kallon kuɗin tace bana buƙata domin nasan kuɗin da zan samu sunfi haka a wurin Gaye sai ya linka yanda zaka bani, hannu ya kai jikin lokar da yake ajiye kuɗi a motar ya sake ƙaro mata bandir biyu ba tare da yace mata uffan ba

Murmushi tayi tare da saka kuɗin a cikin jaka😍shiru sukayi dukkansu babu Wanda ya sake magana har suka karaso a wani katafaren gida kirar gidajen New Delhi, sosai gidan ya hadu fiye da tunanin mai karatu, wani azababben hon ya Danna ya kallon Seema da ke ta yatsina tana ƙara turo mashi mamanta da suke mashi dakuwa.Dan kuwa sosai Allah ya yi ma Seema diri ta kowane bangare,

 

Da gudu malam habu mai gadi ya hangame masa ƙaton gate ɗin gidan, yana ta faman mishi barka da zuwa ,ko kallonshi bai ba ya kunna hancir motarsa cikin gidan a guje Allah ne ya kiyaye malam Habu yayi saurin ɗauke ƙafarshi da yabi ta kanta ya matsa gefe.

 

 

Ko ƙarasawa wurin da aka tanada domin ajiye motocin gidan baiyi ba ya tsaya tare da buɗe ma Seema bangaren da take a Zaune, futowa tayi tana yatsina tare da girgiza Jikinta tana mishi kallo irin na gogaggin ƴan bariki mai matuƙar ɗaukar hankalin Maza tabi bayanshi ganin har yayi gaba wani halaɗɗen ɓangare suka shiga tare da maida ƙofa suka rufe tun anan falo suka Fara aukata ɓarnar da suka saba ……

 

 

✨✨✨✨✨✨

 

Hanan dake tsaye a saman bene tana kallonsu da sauri ta rike ƙarfen da ke kusa da ita ganin yanda lokaci ɗaya gidan yake juya mata ✨ta dafe kanta dake sara mata wasu hawaye masu zafi suna fita daga cikin idanuwanta da kyar ta saita bakinta da zuciyarta ta fara maimaita Innahlillahi wa Innah ilaehir raju’un tun Tana a zuci har ya futo a fili ,Safiyya dake tsaye a bayanta tayi saurin ƙarasowa ta riƙeta ta ta dafa kafaɗarta cikin kwantar da murya ta fara magana itama idonta cike da hawaye duk yanda taso ta daure kar tayi kuka Amma ta gaza hakan,cikin kuka ta dubi ƴar uwarta tace “kiyi haƙuri sister please ki daina damuwa idan kikaga Fahad a cikin kowane irin yanayi dayake aeɓikatawa ki ƙyaleshi duniya ce ta ishi mai rai riga da wando har da babbar riga tun kafin kizo nake ganin abubuwan da suka fi wannan to miye yanzu kuma na tada hankalinki bayan kinsan duk wanda yabar uɓUbangiji to lallai Allah baya tare dashi sai kiyi ta haƙuri watarana sai labari jarabawace kowa da kalar tasa mu cigaba da addua tabbas ubangiji yaana tare da bayinsa aduk cikin halin ƙunci da baƴin ciki da zasu tsinci kansu😭,,,,,,,ajiyar zuciya Hanan ta sauke cikin kuka ta dago ta kalli Safiyya tace “hmmmm sister na rasa dalilin da yasa aɓAbbana ya raba ni da masoyina ɗan uwana ya hadani da Wannan fasiƙin mashayi Wanda kokadan a zuciyarsa babu Allah ya zaɓi ya saɓama Allah daya bauta masa, ya lauki wannan ƙasƙantarciyar duniyar a matsayin rayuwarshi,shin me bayi ma Abbana dahar ya zaɓi ya rabani da Wɓwanda muka kwashe shekaru da dama muna gina siyayyarmu, shin me yasa Abbana yamin haka ❓meyasa ❓me Nayi mishi haka ❓Anya inada sauran farinciki a duniyar nan tunda har Abba ya iya rabani da Yaya Mustapha ❗😭😭❓

 

 

Muje xuwa 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻🤸🏻‍♀️

 

 

 

