Hausa Novels

Yayanah ko ruhi na Hausa Novel

  • Yayanah ko ruhi na Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

YAYA NAH KOH RUHI NAH* ?

Na Pretty BiBi
86:

Sunyi kusan 4 minutes ahaka, jin ta daina kukan ya janyeta daga jikinsa. Zaunarda ita yayi bakin gado shima ya zauna gefenta. Yace “Babu abinda yake faruwa da dan Adam wanda Allah baida masaniya akai, shi yake tsara komai Princess saboba haka na Fawwala mashi komai nima Amma bazan boye maki ba Ina Jin abin acikin raina dukda Ban ta6a jin inason Siyama bah duk iya saninta da nayi har yau, Amma Dan cikin nata ya kasance daga jikina ya fito so I am sorry banida option daya wuce In so shi. Amma kinga yadda abu ya kasance, Siyama is not willing to accept her destiny sai kuka takeyi saying she won’t spare you wai kin Kashe mata Baby. Ga UMMI a dayan bangaren is not ready to listen to me either tace sai ta hukunta ki kuma she seems angry And Serious about it bansan ya zanyi masu bah” riko hanunsa tayi tace “Yaya Kayi wani abu akai, nasan halin UMMI tunda ta rantse akan maganar nan shikenan Babu abinda zai hanani barin gidan nan” ya shafa kanta yace “ya zaayi UMMI tace ki bar gidan nan Princess kinada inda yafi nan neh? Nasan fushi neh kawai dole zatayi hakuri ta kyaleki, yanzu kawai ki zauna cikin dakin nan kada ki fita koh ina zan rufeki ta baya kinji?” Gyada masa Kai tayi a sanyaye tace “Yaya inajin yunwa tunfa breakfast banci komai bah har yanzu” shafa kumatunta yayi cikeda kulawa yace “Kiyi hakuri na rufeki ban dawo da wuri bah, duk Abinda nakeyi kina raina inata Allah Allah in dawo amma babu yadda na iya neh shiyasa na dade” ta tura baki gaba tace Toh “get me something to eat” mikewa tsaye yayi yace “me kikeso kici?” A hankali tace “Fried Rice” Murmushi yayi ya fita daga dakin. Tanajinsa yayi locking kofar ta baya, kwanciya tayi kan gado tana tunanin yadda komai yake faruwa. Wai yau itace ake rufewa a daki saboda a bata kariya daga gurin Umminta kuma duk a sanadin Siyama, tasan halin Ummi tunda ta nace kan maganar nan Toh tasan bazata kyaleta bah.

A Parlo ya tadda Anti Laila da Salman suna zaune, yace “Anti Laila akwai abinci? Rice in particular “ Laila tace “Spaghetti aka dafa Farhaan” ya dan sosa keya yace “Zaa iya preparing min fried rice yanzu? Kadan koh da one plate ne kawai?” Tayi Murmushi tace “ bari In daura” UMMI da fitowarta daga kitchen kenan tace “bazaki daura bah, idan yanaso taci abinci ya shigo ya defa” marairaice fuska yayiI yace “Plsssss Ummina” koh kallon inda yake batayi bah tayi hanyar sama tana fadin “Laila na dai gayamaki kada ki daura mashi wani abinci a gidan nan” ajiyar zuciya yayi ya dubi Anty LAILA yace “Toh zaki koya mun yadda ake preparing?” Salman yayi daria yace “Yaya kada ma ka fara wallahi don Batama kanka lokaci zakayi, gwara kawai kayi order nanda 15 minutes koh 20 akawo maka” zama yayi kan sofa yace “Nice idea” bayan yayi ordern ya mika ma Salman wayarsa yace “zanje part din Daddy idan an kawo ka amso mun”

Bayan sun gaisa da iyayen nasa Daddy yace “Nasan kasan kaddara ta riga fata saboda haka banso ka saka damuwa a ranka tunda dai Allah ne ya bada Kuma ya amshe abinsa. Itama Siyaman ka dinga bata baki kaji, nasan su mata sunada rauni yanzu sai ta sa abin a ranta. Kuma banason a dau laifin kowa, Mommynku tazo tanata mun surutai wai Simraan ce ta 6arar da Babyn. Toh idan ba wauta irin tasu ba taya za’ayi suce Simraan ta aikata haka, tsautsayi ne yazo Simraan ta zama sanadin Zubewar cikin nothing more. Kada kuce zaku pressurizing yarinyar nan Please “ Gyada Kai Farhaan yayi Abbu yace “Nima abinda naketa nanata ma Umminsu kenan, tun a waya ta kirani take jaddada mun Sai ta hukunta Simraan ni koh nace wani irin hukunci zaa yi abinda Allah ne ya nufa hakan zai faru, kasan su mata idan suka tashi yin wani abin sai ka rasa gane kansu da kuma me suke tunani” Farhaan dai shiru yayi yana sauraronsu. Sallama Noor yayi ya shigo palon, ya zauna gefen Farhaan ya gaishe dasu kana yace “Ummi ce tace in sanar maku tanada bukatar yin magana Daku, zata iya zuwa yanzu koh abar maganar sai safe?” Abbu yace “koma menene ai a bari safe yayi koh” Noor yace “Toh shikenan”

