Hausa Novels

Zafin Hawayena Hausa Novel

Zafin Hawayena Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*ZAFIN HAWAYENA*
“`A True Life Story“`

Book1
“`Shafi na sha uku“`

“Lafiya?”
Cikin tashin hankali ta miƙe, ta ɗauki handbag ɗinta tare da jan trolley.
Da sauri ya sha gabanta, tsayawa tayi cak, a kiɗime take kallonsa.
Hannunta ta haɗe alamar roƙo, kafin ta ce “Dan Allah kada ka cutar dani, ni marainiya ce, dan darajar Allah ka tausaya min ka bar ni in tafi.”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya lumshe sexy eyes ɗinsa ya buɗe, tare da zubasu akan fuskarta. A tsorace take sosai dan karkarwa take.

“Yanda kike tunani ba haka nake ba, wallahi ban taɓa riƙe hannun mace dan feelings ba, kada kiyi tunanin na kawo ki nan dan in cutar dake ne, wallahi ko ɗaya, na tsani duk wanda ke aikata hakan, kin ga nima ba zan so na aikata ba”
“Mugu bashi da kama, ni dai ka barni na tafi kawai”
“Ina zancen labarin da za ki bani?”
“Bani da wannan lokacin”
“Kenan ba zaki bani haɗin kai ba, wajen nuna kulawa a gareki”
Jin ana taɓa bell yayi saurin nufar ƙofa, ita kuma da ido ta bishi. _Kenan Hausarshi ce haka, furucinsa ne ban gane ba, ko dai wayo yayi min dan yaga ina neman tafiya baici galaba a kaina?_

Ganinshi tayi ya dawo da leda a hannu, sai daya fara ajjewa kan table, sannan ya dawo inda take tsaye.
“Dan Allah ki bani haɗin kai na taimakeki, tun a jirgi na gane kina da damuwa”
Kallon shi tayi, taga damuwa ƙarara a fuskarshi.
“Meyasa sai ka taimaka min? Baka da hurumi, domin baka da wata alaƙa dani”
“Akwai alaƙa ta musulunci, wallahi Amatul-ahad inda cutar dake zanyi da zan saka abu a cikin lemo yadda idan kinsha zaki bugu, na san a yanzu mutum ba abin yarda bane, amma na miki alƙawarin ba zan taɓa cutar dake ba, dan tun haɗuwata dake ban kawo haka ba”
Kai ta gyaɗa alamar gamsuwa. Da hannu ya nuna mata kujera ya ce “Dan Allah ki zauna”
Komawa tayi ta zauna, tana ƙara kallon ɗakin, shi kuma ya shige ciki.

Da plate ya dawo, ya ɗauki ledar ya fito da robobin takeaway, abinci ne mai rai da lafiya, zubawa yayi ya fara ajjewa a gabanta sannan shima ya zuba ya koma kujerar dake facing ɗinta.
“Kici abinci, nayi order ne anan restaurant da nake yawan zuwa, Allah yasa zai miki daɗi.”
Murmushi kawai tayi ta ɗauka tana ci a hankali, ganin taƙi sakewa ta ci abincin ya sakashi tashi ya bar gurin.
Aikuwa ta samu ta ɗanci da yawa sannan ta rufe sauran, fito da wayarta tayi ta fara yin selfie, har da cire mayafi, tayi anan tayi acan.
Murmushi kawai yake daga bedroom yana hangota ta CCTV.
_Tana son hotuna, na fahimci ita macece mai son walwala sai dai tana da damuwa a ƙasan zuciyarta, wanda ya kan hanata sukuni a wasu lokuta, ya Allah kana gani da zuciya ɗaya nake son taimaka mata, ban san mene manufar haka ba, naji kawai ina so na taimaketa._ Tashi yayi ya fita parlour, ai tana ganinshi tayi saurin zama, ta maze kamar ba ita take yin hotuna ba.
“Allah yasa kinci abinci da yawa”
Murmushi tayi sannan ta ce “Eh na ƙoshi, Alhamdulillah”
“Masha Allah.”

Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce “Amma meyasa kike son zaman Campus?”
“Bani da wani wanda na sani, sannan lokacin dana fara karatu ina da ƙarancin shekaru sosai, sai aka haɗani da Nanny wanda duk ɗaliban dake karatu a makarantar muna da Nanny’s da suke kula damu, so kuma yanzu bayan na gama dana samu admission a columbia sai kawai Daddy ya nema min hostel na ɗalibai, saboda ka san yanayin rayuwa musamman cikin ƙasar da baka da kowa kuma babu yawaitar musulmai a ciki, so hostel ɗin ma yafi min daɗi, saboda ina ganin anan akwai tsaro”
“Amma kamar kina da tsoro ko?”
Dariya tayi tare da cije leɓe “Ai bama mutum kaɗai ba, har duhu ina bala’in tsoron duhu”
Murmushi ya yi sannan ya ce “Aikam ki rage tsaro, domin idan kina da tsoro to ta hakane duk wanda ke son cutar dake zai samun lago a kanki”
“Zanyi ƙoƙarin cirewa insha Allahu, amma kai kaɗai ke zaune a gidan nan?” Ta faɗa tana ƙara bin parlour’n da kallo.
“Eh ni kaɗai ne, yayi min girma ko?” Murmushi kawai tayi.