(ya ubangiji Allah Kada kaba shedan sa’a akaina ta Hanyar ƙawata min rubutun da zai zama silar

 

 

ɓacewar tarbiyyar al’umma Allah ka tsare min zuciyata, da hannuna tare da idanuna🤲🏻)

 

 

Written by Dr Hanan Al’ameen (Maman twins)💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

[18/08, 9:13 pm] +234 903 602 2224: 🤍 YAYA MUSTAPHA 🤍

 

 

 

A ROMANTIC LOVE STORY

 

MALLAKIN DR HANAN AL AMEEN

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

FREE PAGE 🤸🏻‍♀️

 

 

PAGE TWO _2

 

 

 

~~~~~~~~Share mata hawayen fuskarta Safiyya ta yi ta ce “pls sis yakamata ace kin cire wannan abun a ranki ki tuna ubangiji ya na tare dake a ko wane lokaci” haka ta yi ta lallashinta ta na fada mata magana masu kwantar da hankali, a hankali Hanan ta dago ta kalli Safiyya ta na kara jin kaunarta a zuciyarta ta ce “sis Allah ya barmu tare ya fidda mu daga cikin wannan hali da muke ciki ya gwada mana karshen wannan azzalumin” “Ameen” Safiyya ta amsa tare da kama hannunta suka nufi falo, kallo Safiyya ta kunna musu dan su rage damuwar dake tare dasu amma suna farawa aka kwada kiran sallar magriba,,, mikewa ko wace ta yi ta nufi dakinta dan d’auro alwalah

 

~~Falo ne irin mai dakuna biyu kowace daki guda gareta shi ya sa a ko wane lokaci zaka samesu a wuri daya zaune sun fi zama a dakin Safiyya dan watarana ma a dakin suke kwana gaba daya sa bo da ita ce babba ma’ana Safiyya ce uwargida,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

 

Hanan ta na idar da sallah ta haye gado dan ita gaba daya duniyar ta isheta ko abinci rabon da ta ci 5spoons har ta manta, tunda ta kwanta rayuwarta ta baya ta dawo mata abubuwa da dama suka shiga kaiwa da komowa a cikin kwakwalwarta bata ankara ba taji hawaye masu zafi suna bin fuskar ta

 

 

~~~~~

 

 

ASSALIN LABARI ……

 

 

Hanan ta kasance yarinya ce kyakkyawa fara sol da ita Allah ya mata halitta tamkar ita ta tsara kanta hancinta medium size haka ma bakinta dan tsutt dashi idanuwanta farare tas tamkar madara eye boll din ta kuwa bakikkrin dashi ga diri jiki Masha Allah duk wanda ya kalleta sai ya yi marmarin sake kallonta namiji ko mace abinda zai kara sanya kaji ta birgeka nutsuwarta da ladabinta musamman idan ta na tafiya ga uwa uba iliminta ta na da murya mai daukar hankali da kashe jiki musamman a wurin maza.

 

 

Iyayenta ba masu kudi ba ne sosai sai dai kuma alhamdulillah akwai rufin asirin Allah don kuwa akawai ilimin boko da na addini a wurin iyayensu shi ya sa suma suka tashi a haka cikin tarbiyar addinin islama, su uku iyayensu suka haifa ita ce babba sai kannenta maza guda biyu Umar da Usman sun taso cikin so da kauna da kulawar iyaye domin ita ma mahaifiyarsu su biyu iyayensu suka haifa kuma sun rasu tun suna kanana ita da Yayanta Yusuf shi ma yanzu haka ya na da yara biyar uku maza biyu mata Hafsat, Halimatu, sai autarsu Maryam mai sunan mahaifiyarsu shi ya sa suke kiranta da Ummi, yanzu haka Malam Yusuf ya aurar da Hafsat saura su biyu da kannensu maza Hamza da Salisu.

 

Duk duniya burin Yusuf ya kyautata ma kanwarshi kuma yar uwarshi Fatima wacce take mahaifiya ga Hanan *****

 

Mahaifinta kuwa Malam Sulaiman ya na da yayya guda biyu dan shi ne auta Baba Mannir sai Baba Aliyu su kadai ne basu da mace a gidansu ***Ya’yan Baba Mannir shidda shi kuma Baba Ali Ya’yansa hud’u da daya yafi kaninsa Sulaiman Mustapha, shi ne babban dan Baba Mannir tun suna yara yake masifar son Hanan domin gidansu aka yayeta sai da ta yi shekara h’ud’u sannan ta koma wurin Iyayenta.

