Hausa Novels

Yayi min illa Hausa Novel Complete

Yayi min illa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

YAYI MIN ILLA Page One

 

 

 

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

“`Gidan karamci, rubutu don ci gaban al’umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.“`

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

 

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

 

 

 

“`Marubuciyar

Ramin Mugunta

Fulanin Tashi paid book 1&2

Baƙar Ashana

Namiji rigar ƙaya 👉( Yayi min illa) “`

 

 

_Alhamdulil Lah! Allah na gode maka da ka bani ikon fara rubutun littafin nan lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya ka yafemin kura-kuraina ka hane ni da rubuta abinda ya saɓa maka Amin_

 

 

Labari da rubutuwa.

 

*Ruƙaiya Abubakar Umar (Waheedat)*

 

Shafi na farko.

 

_SAHIH INTERNATIONAL SCHOOL na’ibi street goron namaye road U/mu’azu kaduna._

 

Yau monday tushen aiki kenan, sauri sosai ni keyi kamar zan tashi sama saboda lattin da nayi burina ɗaya shine be wuce in ganni a makaranta saboda na makara yau sosai, gashi muna da nisa tsakaninmu da unguwar mu’azu kuma lokuta da dama bama samun ababen hawa da safe.

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

cikin lokaci ƙanƙani na isa makaranta amma duk da haka nayi latti, kai tsaye ajina na wuce na zauna tare da gabatar da abinda zan fara (ma’ana darasin ranar) ana haka se ga ɗaya daga cikin malaman makarantar wadda take ɗaukata matsayin ƙawarta yayinda ni kuma ban cika shigewa mutane ba nafi so nayi rayuwata ni kaɗai bansan rayuwar ance kace shiyasa nafi so na zauna matsayina ba tare da na shiga haƙƙin wani/wata ba, gaisawa mu kayi kamar yadda muka saba tukum ta koma ajinta.

Bayan an tashi tara se gata ta kuma shigowa ajina nan muka dasa labari saboda ita tana da son mutane da kuma son surutu sosai tun ina amsa mata sama-sama harya zamo muna zama muyi hira na lokaci kamin mu rabu, ana haka cikin hirar ne take faɗamin ai shugaban makarantar yace yana so na, ɗaya daga cikin malaman makarantar tace masa an min miji babu yadda za’a yi a nemi aure kan aure.

Cikin rashin jindaɗi ƙaryar da malamar ta min nace.

“Lalle Anty Rahama, Ni kam wa ya faɗa mata an min miji kuwa? saboda ban taɓa kalan wannan hirar da wani ba”,

Galala Anty Zaliha ta sake baki tana kallona haɗi da faɗin.

“Yanzu dama ƙarya tayi masa kenan? lalle idan yaji wannan labarin baze ji daɗi ba, saboda yadda ya nuna yama sonki tun farkon zuwanki makarantar nan amma tace masa an miki miji, yanzu haka maganar da ake Ashirin da bakwai ga watan nan zeyyi aure, dun da ta faɗa mishi an miki miji wallahi wata ƙawar matarsa da ta rasu ta haɗashi da ƙanwarta”,

dariya kawai nayi nace kice zamu sha biki kenan? ɗaga kai kawai tayi itama tana dariya tukum ta miƙe ta shige ajinta saboda hango shugaban makarantar da tayi.

ɓangarena kuwa ba ƙaramin haushi ƙaryar da tamin na an min miji shine ya bani haushi, lalle ma matar yo ita ɗauka take ko da yazo da kansa yace yana so na zan amince masa ne? tab Allah ya kyauta nace tukum na ci gaba da abinda nikeyi har zuwa sanda aka tashi.

Ina komawa gida na ci gaba da harkokina kamar yadda na saba, saboda ni ko da yaushe waya ce ƙawata kuma abar hirata sau da dama bana iya barin wayata ta huta, mamana kuwa ba ƙaramin damuwa take ba in taga na ɗauki waya ina daddanawa musanman taga ina dariya nan da nan ranta ze ɓaci tayi tamin faɗa, ni kuma ɓangarena mafi akasarin lokuta ina harkar rubutuna ne, wani lokacin kuma in buɗe data inta hira da ƙawayena marubuta musanman wata ƴar nijar marubuciya me suna Chafa’atu ina matuƙar jindaɗin hirar da nike da ita, se kuma in leƙa face book inta kallon abubuwan dariya kamar me.

haka dai nike rayuwata wayata ita ce ƙawata dan in bani da class sai in shafe a wanni da yawa ina amfani da ita, sannan rayuwata kyalkyalin duniya be dameni ba,

 

Wash! Na jima banyi typing ba, amma in sha Allah zan ci gaba zuwa dare

YA YI MIN ILLA

 

 

 

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

“`Gidan karamci, rubutu don ci gaban al’umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.“`

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

 

**

 

 

“`Marubuciya“`

“`Ramin mugunta“`

“`Fulanin tashi paid book 1&2“`

“`Baƙar Ashana“`

“`Na miji rigar ƙaya👉🏻(Yayi min illa)“`

 

 

Labari da Rubutawa.

