Hausa Novels

Zaiba Hausa Novel Complete

Zaiba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

Tag: Zaiba Hausa Novel Complete

 

Littafin Mace Guda Daya Tak

Matashin saurayine sanye da kayan yan bautar kasa (N. Y. S. C) kayan sunyi mutukar yimasa kyau, tsaye yake agaban allo yana yiwa dalibai yan department of sociology lecture din biology, a jami’ar tarayya dake jihar bauchi, kowanne dalibi ya nutsu yana sauraron lecture din domin babu karya malamin akwai iya darasi kuma akwai zakin murya radau,wannan shine shigarsa hall din na 3 ,yauma kamar kullum ya kwashe fiyeda awa 1 yana yimusu lecture akan introduction to biology, kwas kwas sukaji tafiyar takalmi alamun ana shigowa cikin hall din, hankalin kowa yakoma kanta, jiyowa shima yayi yabita da kallo daga sama har kasa, farace sosai dan har yellow take dan tsabar fari, bata da tsayi sosai amma tana da dan jiki, idanuwanta manya ne farare tas,tanada dogon hanci da dan mitsitsin baki, tana sanye da wani pink din leshi da mayafinsa takalmin kafarta kuwa mai dan karen tsinine shima pink hannunta rike da jaka pink colour, kanta tsaye ta nufi inda zata zauna, he! Taji malamin ya fada ko jiyowa batayi ba taci gaba da tafiyarta.

[3/11, 6:16 PM] Ummi A’isha: MACE GUDA DAYA TILO…2⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

Cike da haushi yabi bayanta yasha gabanta tare da nuna mata hanyar fita get out from my class taji yafada, idanuwanta ta bude sosai tafara kallonsa farine tas dogo mai tsananin kyau yana da idanuwa sosai hancinsa tamkar biro kuma yana da yar kiba daidai misali ita kanta tasan yanada kyau kuma ya hadu kallon banza ta wurga masa tare da Jan wani dogon tsaki, mamaki ne ya kamashi dan babu macen da ta taba yi masa tsaki sai wannan yarinyar yar rainin hankali, tsawa ya daka mata yace who are you dazaki shigo min class yanzu? Me kike takama dashi? Ke yar gidan uban waye? Gaba daya ajin yayi tsit kowa ya zuba ido yana kallonsu domin idan da sabo to sun gama sabawa da halin wannan dalibar wani mugun kallo ya bita dashi sannam yace oya carry your legs and get out from my class tun kafin na wulakanta ki, ni banma taba ganin wannan fuskar taki acikin class dina ba, ita kuwa gaba daya bakin cikin duniya yagama rufeta batare da tace masa ko kala ba tajuya tafice daga cikin hall din zuciyarta cike da bacin rai, lalle gayen nan yau xan nuna masa ko ni wacece zaisan dani da sauran matan da yasaba yiwa wulakanci akwai banbanci ayau sai naga waye ubansa a kasar nan.

[3/11, 6:18 PM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO

 

3⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

Karanta Littafin Kuruciya Hausa Novel

Dawowa yayi yahau kan step din yaci gaba da lecture din daya keyi, Director din makarantar ne yashigo cikin hall din shida mukarrabansa nan da nan idon kowa ya koma kansu wanda ciki harda shi kansa malamin, dasauri director din yazo gabansa yana cewa me yahadaka da wannan yarinyar junaida mukhtar? Kasan ko wacece ita? Bude baki copper din yayi tareda niyyar yin magana amma cikin tsawa director din ya katse shi tare da cewa look Lamin kaifa ba staff dinmu bane service kawai kazo yi dan haka mun dakatar dakai daga wannan aikin,yanzu ka biyoni office inada magana dakai yana kaiwa nan ya juya yafita shida wadanda suka rakoshi, ajin kuwa tsit kakeji kamar ruwa yacisu shi kuwa malamin wanda aka kira da lamin kayansa yashiga tattarawa ya rufe laptop dinsa ya saka acikin jakarta ya yiwa daliban sallama wadanda akalla zasu kai kimanin dari biyu kasancewar combined lecture ne

