ZALUNCHI HAUSA NOVEL 2021

ZALUNCHI HAUSA NOVEL 2021

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*GUGUWAR ZALUNCI*

PAGE 1 & 2

 

NA

*ZAINAB HABIB (MOM ISLAM)*

 

 

Free page

*Gargaɗi! Gargadi!!! Ban yarda wani ko wata su juyamin littafi ba ta kowace siga ba haƙƙin mallakarsa nawa ne abi doka a zauna lafiya*!

 

 

Bismillahir rahmanir rahim da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai .

 

Ina godiya ga Allah daya bani aron rai da lafiya da kwanciyar hankali har nakai ga fara rubuta wanan littafi mai suna GUGUWAR ZALUNCI ya Allah ina roÆ™onka ka tsaremin hankali na da basirata gurin rubuta alkairi ya Allah ka tsaremin alÆ™alamina da rubuta abinda zai tarwatsa rayuwar jama’a ya Allah ka Æ™ara mana lafiya ka nuna mana Æ™arshe littafinnan lafiya kamar inda ka bani ikon farashi cikin Æ™oshin lpy amen y Allah.

 

 

 

 

 

Aisha Indo Part 

*BIRNIN TARAIYYA ABUJA WUSE TWO.*

 

Anguwa ce mai cike da manyan masu kuɗi ga kuma tsararun gidaje kamar a ƙasar turai .

 

A cikin anguwar akwai wani ƙeraren gida mai kyan gaske gidane daya sami ƙwararun magina masu aiki da ilimi , tun daga wajen gidan zaka gane mai gidan hamshaƙi ne wato Alhaji Sani ana kiransa da Alherin Allah , babban ɗan kasuwa ne sananne a kowace ƙasa kuma kowane fanni yanada kamfanoni da dama dakuma motoci wanan kenan.

daga gefe É—akin mai gadi ne can kuma gefen kudu da arewa shuke shuke ne na wasu kyawawan flowers gwanin sha’awa , ga wasu É—awisu da suke kaiwa suna komowa guwanin birgewa .

Iyalan gidan ne zaune a palon da za’a iya kiransa da aljannar duniya iya tsaruwa ya tsaru nera tayi kuka musamman ma danÆ™ara danÆ™aran kujerun da suka mamaye palon ,wata farar mata ce zaune a É—aya daga cikin jerin kujeru sai wasu Æ´an mata su biyu masu kama da ita amma sun fita haske matashiyar matar ce ta dubi É—aya daga cikin Æ´an matan tace “Diyana zakuyi dare fa kinga har yanzu dadynku bai fito ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wace aka kira da Diyana ce ta taÉ“e baki tare da lumshe fararen idanunta masu É—auke da zara zaran gashin gira tace “mom ni dama bason zuwa Æ™auyen nan nakeyi ba dady ne ya matsa mini wai nice banison zuwa duk cikinmu ,

Budurwar dake gefe ce ta dubi momy fuskarta da alamun É“acin rai tace ” mom village É—innan ya cika sauro gakuma rashin tsafta ,

Diyana ce tace ” good Afreeda ashe kin gane ,jin maganar tasu zatayi yawa ne momy tace ” shiii alamar suyi shiru dan tajiyo takun mai gidan nata ,

ƙarasowa yayi da shiga ta alfarma a jikinsa shadda ce gezna fara wace tasha aiki , momy ce take ƙare masa kallo da murmishi a fuskarta shima mayar mata yayi tare da kallon su Diyana da Afreeda da hankalinsu ke kan wayar dake hanunsu ,

Dady ne yace ” to nagama so ke nake jira rau rau Diyana tayi da ido tana kallon mom ganin batace mata komai ba yasata miÆ™ewa tana bubuga Æ™afa Afreeda na dariya Æ™asa Æ™asa ,

Dan tasan ita zata iya jure wuyar ƙauyennan amma Diyana kam tana tausaya mata, dady waje yayi dan shima ba mai son yawan magana bane kamar mom ,

Hand bag É—inta Afreeda ta É—auko mata tare da wata jaka mai kyau da alamu itace jakar kayan nata ,

mom ce ta miÆ™e ta nufi step É—in dake tsakiyar palon bata É—au lokaci ba sai gata ta fito da wato leda fara Æ´ar baba ta miÆ™awa Diyana , buÉ—ewa Diyana tayi taga su man shafawa ne masu tsada dakuma takalma harda atamfa itama mai tsada kana ga turaruka , taÉ“e baki Diyana tayi tace “mom wanan kayan wa za’a kaiwa granny É—inku taÉ“É“ hmm Diyana tasa kai ba tare da takuma cewa komai ba ,