 

Rukaiya Abubakar Umar (Waheedat).

 

 

Shafi na biyu ✔️

 

 

 

Bana gasa da wani ko wata, sannan bana tara samari da yawa da sunan ado ko wani abin, ni a tsarina idan mutum yazo yace yana so na to tabbas in na aminta da halayensa ina turashi wajen mahaifina ne kawai, tukum ina da lalurar da dole idan mutum yaxo neman aurena sena faɗa masa walau ya tsaya mu ci gaba da soyayya ko kuma ya ƙara gaba ya nemi wata, *(Ina kira gareku ƴammata da samari da kuma jan hankali Don Allah idan mutumin kirki yazo neman auren ƴarku idan kun bincika kunga beda wata makusa to ku bashi aure sannan idan ƴarku ya zama tana da wata lalura wacce take fama da ita ku sanar da wanda yazo neman aurenta karku rufe kuce se bayan aure tukum ya faɗa hakan ba dai-dai bane ba)* wannan dalilin yasa duk wanda yazo neman aurena kafin iyayena su faɗi lalurata na faɗa, wani sa’in ma zuwan farko nike faɗa to kaifa wane ina da lalurar jinnu zaka iya aurena a haka, ko kuwa za muyi haƙuri da juna tunda maza da yawa basa so su auri mace da lalura sedai in bayan aurensu ne Allah ya jarrabeta da lalurar shine wasu zasu haƙura su zauna dasu hakanan babu yadda za suyi ne, sannan kuma akwai masu imani cikinsu wasu idan suka ce suna sonka to suna sonka ne har cikin zuciyarsu, wasu kuma ƴan soyayya ne kawai ayi soyayya a wuce fagen.

Haka na tashi haka nike rayuwata yara sune abokaina da kuma wayata, kasancewar mu goma cif mahaifiyarmu ta haifa ni ce ta biyu, daga Yayata Mardiya seni ke binta sai ƙanina Abba da sauran, sau da dama ƙawayen Yayata ko ƙawayen ƙanwata ummi zasu xo ni kuma babu me zuwa wajena saboda bana ra’ayinsu kamar yadda na faɗa tun farko, Babana har tambaya yake ni bana da ƙawaye ne kwata-kwata bana fita daga makaranta se makaranta, sedai kawai nayi murmushi saboda ko da na shirya nace zani wajen wata ƙawa to bana zuwa sedai na ɗan wasa ƙafata na dawo gida wannan shine kaɗan daga cikin tarihin rayuwata.

A hankali na saba ta malaman makarantarmu har muke zama muyi hira dasu idan an tashu break, har sabo ya shiga tsakaninmu sosai musanman Anty Zulaihat da bata ɓoye min komi dangane da rayuwarta, cikin lokaci ƙanƙani se gashi har mun ƙulla ƙawance na fara zuwa gidansu kums ko da yaushe muna tare a waya.

Yau ma kamar kullum nazo makaranta bayan an tashi break muna zaune muna kwasan dariya sega shugaban makaranta ya shigo (Section) ɗinmu, ajina ya fara shigowa muka gaisa dukkanmu tukum sauran suka miƙe suka shige ajinsu ni kuma na ci gaba da yima yara karatu, ina tsaka da yima yara karatu Anty Rahama ta shigo kanta tsaye ta fara balbaleni da faɗa akan mu dena zama wuri ɗaya da sauran malaman idan antashi break saboda yadda yara ke duduma a cikin azuzuwa ba ruwanmu dasu, gyaɗa kaina kawai nayi ba tare da nace mata komi ba na ci gaba da abinda ni keyi tana tsaye tana kallona, ni kuma a ɓangarena ban cika salwantar da miyon bakina ba akan wani ɗan dalilin da be taka kara ya karya ba, kawai ni abinda na tsana shine in zaka min faɗa ka jani gefe kayi min faɗa ba ka tsaya bainan nasi kana faɗamin ba sukari ba, hakan na ƙona min rai sosai kuma sena dunga gani baka ɗaukeni komi ba shiyasa kale dizgani wajen mutane, ganin bance mata komi bane ba yasa ta fice daga ajin ta wuce ta ajin sauran malaman ba tare da ta musu faɗan da tamin ba, saboda ina iya jiyo duk abinda yake gudana daga sauran ajin, sema wasa da dariya da suka dinga yi harta fita daga azuzuwansu ta wuce nata.

 

Ana tashi daga makaranta bab tsaya ko ina ba, na dawo gida bayan na huta na bama mamana labarin abinda ya haɗamu da Antyn nan ya kaiga tamin faɗa, haƙuri mamana ta bani tace ai wajen aikin kenan dole se kinga abinda bakyaso wata rana kuma haƙuri akeyi baa ramawa dan idan kace zaka rama abinda wani yayi maka ba ci gaba kenan sai ci baya, haka ta dunga bani baki tukum na haƙura.Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Yayi min illa Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!