Zan Rayu Dake Hausa Novel

11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..馃尮*

馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮

漏 *_Haske Writer’s Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )

*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*

1鈨�

 

Gurin dinner ya cika makil da dunbin jamaa kae da gani kasan bikine na masu naira .yan mata top class ke juyi tsakiyar gurin ….yayin da hall din ke fitar da wani azababben kamshi ..Daga gefe kuwa wasu yan mata ne su biyu ko wace zaune take hankalinta naga wayarta kirar Iphone6 sam hankalinsu baga cikin hall din yake ba … ….

Mc ….ya bukaci babbar aminiyar Amarya yar uwa ga amarya ta fito …

Fitowarta tata ita da Aminiyarta ta saka hall din karadewa da ihu tare da sowa ….

Tana karbar abun maganar gurin yayi tsittt kamar daukewar ruwan sama …

daga gefe kuwa wasu dandazon samarine ke ihu…banda “Feenah” …babu abunda suke fada …..

“Sunana Safeenat Khalid Mudassir” …..ta fada kallon kaf mutanen dake cikin hall din ….kafin ta cigaba da fadin …

“Duk cikin ku nan babu shegen da bai san Engineer Khalid Mudassir ba …!

Hall dinne ya sake karadewa da ihun mutane …tayi tsit ..kafin ta daure fuska tace …

“na dauka bikine na masu naira sai naga abun ya banbanta ga dangin ango ..dan banga alamun akwae arziki a tare da su ba.. kaf dinsu sanye suke da yadin da bai wuce 20 thousand ba ..kuma a haka dan tsabar rainin hankali aka gayyaci Feena? ….

Kanwar ango ta taso a fusace da niyar dauketa da mari don ta gama kuluwa da wulakancin ta …..

Aminiyarta dake kusa da ita tayi saurin rike mata hannu tana hararanta …

wani Ja’irin murmushi Feena ta sake kafin ta aika mata da wani irin kallon tana fadin …”Barta Maryam …ki bar shegiya ubanta ya mutu yana nadamar haihuwarta ….!

Wurgar da ab din tayi sannan tayi gaba abunta ….ishak abokin ango ya tare da murmushi don tunda ta shigo ta tafi da hankalinshi …..

” Excuse me Feenat .!….ya sha gabanta tare da harde hannayensa …

Wani kallo ta zabga mashi kafin tace …”what ”

” Just Few mints Swky …ina son contact dinki please”..ya hade hannayenshi guri guda dauke da murmushi ….

itama murmushin ta sake …tare da zabga mashi mari …tayi gaba tana fadin …”take it boy .”.

Hall din ya dauki ihu …..har ta fice bai saki inda ta mareshi ba …!!!

Bayanshi yaji an dafa tare da fadin ….”Weldon …maganinka kenan .. banga amfanin kula macen da bata san darajar bil’adam ba …next time idan zaka kula wata ka fara duba dressing dinta before …”

Bai jira amsar sa ba ya zagayeshi tare da barin hall din…

Amarya kam banda hawaye babu abunda take ….tayi nadamar gayyatar Feenah gurin taronta duk da ita ce babbar aminiyarta amma batayi tunanin zata mata haka ba …ko ba komae ya kamata ta duba alakar dake tsakaninsu ta yan’uwantaka …….

“Excuse me, ko ma ciki inda na zauna zaka ga hanky ka dauko man trappr dinta a kasa” ..ta fada tare da dalloshi da flash din wayarta …

Yarda motarta bata amsa mata ba haka bai ko kalli inda take ba ya saka hannu da niyar bude motar …

See also  Maimoon Hausa Novel Complete

Ji yayi ta fizge keys din tare wurgar dashi kasa ….” Har ka isa ina maka magana ka wuceni …!! Dan gidan uban waye kae ? ..me kake takama dashi ? …

A fizge ya kalleta ya girgiza kai yana murmushi …ba tare da yace mata komae ba ya dauki keys din ya shige motar ya barta tsaye rike da mamaki …

Har ya tada motar yaji tana fadin “Wawan banza bakauye “…

Da sauri ya ja motarshi ya bar gurin gudun matsala …

A falo ta iske grandmah dinta ta wajen dad …gaidata tayi fuska Murtuk sannan ta bude fridge ta fito da robar swan ta balle marfin tana sha ….

“Safeena manya..ke dae haka halinki yake ” …kakar ta fads tare kallonta tana girgiza kai …

Aunty Fati ta fito daga kitchen rike da katon tray a hannunta ta ajiye kusa da kakar tare da tsiyaya mata lemo a cikin cup ta mika mata…

Kakar tace “sannu Fatima Allah ya biyaki kinji ko ..Allah ya jikan Habiba ….!!

“Ameen” ta fada dauke da fara’a sannan ta kalli feena tana fadin …

“Safeena har an dawo ?