[3/11, 6:22 PM] Ummi A’isha: MACE GUDA DAYA TILO

 

4⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

Gaba daya yan ajin jikinsu yayi sanyi domin wannan bashine karo na farko da dalibar tayi sanadiyyar korar malaman makarantar ba, ahankali ya gama hada kayansa cikin jakar ya dauka ya rataya akafadarsa ya sauko ya futa daga cikin hall din, yana fita hall din ya cika da surutun daliban dake ciki, wasu tausaya masa suke wasu kuma bakin cikin tafiyarsa suke yayinda wasu kuma suke Allah wadai da halin wannan dalibar mai suna junaida mukhtar. Kansa tsaye ya nufi admin block,office din director ya shiga suna zaune shida students affairs da registerer da hed of department can gefe kuma wannan kyakkyawar yarinyar ce zaune tana kallonsa, da sallama yashiga suka amsa tareda nuna masa kujerar da zai zauna, yana zama director yafara balbale shi da fada tareda cewa yazama dole kabata hakuri kuma ka nemi afuwarta akan abinda yafaru dazu baki ya bude cike da mamaki wai shine zai bawa wannan yarinyar hakuri instead ace itace zata nemi afuwarshi kallo yabisu dashi daya bayan daya sannan yace impossible yaza ayi ace nine zan bata hakuri bayan itace tayi min laifi? Head of department ne ya katse shi ta hanyar cewa kasan yar gidan waye kuwa? Ko yar gidan waye wlhi bazan bata hakuri ba kallonsa suka farayi cike da mamaki director yace to ai kuwa tunda bazaka bata hakuri ba yazama dole kabar makarantar nan ayau.

[3/11, 6:23 PM] Ummi A’isha: MACE GUDA DAYA TILO

 

5⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

Mamakine karara ya bayyana akan fuskarsa domin kuwa babu dalilin da zaisa akoreshi akan kawai ya hukunta dalibarsa wacce ta karya dokarsa, wata xungureriyar takarda director ya miko masa yace gashi ka zaba acikin biyu nafarko ko kabawa junaida hakuri ko kuma ayau dinnan ka bar mana makarantar nan domin bazamu zuba maka ido ka yimana sanadin aikinmu ba, wannan yarinyar babanta shine permanent secretary na education kuma shine Head of service na wannan state din dan haka kazabi daya, shiru lamin yayi yana tunani wato dan babanta ne head of service shikenan sai ta raina mutane? Shi ai ya zata duk wannan kafafar da take babanta ne governor dama head of service ne kawai? Wani guntun tsaki yaja aransa yace lallai nima dan bakusan waye ni ba shiyasa kuke neman wulakanta ni,ni ai ubana yafi nata matsayi tunda secretary to the state government ne kaf state dinmu ubana shine na 3 daga governor sai deputy sai ubana amma ban taba nunawa ba registerer ne ya katse masa tunani ta hanyar cewa lamin kaifa muke jira kayi magana kallonsu yayi sannan ya juya ya kalli yarinyar yace wlhi bata isa nabata hakuri ba nazabi barin makarantar, takardar ya karba ya tashi yafita daga cikin office din ya nufi motarsa wadda ke ajiye awurin da aka tanada domin ajiye motoci.

