Hausa Novels

Yiwa Kai Hausa Novel Part 1

Yiwa Kai Book 2 Hausa Novel Part 1

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[12/10, 5:29 pm] +234 814 210 5218: _YIWA KAI…!_

 

 

 

Daga marubuciyar.

_*1️Matar*_ _*gwamna*_

_*2Hatsabibiya*_ _*Ramlat.*_

_*3Zee Baby.*_

_*4Aunty*_ _*Rumaisa.*_

_*5Banida Gata.*_

_*6Kamal Ne.*_

_*7Ruwaida.*_

_*8Halaccin maza 2.*_

_*9Abinda zuciyata ta zab’a.*_

_*10Mijin Mamy.*_

_*11Dattijon arziqi.*_

_*12Jikar Bulama (Bahijjah).*_

And Now

👇🏽

_*#YIWA KAI* 13_

 

 

 

_GARKUWA WRITTERS ASSOCIATION_

“`{Marubuta masu garkuwa da alƙalami domin fadakar da al’umma}“`

 

*Duk mai buqatar a tallata masa hajarsa, ta shafin pages ko status, toh hanya a bud’e take a tuntub’i wannan +22798792126*

 

 

_A’uzubillahi Minan Shaid’anir Rajim_

 

_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_

 

 

 

 

 

 

 

*P 1&2*

 

 

_Jigawa dutse._

Yanayi ne na lokacin zafi, yau juma’a an tashi da wani irin zafi sosai, ga rana ga shi ba lokacin damuna ba, bare asaka ran saukan ruwan sama ko za’aji sassaucin zafin.

Hakan yasa sosai jama’a dayawa suke mita akan zafin, ga qaran cin wutar nefa bare wad’anda suke da fanka agidan su su kunna ko sa samu sassauci.

Wasu kuma sun fawwalawa ALLAH ikon sa, basa mita sabida suma abinda suka ga dama suke bare kuma Rabbil samawati.

Amman masu akwai wad’anda sukaci suka tayar da kai, gida A.c mota A.c office A.c basusan anayi ba, sai sun fito.

 

*Bayan sallar juma’a*

 

_Central mosque_

Duk inda ka kalla jeran gwanon motoci ne, narka-narka masu tsada da masu rangwamen kud’i, ko ina sai tarin sojoji da ‘yan sanda suke yawo, alamun akwai manyan k’uso shin k’asar acikin masallacin.

Dan yau yawan cikar al’ummar da yawan motocin sun qaru alamun sun nuna wani babba ne zai aurar da ‘yarsa ko d’ansa, abun sai ya zama biyu, sbd limamin mai bada sallar juma’an masallacin, shine mahaifin uban amarya.

‘Yan uwa da abokan arziqi sun hallara, abin sai wanda ya gani.

 

Zaune suke cikin masallacin suna jiran isowar waliyan ango, aurensu ne za’a fara d’aurawa, amman an d’aura dukkan auren da suke da shi a yau, har yanzu waliyan angon Ummulkhairi basu iso ba.

Mai shela sai fad’i yake.

“Ina waliyin ango na wajan Ummulkhairi Abdallah Umar shattima da fatan sun samu isowa?”

Lokacin da me shela ya idar da shelan hankalin minister Abdallah Shatiima yayi bala’in tashi, ya kalli dubban jama’arsa ‘yan uwansa da abokanan sa, manyan k’uso shin k’asar nan, ya maida kallonsa kan governor.

Kaifafan idanunsa ya janye daga kallon kowa, na cikin masallacin dan yasan kowa jiransa yake.

 

Wayoyinsa har guda 3 ne suka d’auki ruri alokaci d’aya, kamar had’in baki, babban sojan da yake na hannun damarsa ya qaraso wajan minister Abdallah, cikin ladabi yay masa magana k’asa-k’asa, dab da kunnen shi ya beqa masa wuleliyar Samsung d’insa.

Jujjuya wayan yay cikin iliminsa kamar yadda yake minister ilimi, ya kai wayan kunnensa Wanda sai da ya katse kiran cikin ilimi tare da kasheta kafin ya fara magana kamar gaske tare da fad’in.

Ok sai kun iso anata jiranku, No! Ba komai anyi muku uzuri.”

Ya k’arashe maganar ya beqawa sojan wayan.

Sai lokacin na gama k’are musu kallo tsaf.

Sanye dukkan family’s d’in suke da wata irin d’ayan farar shadda mai bala’in maiqo, sai k’yalli suke, ba kamar ta jikin minister Abdallah Umar Shattima.

Baqi ne, amman jin dad’i da hutu tare da kwanciyar hankali ya saka baqar fatarsa qara murjewa tana sheqi,sai bala’in taushi.

Dogo ne kyakkyawan baqin bafulatanin asali, mai cikar haiba da zati Uwa uba kwarjini, yanada cikar halitta amman baida jiki talaulayi ne, d’an kimanin shekaru, 48.

Manyan idanunsa masu lumshewa ya lumshe ya motsa k’aramin bakinsa tare da kiran sunan ubangijin shi, gabansa ya shiga fad’uwa tsoro ya cikasa, tabbas yasan ya gama kunyata cikin dubban al’ummar da ya gayyato auran ‘yarsa, ya kasa bud’e idanunsa.

Yasan kaf cikin masallacin shi aka zubawa idanu.

Muryan mahaifinsa Malam Umar Shattima ya ji yana fad’in.

“Shattima! Wai lafiya har yanzu tawagarsu Alhaji Hashim bata isoba?”

 

Cikin jarumtarsa da juriyar shi, da barwa Allah lamarinsa, duk da kuwa yasan tafaru ta qare anyiwa mai dame d’aya sata, Salim d’an amininsa Hashim ya fasa auren ‘yarsa, hakan bai saka ya ji ya karaya ba, ya bud’e shanyayyun idanunsa ya zuwaba babban malamin wanda yake mahaifinsa, ya saki sansanyan murmushi cikin kamewar shi da juriyarsa da tawakali kamar kullun cikin zazzaqar muryar shi ya furta.

“ALLAH shi temakeka Baffa! Suna hanya aqara haquri da shi mukayi waya yanzu.”

Ya k’arashe mgnar cikin alhinin abinda zai faru jimawa kad’an.

Hannun da ya ji ya dafa shi ne yay saurin maida idanunsa, akan babban aminnsa commissioner Aminu.

Murmushi ya sakar masa yana fad’in.

“Kuyi haquri sun kusa isowa.”

Aminu ya girgiza kasan ya ce.

“Muje daga waje zamuyi magana.”

Ba musu minister Shattima ya miqe yana zuba hannayensa cikin aljihun babbar rigarsa, wadda taci aikin surfanin zamani irin nasu na manya qyalli kawai yake.

Can gefen suka rab’e gefen masallacin, yayin da security’s suke tsare dasu da bindigogi a hannayensu suna shawagi.

 

Alhaji Aminu ya dafa kafad’ar Shattima ya Ce.

“Banyi zaton zaka iya b’oyemin wani abu da ya shafeka ba! Ai ni dakai wlh na d’auka tamkar Uwa d’aya uba d’aya muke, tin yarinta tare muka tashi haka tare muka zama wasu ak’asar nan, shawaramu d’aya mu kashe mu binne, haka matan mu, shin me akazo aka fad’ama da ya d’agama hankali haka? Ni ina gane damuwarka koda kowa bai ganeba.”

Shattima ya zubama commissioner Aminu kaifafan idanunsa, ya fesar da zazzafar iskar bakinsa waje, kafin ya shafi gefen fuskarshi ya furta.

“Aminu! Salim Hashim ya fasa auren Ummulkhairi nah, kasan k’aunar da take masa, ya zanyi da ita? Wlh zan iya jure komai banda ganinta cikin matsanaicin hali. Ya zanyi da jama’ar da suka cika a mosque nan suna jiran su shaida auren gudan ‘yata wacce taci burin aurenta da Salim Hashim? Daman sun shirya hakane domin su tozartani nida ‘yata KO me hakan yake nufi?”

Minister Aminu ya Ce.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!

Allahumma ajirni fii musiibatihi wa khalifni khairan minha. Mu Hashim zai wulaqanta? Toh wlh bamu yayima ba kansu suka yiwa, akwai ranan nadama tana zuwa, wallahi Abdallah duk wanda ubangiji ya rufawa asiri ba mai tona masa, muje yanzu a d’aura auren da Abdullahi d’ana wanda na isa da shi.. Kuma kakaf dukiyar da aka kashe ma Ummulkhairi, aka kai gidansu aka shirya komai acan bamaso abarmusu, ni zan mata komai sabo, ayau akawota gidana bayan d’aurin aure tayi zamanta can, kafin Abdullahi ya dawo daga Singapore, an shirya mata komai na ‘yar gata.”

Ya k’arashe magnar ransa amugun b’ace tamkar Maryam ‘yarsa ce akayiwa cin mutuncin nan.

Ya d’agawa securitynsa hannu, cikin rawar jiki ya beqo masa wata zungureriyar waya mai kyau, ya latsa wata lamba bugu d’aya aka d’aga ya furta.

Kawu Bala yanzu akawomin huhun goro biyar da alewa da dabino central mosque kuzo kamar Ku goma azafafan motoci daman nida jama’ar tawa muna nan kawai inason aga wasu sun qaru ne, abun zaifi bada citta.”

Ya k’arashe maganar yana katse kiran, kawai sai ya zura wayarsa cikin aljihunsa.

 

Shattima ya zubawa alhaji Aminu idanunsa cike da mamakinsa, yana tunanin wata irin k’auna ce Aminu yake masa da zai fitar dasu kunya, yasan shi d’in mai k’aunarsa ne tin tashinsu,duk da Aminu ya basa wajan shekaru biyar ahaife,kawai amince ne suke wanda Allah ne ya had’a jininsu.

Hannayen Aminu ya riqe cikin dattaku yake magana.

“Haba commissioner! Ya zakama my takwara haka baya k’asar ka d’aura masa aure da k’anwarsa? Bayan kasan akwai wacce yake so shima kamar ransa?”

Fuska commissioner Aminu ya had’e ya ce“Dallah can ni fa kaga abinda yake had’ani da kai fulatancin ka, da kawaicin da bazai anfanemu ba, duk da kana ministan ilimi, har yanzu kana nan da fulatancinka, yanzu sbd Allah har na haifi d’an da zan bashi umarni yaqi binsa? Abdulahi ne zan tsaya sai naji ta bakinsa kafin na aura masa wacce nake so? Har yamutu zai samu mace ne kamar daughter Ummulkhairi? Ai kabar mgnar nan kawai Abokina.”

Shattima kasa mgna yayi sosai farin ciki ya gama lulub’e shi ya rungume Aminu yana godiya.

Dukan wasa ya masa abaya ya Ce.

“Kul na kuma ji tsakanin mu ba godiya komai nayi maka ko kamin _yiwa Kai ne.”_

 

Cikin masallacin suka koma, ba’a fi mintuna 15 jama’ar da Aminun yayi kira suka hallara cikin masallacin tare da dukkan abinda ya buqata.

Nan aka gabatar da dukkan abinda ya dace na neman aure, nan dubban jama’a suka sheda aure tsakanin Abdullahi Aminu kazaure, da Ummulkhairi Abdallah Umar shattimai,akan sadaki mai daraja naira dubu d’ari uku, lakadan ba ajalan ba.

 

Bayan d’aurin aure akayi tarin addu’o’i na neman Allah ya basu zaman lafiya,da yiwa k’asa addu’a da neman kwanciyar hankali da arziqi me anfani.

Aka raba goro da alewa da dabino, masha Allah abin sai wanda ya gani.

Haka taron ya watse cikin farin ciki da annushuwa, ba tare da jama’a sun ankare juyin mulkin da akayi ba wajan d’urin auren ba, sai malam Umar da wasu daga cikin ‘yan uwansu.

 

Unguwan (commissioners Quarters).

Wani qerarran gida ne mai kyawun gaske, wanda tin daga dogayen shifkokin da suka zagaye da dogayen katangun gidan, zuwa tamfatsetsan gate d’in gidan zaka san gidan na masu fad’a ajine.