 

*********Duk wanda ya san Yaya Mustapha tabbas ya san Hanan domin duk inda za shi da ita yake tafiya lokacin da ta na karama kwata-kwata baya son bacin ranta koda kuwa a wurin mahaifiyarta ne, tun ta na yarinya yake fadama Hajjo kakarsu ta wurin uba ce wa shi fa Hanan ce matarshi idan ta girma hakan yasa Hajjo ta tara yaranta ta fada musu ko bayan ranta Mustapha baya da mata sai Hanan haka ita ma Hanan Mustapha shi ne mijinta, ai kam kowa ya yi farinciki da wannan hadin na Hajjo mussaman mahaefin Hanan sosae yayi murna da wannan abun alkhairin,, haka ma sauran dangi babu wanda bai yi murna ba kowa ya san da wannan hadi.

 

 

~~~~Tun ta na karama ta fahimci mi ye so akan Yayanta tana sonshi fiye da ranta da duk wani abu da zata mallaka a duniya haka shi ma a nashi b’angaren babu wata mace da zai iya mallaka ma zuciyarshi sai ita ****soyayya suke mai tsafta da burgewa burin ko wane bai wuce ya faranta ma dan uwanshi ba, ji suke idan basu samu juna ba zasu iya mutuwa domin maganarsu a kullum ita ce babu mai tabbacin cigaba da rayuwa muddin aka rasa daya daga cikinsu************

 

 

Babu kunya a gaban kowa Yaya Mustapha zai iya nuna mata soyayya wata sa’in ta biye mishi wani lokacin kuma ta nuna mashi rashin dacewar haka a gaban iyayensu, idan kuwa a gaban Hajjo ne sai dai ta tashi tana mita ta bar musu wurin ta na ce wa ita fa bata taba ganin ‘yan iska irinsu ba marasa kunya ai dai saura kiri’s ya rage ayi auran sai ku cinye juna tsabar so,” duk sadda ta fadi haka sai dai su yi dariya, ogan ne zai ce, “haba Hajjo ai tare dake zamu tare sai ki sake sabon kallo wannan ba abinda kika gani kisha kurunminki.”

 

 

****Duk lokacin da zai koma makaranta kuwa da kuka suke rabuwa har ciwo take kwanciya da kyar ake banbareta daga jikinshi, iyayensu su yi ta fada suna mamakin wannan soyayya ta Yaya Mustapha da Hanan,,,,, har ya dawo bata da walwala in kuwa ya dawo kowa sai ya san ya dawo don Hanan kadai mutum zai gani ya gane ya dawo.

 

 

***Haka rayuwa ta yi ta tafiya har aka saka bikinsu, A ranar kuwa babu kunya su ka yi ta fadama yan uwa da abokan arziki,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, ranar wata alhamis Yaya Mustapha ya dawo daga school ko abinci bai ci ba ya dauki wanka na fitar hankali ya nufi gidan kawu karami dan ganin sahibarsa sosai ya yi kyau cikin kananin kaya tun last week ya ke son ganinta domin kullum idan ya kwanta sai ya yi mummunan mafarki akanta gashi wayarta ko ya kira swich up shi ya sa gabansa ya ke ta faduwa **A tsakar gida suka gaisa ta mishi sannu da hanya, sun dan jima suna fira ya na son tambayarta ina take amma ya rasa ta yadda zai tambayeta, ganin ya yi shiru yasa Umma ta ce ka shiga mana tana daki bata jin dadi ne…. Kafin ta karasa ya yi saurin katseta, Umma me ya sameta ne!?

 