[3/22, 7:56 PM] Ummi A’isha🏻: [3/15, 7:05 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO

 

6⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

 

Motarsa kirar Toyota corolla yabude ya shiga ya fita daga cikin makarantar ,gudu yake shararawa sosai kamar wadda zai tashi sama yafita daga garin bauchi ya nufi birnin yola. Karfe 3 dai dai yashiga cikin yola Chief olusegun obasanjo housing estate ya nufa, ahankali yake tukin har ya iso tangamemen gidan nasu wanda yake cikin jerin gwanon gidajen, hon yayi mai gadi ya bude masa gate din yashiga cikin gidan securities sai daga masa hannu suke yi ajiye motar yayi a muhallinsa sannan ya tasamma cikin gidan, babban falon gidan ya shiga daya daga cikin kannenshi ya hango kwance cikin luntsumemiyar kujera tana kallon Indian film sallama yayi dasauri ta dago tana cewa oyoyo yaya lamin karasowa ciki yayi yana cewa wacece? Hasna ce ko husna? Murmushi itama tayi tace yaya kenan wai kai meyasa baka ganemu? Dariya yayi mata sannan yace to mummy da daddy ma basa ganeku balle ni da bani na haifeku ba dariyar itama tayi sannan tace to husna ce hasna na kitchen tana yimana fried indomie murmushi yayi yace sarakan kwadayi kenan ina mummy? Mummy tana side din dad tabashi amsa mikewa yayi ya nufi side dinshi.

[3/15, 7:08 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO

 

7⃣

 

Na UMMI A’ISHA

 

Dakinsa yashiga ya zauna ya zubawa carpet din dake malale acikin dakin ido, tunanin matakin da zai dauka akan wannan yarinyar shin me take takama dashi? Yanzu kenan duk burin da ya dauka ya rushe? Babban burinsa shine yayi lecturing lokacin service dinsa domin yana kaunar koyarwa a jami’a amma yau gashi wata MACE GUDA DAYA TILo tayi masa sanadi ta rusa masa duk budget dinsa ai kuwa yazama tilas ya rama wannan wulakancin da tayi masa da wannan shawara ya tashi ya shiga hadadden toilet dinsa yayi wanka ya fito yashirya cikin wata green din t shirt mai hoton heart ajiki sai blue din jeans ya taje sumar kansa ya fesa turaren smart collection ya fito, falon mummynsa ya wuce yana shiga ya tarar da ita zaune cikin kawatacciyar shiga tana waya gefenta yan biyunta ne zqune suna cin indomie,kusa dasu yaje yazauna yana fadin hasna kin gama girkin dasauri kanwar tasa ta kalleshi tana fadin lah yaya lamin yaushe ka dawo? Ban jima da dawowa ba ya bata amsa dai dai lokacin mummyn tasu ta gama wayar ta kalleshi tana cewa babana saukar yaushe? Wlh dazu nadawo mummy daddy yana gari kuwa? Kallonsa tayi tace bakuyi waya bane? Dazun nan yadawo daga Holland kaje ka sameshi yana falo mikewa yayi ya nufi falon mahaifin nasa.

[3/15, 7:12 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO

 

8⃣

 

Na UMMI A’ISHA

 

 

Ahankali yake ratsa falikan har ya isa na mahaifin nasa ya sameshi zaune yana hutawa sallama yayi masa sannan ya nemi wuri ya zauna yafara gaida shi cikin murmushi mahaifin nasa ya amsa sannan yace lamin har kadawo daga bauchin? Jikinsa asanyaye yace dady sun sallameni sunce sai dai naje wani wurin nayi service din kallonsa mahaifin nasa yayi sannan yace laifin me kayi musu? Kansa ya sunkuyar kasa sannan yace babu laifin komai daddy to yanzu ya zakayi? Ya tambayeshi dama daddy cewa nayi yanzu zan koma can N. Y. S. C Secretariat din na sanar musu inyaso sai ayi posting dina Bayero university kano ina ganin hakan zaifi, to shikenan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi mahaifin nasa yace dashi amin ya amsa sannan yatashi ya fita daga cikin falon. Ita kuwa junaida tana tashi daga office din director tashiga sabuwar motarta kia 1 door ta nufi gidansu dake unguwar area 7 tana isa ta wuce dakinta ta jefar da jakarta, mayafinta, takalminta, wayarta ta haye gadonta ta kwanta rufe idonta keda wuya tafara ganin wannan saurayin matashin yana yimata gizo gaskiya babu karya ya hadu zuciyarta taji tafara dukan uku uku kamar zata tsage, idanuwanta ta bude sannan ta mayar ta rufe still shi din dai take gani lokacin da yake yayyafa mata masifa acikin hall din.