Tin daga layin da zai sadaka da gidan kake jiyo kid’e-kid’e tare da busar sarewa na tashi, zaka rante gidan sarkin dutse ake aure,maroqa da mawaqa natayi, wasu manyan rumfunane da kujero a qofar gidan da cikin gidan ko Ina ‘yan sandane suke shawagi da bindigugi.

Jiniyar motocin su Shattima ne sun dawo daga d’aurin aure,jiniyar ta kard’e dukkan layin.

Shattima yana zaune a side d’in baya ya kame, idanunsa akan yawan taron da ya gani tin basu qaraso gate d’in gidan ba.

Hular kansa ya cire ya shafi lallausan sumar kansa mai taushi ya sauke ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa, ya bud’e ya zubawa wayoyinsa guda 4 wacce Kira ya kuma shigowa ya d’auka wadda bai san adadin yawan jama’ar da suka kira ba, ya dai ga miss calls 30.

Amsa kiran yay ‘yan tayasa murnane.

Wata number ya kira bugu d’aya aka d’aga cikin kamewarsa ya furta.

“Please kar a kori kowa ayi musu dukkan wani abu na karrama baqo k’unata ta sanya dukkan bayin Allah’n zuwa wajan auren ‘yata, so abarsu kowa ya nuna bajintarsa, sannan asaka idanu sosai akan dukkan masu shigi da fici duk da akwai wadatar CCTV cameras.”

Ya k’arashe maganar yana katse kiran bai jira yaji abinda za’a ce masa ba, tare da lalubo number da akayi saving da sunan.

_(Sweetheart)_ ya danna kira..

 

Wani hamshaqin falone da d’ud’uma-d’ud’uman kujeru har seats uku, baki d’aya adon maroon ne falon tin daga kan kujeru carpets labulaye komai maroon ne, sai wata tamfatsetsiyar Tv plasma wacceta ta kusa cin rabin bangon gusum, falon ya ji kayan alatu ainun.

Matane cike da falon wanda suka kai da Wanda basu kaiba.

Kowacce ajikinta wani dakeken lace mai shegen kyau Green colour mai tsada.

Wasu kuma suna sanye da abinda ya sawwaqane kasancewar akwai baqi daga gari-gari da danginta da dangin shi.

Hajiya Bilkisu kyakkyawar mace fara bafulatana, siririya ‘yar kimanin shekaru 41, amman jin dad’i ya b’oye shekarunta bazaka Ce ta haura shekaru 36 zuwa 37 ba, idan kaga Ummulkhairi bazaka ce ita ta haifeta ba, sabida qaramin jikinta.

Ansha gwala-gwalai wuya da hannu k’unshin nan d’as ya

na baqin lalle da ja.

Tsaye take suna falo na gefen babban falo, suna magana da hajiya Abida mahaifiyar Abdullahi ango😂, akan baqin k’awayensu na kano wanda suke akeb’antaccan waje a b’angaran gidan wajan saukar baqi, suna son suma suyi musu tarba wacce zata saka gobe idan suna safga aguje zasu dawo.

Fauziya k’anwarta ta iso da sassarfa tana fad’in.

“Auntie! Hamma Minister na kira fa!”

Hajiya Bilkisu ta amshi wayan tana sakin murmushi tana fad’in.

“Masha Allah aure ya d’auri Babyn dady hankli zai kwanta,bari na amsa waya Hajiyata nazo.”

Sunan da take fad’awa hajiya Abida kenan sbd amincin da yake tsakaninsu.

Hajiya Abida ta washe baki ta Ce.

“Lallai fa yau zan damqa amanar ‘yata hannun Salim Hashim Masha Allah, Allah yasa bad’i warhaka munci rangan d’in twins.”

Bilkisu wacce ta d’aga wayan tana amsa da.

 

“Ameen Ina kaga Dr Bilkisu Mrs Abdallah da jika d’an Baby khairinmu wow! Abun zai bada citta fa! Hajiyata.”

Ta qarashe mgnar tana kai wayan kunnenta tare sallama.

Hajiya Abida ta k’yalk’yale da dariya ta ce“Ai munyi wajan Azima ko jikana ba naki bane?”

Hannu ta d’aga mata alamar tana zuwa, ta nufi stairs.

Daga can wanda lokacin motarsu ta shige cikin tamfatsetsiyar rumfar Adana motocin gidan, ya amsa sallamar yana fad’in.

“Sweetheart! Ki sameni falon hutawa na, yi sauri zan koma wajan baqina.”

Cike da kulawa tare da tarin soyayyarsa ta amsa da.

“Ok Mi Amor yanzu kuwa.”

Murmushi ya saki yana katse kiran, lokacin da ake bud’e masa motar…

 

Stairs ta haye sai tabi ta can akwai hanyar da zata sauka zuwa falon hutawarsa, tana tafe tana sakin murmushi.

Matashiya ce ‘yar kimanin shekaru 21 baqa, irin baqin nan mai bala’in kyau, cikin wani tsararran falo, wanda ya gaji da had’uwa. Fuskarta na nuna alamun damuwa kad’an.

Tsaleliyar iPhone 13 pro max ahannunta tana famar latsawa,wata number wacce aka rubuta sunan.

_(Nisful Hayat)_

Tai dialing number akaro na biyar bata shiga.

Goshinta ta dafe cikin zazzaqar muryata ta furta.

“Ya Rabbi! Wai nisful Hayat na lfy kuwa ace anyi d’aurin aurenmu shiru bai kiraba ya mun barka kamar yadda muka tsara ni kuma na kirasa bana samunsa?”

Ta k’arashe mgnar cikin zallar shagwab’arta tana mele baki tare da kiran number Abdulrazaq babban abokin angon.

Bugu d’aya ya d’aga tare da sallama.

Ummulkhairi ta miqe cikin nutsuwarta ta fara takawa ta nufi bedroom d’in auntie Balaraba,tana masa sallama.

Amsawa yay tare da fad’in.

“Amarsu ykk?

Ummulkhairi ta Ce.

“Ba yadda nake ina nisful hayat? Inata kiransa bana samunsa fa! Fatan an d’auro?”

Abdulrazaq wanda zufa ta fara karyo masa ya b’oye tashin hankalinsa ya had’iye wani yawu me d’aci da baqin cikin halin da ake ciki ya Ce.

“Eh an d’aura congratulations Ummulkhairi, kiyi hkr jama’a ta ma Salim yawa anjima muna zuwa insha Allah OK?”

Wani fari tayi da matsagaitan lumsassun fararen idanunta, ta saki murmushi wanda wushiryarta ta sama da qasa ta bayyana, tsakankanin fararen jerarrun haqoranta ta ce.

“Alhamdulillahi ko yanzu na mutu burina ya cika na mallaki Salim d’ina, kace masa ina tayasa murnan samun abar son shi bye sai kun zo.”

Ta k’arashe maganar tana katse kiran tai tsalle tana juyi ta nufo qawayenta tana fad’in.

“Alqawalin Allah ya cika k’awayena aure ya d’auru tsakanin Ummulkhairi da Salim d’inta.”

K’awayenta suka zagayeta suna ihu babbar k’awarta Suhailat ta rungumeta tana fad’in.

“Congratulations my dear.”

Maryam ta sumbaci kumatunta ta ce.

“Auntie congratulations. ”

Sauran ma suka zagayeta suna tayata murnan mallakar abin sonta.

Cikin su kowace ka kalla farin ciki take, ‘yan matane ‘ya’yan masu akwai da akasin hakan, kasancewar Ummulkhairi batada raina mutum akwai son mutane ba ruwanta da abota da sai mai kud’i kowa natane,shiyasa yau gidan Auntie Balaraba k’anwar Shattima wacce ta d’auki wunin amarya anan za’a mata wanka ya cika Tabb da ‘yan mata, sunata shagalinsu sai kid’a ke tashi suna raye-rayensu, waqar Umar m Sharif ta amaryar share hawayenkin yau ake d’aura aurenki.

 

Sai ihu suke suna tsalle Kowace ta taci adonta da ankon lace, purple colour,amman kowace iya aljihunta ta d’inka sabida qarfin ba d’ayaba akwai ‘ya’yan talakawa acikinsu.

Wankan su ya zauna ajikinsu ba k’arya.

 

Ummulkhairi sanye take da wani hamshaqin lafiyayyan lace purple wanda qalla kud’unsa zai kai dubu d’ari da hamsin riga da skirt ne, qafafunta da hannunta sunsha k’unshi na jan lalle duk da tana baqa k’unshin ya fito ya mata kyau, haka kitsonta da k’ananu masu irin wata lank’wasa yayi bala’in kyau, jelar rabi ta sauka har gadon bayanta saura gefen fuskarta ya zubo harwucin k’irjinta, sai sheqi take tayi wani irin mashahurin kyau. tanada hanci me tsayi, da d’an qaramin bakinta wanda jin dad’i ya maidasa kalar pink, tanada idanu matsagaita basuda girma sosai haka basuda k’ananu can, fararene tass idan tana kallon ka zaka zaci kallon raini take maka ita kuma haka yanayin halittar kallonta take sai kun saba zaka fahimceta.

Allah ya mata kyawun diri da sura mai d’aukar hankali, akwai hips uwa uba bom-bom matasa masu cikar lafiya, tanada matsagaicin tsayi da jiki bata sahun ramammu,haka bata sahun masu k’iba wato (tsaka tsakiya).

Cikin zallar farin ciki ta ce.

“Bari na kira Sweet Dady.”

Tai dialing number minister Shattima wanda akayi saving da sunan.

_(Sweet Dady)_

 

Acan kuwa gidan minister Shattima Bilkisu tana isowa qofar falon hutawar nashi, wani d’an madanni ne manne jikin glass d’in qofar ta latsa wasu lambobin, atake qofar glass d’in ta bud’e ta shige had’add’an falon mai bala’in kyau da tsari, ga wani irin fitinannan k’amshi tare da sanyin A.c ya gauraye falon mai tsarin na turawa.

 

Tana shiga atake k’ofar ta rufe kanta.

Bakinda d’auke da sallama ta tinkare shi ya lume cikin sofa idanunsa a lumshe amman waya yake amsawa.

Kallonsa take kamar zata cinye shi cike da k’aunarsa.

Dab da shi ta zauna tana sakin murmushi, ta sanya dukkan hannayenta ajikinsa ta fara qoqarin cire mishi babbar rigarsa.

Ba musu ya bata damar yin hakan, lokacin da yake ajiye wayan akan wani had’add’an glass table.

Linke rigan tai ta ajiye gefe ta miqe ta nufi fridge ta d’auko jug wanda yake cike da lemun masoyinsa wato inibi.

A cup ta tsiyaya masa ta zauna kamar zata koma cikinsa, ta tallafo kansa ta manna masa cup d’in abakinsa, tana fad’in.

Barkanmu yau mun sauke haqqin da Allah ya d’ora mana aurar da ‘yarmu ga miji nagartacce.”

Kaifafan idanunsa masu lumshewa ya kafa mata, yana had’iyar lemon cike da nutsuwa.

Sai da ya shanye tass ya janye bakinsa tare da rungumeta tsam k’irjinsa, yana shafa kumatunta, bakinsa dab da kunnenta cikin nutsuwar shi da soyayyar shi da hikimarsa ya zayyanewa hajiya Bilkisu kakaf abinda ya faru ayau d’in game da d’aurin auren yadda abin ya juye aka d’aura auren da Abdullahi Aminu.

 

Bilkisu ta rangad’a gud’a ta Ce.

“Allah na gode maka da hakan ta faru, wlh najima inason had’a zuria da babban amininka, kawai ba yadda na iyane sbd son da Baby take ma Salim ba na wasa bane, wlh tin lokacin da tace min ta kamashi yana shan sigari ya fita araina to kasan baby da kafiya tinda tace shi take so idan bamu bata ba zata kwance mana ciwo, amman alhaji Hashim sunban mamaki shi da zuri’arsa, kuma wani halin ga Allah baiwane, kansu sukayiwa bamu ba, ga shi Allah ya sauya mana da mafi alkhairi.”

