Kiyon Lafiya

Yaya Mutun Zai Gane Yana Da Karancin Mani Ko Kuma Lalacewar Maniyin

Yaya Mutun Zai Gane Yana Da Karancin Mani Ko Kuma Lalacewar Maniyin ?

Assalamualaikum likitocin wannan gida masu albarka Dan Allah a sakaye sunana tambayace Dani Dan Allah ta Yaya mutun zai Gane Yana da karancin Mani ko Kuma lalacewar manidin wlh Ina cikin ko kwanto watana 8 da aure ammafa babu labari Kuma wlh inde ta wajan bangaren aikine babu a magana Amma ba labari .

AMSA 

Yayi wuri ka fara tunanin cewa kanada matsalar karancin maniyyi (low sperm count) mai hana namiji haihuwa. Jagoranmu Pharm Dr Kabir Danwuri ya sha fadin cewa bai kamata ma’aurata suyi tunanin sunada matsalar haihuwa a kasada shekaru 2 dayin aurensu ba. Don haka wata 8 kawai, me akayi da maza, inji masu iya magana. Ka cigaba da ibadah kawai.

Abubuwan da suke haddasa rashin haihuwa ga maza suna da yawa, kamar karancin maniyyi (low sperm count), rashin ingancin halittar ‘ya’yan maniyyin (poor sperm quality), kumburin maraina (vericocele), rashin daidaiton zubar ruwan sinadaran testosterone da follicle stimulating hormone (FSH) da leutinizing hormone (LH), da gado daga iyaye ko kananni (genetic factors).

Abubuwan da suke haddasa rashin haihuwa ga mata sune rashin saka kwan haihuwa (anovulation), toshewar bututun fallopian tube (fallopian tubes blockage), cututtukan mahaifa (uterine disorders), daukewar al’ada saboda nisan shekaru (menopause), rashin daidaiton zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone (hormonal imbalance), gado daga iyaye ko kananni (genetic factors), da sauransu.

Don haka, koda kunada matsalar rashin haihuwa, to, babu hujjar da zata sanya kace kaine kake da matsalar ko kuma matarka ce. Binciken kimiyya na asibiti ne kawai zai iya tabbatarwa. Sa’annan sakamakon binciken ne kawai zai iya nuna irin matsalar da kuma tsananinta.

Bayan haka, matsalar karancin ruwan maniyyi ko ‘ya’yan maniyyi ba’a iya gane ta a ganin ido, sai ta hanyar binciken kimiyya na asibiti (laboratory tests).

A takaice, ka cigaba da aiki kawai, sai abinda Allah SwT yayi.

WalLahu A’lam.

Leave a Comment

error: Content is protected !!