[3/15, 7:13 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO

 

9⃣

 

Na UMMI A’ISHA

 

 

Zaune ta tashi cikin sauri, Fara zagaya cikin dakin nata tayi sannan ta saki wani kayataccen murmushi toilet ta shiga ta silla wanka sannan ta fito ta sanya wata doguwar riga ta shan iska ta nufi falo acan ta hango mahaifiyarta zaune tana kallo karasawa tayi cike da shagwaba ta fada kan cinyarta tana cewa umma nifa yunwa nake ji dasauri takalleta tace haba autana me yasa kike son zama da yunwa kira tafara kwallawa daya daga cikin yan aikin gidan dagudu ta runtumo tazo ta durkusa agabansu kallon junada ta yi tace auta me zaki ci?? A yangance tace ta dafa min indomie with egg da sauri mai aikin ta tashi ta nufi kitchen domin aiwatar da abinda aka sata ita kuma taci gaba da zubawa uwar shagwaba.

[3/15, 7:15 AM] Ummi A’isha: MACE GUDA DAYA TILO..

 

1⃣0⃣

 

Na UMMI A’ISHA

 

Tun da sassafe lamin ya baro garin Adamawa ya nufi bauchi gudu yake babu kakkautawa ya kure A. C din motar ya kunna wakar no one be like you yana saurare amma acan kasan ransa kuwa abinda zai aiwatar kawai yake tunani. Karfe takwas ya shiga cikin bauchi dan haka wani guest house ya zarce inda zai huta. Sai 10 ya fito yashiga cikin garin kofar jami’ar yaje ya yi packing yana ganin shige da ficen daliban yana nan xaune acikin motarsa ya rurrufe glass din wanda ya kasance mai mutukar duhu ne na waje baya ganin na ciki sai na cikine ke hango na waje, wata mota pink colour ya hango tana tahowa kirar new discussion R888 sai datazo saitinsa sannan yaga ashe wannan yarinyarce junada aciki tasha ado tamkar wata sarauniya komai blue nan da nan ta kutsa kan motar tata cikin makarantar shi kuwa murmushin mugunta yayi tareda fadin yarinya kin tabo gidan rina dan haka zaki yi bayani.

[3/22, 7:56 PM] Ummi A’isha🏻: [3/17, 9:52 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..

 

1⃣1⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

Yana nan zaune har ya hango adam dama shi yake jira, Adam daya daga cikin dalibansa ne wanda yafara koya musu kuma course mate din junada mukhtar ne shigowa motar adam din yayi sannan yafara gaida lamin ta hanyar cewa morning sir, morning lamin din ya amsa yace dama zuwa nayi kabani duk labarin da kasani akan wannan yarinyar junada mukhtar murmushi Adam yayi sannan yafara bashi labarin. Alhaji mukhtar Magashi shine mahaifinta kuma asalinsu yan garin bauchi ne cikin karamar hukumar Giyade babanta ya rike madafan iko da yawa daga karshe aka bashi mikamin head of service na wannan jahar matarsa 1 da yaransu uku junada ce yar auta sai yayunta maza guda 2 Khalid da Amir, yar gatace ta karshe kasancewar ita kadai ce mace kuma gata yar auta komai daka sani na rayuwa yimata ake bata da wata matsala sai kwaya daya.