 

Minister ya murmusa yana sakinta yaja hancinta ya ce.

“Kul ki sanar da kowa har sweet daughter ki barni da abata zuwa dare zanji da ita.”

Bilkisu ta murmusa tana sanya yatsarta ramin dimples d’insa ta ce.

“An gama yallab’ai mi Amor, Amman hajiya Abida bata san komai ba ita koh?”

Zaiyi magana

Daidai lokacin ne kiran Ummulkhairi ya shigo wayansa.

Ganin me kiran ya d’auki wayan yana picking call d’in.

Kafin yakai ga magana ya ji tana kyalkyala dariya da tsallen da take daga can yana shigowa cikin dodon kunnensa.

Kallon Bilkisu yay yana girgiza kansa ya saka wayan a speaker, yana jiran ta gama haukan murnan.

Shattima ahankali ya furta.

“ALLAH na gode maka da ka bani wannan d’iya tawa marar kunya.”

Bilkisu tai dariya zatayi magana taji muryan Ummulkhairi tana fad’in.

“Hello sweet Dady! Ngd Allah ya barku da sweet mamytah, ngd da aura min wanda nakeso muahhhhh i love you sweet Dady.”

Shattima dariyar da yake dannewa ta kub’uce masa, yay kad’an ya tsagaita jin ta biye masa daga can.

“Sweet daughter na dakatar da dinner d’inku da duk wani shagali walima kawai na yarda ta zallar mata kuyi shima dan a wa’azintar dakune, na Kira Balaraba nace maza ta koma wajanku, kashe wayarki yanzu bana son ki kunnata sai bayan an kawoki gida OK?”

Kai ta langwab’e tana mele d’an qaramin pink d’in bakinta,asakalce ta ce.

“Kai! Sweet Dady! Anata fa kirana kuma anjima su nisful Hayat zasu shigo.”

Cike da umarni ya ce“Na ce ki kashe wayanki karki kunna sai an kawoki daga gidan Balaraba, karki kuma ari wayan kowa ki kira kowa Ku dakatar da dinner, kinaji KO bakya jina?”

Tsaf ta nutsu ta nemi waje ta zauna ta fara rarraba idanu jin Dadyn ya dawo asalin halinsa, cike da tsoron shi ta amsa.“Ok toh Dady kayi hkr zanyi dukkan abinda ka ce yanzu, Ina sweet Mamy?”

Ba wasa ya ce“Tana jinki oya kashe wayan yanzu.”

Da

“Toh”

ta amsa ta kashe wayan baki d’aya tana tutturo baki gaba tana diddira k’afafunta.

Banda dariya babu abinda k’awayenta suke mata, nan ta Samar dasu walima kawai za’ayi bayan la’asar.

Haka kuwa akayi wajansu Ummulkhairi walima kawai akayi, haka wajansu hajiya Bilkisu ma ita akayi ta manyan mata, ayau almajiran da suke jigawa sun san anyima d’iyar gata aure sunci sun Sha.

 

Quarter

*ASOKORO*

Matashine d’an kimanin shekaru 27 wankan tarwad’a ne, ba laifi yanada kyau da dirin maza mai kyau daidai shi, dogone kana kallonsa kasan d’an hutune.

Kwance yake saman lafiyayyan bed d’insa, yana d’aure da drip ajikinsa.

Cike da wata irin muguwar kasala ya fara bud’e k’ananun idanunsa masu kyau, wanda,sukayi masa nauyi bai sauke kallonsa a ko ina ba sai akan drip d’in jikinsa.

“Subanallahi me kuma ya sameni?”

Yay mgnar yana waigowa ya kalli Abdulrazaq babban amininsa yana riqe hannunsa ya ce.

Abdulrazaq ya ce.

“Wlh idan nace ga abinda ya sameka nayi qarya, na gama shiri zan taho lokacin da ka gama kirani nayi sauri nida Najib mu kaima su Ummulkhairi saqonsu, na shiga mota kenan naga kiran Father yace nazo gida sun ganka ka zube ba rai amman an kira Dr families naku yana dubaka agida…”

Daga nan ya basa labarin dukkan abinda ya faru kakaf da fasa aurensa da akayi da Ummulkhairi wanda umarnin Father ne, amman bai fad’a masa labarin d’aya ba.

 

Ahaukace Salim ya fasa ihu ya fizge drip d’in jikinsa, atake jini ya fara fita daga hannunsa,wani irin ashar ya lailaya, yana fad’in.

“Wallahi ko uban waye ya auri Jewel sai ya saketa ko na kashesa na rantse da Allah ba wanda ya isa ya zauna min da matata afad’in duniyar nan.”

Ya k’arashe mgnar ya dirowa daga saman bed d’in.

 

Abdulrazaq ya riqeshi da niyar kwantar masa da hankali, ya fizge da k’arfi yana hankad’e shi ya nufi qofar fita.

 

A haukace ya shigo babban falon nasu ko ganin baqin da suke cika falon ‘yan zauwa biki baiyi ba.

Cike da masifa da bala’i Salim yake kiran mahaifiyarsa.

“Umma! Umma!! Umma!!! Kina ina..? Wallahi yau akwai masifa da bala’i agarin dutse…..”

 

Toh my guys ya kukaji salon?😄😉

 

 

_RAHMA Mrs Jaana♥️_

[12/10, 5:29 pm] +234 814 210 5218: _YIWA KAI…!_

 

 

 

RAHMA L Oum Farisah

 

 

 

 

_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_

 

 

 

 

 

*P 3&4*

 

 

“Akan me kika shirya dukkan tuggun nan Ko ince kuka shirya keda Father, dan ku rabani da muradin raina? Me namuku, anya kune iyayena…”

Fauuu kakeji hajiya Sa’idah ta d’auke shi da gigitattun maruka har guda 3.

Kumatunsa ya dafew yana kallonta ya ce.

“Umma! Ni kika mara sabida gaskiyata, ina tambayar meyasa kuka tauyemin haqqina,na hanani abar sona?”

Ya k’arashe mgnar hawaye na zarya akan fuskarshi.

Cikin b’acin rai take magana.

“Toh maras kunya, nace maras kunya nunawa duniya kai bakada kunya bare tarbiya dan babanka, naji na qara tsanar Ummulkhairin, ka tab’a ganin iyaye sun cutar da d’nsu? Kasan irin gatan da muka maka kasan taimakon da muka maka, kasan yadda muka kauda Sani da nunawa namu namune dan mu tsiratar da kai daga wannan k’addararan auren? Kasan yadda akayi aka tsiratar da kai da mukayi, akan k’in amincewa ka auri Ummulkhairi? Yarinyar masifa ce annoba ce, da acan baya kafin ta shigo rayuwarka haka kake? Nace haka kake? Jibeka ka zama wani sakarai mahaukaci zautacce.”

 

Ta k’arashe maganar cikin zafi tana fizgar hannunsa suna tafiya.

Baki d’ayan falon kallonsu akeyi cike da mamakin kalaman umma Sa’idah.

Salim kasa magana yayi zuciyarsa na tafarfasa, binta kawai yake har suka shiga b’angaren alhaji Hashim, wanda shigowarsa kenan yana amsa waya.

Kusansa ta saki hannun Salim wanda yake d’igar da jini.

alhaji Hashim ya katse wayan yana miqewa tare da fad’in.

“Subanallahi my son hannunka na fitar da jini, sannu ka farka?”

Salim ya matsa gefe yaqi yarda Hashim ya tab’asa.

Cikin tashin hankali yake fad’in.

“Karku tab’ani sai kun fad’amin akan me zaku rabani da farin cikina? Me na muku kuka rabani da abinda nafi so?”

Alhaji Hashim yay murmushi yana fad’in.

“Yaro man kaza.”

Ya kamosa ya nad’e hannun da yake fitar da jini, da handkerchief, ya zaunar da shi saman 3 seater, ya zauna kusan shi, ya ce.

“Sa’idah! Zauna mu masa bayani ko zai dawo hayyacinsa.”

Ba musu ta zauna suka sanyasa tsakiyarsu.

Idanu ya zuba musu yana jiran abinda zasu fad’a.

Alhaji Hashim yay gyaran murya ya ce.

“Inaso kaje kayi nazari da kanka tin lokacin kuka k’ula alqa ta soyayya da ‘yar gidan minister Shattima, asara nawa kayi, accident nawa kayi rashin lafiya nawa kayi, na rantse ma da Allah ayau babu abinda muka baka sbd ka fita daga hayyacinka dan kar ka auri Ummulkhairi.

Ranar da kayi gobara motarka ana sauran sati d’aurin aurenku motar ta k’one qurmus, bazan manta ba ranan ai naje k’auyen zakirai wajan Malam ILU mai taimakamin, nake masa bayanin irin yawan tsautsayin da yake samunka.

Ya cemin zai min istiharah ta kwana washegari zai min bayani, washegari da safe ya kirani awaya yake fad’in wacece Ummulkhairi da so samu ne ka yanke aqa da ita.

Ranan hankalina ya tashi nayi juyin duniya ya fad’amin meke faruwa ya dai ce nayi qoqari na rabaku idan zaka hanu, shi bazai zayyano min komai ba, nan gaba akwai gagarumar matala, zamanku ba alkhairi.

Wlh tin ranan har zuwa yau ban kuma barcin kirki ba, na rasa ta inda zan b’illowa al’amarin, inajin matuqar nauyin minister Shattima, amman yau lokacin da naganka akwance babu rai na cire kunya da jin nauyi na aika musu saqon suyi haquri aure ya fasu duk da nasan zan sha zagi tinda bazan fito na fad’i gsky ba, taron da mukayi dan zuwa d’aurin aurenka da Ummulkhairi sai ya juye muka d’aura maka aure da Aliyah d’iyar yayana Basiru wacce take karatu a A.B.U Zaria sabida kar mutane su ankare, ita kuma acan an d’aurawa mai tsautsayi, Abdullahi Aminu kazaure.”

Salim da idanu kawai yake binsu da kallo ba ko k’iftawa,mamaki fal zuciyarsa, kawai dan k’addara ta haushi sai ad’aurawa Ummulkhairi? Jin da wanda aka d’aura mata auren hanklinsa ba qaramin tashi yay ba.

 

Miqewa ya yi bai ce uffan ba ya fice daga falon yana tangad’i hawaye tab sun cika masa idanu, shi kad’ai yasan me yake ji me kuma zaiyi.

Hajiya Sadi’ah ta ce.

“Ya Allah ka kawo mana k’arshen musibar nan.”

Alhaji Hashim ya ce.

“Amin kuma dan ubansa sai ya zauna da Aliyah ya gama jimamin rashin annobar ta sa…”

 

Misalin qarfe shidda na yamma commissioner Aminu ya bar gidan minister shattima, ya nufi gidansa da yake cikin nan unguwar commissioners Quarters, titi biyune ya shiga tsakanin su da Shattima.

Yana isa gida wanka yayi ya d’auro alwalan Maghreb sbd ta kusa, ya nufi cikin lambu ya zauna, ya lalubi number d’ansa Abdullahi ya danna masa kira, yana so sai ya gama magana da shi kafin ya tara iyalinsa ya musu bayani.

 

_*’Kasar*_

(Singapore)

 

Matashine d’an kimanin shekaru 28 sanye da kayan motsa jiki, yana tsaye ad’akin motsa jiki, ya had’a uban gumi daga ganinsa yanzu ya gama motsa jikinsa, sbd uban gumin da yake yana famar goge zufar.

Farine dogo ingarman namiji tsayayye mai murd’add’an jiki, kyakkyawa ma’abucin fara’a, yanada manyan idanu farare da dogon hanci bakinsa mai fad’ine jajir da shi, yanada gashin gira da na idanu akwai yawan sumar kai bai fiye askewaba sosai, kallo d’aya zaka masa kasan shi d’in bafulatanin asaline fararen fulani.