See also  Jidda Hausa Novel Download

Jerowa sukayi tare da Afreeda idan kaga yanayin tafiyarsu kai kace Æ´aÆ´an sarakuna ,

Fuskar Diyana babu fara’a kasancewar dady na cikin mota yana waya hakan ya basu damar yin magana , Afreeda ce tace “Anty Diyana saifa kin daure da mutanen village É—innan dan lokacin da mukaje wlh cemin sukeyi anyi jar fata tashigo Æ™auye kokuma sudinga bina suna kallo na ,

 

 

 

 

 

 

 

 

Auren Lagos

Dafe kai Diyana tayi kana tace ” nashiga uku nikam nima haka zasuyimin ? har Afreeda zata yimata magana dady ‘ ya katsesu zo mu tafi ,

dady na back side ita kuma ta shige gaba dan batason zama kusa dashi kasancewar ba tun yanzu ba ya hanasu chart eyepice tasa a kunnen ta kana ta jingina kanta da kujera ta lumshe ido driver na shiga suka ɗauki hanyar ƙauye .

 

*KANO. ƘAUYEN SHAFA*

Ƙauye ne mai gidaje jifa jifa dakuma mutane iri iri yawancin gidaje nasu duk rufin ɗakin anyishi ne da jinka basu damu dayin katangu ba wasu kuma sunayi kana babu ginin siminti sai a wani gida dake gefe shi kaɗai .

 

Bacci mai daɗi ne ya ɗauki Diyana dady kam hankalinshi na hanya dan sun shiga kano a halin yanzu ma hanyar ƙauyen suka dosa , wata irin gargada suka shiga wace tayi nasarar farkawar Diyana a tsorace ihu ne kawai bata kurma ba ga mumunan faɗuwar gaba ,

Ƙarewa Æ™auyakun kallo tashiga yi tana salati badai nan ne kauyen ba taÉ“É“ gashi dady yace ” 5 days zanyi ina bazan iya ba , duk cikin zuciyarta take wanan maganar jin anyi parking yasata É—ago kai tare da juyawa ta kalli dady dake tattara wayoyinsa a kan siddin motar dady har mun iso ne ?” yes daughter yau zakiga granny É—inki , yana maganar da murmishi a fuskarsa,

driver ne ya fito ya buɗewa dady mota kana ya buɗewa Diyana , a tare suka fito daga motar hanunta riƙe da wayoyinta guda biyu tabi bayan dadyn ,

Daga bakin Æ™ofa dady yai sallama jin muryar wata tsohuwa yasa Diyana waro ido dan ganin wacce mata ce zata fito ?”.

Wata tsohuwar mata ce fuskarta taÉ—an tamushe haÆ™oranta sunji jiki tsabar cin goro tasa riga da zani dakuma É—ankwalin yadi barka da zuwa Alhaji tanata faÉ—aÉ—a fara’arta ywwa Hajiya , Hajiya ce tace ” to kuzo mushiga jikalle ansha hanya ta dubi Diyana ,

Yamutsa fuska Diyana tayi batare da tace ” komai ba suka shige ciki .

Tsakar gidan da yaji siminti fess yake a share ko tsinke babu amma hakan bai sa Diyana dena yatsina fuska ba tana tattare kayanta wai karsu ja Æ™asa , shiga cikin É—akin sukayi da yake malale da leda babu kujera sai Æ´ar tuguno Hajiya ta miÆ™awa Diyana batare da tayi magana ba ta karÉ“a ,Hajiya ce tace ” Alhaji a ina ka samo wanan Æ´ar gwallin ?”dan naga kamar ba wannan bace da ta taÉ“a zuwa shekarun baya ?.

Kawar da zancen dady yayi ta hanyar durÆ™usawa yace ” Hajiya bamu gaisa ba ina wuni washe baki Hajiya tayi tace” lafiya lao Alhaji ya aiki ya hidima yakuma FaÉ—imatun buÉ—e baki Diyana tayi cikin zuciyarta tace ” waye FaÉ—imatun komai sai an É“atawa mutum suna mom ce FaÉ—imatu taÉ“É“ ,

Dady ne yace ” tana gaisheki Diyana ce ta kalli driver tace ” kaje motor ka É—auko wata farar leda ka kawo min , to driver yace ” cikin rawar jiki ya fice Hajiya ce ta miÆ™e ta fita sai gatanan da kwanon fura da nono a wani baban kwanon silba da suga a leda dakuma ludayi ,