Ba tare da ta kalleta ba tace …”baki so dawowata ba ko ? ..saboda na tsare maki gidan uba ko ? ..ta dago tare da zuba mata ido tana aika mata da kallon da ke kunshe da tsabar raini ..

Kakar tace ..”.kaniyarki Safeena ashe baki da mutunci …matar ubanki kike fadawa wannan maganar ….?

“Uwata ce ? ….ta fada ta Fada a hasale…..

“Ai kanwar uwarki ce mara mutunci …matar da tun kina cikin tsumma ta raineki?.ta goyaki …,ta baki abinci ..ta baki tarbiya …haba safeena ..!

“Ince abincin ubana ke kawowa ? ko daga gidan kaka ta zo dashi ? ..ina jin tun da ya hada mata garan biki bai kuma aiko mata da ko tiyar shinkafa ba ?

 

*FEEDOHM馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [8/24, 8:27 PM] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE…馃尮*

馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮

漏 *_Haske Writer’s Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )

*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*

*this page goings to …Fa’izahbarwa, Safiyya galadanci , Meela Adeel & It’z Ruky….Allah ya barku da Lanto mai dinki ….馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀*

2鈨�

 

Rike baki tayi tana fadin …Safeena!!!

“Kinga grandy …idan gulma ta kawoki gaskia ki tafi …abinci dai na ubanane …Goyo kuma da kike magana ..ta dauko zani taga idan ban goyata ba …tarbiyya kuma ai ba da kudinta ta biya man kudin islamiyya ba …!!ta jefar da robar ruwan tare da shigewa daki abunta …

“Uwaki nace …kaji man ja’iran yarinya to dan ubanki ki zo na balle maki zanina ki goyatan mu gani mara kirki !!

Aunty Fati tace…”kiyi hakuri sae dae Allah ya shirya ….!!

Kaka ta amsa da “Ameen Fatima kina kokari …”

Da sauri tayo baya tare da nuna shi da hannu …”Kaine dan Iskan nan da na aikeka last gurin dinner beebarh kika zuwa ko ?

Da mamaki ya kalleta tare da kauda kai gefe guda yaci gaba da tafiyarshi zai shige cikin falon …

“Wane dan iska ne ya bar wannan abun ya shigo nan gidan” ….ta fada cikin tsawa tare da nuna Abdulmaleek da hannu …

See also  Wayyo Gindina Uncle Hausa Novel

Cak ya tsaya tare da juyowa yana kallonta …kar dae ace wannan yarinyar diyar oga ce …tab Albasa ba tayi halin ruwa ba …..

Wani yaji yana fada mata …”wae Alhaji yace a shigo dashi ..”.

Cigaba yayi da tafiyarshi ya shige falon da sauri ….itama dawowa tayi cikin sauri ta komo cikin gidan …tana bala’i ita kadae …

A babban falo ya iske Alhajin zaune saman kujera …har kasa ya zube yana gaidashi cikin girmamawa ….

Cikin faraa ya amsa mashi yana fadin ya zauna da kyau …girgiza kai yayi tare da dukar da kanshi kasa …

“Abdulmaleek”….Alhajin ya kira sunanshi cikin natsuwa ….

“Naam .”..

“So nake ka baro office ka dawo gidana …Driver dake kai Safeeena unguwa shine ta kora ..ni kuma bana so na ta dinga fita ita kaidai …tunda aikin nan da office din duk dayane …anan ma kafi samun sauki ..tunda akwae boys quarters da zaka zauna wanda zai fi maka sauki …amma sae kayi hakuri da halinta ..na yaba da hankalinka shi yasa ma na nemoka …ina fatan ba matsala ….?

: Zufa ta fara keto mashi ta ko’ina …duk da Ac dake gauraye da. Falon ….a iya saninshi sam yarinyar bata da mutunci duk da sau daya ya taba ganinta ….sannan ko kadan baiyi tunanin itace tayi wannan rashin mutuncin ba …..sannan sam albasa batayi halin ruwa ba saboda mahaifinta mutumin kirki ne …muryar Alhaji ta katse mashi da tunani da yaji yana fadin …

“Kayi Shiru Abdulmaleek ko kafi son zama can ne?

Dagowa yayi a wahale yana fadin ” Ba matsala Alhaji nagode sosse” …shi kanshi bai san abunda yake fada ba

Cikin jin dadi yace “Ameen Abdulmaleek Allah ya maka albarka yaji kan mahaifinka …”

A hankali Alhajin ya juya ga Safeena dake tsaye bakin kofa tare da mika mata hannu ….