Zaune ya tadda Salman a parlo Da Ledar abincin a hanunsa. Ya amsa tareda wayarsa ya haura sama, Bude kofar dakin yayi ya shiga. Kwance take kan gado ta dukunkune cikin duvet, Zama yayi kusada ita ya janye duvet din yace “ki tashi ga rice din” mikewa tayi ta amshi ledar fuskar ta daukeda Murmushi tace “Fried din neh ciki ?” Ya Gyada mata Kai tace “Nagode Yaya” saida ya tabbatar ta cinye abincin duka kamin ya bar dakin zuciyarsa cikeda Kauna da kuma Tausayinta.

A kan gado ya tadda Siyama zaune ta hada Kai da gwuiwa tana sheshekar kuka. Karamar tsaki yaja a ransa yace “abin nata ma ai yayi yawa, cikin 5 weeks din takema kuka haka sai kace wacce ta haihu Dan ya koma” Bathroom ya shiga ya watsa ruwa, koh kulata baiyi bah yayi sallar isha’i kana ya haye gado ya kwanta. Tun Yadda ya shigo ya taddata kanta a hade da gwuiwa take har yanzu tana kan kananan kukan, kallonta kawai yakeyi yanajin wani bacin rai na taho masa kamar Yace mata ta fita parlo tayi kukan nata don tanaso ta hanashi Bacci. Wayarta dake ajiye kan gadon tsakankaninsu neh yayi haske, kallon screen din wayar yayi yaga call neh na HDR Amma kasancewar wayar na Silent yasa bataji bah. Kusan 4 calls Haidar yayi dropping kamin a hatsale Farhaan yace “Ke wannan cousin din naki maye neh shi koh mutum? Ya zaayi yayita kiran matar Aure dare dare haka sai kace kinci masa bashi” zabura tayi ta dago Kai dubi Farhaan din. Ya harareta yace “ki daina kallo nah ni wayarki ake kira” daukar wayar tayi ta kashe gaba daya zuciyarta na tsananta bugawa. Farhaan yace “idan kinsan kuka zakiyi Toh ki fita palo ki kwanta kada kice zaki min anan don Bacci nakeso nayi” share hawayen idanunta tayi ta kwanta.

Washe gari tunda sassafe ya fita zuwa dakin Simraan. Bacci ya tadda ta takeyi, Kissing goshinta yayi Yace “Princess wake up” bude Big eyes dinta tayi ta zuba kan kyakyawar fuskarsa, yayi Murmushi yace “kinyi Sallah? Ta Gyada mashi kai ya kuma ce “kinajin yunwa?” Nan ma Girgiza mashi kai kawai tayi. Yace “Sorry na tasheki I thought kin makara Sallah neh, ki koma Baccinki kawai” a shagwabe tace “Yaya har yanzu UMMI bata huce bah?” Yayi Murmushi yace “zata huce ne nan bada jumawa ba kinji koh”

bayan ta karanta sakon haidar a kidime tayi dialing numbarsa. Yana picking tace “Haidar the Baby is fine wallahi, bana kusa da wayar neh duk calls dinda kake ta yi” a tsawace haidar yace “Dallah Mallama kiyi ma mutani shiru, keh a nawa kike da zakiyi fooling dina. Koh an gaya maki bansan abinda ya faru bane? Murya na rawa tace “Menene ya faru haidar?” Tsaki yaja yace “Siyama you messed with the wrong person wallahi, ba zai da nace kada ki bari wani abu ya sami Babyn nan bah? Shine kika biyema Dan iskan mijinki ya dinga surfa ki har kuka zubar mun da Baby, Toh wallahi kinyi kadan Siyama. Pleadingly tace “Haidar don Allah kayi hakuri, idan kanaso zanzo inda kake koh Gobe neh. Duk abinda kakeso zan maka in fact koh Sabon ciki neh na yarda kamin” Murmushi mai sauti yayi yace “Keh ni koh sha’awarki ma banayi yanzu, abinda na sani kawai shine sai na dau fansa. Saboda haka zan baki zabi, koh ku bani makuden kudadenda kuka min alkawari koh kuma In tona maki asiri gurin mijinki, idan kuma yaki yarda da zance na zan kasheki In kashe sa In kuma kashe uwar ki” fashewa da kuka tayi tace Haidar don Allah kada ka tona min asiri na maka alkawarin Zaa baka kudin nan Amma ba yanzu ba, Mijina bai fara sake min kudi bah wallahy amma Da zaran ya fara bani kudi zan na aiko maka” wata doguwar tsaki Haidar yaja, tace “Haidar Please….!” Kamin ma ta gama magana Ya kashe wayarsa. Farhaan da shigowarsa kenan kuma yaji lokacin da take Cewa haidar please neh yace “Idan na kuma ji koh nagani da idanuna wannan haidar din ya kiraki zakisha mamakin abinda zan maki neh”
[29/08, 10:39 pm] +234 704 505 8091: YAYA NAH KOH RUHI NAH?