[3/17, 9:54 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO…

 

1⃣2⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

Matsalarta shine bata son karatu ko kadan gata shagwababbiya ce ta karshe amma duk da haka mahaifinta yana hukuntata idan ta aikata ba dai dai ba sai dai ita mahaifiyarta tafi batata don bata tsawatar mata idan tayi ba dai ba, tunda muka shigo makarantar nan bata zuwa lecture sai time din data gadama, bata respecting din malamai balle yan uwanta dalibai bata da lokacin tsayawa tayi karatu amma kuma babu malamin da ya isa yabata carry over saboda director yana daure mata gindi, yana iya korar mutum akanta saboda kawai yana jin tsoron kar ta fadawa mahaifinta abashi query bayan kuma shi mahaifinta ba irin wadannan mutanen bane masu zarmewa akan yayansu, ka ganta nan har muka shiga level 300 bata taba samun carry over ba alhalin kuma ba karatun takeyi ba. Wani matashin murmushi lamin yayi tabbas yanzu ya samu hanyar da zai rama abunda tayi masa ta hanya mai sauki juyawa yayi ga Adam yayi masa godiya sannan ya yi masa sallama yatashi motarsa ya bar wurin, garin kano ya nufa yana tafe yana nishadi ya kunna wakar you are my African queen ahaka har ya isa B. U. K.

[3/17, 9:56 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..

 

1⃣3⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

 

Yana isa ya kai takardunsa cikin sa’a sukayi accepting dinsa musamman ma da suka ga cewar ba a Nigeria yayi karatunsa ba a Malaysia yake yi, psychology department suka turashi suka bashi yan level 100 inda zai daukesu Biology, sati 1 suka bashi tareda bashi inda zai zauna amma bai karbi masaukin ba kasancewar yanada inda zai zauna. Karfe 4 yagama abinda zaiyi yabar cikin makarantar ya nufi yola. Bai isa garin yola ba sai kimanin karfe 7 nadare yana zuwa mahaifinsa ma na karasowa dan haka cikin gidan ya shiga yajira karasowar mahaifin nashi wanda bodyguard dinsa suka ysnyameshi kamar wanda za adauke,da fara’arsa ya tari dan nasa yana fadin tafiya tayi sauri my son dafatan andace? Murmushi yayi sannan yace yes dad sunyi accepting dina dafa kafadarsa uban yayi tareda jan hannunsa suka jera suna tafiya tamkar wasu abokai har suka karasa cikin falon uban sannan shi lamin din ya juya ya wuce side din mummy yana shiga ya tarar da babban yayansa yana zaune yana cin abinci akan dinning wajensa yakarasa yabashi hannu suka gaisa sannan shima ya nemi wuri ya zauna yace broz nabar bauchi university fa na koma kano murmushi yayan nasa yayi wanda suke mutukar kama amma shi bakine sabanin lamin wanda yake fari sol, dubansa yayi yace to nidai ina baka shawara wlhi babu kai babu yan matan jami’a, dan nasan halinka da shegen neman mata.

[3/17, 9:59 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO…

 

1⃣4⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

Kai ko tsoron Allah bakaji balle tsoron wadannan cutukan na zamani, rai lamin yabata sannan yace kaifa kanada takurawa wlh shigowar mahaifiyarsu ne yasashi yin shiru domin baya son taji zancen da yakeyi kasancewar yanada yakinin duk gidan babu wanda yasan yana neman mata in banda yayan nasa cikeda murna tace sannu babana shima cikin sigar shagwaba yace yawwa mummy dama nazo miki da wani albishir murmushi tayi tace to Allah yasa alkhairi ne ai kuwa mummy alkhairi ne kuma nasan zakiyi farin ciki sosai kallonsa suka tsaya yi itada yayan nasa tace to fadi inji cikin farin ciki yace na samo matar aure a bauchi dan haka kisanar da dad aje a tambayo min domin aure nake so, wani farin cikine ya lullube uwar tace to Allah yasa albarka kuma naji dadi bayan kagama karatu za ayi bikin? Dasauri yace no nanda 3 months nake so ayi cikin mamaki tace to zai yiwu ahada da na abdulrahman yayankane? Yes mum haka nake so ayi cikin fara’a tace to Allah ya yarda tatashi ta fita daga cikin falon. Yayansa ne ya kalleshi yace ai gara kayi auren yafi maka amma kana yaronka dakai sai jarabar mata just 26 years? Koni da nake 29 bana bin mata sai kai? Cikin kunkuni lamin ya mike yabar cikin falon ya nufi side dinshi aransa kuwa fadi yake wannan dinma da zanyi ai na ramuwar gayya zanyi bana Allah bane.