See also  Izzar So Hausa Novels Story

Tunda Hajiya ta shigo da nonon Diyana take keÉ“e baki dan inba na kanti ba batashan wanan , driver ne ya dawo hanunshi riÆ™e da ledar ya durÆ™usa yace ” ranki shi daÉ—e gashi karÉ“a tayi ta ajiyesu gaban Hajiya batayi magana ba , kallonta kawai Hajiya takeyi dan a bisa dukka halamu jininsu bai haÉ—u da Diyana ba , dady ma ya lura da rashin sakewarta dama yasan halin abarsa ko anyi abinci a gida bataci inba tayi ra’ayi ba drinks sune kayan shanta sai cake da shauransu .

 

Alhaji nayima magana a inaka samo wanan yarinyar mai kamada aljana kayimin kunen uwar shegu ko ? dady ne yace “Hajiya Diyana ce fa ko kin manta ta yayar Afreeda ,kaji ai kusawa yara sunan mutunci bazaku sa ba sai wani suna mai kamada na biririka ,dariya ce taso kuÉ“ucewa Diyana amma ta make , miÆ™awa dady haÉ—in furar tayi kana ta miÆ™awa driver dake zaune can gefe a tabarma takuma ajiyewa Diyana a gabanta yatsina fuska Diyana tayi kana tace “I dont like this thing dady ta miÆ™e tana tari , la haula wala Æ™uwata illabillah Hjiya take ta mai maitawa tana tafa hannu ta dubi Alhaji tace ” mudai bamu É—auko wanan mugun halin ba gaskiya É—ayar Æ´ar uwarta tafi daÉ—in sha’ani ,

Nikam yaushe zamu jitu da wanan mai kamada zabiyoyin chaɓɗijan ,

Diyana dai na zaune dan hankalinta na kan wayarta maganar da taji dady nayi ne yasa ta juyo a tsorace ” zaku jitu ita da zata yimiki sati ,

Washe baki Hajiya tayi tace “aiko dana sami Æ´a suka haÉ—a ido da Hajiya Diyana ta sakar mata harara ,

Dady ne ya kalli Diyana yace ” wai kin mance gurin wacce nace miki zanzo ne ?” wanan fa da kike gani mahaifiyata ce walh zan saÉ“a miki , Diyana dai kanta na Æ™asa ba ma’abociyar surutu bace , wata yarinya ce ta shigo da gudu tana cewa kaka yau bazakije itacen bane ? Hajiya dake shan rahowar furar da dady ya rage tace ” nayi baÆ™i jeki cewa mamanki Alhaji yazo to yarinyar tace ” kana ta fice da gudu .

Da isarta gidan nasu dake zagaye da dangar kara tafara Æ™walawa mahaifiyar tata kira tana cewa ” Talatu ki fito wanan yayan naki na bini yazo wlh harda baturiya kiyi sauri ,

Talatu dake ɗaki tana fere rogo ta leƙo tare da cewa da gaske kike yi tinene eh ? yasin kizo zaki ganhi harda baturiya ,

Yafo gyale talatu tayi jiki na rawa ta saka takalmin ta ‘ ta fice ta kwashi sauri dan tasan yau ta warke .

Kasancewar basuda nisa sosai dan danan sai gata a Æ™ofar gidan ganin sabuwar mota ne yasata tabatarwa ,tinene ce ta biyota da gudu tana cewa ” Talatu kinga zahiri ko ga motarhi nan , Æ™arasawa sukayi tayi sallama Hajiya ce ta amsa gimbiya Diyana na sallah a sallayar da ta É—auko a mota ,

Harkin iso Hajiya tace tana washe baki yayanki ne yazo kuma yau ze wuce shine nace “tinene ta kirawo ki , Talatu na fama da susar kai tace ” ai ganinan Inna ina yaje ne ? Hajiya ce tace?yaje sallah ai ba jimawa zaiyi ba yanzu zai dawo,

Talatu ce ta cire mayafin kanta tare da cire É—ankwali tasa hanu biyu tana sosa kanta ,

Hajiya ce ta dubeta tace ” wai talatu har yanzu baki sawa Æ™warÆ™watar magani bane ?dagudu Diyana ta miÆ™e ta daka tsalle sai gata a waje , shigowar dady ne yasata sunkuyar da kai tace “sannu da dawowa dady ywwa daughter lafiya na ganki a nan ?” kafin tayi magana Hajiya tace ” uwarta Talatu take gudu dady ne yace ” to maiya faru ? Diyana idanunta cike da hawaye tace ” Dady ka tafi dani wlh bazan iya zama a nan garin ba ,