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Na Pretty BiBi
🥺❤️87:

Kallon UMMI kawai Abbu yakeyi da mamaki, shi bai taba kawo zata zo Da wannan batun nan kusa bah. Hade rai tayi taki koh kallon inda yake, Daddy yace “Amma Ummin Sadeeq, lokaci daya kawai kika yanke shawaran ayi auren Simraan da Alhaji Majeed bayan ke da kanki kikayi objecting kwanakin baya da akazo maki da batun” A natse Ummi tace “ Sauyin ra’ayi na samu Alhaji, saboda naga babu amfanin zamanta haka babu aure zata iya yin karatun ta koda tana gidan mijinta neh tunda dama lokacin da zaayi aurensu da Farhaan anyi akan zata ci gaba da makarantan ta neh, Toh inaga babu Wani damuwa indai shi Alhaji Majeed din ya amince” Daddy ya gyada Kai yace “shikenan Zamuyi magana da Farhaan duk yadda ake ciki zai sanar maki” UMMI tace “Alhaji Dama nafiso duk rintsi kada bikin ya wuce nan da kwanaki bakwai” Abbu yace “Ummin Sadeeq kamar yaya kwanaki bakwai Kuma? Babu shiri babu komai kawai kinaso abiye ma taki, koh Simraan din ta tsare maki wani Abu neh?” Murmushi UMMI tayi. Daddy ya dubi Abbu yace “kwanaki bakwai ba matsala bane indai komai ya daidaita, munaso dai muji ra’ayin Ita Simraan din tukun” UMMI ta gyada kai tace “shikenan Hakan ma yayi”

da Dan karfi Farhaan yace “What! Daddy, wani Alhaji Majeed kuma zaa Aura mata? Yarinyar da bata gama University bah” Daddy Yace “idan banda Kai da abinka Farhaan ai Aure baya hana makaranta, Kai dama da zaka aure tah ai an tsayar Da magana kan A gidanka zata gama. Toh miye kuma kake mayar dashi big deal yanzu” Farhaan yace “Na sani Daddy Amma dai Inaga kamar ya girme mata ai Alhaji Majeed din” Abbu yayi Murmushi yace “Ina wani girma a lamarin aure Farhaan, kuma ma ni yadda naga Majeed din Sam baida wani girma Sosai da har zakace ya girme mata. Farhaan yace “Shikenan Daddy zaasan yadda zaayi Amma da an dan dakata Da maganar”