K’aramin towel d’in hannunsa wanda ya gama goge zufa ya rayata saman dogon wuyansa, ya fara takunsa mai burgewa ya bud’e qofar ya fito ya nufi tsararran d’ank’aramin falonsa.

Fridge’n ya bud’e ya d’auko gorar ruwa mai sanyi ya bud’e tare da bismillah ya kafa bakinsa.

Sai da yasha sama da rabi ya rufe ya maida fridge’n ya qaraso ya zauna saman sofa ya zuba dogayen k’afafunsa saman center table, ya lumshe idanunsa cikin daddad’ar muryashi yake fad’i.

“Ya Allah! Ni kam yau fad’uwar gaban me nakeyi ne?”

Ya k’arashe maganar yana bud’e idanunsa, wanda bai sauke su ako Ina ba sai kan wayasa da take ajiye saman table d’in tin kafin ya shiga motsa jikinsa ya barta anan kuma a silent take.

Hannunsa ya beqa yana fad’in.

Abby! ”

Yay picking call d’in ya nufi kunnensa da wayan, yana miqewa tsaye ya fara takawa zuwa bedroom da nufin idan sun gama magana yayi wanka.

Kamar an kwab’e wayan ta sulale tafad’i k’asa saman tayis tayi wani irin fashewa glass d’inta yay raga-raga.

Abdoul ya dafe kansa yana fad’in.

“Hasbunallahu wa ni’imal wakil.”

Ya duk’a ya d’auki tsadaddiyar wayan ta shi da ta canza kamanni, ya danna ba’a ganin komai ta tashi a aiki, yakai wayan kunnensa ya ji ko zaiji magana mahaifin nasa.

Cikin sa’a kuwa ya ji muryasa yana fad’in.

“Abdoul! Lfy kuwa? Me ya farune?”

Falon ya dawo ya zauna yana murmushi ya gaishe da mahaifin nasa, yana fad’in.

“Wlh Abby wayana ne ta fad’i kaga fashewan da tayi komai bana gani taci screen, glass d’in ya farfashe sai wata.”

Daga can commissioner Aminu ya ce.

“Subahanallahi sannu Abdoul, yauwa nace kuwa ka Kira k’anwar taka Ummulkhairi ka mata barka yaune aurenta fa!”

Kansa ya shafa yana murmushi ya ce.

“Wlh na manta Abby amman zuwa gobe insha Allahu zan kirata.”

Daga can Aminu yay gyaran murya ya Kira sunansa.

“Abdullahi! Kasan dai Ina sonka bazan tab’a abinda zai cutar da Kai ba koh?”

Abdoul ya amsa da.

“K’warai kuwa Abby ni shaidane me ya faru?”

Abby ya ce.

“Allah ya maka albarka yasa ka gama da duniya lfy.”

Ya amsa da.

“Amin Abby fad’amin me ya farune?”

Gyaran murya yay ya ce.

“Alhaji Hashim da d’ansa suke son raina mana hankali cikin taron baina nasi, mu kunyata ni kuma sai nayi abinda da nasan insha Allah alkhairine…”

Tass ya labarta masa komai akan aurensa da Ummulkhairi..

Abdoul ya miqe tsaye yana firfito da manyan idanunsa waje, jikinsa har tsuma yake bakinsa na rawa dak’yar ya iya furta.

“Abby! Aure kuma nida Ummulkhairi? Ya zanyi da Azizah?”

“Ok saki Ummulkhairi da na aura maka tinda ban isa da Kai ba Abdoul. ”

Hankalinsa atashe ya ce.

“Duk ba haka bane kayi hkr Allah ya sanya alkhairi.”

Aminu ya amsa da.

“Amin Allah ya maka albarka daman nasan bazaka kunyatani ba.”

Abdoul hannunsa dafe da kansa ya amsa da.

“Amin Ngd Abby Allah ya k’ara girma…”

Suna sallama ya buga wayar da bango ya fara Kai komo daga tsakanin bedroom zuwa falo, yana dunk’ule hannayensa, shi kad’ai yasan azabar da yake ji azuciyarsa, akan me za’a aura masa wata Ummulkhairi?

“Shin wai su ansan dalilin da yasa suka fasa aurenta ni Abby ya liqamin? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”

Abinda yake fad’a kenan ya nufi bedroom.

Acan kuwa Nigeria.

Bayan sallar isha’i commissioner Aminu ya Kira hajiya Abida ta dawo gida, dan har lokacin tana can gidan minister Shattima sai ta kai amarya d’akinta daga can zata wuce gida.

Zazzaune suke a falon hajiya Abida na gefensa sai yaransu guda uku sun zagayesu Habib Nafisa Auta Sabir, Maryam na can wajan amarya.

Gyaran murya yay ya kirata.

“Abida! Akwai al’amarin da ya faru yau wanda daman can ubangiji ya k’addara zai farun, ni nawa cikawane akan umarnin da ubangiji ya bani, dan nasan komai da umarninsa muke aiwatarwa…”

Kakaf ya zayyane mata abinda ya faru ayau d’in ya d’ora da cewa.

“Bana son kice komai ki sanya musu albarka kawai da fatan alkahiri, sai ki tura masu aiki da Nafisa su gyara b’angaran Abdoul na nan, anjima nida ke zamuje mu d’aukota ta zauna wajanmu kafin yazo dan gagarumin biki za’ayi insha Allahu idan ya dawo.”

Hajiya Abida ta rangad’a gud’a ta ce.

“Alhamdulillahi wlh naji dad’i sosai da wannan abun, najima inama Abdoul kwad’ayin samun Ummulkhairi Amman ganin ga inda hankalinta ya karkata shima hankalinsa wajan Azizah take ko wa? Wlh shiyasa naja bakina nayi shiru, ashe duk wannan hidimar da nayi yau d’ana nayiwa, Kai Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi.”

Commissioner Aminu ba qaramin dad’i ya ji ba ganin matarsa tayi na’am da auren.

Habib ya ce“Gsky naji dad’i bro Abdoul yayi sa’ar mata, dan wlh Ummulkhairi tafi Aziza komai har tarbiya farar fata kawai Aziza ta fita.”

Nafisa mai bin Maryam ta ce“Kwarai Yaya Habib, ai kuwa ranan tarewarsu akwai shagali, sai mun sake anko.”

Auta Sabir ya ce.

“Ni kuma zan koma gidan auntie Ummulkhairi.”

Dariya dukaninsu suka sanya zuciyoyinsu fari k’al.

Abidah ta kira Lantana da Kulu masu aiki ta ba Nafisa key tace suje su gyara part d’in Abdoul a saka turarukan d’aki na wuta da ruwa.

Ai kuwa kafin 40 minutes sun gyara tsararren falonsa da bedroom d’insa da toilet, wanda ka rantse d’akin amaryane, amaryama ‘yar gata babu abunda babu aciki ko ina sai k’alli yake.

Misalin 8 pm Auntie Balaraba da auntie Madina yayar Bilikisu suka shigar da Ummulkhairi toilet suka Fara gurjeta, da ruwan lalle wanda yasha maguguna da turaruka,sai mita take.

Auntie Balaraba tana mata dariya.

Tsaf aka shiryata cikin wani had’add’an material pink, wanda tsaya fad’in tsadarsa bata lokaci, anyi mata makeup na kece raini turaren wuta na jiki ya kamata, da na ruwa dole idan ka kalli baqar yarinyar nan ka kuma kallonta sabida bala’in kyau d’in da tayi.

 

K’arfe 8:40 pm cif motocin su auntie Balaraba suka iso qofar gidan minister, tamfatsetsan gate d’in aka bud’e musu suka shige motar amarya bata tsaya ko ina ba sai dab da qofar sashen minister falonsa na hutawa dan nan yace ma Balaraba su kawota.

 

Falon shiru kakeji sai qaran A.c da TV wanda qaran sautin TV ahankali yake fitowa, tashar CNN ana gabatar da labarun harshen turanci.

Dogayen baqaqen k’afafunsa meqe suke saman sofa, ya jingina bayansa da pillow, hannunsa d’auke da wani farin cup glass fura ce yake k’urba taji nonon shanu mai lunk’um asaman cup d’in.

Sanye yake da wani yadi fari k’al mai taushin gaske, d’inkin shan iskane na hutawa agida, fararen manyan idanusa kafe akan TV, yana girgiza k’afafunsa.

 

Suna isowa Balarba password d’in da minister ya fad’a mata ta saka, qofar glass d’in ta bud’e suka shige bakinsu d’auke da sallama.

Kansa ya juyo ya zuba musu idanu bakinsa na motsawa alamar sallama yake amsawa.

Kusan shi Balaraba ta zaunar da Ummulkhairi tana fad’in.

“My brother ga Baby Ku gama bari muje falon auntie Billy mujiraku kafin ‘yan d’aukan amarya su zo.”

Minister ya saki sansanyar murmushi ya ce“Ok ba damuwa ki turomin Bilkisu, ah Maryam! Kina nan baki koma gidaba? Sannunku da qoqari, Suhailat Allah ya muku albarka.”

Ya k’arashe mgnar yan kauda kansa sbd kallon da Maryam take yi masa kamar zata cinyeshi, idan da sabo ya saba da kallon yarinyar abun na bashi tsoro wani lokacin.

Su Sulahilat suka amsa da “Amin.”

Suna ficewa.

Maryam kuwa bata tafi ba, aladabce tai k’asa da kanta ta ce.

“Eh Dady sai munkai auntie khairy daga can sai na wuce gida ai Ammi tana nan, tare zamu tafi.”

Ta k’arashe mgnar tana juya anutse tana tafiya cikin nutsuwarta.

“Ok.”

Shattima ya amsa yana kamo hannayen Ummulkhairi yana murmushi ya ce.

“Masha Allah,sweet daughter yau za’a bar Dady koh?”

Ya k’arashe mgnar yana leqa fuskarta ta cikin mayafin.

Kuka Khairy ta fashe da shi ta fad’a jikin Shattima tana shasheqa.

D’agota yay cikin nutsuwarshi yana fad’in.

“Lah! Haba My sweet kar muyi haka mana, kuka kuma sabida Allah? Toh bari nima nayi kukan sai arasa mai rarrashi wani tsakanin uba da ‘yarsa koh?”

Ya k’arashe mgnar ya d’ago fuskarta da tafukan hannunsa ya mele baki irin zaiyi kukan nan yayi narai-narai da idanu, yana kallonta, ya fara kukan gangan harda shan majina.

K’urr ta masa da idanu tana shasheqar kuka, amman ganin abinda yake ya saka ta had’iye nata kukan sai kawai ta k’yalk’yale da dariya tana maqalqaleshi ta sak’ala hannayenta wuyansa tana tab’a dimples d’insa da yake lob’awa.

Cikin dariya hawaye na zarya akan kuncinta, da zazzaqar muryata ta ce.

“Wallahi sweet Dady! Kukan ya maka kyau daman kayi na gaske na tab’a ganin hawayen sweet Dady na farin ciki ya aurar da babynsa.”

Ta k’arashe maganar a shagwab’e tana Jan gemusa da gashin sajansa.

Baki da hanci ya Saki yana kallon ikon Allah.

Bilkisu ce ta shigo falon tana kallonsu ta ce.

“Ya dai? Duk kallon k’arshen ne akeyewa baby haka ba k’iftawa?”

Murmushi yay ya ce.

“Sweetheart! Baby ta ce kukana take son gani yau, zo ki zama sheda.”

Ya fad’a yana Jan dogon hancin Ummulkhairi,tare da zungurinta akai cikin sigar wasa.

Zama tayi kusan Shattima tana dafa cinyarsa tayi dariya ta ce.

“A’a ni wannan mgna bana shiga tsakanin uba da ‘yarsa ba ruwana, ai sai ka mata kukan mugani musha dariya.”

Ta fad’a tana Jan dogon karan hancinsa.

Shattima ya murmusa ya janye Ummulkhairi daga jikinsa ya zaunar da ita akan cinyar Bilkisu.