Zazzabi da ciwon kai ne kuma ka san halinta bata son shan magani may be kai idan ka bata tasha ta karasa maganar ta na wucewa kicthen, cikin sauri ya shige dakin hade da sallama amma shiru bata amsa ba hakan yasa ya kunna kai cikin dakin jin kamar numfashin mutum sama-sama ya na fita acikin dakin a saman gado ya hangota kudundune cikin bargo sai rawar sanyi take duk da uban bargon da ta rufe jikinta dashi *******Hanan!!! Hanan!!! Ya ke fadan kira cike da alamun razana da tashin hankali ya na kokarin tada ita zaune, da kyar ta iya daga kanta ta kalleshi da jajayen idanuwanta ta na magana a hankali,, matsota ya kuma yi jikinshi ya na kara kankameta a kirjinshi, da kyar ta iya furta ta na mishi nunu da kirjinta cikin matsanannaciyar azaba ta ce “Yaya Mustapha kirjina!!, zuciyata zata buga mutuwa zan yi ka taimakeni zan………………lokaci daya ta sandare ta mimmike……

 

 

Muje zuwa 🤸🏻‍♀️

 

 

 

(Ya Ubangiji Allah kada kaba shedan sa’a akaina ta hanyar kawatamin rubutu abinda zai zama silar bacewar tarbiyar Al-umma, Ya Allah ka tsaremin zuciyata da hannuna tare da idanuwana 🤲)

 

 

 

Comments ☑️

Share ☑️

Edit ❌

 

 

Written by DR HANAN AL AMEEN (maman twins) 🤸🏻‍♀️

[18/08, 9:13 pm] +234 903 602 2224: 🤍YAYA MUSTAPHA 🤍

 

 

A ROMANTIC LOVE STORY

 

 

MALLAKIN DR HANAN AL AMEEN

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

FREE PAGE 🤸🏻‍♀️

 

 

PAGE THREE -3

 

*********Hanan! Hanan! Da karfi yake kiran sunanta ya na girgiza ta amma ko kadan babu alamun rai a tare da ita” Umma data shigo yanzu ta dafe kanta ta na maimaita Innalillahi wa inna ilaihir raju’un” Hasbunallahu wa niemal wakil” cikin tsananin tashin hankali ya fita tsakar gida ya debo ruwa Yana shafa mata a fuska” kusan tsawon minti goma kenan bata farfado ba “”Innahlillahi wa Innah ilaehir raju’un Allahumma ajirni fil masibati wa’aklifni khaeran minha Umma Dan girman Allah ki ce ta daina min kalar wannan wasan meyasa take son sakamin zuciya ya buga! …… Surutu kawai yake batare da yasan abinda yake fada ba ”cikin karfin hali Umma ta ce “calm down Mustapha babu abinda ya sameta ina tunanin doguwar suma ce sanya mata hijabinta mu tafi a asibiti ****

 

Emergency aka karbeta sosae Doctor’s suke kokarin ganin sun dae dae ta numfashinta Amma hakan ya gagara kusan awa daya suka kwashe akanta ,, jiki a sabule suka fito daga room din duk sunyi zufa’ da sauri Mustapha ya karasa ya na tambayarsu jinkin nata ”doctor pls yajikin nata kamin bayani rayuwata ce ita gabaki daya doctor ina jin ajikina some things wrong happened ”calm down bro doctor din ya fada Yana dafa kafadarshi cikin tsananin tausayin sa yace “please Muje office” tare da Umma suka shiga office din ko wane zuciyarshi na tsananin bugawa ” cikin kwantar da murya ya Fara musu bayani ‘ alhamdulillah a halin yanzu mun samu nasarar dai-daita numfashinta but sorry to say gaskiya Nayi mamaki sosai ace karamar yarinya like her ta na tare da ciwon zuciya wanda yake barazana da rabata da rayuwar ta a gaskiya irin wanan case din dole ya na bukatar natsuwa da hutu kuma duk wani Abu na tashin hankali bae kamata ace masu irin wannan matsalar Suna jinshi ba be cause hakan zai iya haifar musu da wata matsalar ** ahankali suka mishi godiya jiki a sabule suka baro office din bayan minti biyar sae ga abbanta shima yaxo hospital din hankali a tashe kafin awa biyu sae ga iyayensa da Matar baba Ali tare da kawu yusuf ” zaune suke shiru babu mae magana sai kawu Yusuf dake lallashin Mustapha Yana bashi baki,, waye