Shi ya ɗauketa ya kaita har inda take zama, sannan ya karɓi number wayarta sukayi sallama ya tafi.

Tana kwance akan ɗan ƙaramin gadonta, ta rungumi ɗan ƙaramin pillow, idanunta na kallon silin.
_Wataƙila wannan mutumin shine zai kawo sauyi a cikin rayuwata, ina ji a jikina zai zame min alkhairi, kuma zai zamo mutumin da zai kawo farin ciki a cikin duniyata, naji ina sonshi sosai._ ta furta tare da murginawa tayi rubda ciki. Duniyar tunanin Fauwaz ta faɗa, babu abinda take gani sai murmushinsa a cikin idanunta.

Ta ɓangaren Fauwaz kuwa, baccinsa yasha, baima saka ta a ranshi ba, sai dai kuma da ita ya farka, ya matsu kawai yaji labarinta.
So yake ya kirata amma kuma ayyuka sun masa yawa sosai, dan haka kawai shiryawa yayi a gurguje ya nufi gurin aiki.

*02:30pm*

Kallon wayarta tayi taga babu missed call ko ɗaya, ɗan ɓata rai tayi sannan ta ce “Ko dai ya manta dani ne?”
Zama tayi kan gadon tare da kalmashe ƙafafunta.
_Fauwaz._ ta maimaita sunan a ranta.
“Ni kuma bai bani number ɗinshi ba bare na kirasa” ta ƙara furtawa a fili.

Ranar dai haka ta yini cur tana duba waya tana jiran kiransa, amma shiru babu labari,duk da wayarta ba a silent take ba amma sai ta kasa samun nutsuwa dole sai ta duba ɗin.

*10:30pm*

Kasancewar ƴan ɗakinsu duk basu nan, dama su huɗu ne a ɗakin, kuma ita kaɗaice ƴar Nigeria kuma musulma a cikinsu, so tun ƙarfe 09:00pm suka shirya cikin banzar shiga suka fita yawo, itama sunyi-sunyi taje amma ta ce ita sam ba zataje ba.
Shine dalilin da yasa suna fita ta kashe light ta kwanta, ta daɗe bacci, bai ɗauke ta ba, tana farawa kuwa, lokacin kuma kiran Fauwaz ya shigo wayarta.

Zaune ta miƙe tare da ɗaga wayar “Allah yasa dai kana lafiya?” Shine abinda ta fara faɗa.

Gabanshi ba ƙaramin faɗuwa yayi ba, amma ya daure ya ce “Lafiya lau, ina fatan kema haka?”

“Eh ina lafiya, amma dai na ɗan shiga damuwa domin kace zaka kira da safe to nayi tunanin kuma wani abu ne ya faru danaji shiru”

“Lafiyata lau, wallahi aiki ne yayi min yawa a office”

“Allah sarki, to Allah ya taimaka”

“Amin ya rabbi, yanzu kina ina haka?”

“Gani a hostel, room mates ɗina kuma sun fita, gaskiya rayuwar ƙasar nan akwai haɗari ka tayani addu’a Allah yasa nafi ƙarfin zuciyata”

Amin, amma lafiya dai?”

“Lafiya lau, kawai dai maganganun da room mates ɗina keyi basa mini daɗi”

“Wane maganganu kenan?”

“Suna son lalata rayuwata ne ko ta wane hali”

“Ban fahimta ba”

“Zanyi maka bayani zuwa da safe, yanzu ina tsoron kar bacci ya bar idona na kasa”

“Ba zan iya bacci ba idan har baki faɗa min abinda ke faruwa ba”

“Zan faɗa maka….”

“Bari kawai nazo hostel ɗin”

“Securities ba za su yarda ba”

“Za su yarda mana, idan har na basu abinda wannan ƴammatan suka basu, har suka barsu suka fita”

“To shikenan sai kazo.” Katse wayar tayi cikin jindaɗi ta miƙe ta shiga toilet ta sakeyin wanka.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin doguwar riga straight gown mai kyau, tayi rolling sannan ta zauna zaman jiranshi.

Wayarta data fara ringing ta ɗauka tana ganin shine tayi saurin ɗagawa “Hello” Ta faɗa cike da zumuɗi.

“Ki fito main gate ina jiranki”

Miƙewa tayi ta ɗauki sidebag ɗinta sannan ta fita.
Da gudu-gudu take wuce duk wani guri da yake da duhu, wanda babu alamar ƙafa a wajen, a haka har ta fita.
Wajen kuwa babu alamar dare, mutane kowa nata harkar gabanshi, ga kuma haske ta ko ina, sama kawai zaka kalla ya tabbatar maka da dare ne.
Waige-waige take tana neman inda yake, ta bayanta taji ya ce mata “Gani” da sauri ta juya ta kalleshi.