“Aushhhh! Mi Amor kafa San baby da nauyi ai sai ta karya maka ni sauke min ita gaskiya, yadinya taykusa biyuna.”

Shattima ya zaro mata idanu tare da murd’e mata baki ya sumbaci bakin ya ce“Tubarkallah bazaki cinyemin ‘yata ba, idan ta karyaki ba sai ta zabomin k’aramar yarinya sabon jini cikin k’awayenta ba na aure mubarki da jinya can da tsaminki.”

Ya k’arashe maganar cikin kamewarsa kamar gaske yana mata gwalo.

Dariya Ummulkhairi tayi ta sake shigewa jikin Bilkisu tana fad’in.

“Wlh wannan salon love d’in naku yake burgeni tin ina k’arama shiyasa nakeda burin nunawa nisful Hayat ba wani sai shi, kamar yadda nake kyautata zaton nima ba kishiya irin na sweet Mamy ko sweet Dady?”

“Yeah Baby, yanzu dai sweet daughter ban hankalinki nan.”

Ya k’arashe maganar ba wasa yana kamo hannunta, ya ce.

“Sweet daughter! Kinsan dai bazan tab’a cutar dake ba koh?”

Kai ta jinjina ta ce.

“Eh Dady nasani.”

“Good Baby abinda nakeso dake akoda yaushe ki amshi k’addaraki mai kyau da akasin hakan, kisani ni bazan tab’a cutar dakeba…”

Nasiha yay mata mai kashe jiki akan tama mijinta biyayya da iyayansa taso ‘yan uwansa da duk wanda ta gani tare dasu,sannan ta kasance mace me sakin hannu kar abun hannunta ya gamata da kowa, ta kyautatawa makotanta koda ba musulmai bane,ta zauna da kowa lafiya, ta tsayar da sallah, ta kasance kamar baya kullun cikin karatun Qur’ani, ta kasance kamar baya azikhar na safe da yamma.

Bayan ya gamata nasiha mai ratsa jiki, ya umarci Bilkisu ma ta mata nasiha sosai amatsayinta na mahaifiyarta sosai suka kashe mata jiki da nasihar su, ta fara kuka ta rungumesu jikinta yayi sanyi wata irin kewarsu take ratsa dukkan sanssan jikinta.

Shattima ya shiga buga bayanta ya ce.

“Daughter! Bar kukan haka kar kanki yayi ciwo, kuma kinga kwaliyarki zata b’aci fa! ina mai baki haquri sweet daughter ki amshi k’addaraki ki mana biyayya zakiga sakammako mai kyau…”

 

Tsaf ya zayyane mata dukkan abunda ya faru wajan d’aurin aurenta da Salim Allah yayi ikonsa aka d’aura mata aure da Abdulllahi d’an aminsa commissioner Aminu.

Ummulkhairi tayi wata irin zabura jikinta ya fara rawa gab-gab, dak’yar cikin wani irin matsanaicin kuka mai tsuma zuciya take fad’in.

“Dady! Salim bai aureni ba? Me na masa? Yanzu na rasa muradin raina? Meye aibuna da ya gujeni? Dady! Meyasa Salim zaimin haka? Ya zanyi da tarin k’aunarsa da nakeyi? Yanzu ban samu Salim ba amtsayin abokin rayuwata? Dad Abdoul na aura..?”

Ta k’arashe maganar cikin fitar hayyaci idanunta na lumshewa kawai sai gani sukayi ta zube jikin Shattima babu alamar rai atare da ita…

Bilkisu ta kamata tana fashewa da kuka tana fad’in.

“Na shiga uku! Dadyn Khairy kaga abinda nake gudu koh? Yanzu Allah kad’ai yasan ranan tashinta….”

Shattima ya rufe mata baki yana fad’in.

“Please kayi hkr karki saka damuwa tamin yawa, insha Allahu zata farka ayau d’in nan, d’auki wayana kira Dr yazo yanzu please kafin Aminu su iso d’aukarta.”

Ya k’arashe maganar yana kwantar da Ummulkhairi, ya shiga muraza tafin hannunta da sauri-sauri yana kiran sunanta.

Bilkisu cikin rawar jiki cikin wayoyinsa ta d’auki gudu ta kunna sabida ya kashesu.

Tana kunuwa ta cire password d’in ta lalubo number Dr Safwan ta kirasa.

Cikin sa’a bugu d’aya d’aga.

Beqawa Shattima wayan tayi, ya amsa bayan sun gaisa ya ce.

“Dr Baby ba lfy tayi suman nata please kayi sauri kazo ajaraba agida muga ko za’ayi sa’a ta farfad’o yanzu.”

Dr Safwan ya amsa cikin mutuntaka sukayi sallama ya katse kiran, ko ajiye wayan baiyi ba kiran commissioner Aminu ya shigo.

Idanunsa ya k’urama wayan ya kasa d’aga kiran…

 

Mrs Jaana♥️🥰

[12/10, 5:29 pm] +234 814 210 5218: _YI WA KAI…!_

 

 

RAHMA Oum Farisah

 

 

 

 

 

_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_

 

 

 

 

 

 

 

*P 5&6*

 

 

Hannunsa mai riqe da wayan, Bilkisu ta riqe tana d’ora yatsarta akan setin inda za’ayi piking call d’in.

Cikin kwantar da murya ta ce.

“Mi amor don Allah ka amsa su da kansu sun san dole idan taji labarin abinda ya faru, sai ta shiga wannan halin.”

Ta k’arashe maganar tana picking call d’in, tare da kai masa wayan kunnen shi.

Anutse yama Aminu sallama.

Daga can commissioner Aminu ya amsa tare da fad’in.

Gamu nan ahanya ashirya mana ‘yar mu.”

Murmushi Shattima ya yi ya ce.

“Please nima tinda d’ana ne za’a Kai wa ita, toh abarni na kawota, gata kwance ba rai tinda taji abinda yake faruwa, Dr muke jira ya dubata.”

Aminu ya ce.

“Subahanalahi wlh daman nasan hakan sai ta faru, tayi haquri haka Allah ya k’addara, OK toh bari mukoma sai kunzo, Allah ya bata lfy dan Allah idan yau d’in tace bazata zoba, karku takura ta, abarta zuwa goben ta huta ko zuwa dare ne please.”

Sosai minister Shattima ya ji dad’in maganar aminin nasa ya amsa da.

“Ok insha Allah.”

Sallama sukayi ya kalli Bilkisu wacce take famar zubar da hawaye, ya girgiza mata kai, yana cigaba da murza hannun Khairy, tare da kiran sunanta.

15 minutes Dr Safwan ya iso Shattima ya masa iso har falon.

Cikin gaggawa ya fito da kayan da zai bata taimakon gaggawa.

Cikin ikon Allah kuwa, ba jimawa ta farfad’o tare fashewa da kuka tana kiran Salim.

Shattima ya ce.

“Dr! Abu mafi sauqi had’a alluran bacci banka mata, bazan jure wannan tashin hankalin ba…”

Qafafun Shattima ta riqe tana wani irin kuka tare da roqon shi.

“Dady! Don Sonka da ma’aikin Allah ka raba auren nan na auri Salim, wlh yana sona shima…”

Bakinta ya rufe mata yana rungumeta yama Dr nuni ya mata alluran.

Ai kuwa take cikin dubara ya tsira mata allurar.

Tana ji amman yanayin tashin hankalin da take ciki, ya hanata nuna taji zafin allura, kanta kawai take bugawa a k’irjin Shattima tana kiran Salim.

Bata rufe minti biyar ba sai bacci.

Bayan Dr ya tafi ya gyara mata kwanciya saman sofa, yana kallon Bilkisu ya ce.

“Kije ki sallami ‘yan rakiyar amarya kice na kaita da kaina suyi haquri, zan kai miki ita yanzu b’angaranki.”

Bilkisu ta amsa da.

“Toh.”

Tana share hawayen tausayin tilon ‘yarta.

Can a falon kuwa cike da jama’a anata hira su auntie Balaraba, Maryam Suhailat babbar k’awa.

Bilkisu na shigowa auntie Balaraba ta miqe ta ce.

“Toh ku tashi muje Dady amarya ya gama da ita, ko auntie Billy? ”

Murmushi Bilkisu tayi ta ce

“Ai kuwa dai ‘yan rakiyar amarya Dadynta dai ya tafi da ita, ya barku da jira, sai kuyi haquri Suhailat! Maryam! Bari na saka amaryar daku gida da sauran k’awayenku.”

Ta k’arashe maganar tana latsa wayanta, bugu biyu aka d’aga, ta ce.

“Yawwa dan Allah amayar da k’awayen amarya, kowace akaita har gate d’in gidansu.”

Balaraba ta ce.

“Kai amman brother ya gama damu kawai ya tafi yakai ‘yarsa muna nan zaune, ai kam sai ku tashi mu fece.”

Ta fad’a tana yafa mayafinta.

Maryam ta maqale kafad’a ta ce.

“Mamy ni dai ki kira Ammi kice mata nan zan kwana please. ”

Bilkisu ta ce.

“Ok daughter shi kenan kuwa na riqe ki sai kinmin kwana biyu.”

Dariya ‘yan falon sukayi, nan masu tafiya sukayi haramar tafiya baqi na ‘yan zuwa wajan biki kuma kowa ya nufi makwancin sa, Bilkisu taja Maryam suka haye stairs, ta kaita d’akin Ummulkhairi.

Sai da minster Shattima ya ji gidan tsit kowa ya Kama makwancin sa, ya ciccib’i Ummulkhairi ya nufi b’angaran Bilkisu da ita.

Bilkisu na kwance cikin shirin bacci taji sallamarsa, daman k’ofar karota ne tayi sbd zuwansa.

Sallamar ta amsa tana miqewa zaune tana kallonsa tana gyara hular kanta.

Dab da ita ya kwantar da Khairy, yana fad’in.

“Sweetheart kiyi dubara ki cire mata kanyan jikinta, sai ki saka mata na barci marasa nauyi, dan wannan ko ta farka sai zuwa safe, good night Allah bamu alkhiari sweetheart. ”

Ya k’arashe maganar yana kamo fuskarta ya sumbaci labb’anta ya shafi gefen fuskarta ya juya ya nufi k’ofa yana zura hannayensa cikin aljihun wandonsa.

“Ok night mi amor ka kularmin da kanka, I miss you. ”

Murmushi yay ya janyo musu qofar.

*Asokoro*

Salim tinda ya dawo d’akinsa bayan tafiyar Abdulrazaq ya rufe k’ofarsa, bugun duniya alhaji Hashim yayi yaqi bud’ewa kuka kawai yake kamar qaramin yaro yana kiran Ummulkhairi.

Tsaye yake yana kai komo ya saqa wannan ya kwance wannan, ya rasa hanyar da zaibi ya samu ganin Ummulkhairi sabida kaf wayoyinsa an b’oye shi kuma zuciya ta hana shi tambayar su.

K’ofar ya ji ana tab’awa, ya kalli wajan ya kauda idanunsa, ya koma kan kujera ya zauna, ya d’auki sigari ya kunna ya zuqa ya fesar da hayaqin ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya, yana girgizawa ya zubama k’ofar idanu jin ana yanke qofar.

Alhaji Hashim ya iso ransa b’ace ya d’auke shi da mari ya rufeshi da masifa.

“Dan ubanka ni zaka d’auka d’an iska? Sbd inason ginama rayuwarka, shine kake shamin taba agida?”

Murmushi yay ya ce.

“Wai kana son ginamin rayuwa humm kuna son lalatamin rayuwa dai, tinda kun haramtamin abinda nakeso, ina wayoyina?”

Alhaji Hashim ya saki baki yana kallon Salim,tsabar takaici kasa magana yayi ya wurga masa wayoyinsa biyu ya wuce yabar d’akin.

Cikin rawar jiki ya d’auki wayan ya shiga ma’adanar lambobinsa, amman wayam yaga ba sunan kowa sai na Umma da Father da Aliyah layinma sabone.

Allah yasa yanada number Ummulkhairi akansa.

Loda number yay ya danna mata kira.