yaya mustapha? ‘wata sister data futo daga dakin take fada yayin da take kallonsu, da sauri ya Mike yace nine” Ohk Dan Allah kashiga Dan tun data farka take kiran sunanka pls ka kwantar mata da hankali I think hakan xae Kara nutsar da bugun numfashinta ” Insha Allah ya fada tare da shigewa dakin ” da sauri ya isa gareta ganin Tana neman balle Karin ruwan da aka Sakamata ta sauka a gadon, hannunta ya rike ya tallabe fuskarta Yana mata kallon ido cikin ido murya a tausashe ya Fara magana Yana cigaba da kallonta kamar yace ita ma ta kafe sa da sexy eyes dinta ” meyasa kike son jima kanki ciwo precious? laifin me na miki da har yasa kika xabi ki hukuntani ta wannan sigar? Hannunta ya dora akan kirjinshi zuciyarshi na cigaba da bugawa fat fat yace meyasa kike kokarin kashe mana zuciyoyinmu bayan munada rai baby? Why? Ya fada kamar xaeyi kuka ****jikinsa ta fada ta kankamesa sosae cikin kuka ta Fara magana” Yaya Mustapha tabbas ina matukar sonka da kaunarka bana tunanin zanci gaba da rayuwa muddin aka rabani dakae kae ne duniyar farinciki na…. Zuciyata da gangar jikina Mallakin ka ne mafarkina da buri bae wuce ganin mu a inuwa daya ba!! Amma meyasa Rayuwar Soyayyarmu take shirin zama mafarki! Why? Ta karasa fada cikin matsanancin kuka!!!!!

 

***sosai shi ma ya kara rungemeta a kirjinshi zuciyarshi na cigaba da bugawa sam ya kasa fahimtar abinda take fada Ji yake kamar ya bude kirjinshi ya sakata a Ciki su zama Abu guda daya tilo ” kwata kwata ya tsani abinda zae sakata damuwa bare har ta kai ga zubar da hawaye muryarshi har ta shake saboda damuwa yace “pls baby ya isa haka ki daena tunanin xan iya rayuwa babu Ke Yaushe shedan ya samu nasarar shiga xuciyarki ya Fara gina miki tubalin toka,, Mustapha Mallakin kine Insha Allah har a lahira ki daena saka wanan tunanin a xuciyarki ………ya dagota Yana share mata hawayen fuskarta,, wasu hawaye ne masu xafi suka sake zubo mata ta bude baki za ta yi magana kenan aka bude Kofar dakin aka shigo**gaba ki dayansu suka maeda kallonsu ga Kofar ………………

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
 

Muje zuwa 🤸🏻‍♀️

 

 

(Ya Ubangiji Allah kada kaba shedan sa’a akaina ta hanyar kawatamin rubutu abinda zai zama silar bacewar tarbiyar al-umma ya Allah ka tsaremin zuciyata da hannuna tare da idanuwana 🤲)

 

 

More comments more typing 📝📝📝📝📝

 

 

Comments☑️

Share ☑️

Edits ❌

 

 

 

Written by Dr Hanan Al Ameen (maman twins) 📝🤝

 

🤍YAYA MUSTAPHA 🤍

 

 

A ROMANTIC LOVE STORY

 

MALLAKIN DR HANAN AL AMEEN

 

FREE PAGE 🤸🏻‍♀️

 

PAGE FOUR -4

 

******Umma ce ta shigo ”miye haka Kuma? ta fada yayinda take kallon su ‘har kin samu sauki kenan tunda kika fara ma Mutane kukan banza ta karasa maganar tana Jan tsaki…. ”fuska ta bata tare da turo baki sai dai Kuma bata ce komai ba ‘a hankali ta zare jikinta daga nashi ta zauna gefe tana cigaba da share hawayenta ”Murmushi yayi Yana shafa Kai da alamun rashin gaskiya a tare dashi ya ce ”Umma ki mata a hankali mana yanzu nake mata fada sai….” Ko kuma kana lallashin ta ba ta katseshi kafin ya ida fadar abinda yayi niyya ‘Murmushi yayi yana Mai kallon k’ofa ganin su Abba ne suka shigo yasa