See also  Yar Gado Hausa Novel Complete

 

Kinci gidanku dady ya cewa Diyana , ya shige É—akin Hajiya washe haÆ™ora Talatu tayi tace ” yaya hannu da zuwa kunsha hanya , wlh kuwa ya yara ? lafiyansu lau Alhaji ya hidimomi mungode fa , babu komai Alhaji yace ” yana kallon tinene wanan Æ´ar gurin waye ?, Hajiya ce tace ” É—iyar Talatu ce fa gatanan kamar ka kifeta da kwando ga guru gurun idanuwa kamar na waccan ta wajen ,

 

Kwashewa da dariya sukayi Alhaji ya miÆ™e yace “toni zan tafi Diyana kiramin driver kokuma kice ya kwaso kaya a mota oky tace ” ta fice tare suka shigo da drivern hanunsa É—auke da buhunnan shinkafa da katan É—in taliya da jarkar man gyaÉ—a da maggi da gishiri , dubu arba’in dady ya miÆ™awa Hajiya ita kuma Talatu ya bata dubu ashirin ai kamar an jefata a aljanna tahau zuba godiya tana Æ™arawa ,

Dady ne yace “hajiya nanda wata É—aya zaki dawo ABUJA dan wlh kina kusa abin zai fi ,zaro ido Diyana tayi tana nazarin irin zaman da zasuyi da wanan tsohuwar mai bala’in sa ido amma babu komai da Æ™afarta zata nemi ta dawo Æ™auyensu , hajiya na kuka tana sanyawa dady albarka tare da duk abinda yasa gaba ,

Shigewa cikin palon Diyana tayi tare da É—auko jakarta ta dubi dady zan bika bazan iya zama a nan garin ba cikin É“acin rai dady yace ” anan na girma komai nawa anan yake kaf cikin Æ´aÆ´ana kece mai tsananin Æ™yamar jinina ,to dole ki zauna har sati ya zagayo saboda zumunci abu ne mai Æ™arfi , kuka Diyana takeyi kamar ranta zai fita da ajinta da komai ta zauna a wanan banzan gidan wanda ko É—akin zuba shararsu bai kai ba wajen kyau , niko nace wanan gida da kike rainawa shine Æ™urewa gurin kyau a wanan Æ™auyen ,

20k dady ya bata yace ” to mu mun tafi Hajiya najin duk dramar da sukeyi taÆ™i kulasu Talatu ko tsabar murna har yanzu murmishin fuskarta bai É—auke ba, dady 20k is to shot tana bubuga Æ™afa 5k ya ciro ya daÉ—a mata yana bata haÆ™uri akan zai turo driver ya zo ya É—auketa , Hajiya ce ta matso tana cewa maganar sai kace ta munafurci da wani yare kukeyi dan kar ajiku ko , wlh Alhaji ka sakalta Æ´aÆ´anka da kashe kuÉ—i , dariya dady yasa dan inya biyewa Hajiya bazai tafi yanzu ba , shigewa mota yayi yana É—aga musu hannu ,

Tinene dake gefe tana Æ™arewa Diyana kallo gaskiya kaf cikin Æ™auyenan bata taÉ“a ganin mai kyau irinta ba gaskiya Æ´an binni sunji daÉ—i ko kaushi basuyi bare faso, Hajiya ce tace ” baiwar Allah taso mu higa gida yamma tayi Talatu ce tace ” Hajiya nikam nayi gida yau zamu hyarÉ“i jar miya yasin yaya Sani ya jiÆ™ani da nera ai wlh ko Ado bazan nunawa ba dan yana Æ™yala ido to zai rabani dasu ,

Hajiya ce tace ” harkin gama abincin ne ? a’a wlh ina cikin gyaran rogo he ga tinens tazo kirana wai Alhaji yazo inafa zan gama tinene ce ta kwashe da dariya kana tace ” wayaga kaka a binni yasin sai sun koroki ,

 

Hajiya da haushi ya É—ebeta tace ” cin uwaki niÉ—in bzan iya zama a can É—in bane to kikasa wasa ma dake zani , Diyana ce takuma cika a zuciye ta shige tabarsu anan sunata surkulllen maganarsu….!

 

Kubiyo ni dan jin cigaban labarin ya rayuwar Diyana zata ƙare a ƙauye biya 200 ki karance shi cikin kwanciyar hankali ko kuma ku tuntuɓeni ta wanan lambar 07064551049

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top