Wayan na wajan Shattima.

Ganin number ba suna ya d’aga yana jin muryan mai kiran, ba b’ata lokaci bai ko tsaya kashe wayan ba, ya ciro layin daman da Sim d’aya take anfani ya jefasa bakinsa ya taune ya shafe komai na kan wayan.

Salim kamar zaiyi hauka ya loda number Abdurrazaq.

Bugu biyu ya d’aga ko magana baiyi ba,Salim ya ce.

“Don Allah Salim ka samomin number Abdoul Aminu.”

Abdulrazaq dan kar aja magana ya ce.

“Ok ba damuwa za’a samo,ka canza layine?”

Katse kiran yayi bai tanka ba, yayi jifa da wayan, ya kunna sigari ya zuqa.

Misalin qarfe biyu na dare.

Unguwar _(Galadanci)._

Gida ne mai kyau da tsari Masha Allah.

Liman Umar zaune a bedroom d’insa, saman darduma sanye cikin fararen kaya,sai k’amshi yake casbi ne k’ato ahannunsa yanata ja.

Har yanzu lamarin auren Ummulkhairi na d’aure masa kai, ya jira Shattima ko zai kirasa ya masa bayani shiru bai kirasa ba, haka ya jira ya ji ko inno matarsa zata ce wani abun tinda can suka wuni amman shiru.

“Allah ya kyauta, bari na Kira naji kan abun.”

Yay maganar yana d’aukan wayansa ya danna number Shattima.

Alokacin Shattima yana zaune shima bayan ya gama sallar nafila yana addu’o’insa na yau da kullun, sai dai yau addu’arsa tafi raja’a akan nemawa ‘yarsa zaman lfy, da bata dangana akan rashin masoyinta da tayi.

Hasken wayarsa da take kan bedside ya hango, kasancewar bai fiye barin wayoyinsa da sauti ba, mafi akasari silent suke, ko vibration.

Da mamaki ya miqe domin ganin wa yake kiranshi tsakiyar dare.

Ganin sunan mahaifinsa yana yawo saman screen yay saurin d’aukar wayan, yay picking call d’in, yakai wayan kunnensa tare da sallama yana zama gefen bed.

Baffa liman ya amsa yana fad’in.

“Abdullahi! Na kasa bacci inata jimamin shin ya akayi auren Khairy ya koma wajan mai sunanka d’an gidan Aminu? Wlh abun ya tsayamin arai, inata jiranka ko zaka zo kamin bayani haka inarka su da suka wuni acan ko zanji wani batu amman shiru.”

Shattima ya gyara zamansa ya ce.

“Baffa! Wlh alhaji Hashim ban tab’a zaton haka daga garesu ba….”

Tsaf ya zayyanewa Baffansa abinda ya faru da taimakon da Aminu ya masa suka fita kunya.

Liman ya ce.

“Hasbunallahu wa ni’imal wakil, ikon Allah! Kai duniya haka ta lalace? amman ba komai karka damu Kansu sukayi wa, wanda Allah ya rufa masa asiri ba mai tona masa, yanzu ya ita Ummulkhairi ba abinda ya sameta koh?”

Shattima ya shafi lallausar suman kansa ya ce.

“Toh Baffa da sauqi dai sai gobe ma Zan kaita gidan nata da kaina insha Allahu.”

Liman ya ce“Allah yasa haka yafi alkhairi, shi kuma Aminu Allah ya masa albarka, ya biya masa buqatunsa na duniya da lahira.”

Shattima ya amsa da.

“Amin Baffa.”

Sukayi sallama.

*Singapore*

Abdoul zaune cikin falo yana sanye da 3 quarter, da singlet fara yana dafe da kansa, ya rasa me yake masa dad’i aduniya.

Wayansa ta d’auki ringing, ya waiga ya kalli gefen da take ajiye saman table yaga sunan Aliyah wanda yay saving da.

_(My love)_

Dogon numfashi yaja yana murza goshinsa, ya beqa hannu ya d’auki wayan, tare da d’aukan kiran, ya kai wayan kunnensa ba tare da yayi magana ba.

Daga can wata farar matashiya ce ta fara magana cikin yauqi tana wani lumshe idanu kamar bataso take mganar.

Siririya mai fad’in hanci sam baida tsayi sai dai farinta mai kyaune, tanada ido ba laifi dogowa ce mai cikar gashin gira da ta idanu, sai dai batada wata k’ira mata sabida sirintakarta, amman ba laifi tana k:irji sai dai sun kwanta kad’an, amman akwai goshi ba laifi, shekarunta na haihu 24.

“Baby! Wai yau lafiyarka kuwa? Tin fa d’azu nake online ina jiranka.”

Abdoul ya sake sakin dogon numfashi ya ce.

“My love! Ina lfy akwai abinda nakeyi ne shiyasa kika jini shiru, hope kina lfy?”

Fari tayi da idanu ta ce.

“Ina lfy Baby fatan kaima haka?”

Sama-sama suka tab’a hira ya mata sallama akan zai kirata gobe, sabida baida nutsuwa sam ayau.

Yadda yaga rana haka yaga dare bai iya runtsawa ba,har gigin asubah wayoyinsa na kashewa yayi,sabida baya son magana da kowa,shiyasa bayan yayi sallar asubah bacci mai nauyi ya d’auke shi.

Washegari misalin 7 am, Ummulkhairi ta farka da kuka tana sambatu.

Bilkisu ta kamota ta rungume ta ce.

“Haba! Baby don Allah kiyi hkr tinda sun nuna basa k’aunarki sun so tozarta mu Allah ne baiyi ba, ko wannan kad’ai ai ya isa ya saka ki godema Allah, kiyi qoqarin cire Salim aranki kamar yadda shima ya cireki,na roqe ki karki kunyata mahaifinki Khairy dan Allah. ”

Ummulkhairi cikin kuka ta ce.

“Allah Mamy duk yadda akayi badaga nisful Hayat bane, ni nasan irin son da yake min bazai tab’a guduna ba…”

Bilkisu ta katse mata hanzari cikin b’acin rai ta ce.

“Ok Baby yayi kyau kiyi abinda kika ga dama tinda mu muke miki k’arya Salim bazai iya tozartaki ba, mune zamu iya tozartaki. ”

Ta k’arashe maganar tana janye jikinta daga na Ummulkhairi ta sauka daga bed d’in ta nufi qofar fita.

Ummulkhairi ta d’ora hannu akai tana rusa kuka tana fad’in.

“Innalullahi wa’inna ilaihir raji’un! Na shiga uku na lalace, ya Allah ka kawomin d’auki, Mamy tayi fushi dani wa zai fahimci halin da nake ciki ayau?”

 

A qofar d’akin sukayi karo da Shattima zai shigo, ya riqo hannunta yana kallonta cikin kwantar da murya ya ce.

“Please kar kiyi fushi da ita, ahalin da take ciki ayanzu, dole zamu lallasheta Musa ta dawo normal, yi hkr muje kinsan duniya zaune ma bata k’aunar kiyi fushi da ita.”

Bilkisu hawaye suka silalo kan kumatunta, ta kwantar da kanta saman k’irjinshi ta zagaye hannayenta bayansa tana shasheqar kuka.

Shattima ya matseta jikinsa yana fad’in.

“Ya Salam! Kinga fa matsalata dake, toh ke kina kuka ita fa? Haba! Sweetheart yi shiru muje mu lallashi d’iyarmu.”

Abinda ya sake tayarma da Ummulkhairi hankali kenan agigice ta diro daga saman bed d’in aguje ta nufo wajan iyayan nata.

Hannunsa d’aya Shattima ya bud’e mata, ta shigo ya rungumesu su duka yana buga bayansu, yana murmushi tare da fad’in.

“Wallahi kun cika fitinar kuka Billy kece kika b’atamin Baby da kukan nan naki gaban nan zaneki ma zanyi Sam tinda bakya girma da kuka.”

Ya k’arashe mganar yana Jan kumatunta, tare da kwaikwayon kukan kowace a cikinsu.

Sai yaga dukansu suna dariya harda k’yak’yatawa, suna ruqunqumeshi.

Wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa tare da samun nutsuwa,arayuwarsa yana son ganin iyalinsa cikin farin ciki da annushuwa, yafi masa komai.

Hancin Ummulkhairi yaja ya ce.

“Sweetheart! Ya naga baby da kayan bacci ta kuwa yi sallah?”

Bilkisu ta ce.

“Yanzu fa ta farka tin jiyan.”

Sakinsu yay ya ce.

“Oya je kiyi wanka kiyi sallah sai kizo ina son magana dake OK sweet daughter? ”

Kai ta d’aga masa tana tafiya kamar k’wai ya fashe mata a cikinta.

Hannun Billy ya kama suka fita.

Khairy anan d’akin Mamynta tayi wanka ta shirya tana kaya anan ta saka doguwar riga ta atamfa, ta sanya hijab ta tayar da sallah.

Suna zaune afalonsa ta shigo bakinta d’auke da sallama.

Jikin Bilkisun ta shige tana turo baki gaba ta ce.

“Mamy! Kiyi hkr karki kuma fushi dani bazan sake mgnar Salim ba.”

Cikin farin ciki Mamyn ta rungumeta tana sanya mata albarka.

Shattima yay gyaran murya ya ce.

“Baby! Kinsan ina sonki bazan tab’a cutar dake ba koh?”

Kanta ta d’ora kan kafad’arsa ta ce.

“Yeah sweet Dady na sani.”

“Yawwa Baby Allah miki albarka dan haka inaso ki amshi Abdoul amatsayin mijinki da hannu biyu insha Allah bazaki tab’a kuka koda nasanin aurensa ba, dan Allah wannan taimakon zakimin bana son nasake ganin kukanki akan wannan auren.”

Ummulkhairi ita tasan me takeji acikin zuciyarta, amman azahiri sai ta murmusa ta ce.

“Na amshesa har abadan Dady ka kwantar da hankalinka, insha Allah bazan baku kunya ba, Zan masa biyayya daidai iyawata bazan tab’a k’in abinda ya fito daga hannun mahaifina ba, wanda banda kamarsa afad’in duniya.”

Sosai minister Shattima ya ji dad’in kalaman ‘yarsa, rungumeta sukayi suna saka mata albarka.

Bilkisu ta ce.

“Sai muje muyi breakfast, Baby je ki taso Maryam tana d’akinki.”

Ummulkhairi cike da farin ciki ta miqe tana fad’in.

“Lah! Ai ban sanaiba Mamy.”

Shattima ya ce.

“Bata tafi ba kenan?”.

Kai ta d’aga masa ta ce“Kasan Maryam da k’aunar gidan nan, jiya tace bazata tafi ba nan zata kwana, na Kira hajiyata na fad’a mata na riqeta sai ta kwanan min biyu na fitar da kewar baby tinda ana hutun makaranta.”

Kai ya jinjina ya d’auki wayansa wadda Kira ya shigo…

Misalin k’arfe 9 na dare Bilkisu ta shirya Ummulkhairi tsaf cikin wata lafiyayyar lafaya, milk colour tayi kyau matuqa, nasiha mai ratsa jiki ta mata tana kuka haka ta kaita har mota, Shattima na zaune yana jiransu, ta zaunar da ita front seat tana hawaye ta juya zata tafi Ummulkhairi ta riqota gam tana kuka.

Shattima ya b’anb’are hannunta yace.

“Please sweetheart ku shiga ciki sai na dawo.”

Ya k’arashe mgnar yana rufe motar.

Mamy tana hawaye ta Kama hannun Maryam suka nufi ciki.

Key yama motar da kansa tare bada umarni kar kowa ya bisa.

Gate ya nufa anutse yake murza stiyarin motar ahankali yana horn.

Mai gadi ya danna remote k’aton gate ya fara yin sama har ya bud’e baki d’aya.

Ya silala hancin motar waje.

 

*Asokoro*

Salim zaune a cikin motarsa,a gate d’insu, sai gwada kiran number Abdoul yake tin jiyan da Abdulrazaq ya turo masa yake famar gwadawa amman bata shiga.