Zaune ya sami UMMI da Sapna a palo, Amsar Babyn Sapna yayi ya zauna kan kujera yana kallon Babyn with much love. Bayan few minutes ya dubi Ummi yace “Ummi Magana nakeso muyi” UMMI ta hade rai tace “Nasan abinda zakace kuma ban shirya sauraranka bah” ya marairaice fuska yace “UMMI dan Allah dai” mikewa Sapna tayi ta amshi Babyn hanunsa ta haura sama. Komawa yayi kan kujerar da UMMI ke zaune ya zauna dab da ita yace “Ummi Dama wannan shine hukuncin Simraan?” Gyada masa Kai tayi tace “kwarai kuwa” Yace “Haba mana Ummi, abin nan fa tsautsayi neh ba wani abu bah. Kiyi hakuri ki janye maganar aurar da Ita please” Ummi ta hararesa tace “ai dama na maku rantsuwa idan ta kureni sai ta bar gidan nan, Simraan batason halin matarka bataso suyi zaman lafiya. Duk tabi tasata gaba da rashin kunya, karshe tazo ta sama Dan’cikin ta idanu har saida ta barar dashi tukun ta sami sukuni. Kaji na kuma rantse maka Farhaan dole Sai Simraan tayi Aure tabar gidan nan, wannan Alkawari neh dana daukar ma kaina” wani bugawa zuciyarsa tayi jin rantsuwarda UMMI tayi. A kidime yace “UMMI kiyi hakuri, nasan bacin rai ne Amma ai zaki huce dan Allah karkiyi haka” A hatsale Ummi tace “Idan ban aurar da ita ba me zan mata Farhaan, aikin me take mun a gidan nan banda zaman daki iyeh? Daga zaman daki sai neman matarka da Fada, Kuma dai Siyama kamar amana iyayenta suka bamu bazai yiwu Ace mun Zubama Simraan ido tana tozartar da ita bah. Allah zai kamamu idan muka aikata son zuciyarmu kan Siyama. Abinda zanyi din nan shine adalci” Mikewa yayi a sanyaye ya shiga kitchen, Abincinda yasa anty laila ta zuba mashi a food flask ya hada dan karamin tray din komai da komai. Da ido UMMI tabisa har ya haura Sama ta girgiza kai kawai. Bude dakin yayi ya shiga, tana ganinsa ta tura baki tareda hararinsa. Ya ajiye Trayn kan bedside drawer ya dubeta yace “I can see my Princess is Angry with me, gayamin Toh me laifin me nayi? Ta shagwabe murya tace “Tun dazu nake jiranka da abinci nah bakazo bah” Murmushi yayi yace “ina gurin Daddy neh” food flask din ta bude tayi serving kanta Shinkafa Da miya. Yana zaune yana kallonta tana ci a nitse. Bude kofar dakin akayi UMMI ta shigo, dafe kansa yayi a ransa yace “Darn it!” Shi mantawa yayi bai rufe kofar da makulli bah gashi UMMI ta shigo. Da kyar Simraan ta hadiye rice dinda ta sanya bakinta, sadda kanta kasa tayi saboda wani mugun kallo da UMMI ta mata. Zama tayi bakin gado tace “Ina fatan Yayan naki ya sanar maki da sako nah? Da sauri ta Girgiza Kai. Ta dubi Farhaan tace “Bamu guri” a sanyaye ya mike ya fita daga dakin. Ta dubi Simraan fuska a murtuke tace “Saida na gargade ki akan cikin Siyama Amma kika qi ji sannan kikayi son ranki ko? Girgiza Kai tayi hawaye na taruwa a idanunta tace “UMMI ban mata komai bah itace ta nemeni Da magana tsautsayi ya auku ta fada” hararta UMMI tayi tace “Nayi rantsuwa sai kin bar gidan nan kuma inakan baka ta” Simraan ta riko hanunta tace “UMMI kiyi ma Allah kada ki koreni daga gidan nan banida inda zanje kema kin sani” Janye hanunta tayi tace “Ni bance zan koreki daga gidan nan bah, a ruwan sanyi zaki tafi” kallonta Kawai Simraan takeyi. Ta hade Fuska tace “Bayan an soke maganar ki da Farhaan kin sami wanda kikeso? Akwai wanda kikeji a zuciyarki?” Da sauri ta Girgiza Kai tace “banda kowa UMMI” Ummi ta Gyada Kai tace, “Naji dadin haka, abinda nakeso ki sani shine an maki miji. Dama akwai Alhaji Majeed da ya ganki tun ranar daurin Auren Farhaan da Siyama, ya sami Alhaji da magana ni ce nace a dakatar Da maganar zuwa Wani lokaci. Toh yanzu neh lokacin, na riga na masu magana sunce zasu tambayi ra’ayinki. Shiyasa ma nazo In maki gargadi, koh da wasa kada ki kuskura ki ce bakison Alhaji Majeed idan ba haka ba zaki fuskanci Fushi na da bacin rai na wanda baki taba gani bah, kin fahimce ni koh kuwa?” da sauri Ta Gyada Kai hawaye na Tsiyaya daga idanunta tace “naji na Fahimta UMMI” mikewa Ummi tayi ta fita daga dakin. Kuka sosai ta fashe dashi, tanaji zuciyarta na mata nauyi. She can’t believe abinda UMMI ta gayamata, ji kawai take kamar a mafarki hakan ya faru. Wai ita Zaayi ma Aure da wani Alhaji Majeed. Bude kofar yayi ya shigo da Sauri yayo gurinta, zama yayi kan gado ya jawota jikinsa. Kara karfin kukanta tayi, patting bayanta Ya fara yi a hankali. Cikin kuka tace “Ruhi kaji abinda UMMI take fadi wai aura ni zatayi ma wani, ka taimaka ka hana hakan Faruwa wallahi banason Auren kowa inba Kai bah ni Kai nakeso” Da kyar ya budi bakinsa yace “Princess kinsan babu aure tsakanina dake koh, banaso inga kina wannan kukan plsssss kiyi shiru kinji”

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!