ya tashi daga kusa da ita ya tsaya a gefenta ”sannu da jiki suka mata kafin su wuce gaba dayansu zuwa masallacin da ke cikin hospital din jin ana kiran sallar magriba ”daga masallaci gida su dadynshi da baba Ali suka wuce ‘Abba Kuma da kawu yusuf suka samu gefen hanya bisa wasu kujerun roba dake kusa da masallacin suka tsaya Suna magana ”zaune yake cikin masallacin bayan sun idar da sallah kowa ya fita sai shi ka d’ai ya rage ‘sosae maganganunta Ke mashi yawo a cikin Kai ‘to me ta ke son fad’a Mashi ne Wanda shigowar Umma ya hanata? tabass yana ji ajikinshi dole da akwai abinda Ke faruwa a gidan kawu k’arami Wanda su Ke b’oyewa masa ‘ wani b’angare na zuciyarshi Kuma ya nata k’ara nusar dashi akan maganganunta na d’azu ‘shin to miye silar ciwon Hanan Wanda har yake barazana da rayuwarta?? Tabbas ya hango damuwa a tattare da ita ‘haka zalika Kuma yaga tashin hankalin a fuskar Umma lokacin da ta Ke shigowa daki dazu har ta katse musu firarsu!….kwarai akwai abinda ba dai dai ba Wanda Kuma ya kamata ace ya samu k’arin haske a kansa ‘lokaci daya yaji zuciyarsa ta buga saboda wani hasashe data mashi ‘Innahlillahi wa Innah ilaehir raju’un Allahumma ajirni fil masibati yayi ta Mai maitawa yana nan zaune har akayi ish’sha’i sannan ya fito ya nufi oisis shop dake cikin hospital din ya siyo musu abinci ‘a hankali yake tafiya har ya isa bakin room din zai bude K’ofar dakin kenan yaji kamar muryar Abba da Umma natashi a cikin dakin like masu maida ma juna magana ” sautin muryar Umma yaji cikin rauni tana fadar ”Haba Abban Hanan meyasa Kake son lalata alakar dake tsakaninka da ‘yan ‘uwanka’ kaji tsoron Allah ka tausaya ma yaran nan ka canza mummunar akidarka daka tsira’ Kada kace zaka Dora rayuwar auren ‘yarka abisa tubalin toka ‘domin Allah bazai taba barinka da hak’kinsu ba! miye ribar wannan abun da ka ke ko’ko’rin yi? Miye makomar Rayuwar ‘yarka akan tursasata wurin yi maka biyayyar da ko a addinin islama haramun ne? Kada ka manta Nima fa inada hak’k’i a kanta Kuma wallahi bazan bari kayi mata abinda iyayena da naka basu mana ba!! ”a hankali ta sassauta murya tace kaji tsoron Allah Abban hanan Kada ka aikata abinda zaka dawo daga baya kana dana Sani baka isa kace zaka canza abinda Allah ya rubuta ba sai dai ……”rufe min baki Fatima wallahi ranki zai mummunan b’aci yanzu wallahi bana son shashancin banza da wofi, d’anki ne ni da zaki tasa a gaba kina ma fada, ni nake auranki ko Ke ce kike aurena, ya fada a d’an tsawace Yana huci ”Allah ya baka hakuri Abban Hanan gaskiya ce dai baka so, Kuma dole na fad’a maka ko zaka cire wuyana daga jikina…. ”Ohk Allah ya baki sa’a ya fada yana ko’k’arin juyawa ya bar dakin ………………………………………….✍️

 

 

 

Kuyi hkr da wannan kunsan jiki da jini🥱🥱🥱

 

 

Muje zuwa 🤸🏻‍♀️

 

 

(ya ubangiji Allah kada kaba shedan sa’a akaena ta Hanyar kawatamin rubutu abinda zae zama silar bacewar tarbiyar Al umma ya Allah ka tsaremin xuciyata da hannuna tare da idanuwana 🤲)

 

 

Comments☑️

Share ☑️

Edits ❌

 

Written by Dr Hanan Al Ameen (maman twins)

 

 

 

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

🤝

Leave a Comment

error: Content is protected !!