Ashar ya lailayo ya maka tare da fad’in.

“Munafukin banza ba dole ba ka rufe waya,tinda ka samu tsuntsu daga sama gasashe.”

Ya k’arashe maganar yana sake gwada kiran number.

Cikin sa’a ta shiga sai dai har ta katse ba’a d’auka ba, sai da ya Kira sau biyar aka d’aga ba tare da anyi mgna ba.

Salim cikin k’ufula ya ce.

“Munafukin banza ka auremin mata ko? Toh wallahi tallahi kwana d’aya na baka daga yau zuwa gobe ka saketa, idan ba haka ba zakaga abinda zai biyo baya kare ma sai ya fika daraja a k’asar Singapore d’in dan uban babanka…”

Daga can Singapore kuwa abinda yake faruwa shi ne…..

Mrs Jaana♥️🥰

[12/10, 5:29 pm] +234 814 210 5218: _YI WA KAI…!_

 

 

RAHMA Oum Farisah

 

_DEDICATED To_ _*Zuwaira Mohammed.🥰and Nafisa Nasir hard’o.♥️*_

💃🏻Billahi na gode muku ALLAH ya saka da alkhairi yabar zumunci saqon Ku yazo min, much love.🥰🥰♥️

 

 

 

_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_

 

 

 

 

 

 

 

*P 7&8*

 

 

A gate d’in gidan commissioner Aminu minister Shattima ya tsaya yana horn.

Ya waigo yana kallon Khairy, ganin har lokacin kuka take, ta cusa kanta tsakanin guiwowinta.

A hankali ya furta.

“Ya Rabbi! Baby! Yi haquri mana please, ba fa rabuwa zamuyi ba, ta har abadan.”

Ya idar da maganar tare da sauke ajiyar zuciya, me qarfi lokacin aka bud’e masa gate d’in gidan ya danna hancin motarsa cikin gidan.

Murmushi ya sub’uce masa lokacin da ya ga commissioner Aminu, da iyalansa suna tsaye a compound d’in gidan, fuskokinsu asake cike da annushuwa.

Parking yay nan dab dasu, bai shiga parking space ba.

Ya kalli Ummulkhairi wacce ta k’ara sautin kukanta, tana d’ago kanta jin an kashe motar.

Hannayenta ya kamo wanda suka sha jan lalle cikin lallami ya ce.

“Sweet daughter! Kiyi haquri kukan ya isa haka, kin manta inda kikazo ne? Ai ko kullun kike son ganinmu da mamynki kiranmu kawai zakiya awaya muzo ji ganmu muA, ko kizo gobe idan Maryam zatazo zan bayar da wayanki akawo miki kinji baby?”

Kamar jira take ta qara sautin kukan, tare da qamqame shi tana kuka mai tsuma zuciya tare da fad’in.

“Dady! Ni ban saba da rashinku ba, yanzu haka zanyi rayuwa ba iyayena akusa dani? Wa zai dinga riritani da shagwab’ani, tare da sani ahanya idan nayi ba daidai ba?”

Murmushi me sauti ya yi tare da buga tsakiyar bayanta, ya ce.

“Mijin ki mana baby ga kuma Dadynki Aminu da Amminki Abida, kafin ku tare agidanku, don Allah ki daina kukan nan yi shiru kinji? Sannan kiyi aiki da dukkan nasihar da muka miki kullun zamu dinga zuwa tinda sassafe ganin ki, shi kenan koh?”

Kai ta d’aga tana share hawayen fuskarta da tafin hannunta.

Handkerchief ya zaro cikin aljihunsa ya goge mata fuskar da kyau, ya sumbaci goshinta, ya ce.

“Oya murmushi mugani.”

Ummulkhairi ta saki murmushi.

Yaja dogon hancinta ya ce.

“Good baby oya muje.”

Ya k’arashe maganar yana zura hannunsa ya bud’e mata motar.

Shima ya bud’e b’angaransa ya fito.

Abida ta rungumeta tana fad’in.

“Oyoyo sweet daughter, barka da shigowa families d’inmu.”

Ummulkhairi tai k’asa da kanta, tana neman zubewa k’asa ta gaishesu Abida ta hanata.

Shattima sukayi musabaha da Aminu, yana amsa gaisuwar yaran cikin sakin fuska, ya ce.

“Toh ga ‘yarku nan na kawo muku amana, ni zan koma Allah ya bamu alkhairi, Maryam na gaisheku.”

Aminu ya ce.

“Wlh baka isa ba sai mun shiga kaga wajan zamanta. Wai kai kad’ai ka fito ne?”

Dariya ya yi yana fizge hannunsa ya shige mota yana fad’in.

“Nafi kowa sanin wajan da na kawo Khairi meye na ganin d’akin da zata zauna kuma? Toh meye dan na fito ni d’aya? Ai Allah yake tsare damu ba mutum ba, kaga na tafi seda safe bye.”

 

Ya k’arashe mgnar yana rufe qofar yama motar key yana ja da baya har ya juya ya nufi gate.

Aminu ya girgiza kansa yana d’aga masa hannu. Can falonsu sukaje da Khairy sukayi mata nasiha sosai,taji dad’in hakan, ta dan sake kad’an.

Abida ta kai Ummulkhairi har b’angaranta, tare da sake mata nasiha kamar yadda,zatama Maryam da Nafisa, ta ce Nafisa ta zauna wajanta su dinga kwana har Abdoul ya dawo.

Hakan ba qaramin jin dad’i ya saka Khairyn ba! Sai dai taqi nunawa azahiran ce.

_Abunda ya faru a Singapore kafin kiran da Salim yama Abdoul shi ne._

 

Abdoul tin bayan kwanciyar da ya yi bayan sallar asuba, wani irin zazzafan zazzab’i ya tashi da shi.

Da k’yar ya iya miqewa ya yi wanka ya had’a tea me kauri ya sha, ya sha magani ya koma ya kwata.

Bai sake tashi ba sai wajan 1 na rana, cikin ikon Allah bai tashi da zazzab’in ba, ya yi wanka yay sallar azuhur, ya shirya zuwa makaranta sunada lecture k’arfe 3.

Tsautsayi da bai wuce lokaci, bayan sun tashi daga makaranta 1 hour kawai sukayi, ya biya super market ya yi shopping, a ciki yana zagayawa yana zab’ar abinda yake so, wata yarinya da bata wuce 6 years ba, suna tafe da iyayanta, suna zab’ar abubuwan da suke buqata, tana shan ice cream, dai-dai lokacin da Abdoul ya biyo ta wajansu, suna dab da juna, idanun yarinyar ya sauka akan wani kwalin biscuit, ta saki roban ice cream, d’in, cike da shagwab’a take nunawa iyayan nata kwalin biscuit d’in.

Abdoul sam bai kula ba, hankalin shi agaba ya take robar ice cream d’in samtsi ya kwashesa, ikon Allah kamar ana jansa ya tafi shuuuuu, yana kiran sunan Allah, yana duba abinda zai riqe amman ina abunka da tayis mai shegen sulb’i, sai ga shi k’asa wanwar yayin da kwandon hannunsa ya fara kaiwa k’asa shi ya biyu baya, ya yi muguwar fad’uwa akan hannunsa na hagun, wanda atake hannun ya karya.

Idanunsa ya rumtse cike da jin azaba, lokacin da yaji qaran karayar qashin hannunsa, tabbas yasan karya ya yi.

Iyayan yarinyar sukayo kasan aguje hankalinsu atashe ganin robar ice cream d’in da Diana ne ta yar.

Kamasa sukayi suna masa sannu tare da ba shi haquri.

Kai ya girgiza musu.

Su suka kaishi hospital, mahaifin Diana shi ya tsaya akan komai, har kuka yayi jin Abdoul karaya ya yi.

Abinka da harakar manyan mutane kafin qarfe 6:30 pm, lokacin su na can har an d’ora hannun, an masa qarin ruwa tare da allurai, ya samu bacci.

Mahaifin Diana ya kasa ya tsare ya kasa tafiya gida, har sai da ya farka yaga jikin nasa da sauqi ya tafi, daman asibitin basa barin masu jinya su kwana, sunada masu kula da majinyaci, za’a amshi number mutum idan sun ga majinyaci na matse zasu kira.

A lokacin da josnny suka tafi gida da iyalansa ne, Abdoul ya ji yana sha’awar kiran mahaifinsa ya sanar da shi tsautsayin da ya sameshi.

Da hannunsa mai lafiya ya kunna sabuwar wayan da siya jiyan, yana kunnata ne kiran Salim ya shigo, daga d’agawa ne, ya ji irin zagin da yake masa, har yana basa umarnin ya saki Khairy wai matarsa ce.

 

Cike da mamaki Abdoul ya muskuta yana ciza lips d’insa, tsabar zafin d’orin hanunsa da yake ji.

Ahankali ya furta.

“Please ba wanda kake nema bane, karka sake kirana, kai kasanta ma wacce kake maganar kanta.”

Daga can Salim ya bud’e motarsa ya fito, yana zuba ruwan masifa.

“Wallahi k’arya kakeyi kace baka san Ummulkhairi ba, tsohon munafuki daman can sonta kakeyi, wallahi ko kaffara bazanyi ba, daman can sonta kakeyi, kaida iyayanka kuka shirya makirci dan ku rabani da ita, toh wallahi k’arya kukeyi sai naga bayanku Ku zuba ido ku gani…”

Abdoul yay murmushin k’arfin hali ya ce.

“Kai kasan suwaye iyayena, ba tsaffin ala gwangwan bane, basa b’atawa sai dai su gyara, dan haka anqi a saketa idan akwai inda zaka kaini a fad’in duniyar nan a sakani na saketa toh bismillah, sakarai k’idahumi wanda baisan Annabi ya k’aura ba! Mahaukacin gangan.”

Ya k’arashe mgnar yana kashe wayan baki d’ayanta, yana Jan tsaki tare dafe kansa, ya lumshe idanunsa, yana fad’in.

“Haka kawai ina zaman zamana an had’ani da masifa, Ina dalili daman hakan Salim d’in nata yake? Mstwwww!”

Daga can kuwa Salim ya kama masifa da bala’i sai ashar yake lailayawa Abdoul jin yace bazai saki Ummulkhairi ba.

Motarsa ya shiga yana zuba horn aka bud’e masa gate ya shiga ciki.

A farfajiyar gidan yay parking, koh rufe motar baiyi ba, y nufi b’angaran iyayan nasa.

 

Falon ya fad’o kamar ana koro shi yana famar masifa.

Cikin sa’a alhaji Hashim na zaune.

“Father! Umma! Nace kunga abinda kuka jazamin koh? Ga shinan na kirasa ya sakar min mata yace bazai Saki ba Toh wlh na rantse muku da Allah za kuga binda zai biyo baya, ba abu bane me kyau idan na fasa binda nayi niya akan Ummulkhairi ni ba dan halak bane, daga yau bazan sake maganarta ba sai abubuwan sun fara fitowa a aikace. Ita kuma Aliya ko zataci ubanta na rantse da Allah sai ta tsani me sunan Salim arayuwarta.”

Ya k’arashe maganar yana juyawa fuuuuu yabar falon ba wanda ya tanka masa.

Sa’idah ta ce.

“Kana jinsa yana mana rashin arziqi bazaka iya masa komai ba? Wlh da nasan iskancin Salim ya kai haka, daman munbarsa da annobar yarinya can…”

Alhj Hashim ya girgiza kansa yana fad’in.

“Kashhh! Sa’idah! Bakya ganewa, kin tab’a ganin mahaukaci ya warke ne? Barsa dan ubansa nasan maganinsa.”

Ya k’arashe maganar yana miqewa ya d’auki wayoyinsa ya nufi hanyar barin falon.

Hajiya Sa’idah tayi tagumi tana nadamar rabashi da Ummulkhairi da sukayi, tana tsoron abinda zai je yazo, tabbas ko kashewa Salim ya ce zaiyi to fah… . Dan ba zata tab’a manta abinda ya tab’a faruwaba, kud’ine da matsayi da cikkakun takardunsa kawai suka nuna komai ya wuce kamar ba’ayi ba, hakan sirrinsu ne sai likitoci duk duniya ba wanda ya Sani, ko acikin family d’insu mutum biyu kawai suka sani.