Dan takowa tayi har gabanshi ta zauna bisa hannun kujeran da yake zaune ….tana bata fuska

 

*FEEDOHM馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE…馃尮*

馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮

漏 *_Haske Writer’s Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )

*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*

*Devoted to Ummi A’isha馃憣馃徎*

3鈨�

Hannunta ya kamo yana karantar yanayin fuskarta sannan yace “Safeena ga sabon driver nan kullun zai dinga kaiki inda kike bukata Bana son matsala wannan karan Safeena”

“Abbah da wannan abun zanyi yawo?…ta fada a dakile

“Kwarae don na gaji da shashancinki Safeena ki kiyaye ni wallahi bara ta yiyu ki dinga wulakanta duk wanda aka kawo aiki karkashinki ba …AbdulMaleek ba wae yaro kadae na daukeshi ba aa amintaccenane …!!

Mikewa tayi tana bubbuga kafa tare da turo baki ….

“Mene matsalar Safeena? …Abbah ya tambaya tare da mika mata hannu …

“Bana sonshine kawae Abbah last week fa bikin berbah ya raina man hankali ashe ma da motar Abbah na yake tutiya ni dae ……

Katseta yayi yana fadin …”Wuce Safeenah …”

Da Sauri ta fara hawan stair tana gunguni ….Bakin part dinta tayi karo da Aunty Fatee wani sakaran kallo ta watsa mata tare da shigewa daki abunta ….

Bayan ya bar Gida direct gidansu ya nufa …Nana kanwarshi ya iske tsakar gida tana wanke wanke ….

See also  Zuciya Kowa Da Irin Tasa Hausa Novel

“Subhanallah Nana waya baki wannan aikin bayan bakya lafiya? …ya tambaya a rude tare da matsawa kusa da ita …

“Ni ce nan dan Ubanka ko zaka dakeni ne mara mutunci ” ….Inna Sahu ta fito daga dakinta tana fada …

“Me ya kawo na duka kuma Inna? Kawae naga bai dace ba tunda bata lafiya a bata aiki irin haka ..Tashi Nana jeki bara na ida kinji ko !!

“Da kyau Uwarta to bana son nakan banza na mata” ….ta fada a harzuke tare da matsowa kusa da Nana…

Nana tace “Bandee ka barsa na ida kaji ….Allah na warke ”

A harzuke ya juya zaya fita wayarshi ta dau ringing har ta yanke ba dauka ba ….Sae da ya zauna saman dakalin gidan sannan wayar ta sake kara karo na biyu ….Sunan Oga da ya gani ya sa shi ya dae dae ta natsuwarshi tare da daukar wayar …

Oga yaji yana fadin “Abdulmaleek kana lafiya kuwa tun dazo Safeena ke kiranka kazo ka kaita saloon baka dauka ba ?

“Wallahi Alhaji ban lura da kiran bane amma gani nan zuwa ” …ya fada tare da mikewa …

“Ayyah nima abunda na fada mata kenan amma kasan Safeena da rigima ” ….Alhajin ya fada a hankali

Dan murmushi yayi yana fadin …”Afuwan Alhaji gani nan a hanya ”

” Ok” …ya fada tare da yanke wayar …

Missed call din ya buda a tunaninshi zai ga irin kira uku ko biyu amma sae yaga sau daya ta kirashi shine har ta fadawa Abbanta ….”huh” …ya fada tare da gyara mirrow din left hand dinshi ….Cikin mintina 10 ya isa gidan …ga mamakinshi sae ya ganta zaune ita da wani saurayi bisa carpet a harabar gidan don duk tunaninshi zaya iskeshi tana jiranshi amma sai yaga zancenta take hankali kwance …..

Ba wani dalili kawae yaji gabanshi ya fadi ….a sulale ya idasa gurin da suke zaune tare da fadin “Madam gani” a hankali …

Bata kalleshi ba sae dae saurayin ne ya kalleshi ya dauke kai ….yayi tsawon mintina goma kafin ya sake fadin “Madam Gani fa”

“Uwar me zan maka ….”. …ta fada a fusace

Yaji ciwo amma ya daure tare da dai daita fushinshi yana fadin “Oga yace kina kirana ..Sorry ni sam banga lokacin da kika kira wayata ba ”

“Dama taya zaka gani? ..Kwalwa ta tunkushe da tuwan dawa !! ..

Shiru ya mata ba tare da ya kalleta ba …saurayin nata yace “Feenah please ki sallameshi ya zo ya mana tsaye a kai ya bata mana iskar guri !!

“JB Barsa yayi ta tsayuwa idan ya gaji ya tafi don banga uwar da zai man ba yanzu lokacin da na kirashi ai bai zo ba …kawae Abbah ya ja man raini !!!

A hankali ya ja kafafuwanshi zaya fita …sae da ya kai bakin kofa yaji tana fadin ” Maleek ” …

Duk da yana cikin bacin rai hakan bai hanashi jin dadin sunan daga bakinta ba …cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba …

“Ka jira a waje idan na gama zan duba idan da lokaci sae ka kaishi ….”

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top