[3/17, 10:00 AM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO…

 

1⃣5⃣

 

Na UMMI A’ISHA

 

Yana shiga hadaden dakinsa wanda ya kawatu mutuka da kayan alatun more rayuwa ya fada saman gado ya jawo wayarsa BlackBerry B210 Vicky yakira daya daga cikin yanmatansa ringing 2 ta dauka cikin harshen turanci tafara gaida shi murmushi yayi yace nayi missing dinki daga can kamar zatayi kuka tace nafika damuwa da rashinka kusa dani yanzu yaushe zakazo? Silin din dakin ya kurawa ido yace gaskiya Vicky zaki dade baki ganni ba amma next week zan shigo kano to idan nazo i will call you murmushi tayi tace ok sai najika i luv you, luv you too ya amsa mata ya ajiye wayar ko minti 2 ba ayiba wayar tasa tasoma ruri hannu ya mika ya dauko yana dubawa yaga Jenifer ce cikin murmushi yaje hello madam j how are you? Daga can ta amsa da fine my Prince.

[3/22, 7:56 PM] Ummi A’isha🏻: [3/22, 4:21 PM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..

 

1⃣6⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

Kamar zata saka kuka tace yaushe zamu hadu? Wani malalacin murmushi yayi sannan yace very soon but yanzu ina yola ne kin san babu halin kizo amma idan nasamu time zanzo dakaina cike da jin dadi tace to ina jiranka i love you me too yabata amsa ya kife wayar. Daya wayar tashi ce ta soma kara ya dauka ya duba sunan Mary yaga ajikin screen din cikin sauri ya daga yace hello my Mary yakike? Daga can tace abnormal murmushi ya aika mata dashi yace what’s wrong? Cikin shesshekar kuka tace kamanta dani kwana biyu baka nemana rarrashinta yafara yi domin duk cikin yanmatan sa itace star yafi ji da ita domin Mary akwai kyau ga diri shiyasa ma yafi sonta fiyeda sauran dakyar ya samu ya lallasheta tadaina kukan sannan yayi mata alqawarin zai tura mata kudi ta account dinta sai ta yanki ticket din jirgi daga Lagos tazo kano ta sameshi saida yayi da gaske sannan ta hakura sukayi sallama yana ajiye wayar yaga yayansa daga bakin kofa yana tsaye yana kallonsa fuskarsa babu walwala yace lamin abinda kakeyi baka kyautawa wai kai me yayan arnan nan suke baka ne ka manne musu? Wlh kaji tsoron Allah dan babu mamaki yanzu yana fushi dakai kuma inajin ma har giya kana sha sai asannan lamin yayi magana yace ni babu abinda nake sha nasan dai ina neman mata amma bana shan ko sigari balle giya.

[3/22, 4:22 PM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO…

 