 

_Commissioners Quarters_

Shattima yana dawowo gida, bai shiga ciki ba, cikin mota yake, yana waya.

Can ciki kuwa Mamy wata irin matsanaiciyar kewar Ummulkhairi ta addabeta, ta kasa zaman falon tabar Maryam ta ce tayi kallo idan taji bacci ta kashe kayan kallon ta hau saman, kanta yake ciwo.

Maryam kuwa zamanta tayi tana kallon wani flim na larabawa tashar MBC 2.

11 pm. Minister Shattima ya shigo falon bakinsa d’auke da sallama.

Duk irin nisan daga qofar zuwa falon bai hanawa da kayi sallama aji, sabida yanayin tsarin ginin.

Maryam jin daddad’ar sautin amon murya Shattima yana sallama taji wani irin bala’in sanyi acikin zuciyarta, tare da sa bud’e k’ofofin hancinta, ta fara shaqo daddad’an k’amshinsa mai sanyaya zuciya, ta bud’e bakinta tana rarraba idanunta ta idan zata hango shi, ai kuwa ta hangoshi hannayensa zube cikin aljihun wandon dakekiyar shaddarsa,ta amsa sallamar.

“Wa’alaika salam, welcome Dady.”

Tsakiyar falon ya shigo yana amsawa.

“Thank you daughter, ina mamynki?”

Ya mata tambayar yana janye idanunsa daga kallonta.

K’asa tai da kanta tana wasa da yatsun hannunta, sbd wani bala’in sanyi da ya fara ratsa dukkan sassan jikinta, SBD kaifafan idanunsa masu wani iri sinadari da mata basa jure kallonsa na wani lokaci.

Can k’asa cikin sanyin da gab’ob’inta sukayi ta ce.

“Mamy tin da muka shigo bayan mun rakaku da auntie mota tace kanta na ciwo zata kwanta.”

“Subahanallahi.”

Shattima ya nufi seat d’in kujerun da suke b’angaran gabas ya zauna yana ajiye hular kansa tare da cusa hannunsa cikin yalwatacciyar sumar kansa yana shafawa, ya miqe qafafunsa zuwat saman kujeran, yana jingina bayansa da allon kujerar.

Wayarsa ya d’auka ya latsa number Bilkisu ya danna mata kira.

Kwance take saman makeken bed d’inta sai juyi take takasa bacci jiran Shattima take yazo ta kwanta cikin jikinsa ko ta rage kewar Khairy.

Sanye take cikin kayan bacci Riga da wando masu samtsi sun mata kyau sosai, duk da ramarta.

Jin ringing d’in wayanta, ya sanye ta bud’e idanunta ta mirgina ta iso dab da wayan da take kan pillow.

Ganin me kiran ya saka ta d’auki wayan tare da picking call d’in.

Asanyaye ta amsa.

“Hello Mi Amor! Ka shigo?”

Murmushi mai kyau ya saki tare da furta.

“Uhmm! Duk kewar babyn ne koh?”

 

Maryam asace ta d’ago da kanta ta kalli b’angaran da yake zaune, jin yadda yake magana cikin kamewarsa tare da nutsuwa, sautin amon daddad’ar murya shi tana zagaya falon ahankali.

 

Maryam bata san lokacin da a zuciyarta ta furta.

“Wow! Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci Dady Shattima, Allah ya masa tsari me kyau, ga shi kamar sauriya Sam baya tsufa ko alamar tsufa basu fara bayyana ba atare da shi, Sam bazaka ce shi ya haifi auntie Khairy ba wayyo Dady I love you so much, son so domin Allah, my dad, inama Mamy Billy ba mutuniyar kirki bace wallahi da bazan iya b’iye son da nake maka ba, sai na bayyana amman ina ba hali ana barin halak dan kunya.”

Ta furta duk wannan bayanan acikin zuciyarta, ta masa k’ura da idanu tanajin ruwa sun fara taruwa acikin idanunta, tana son salon yadda yake tafiyar da rayuwarsa, shi d’in gwanine wajan nunawa iyalinsa soyayya ga nutsuwa ga tsaf ga kyau,duk da yana baqi amman yanada wani irin bala’in kyau mai d’aukan hankali, ga shi bayada wulaqanci ko girman kan shi wani ne.

“Yanzu dai sweetheart oya sauko ki dafamin black tea.”

Ya k’arashe mgnar yana katse kiran.

Bisa tsautsayi ya waigo b’angaran da Maryam take zaune.

Karaf ya kamata tana kallonsa idanunta akwai kwancin k’walla acikin su.

Muguwan kuyan taji lokacin da ta tsinci muryasa mai rud’ar mata da k’wak’waluwa yana fad’in.

“Subahanallahi daughter! Me ya sameki kamar hawaye kike? Ko bacci kikeji?”

 

Daburcewa tayi ta rasa me zata ce sabida bata iya wani katab’us idan yana kusanta.

Cikin inda-inda kamar zatayi kuka ta ce.

“Wallahi Dady cikina yake ciwo tin yamma, yanzune nakeji kamar yana qaruwa.”

Ta k’arashe mgnar kanta aqasa.

Shattima cikin kulawa ya ce.

“Subahanallahi sannu daughter, bari mamynki ta sauko yanzu sai ta dubaki ta baki magani kisha, ko muje hospital.”

 

Maryam gabanta ya fad’i ta shiga raba idanu dan ta tsani maganar hospital ko shan magani sbd tsanar da mata allura da magani.

Cikin inda-inda ta ce.

“Dady! Zai bari wallahi ba sai nasha komai ba!”

Bai kalleta ba ya ce.

“No! Dole fa sai anyi d’aya cikin kota baki magani ta miki allura agida ko muje hospital. ”

Shasheqar kukanta yaji kamar wasa na tashi a falon.

Manyan kaifafan idanunsa ya zaro waje cike da mamaki zaiyi magana yaji takun saukowar Bilkisu daga stairs.

“Innalillahi! Mi amor! Me ya samu daughter?”

Kai ya girgiza yana murmushi ya mata bayanin abinda yake faruwa.

Bilkisu ta ce.

“Dan mafi akasari idan tazo gidan nan har ta tafi baka k’asar Baku fiye had’uwa anan ba, sai idan wunine tazo baka San k’iyayyar Maryam da magani ba, ko allura ai bata k’auna.”

Ta k’arashe maganar tana isowa wajan Maryam ta kamota ta rungume tana buga bayanta ta ce.

“Yi shiru k’yale dady, ya kikejin ciwon cikin?”

Maryam ta ce.

“Na rantse da Allah Mamy naji sauqi komai banaji yanzu Allah Mamy.”

Dariya sosai ta k’wacema Shattima ya fara yana k’yak’yatawa, cikin sauti me fita a sannu.

Mamy ta girgiza kanta ta kamata ta ce.

“Ok muje ki kwanta.”

Hayewa sukayi sama da dubara Mamy taba Maryam maganin ciwon ciki harda su sweet dan ta manta maganin, ta sakata ta shirya cikin kayan bacci sai da ta kwanta ta lullub’eta ta sakata tayi addu’ar bacci kafin ta rufo mata k’ofar ta sauko wajan Shattima.

Black tea ta dafa masa ta saka kayan k’amshi da citta ta kawo masa.

Saman cinyarshi ta hau tana basa abaki yana Sha, suna magana k’asa-k’asa cike da soyayyar junansu, daga k’arshe suka haye stairs, can suka k’arasa soyewar.

Washegari Ummulkhairi sai ta shi wasai batajin wannan k’uncin da takeji abaya na rashin Salim,sai da sonsa da k’aunarsa na nan daram zaune acikin zuciyarta.

Tin bayan sallar asuba da tayi sallah ta gyara falon da bedroom d’inta tsaf, ta sanya turaren wuta, ta ce da Nafisa tafi part d’insu Ammi su d’ora girki.

Nafisa ta ce.

“Lah! Auntie Khairy ai mu bama komai masu aiki sukeyi, girki Abba ne kawai Ammi take yi.”

Khairy ta ce.

“Eh muje na tayata nifa na saba bana iya bacci bayan asubah har na tafi school, ba ruwana da masu aiki komai yi nakeyi muje don Allah.”

Ba yadda Nafisa ta iya suka fito suka nufi part d’insu Ammi.

Lokacin da suka shigo Lantana na shara Lami tana mopping ko ina sai k’ylli yake, kai tsaye kitchen Nafisa ta jata suka shige.

Ammi tsaye tana juye ruwan tea a flask, taji sallamar su Khairy.

Cikin sakin fuska ta amsa, tana fad’in.

“Ah Khairy! An tashi?”

Rusunawa tayi aladabce ta gaisheta.

Ammi ta amsa tana tambayarta baqunta.

Ummulkhairi ta amsa tana juye ruwan tea d’in Ammi ta ce.

“Ki bari mana Khairy kuje ku kwanta ku huta.”

“A’a Ammi bari mutaya ki aiki.”

Haka kuwa akayi tsaf da Khairy da ita akayi komai na breakfast ta shiya a kan dining area, taje ta gyara kitchen tsaf, Ammi sai albarka take sanya mata.

 

*Singapore*

Abdoul zaune idar da breakfast d’insa kenan , wanda haka yake daman baya breakfast da wuri ko yanada lafiya, wannan ma sai da Johnny ya matsa masa ganin har lokacin shan nayaman na qoqarin shigowa, ya yardayaci abinci kad’an, ya basa maguguna yasha, ya masa nuna ya beqo masa wayansa.

Wayan ya ciro masa acaji ya beqa masa, da harshen turanci yana fad’in.

“Please bani address d’in gidanku naje anutse nayima iyayanka bayani,sai muzo dasu koh?”

Abdoul ya lumshe fararen manyan idanunsa,baice komai ba, ya shiga ma’adanar lambobinsa,yay dialing number commissioner Aminu.

Daga can Nigeria sun hallara akan dining area suna breakfast, Ummulkhairi kanta aqasa dak’yar take breakfast d’in sabida kunyar surukan nata.

Wayarsa da ta d’auki vibration, commissioner, ya zaro wayan gaban aljihun rigar suit d’in da take jikinsa, ganin sunan me kiran ya sanya shi ajiye spoon d’in hannunsa, ya cira tissue ya goge bakinsa, ya d’auki wayan tare da sallama.

Farar fuskar shi ta gushewa tare da kallon Ummulkhairi yana fad’in.

“Ok karkaji komai.”

Ya k’arashe mgnar yana katse kiran ya ce.

“Daughter Khairy! Idan kin gama ki sameni mota, ina jiranki…”

Ummulkhairi cike da girmamawa ta amsa da.

“Toh Abba.”

Ta k’arashe mgnar tana cira tissue ta goge bakinta had’i da miqewa.

Abinda ta biyosa tana tambayar shi.

“Abban Abdoul lfy? Ina zaka da ita?”

Bai juyoba ya ce.

“Nan kusa.”

Ya fad’a yana tafiya.

Khairy kuwa daman cikin shigarta tsaf take sanye da hijab tama Ammi sallama ta fito.

Motar da taga securities a tsatsaye nan ta nufa kanta a qasa, tafiyarta cike da nutsuwa duk da tana sanye da hijab har qasa, amman jikinta haka yake motsawa kamar tarwad’a masha Allah.

Tana dosar motar ta ga an bud’e mata side d’in baya idan commissioner Aminu yake zaune, riqe da jarida hannunsa yana dubawa.

Da sallama ta shigo zauna kanta k’asa, ya amsa sallamar ya ce.

“Yawwa daughter kin qara so? Garba muje koh.”

Daidai lokacin ne kiran Abdoul ya shigo wayansa.

Bai d’aga ba har direba yaja motar ya nufi gate…

Mrs Jaana♥️🥰

Leave a Comment

error: Content is protected !!