Murmushi tayi tare da ɗan rufe fuska da hannu.
“Tun fitowarki na ganki ai”
“Amma shine baka min magana ba?”
“Ina so naga kin fara gane Yayan naki ko kuma da saura”
“Ai ko ina bacci aka tasheni aka nuna min kai, to zan ganeka”
“Kina da basira Amatul-ahad”
Bata ce komai ba. Ya ƙara da faɗin “Ina fatan kin ɗauko kayan da zaki saka gobe?”
Ɗan zaro ido tayi ta ce “Gobe kuma?”
“Kefa kin cika tsoro, ba a gidana zaki kwana ba, akwai inda zan kaiki ajiya, tunda kika faɗa min halayyar room mates ɗinki naji hankalina bai kwanta dana barki tare dasu ba, dan haka zuwa gobe zamu zo kiyi sign out ki bar nan ki koma can wani gurin da ban, inda zaki riƙa ganin ƴan Nigeria”
“Wow ƴan Nigeria? Kuma musulmai?”
“Eh mana, amma sai kin cire tsoro kuma kin saka a ranki ba zan taɓa cutar dake ba”
Kai kawai ta gyaɗa.
“Muje ga mota can”
Tare suka jera har bakin motar, shiya buɗe mata ta shiga sannan ya rufe ya zagaya ya shiga.

Driving yake a hankali, ya kunna cool music yana tashi kaɗan a cikin motar.
Jin shiru yayi yawa ya sakashi faɗin “Wannan motar a gurin aiki aka bani kyautarta saboda ƙwazona, da kullum taxi nake hawa, sannan gidan da nake zaune ma su suka bani.”
“Kenan nima idan na gama karatu zan iya samun aiki anan?” Tayi tambayar tana kallonshi.
“Eh mana, muddin kika samu kyakykyawan sakamako to za su riƙeki”
“To Allah yasa na samu”
Shiru yayi bai ce mata komai ba.
“Ya baka ce amin ba?”
“Amatul-ahad ke macece, nafi son kiyi aure da zarar kin gama karatu”
“To ai ina fatan samun miji anan”
“A’a nafi so ki zauna a Nigeria ki samu miji a ƙasarki kiyi aure a ƙasarki hakan yafi”
Shiru tayi bata ce komai ba, ya ɗan kalleta yaga yanayinta ya sauya.
“Ya kika ɓata rai dan na miki fatan alkhairi”
“Ni fa rayuwar can bata burgeni nafi son nan”
“Tunda anan kika tashi zaki fi son nan mana, amma can ɗin dai yafi.” A dai-dai lokacin ya faka motarshi harabar wani estate.
Fitowa sukayi, yana gaba tana biye dashi, har suka ƙarasa flat 6. Hannu ya saka ya taɓa door bell suka tsaya.
Wani matashin bature ne ya buɗe ƙofar, jikinsa duk tattoo, daga shi sai gajeran wando. Kallon mamaki Fauwaz yake masa, yayinda daga ciki ya jiyo muryar Manal tana faɗin “Baby waye yazo” da harshen turanci.
“Wani matashine tare da wata amma ni ban gane su ba” ya mayar mata da amsa.

Tana fitowa taga Fauwaz, aikuwa hankali a tashe ta ce “Fauwaz, meya kawo ka gidan nan? Na san baka zuwa a wannan lokaci,”
“Shiyasa kike sheƙe ayarki ko?”
“Fauwaz….”
“Dakata, baki da abinda za ki faɗa min na yarda dake, domin dubunki ce ta cika” Ya kalli Amatul-ahad ya ce “Muje” Duk wannan maganar da suke cikin harshen turanci sukeyinta.
Manal biyoshi tayi amma ya daka mata tsawa, ba ita ba, har Amatul-ahad sai da ta tsorata. Ya gargaɗi Manal da kada ta sake zuwa inda yake.

Suna shiga mota ya ɗora kanshi a jikin sitiyari, Amatul-ahad kallonshi kawai take ta kasa magana, ita tsoronshi ne ya kamata tun lokacin da yayiwa Manal tsawa.

Ganin sun fi minti biyar a haka ya saka ta ce “Kayi haƙuri…” Ɗago kai yayi ya zuba mata sexy eyes ɗinsa da suka gama rinewa, ta tsorata sosai, dan haka tayi ƙasa da kanta.
_Meye tsakaninsu?_ Shine abinda ta tambayi zuciyarta.

Da gudu ya fizgi motar suka bar gurin, gudu yake sheƙawa akan titi, yayinda take ta addu’a Allah ya saukesu lafiya, tana ta salati a zuciyarta.
Ganin abin nashi ba mai ƙarewa bane ya saka ta fashe da kuka a fili. Sassauta gudun yayi a hankali ya parker a bakin titi.

“Ya kake gudu da mota kamar a cikin game, so kake ka kashemu?”
“Na fara fita a hayyacina Amatu”
Ba ta kallonshi dan ta san idan ta kalleshi za ta ƙara tsorata ne.
“Amma wannan abin shine zai saka ka nemi halakamu, akan mace?”
Shaƙo wuyanta yayi cikin ɓacin rai…..

Kada ku manta kuyi SUBSCRIBE na youtube channel ɗinmu wato *KARAMCI TV*

Leave a Comment

error: Content is protected !!