1⃣7⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

Harara ya wurga masa sannan yace kalli lips dinka yadda sukayi ja ahaka xakace min baka shan giya na yarda? Kallonsa yayi yace yaya sai dai idan sharri zaka yimin amma wlh bana shan giya hararsa ya kuma yi yace kaji dashi dai ya juya yayi ficewarsa shi kuwa lamin tashi yayi ya shiga toilet domin watsa ruwa. Abangaren junada kuwa tun ranar data sa aka kori lamin duniya tayi mata zafi domin ta tsinci kanta dumu dumu cikin kaunarsa gashi bata san a inda yake ba bare tasa anemo mata shi, yauma ranta abace ta shirya cikin wani brown din material ta nufi sch amma sam zuciyarta babu dadi gaba daya ranta abace yake kuma ko yaya ta rufe idanuwanta shi take gani abinda yafi tsaya mata arai shine yadda kullum sai tayi mafarkin kyakkyawar fuskarshi, ranta ajagule ta fito daga dakinta ko ummarta bata yiwa sallama ba ta fita sabuwar motarta Prado baka ta dauka ta nufi makarantar zuciyarta cike da fatan dama taga wannan matashin saurayin.

[3/22, 4:24 PM] Ummi A’isha: MACE GUDA DAYA TILO…

 

1⃣8⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

 

Da wannan tunanin ta isa cikin makaranta kowa mamakin canjawarta yake tun ranar da abin yafaru bata kara yiwa kowa maganar bacin rai ba sannan yanzu ta daina makara da wuri take zuwa school sabanin da dasai lokacin data gadama kuma babu wanda ya isa ya hanata shiga lecture, ahankali tashiga hall din ta zauna ziciyarta cike da dana sanin fadawa director datayi har aka kori wannan dan bautar kasar da haka tagama sauraron lectures din ta tashi ta tafi gida. Shi kuwa lamin tuni yafara zuwa lecturing a kano B. U. K wani dan madaidaicin gida ya kama a unguwar jan bulo kabuga tuni budurwarsa Vicky ta yi masauki agidan tana tafiya Mary tazo, haka ya rinka sheke ayarsa batare da iyayensa sun sani ba dama ko lokacin da yake Malaysia haka haka yake ajiyesu agidansa daga wannan ta tafi wannan zatazo. Yan matan jami’a kuwa ba acewa komai domin ganinshi kyakkyawa mai class kuma ga kudi nan da nan suka Fara cusa kansu wurinsa sai dai har yanzu babu wadda ta samu shiga domin shi baya harka da hausawa duk yan matansa Christian ne babu musulma ko daya kuma bashida standard budurwa domin bai shirya aure yanzu ba sai auren ramuwar gayya.

[3/22, 4:25 PM] Ummi A’isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO…

 

1⃣9⃣

 

Na

UMMI A’ISHA

 

 

Yau tunda yagama lecture yakoma gida yafara hada kayansa ya gama Mary dake kwance tana bacci yafara tashi dakyar ta tashi tana faman murtsuke ido tana tambayarsa har yadawo eh ya amsa mata sannan yace kitashi ki shirya kitafi sai next week zan dawo kinga yanzu ni nagama shiryawa kamar mai shirin yin kuka tace to sai munyi waya tashi yayi yadau jakarsa yatafi tareda bar mata sallahun idan tagama ta rufe gidan. Karfe 2 na rana ya isa gida mummy yatarar zaune afalo yan biyunta sun zagayeta sai surutu suke mata ganinsa da sukayi yasa suka dan nutsu suna fadin oyoyo yaya harara yabisu da ita yace kunzo kun wani zagayeta kamar wasu kananan yara, ke hasna kin share min dakin dana saki? Dasauri tace yaya bani bace sai dai ko husna cikin sauri itama tace wlh bani bace banza yayi dasu domin dama haka suke masa irin wannan rainin hankalin idan yasa daya aiki to idan batayi ba sun rika cewa wance ce itama dayar tace ba ita bace ,mummy ya kalla yace mummy ina wuni cikin fara’a tace lfy babana kallonta ya sakeyi yace yakukayi da dady akan maganar nan? Dariya tayi tace kaifa kafiya zumudi ai mun gama maganar dashi ashema yar gidan Alh mukhtar magashi ce? Ai tuni dadynku yayi masa magana kuma yace bai mata miji ba dan haka yabaka ita yanzu saura aje ayanke rana, farin ciki ne ya cikashi ya mike ya nufi side dinshi.

4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!