Hausa Novels

Zargi 1 and 2 Complete Hausa Novel

Zargi 1 and 2 Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Kano state G R A

……..k’was k’was take takowa acikin parlourn” tafito cikin shirinta na d’aukar hankali”tana zuba wani fitinan nan k’amshi.

 

sanye take da riga da siket na kanti”tayafa gyale da zamu iya kira dashi gara babu”siket d’in yakamata sosai ya fito mata da sharf.yyinda rigar me gajeran hannu ce”dg gaban rigar ta bud’e”har ana hango shatin nashanunta dasuka cika rigar…

 

tayi parking bak’in gashinta”da wanda baisaniba zaiyi zaton attached ne..fuskarta tayi light make up bamai hayaniya ba…SALMA kenan da akema lak’abi da ( baby)”yarinya me tashe da gayu”tana tak’ama da kyawunta da iliminta.kallo d’aya zaka mata kasan ta amsa sunanta *classic lady*

Tana rik’e da hand bag nata da key d’in motarta….

 

ummi dake zaune kan kujera ta dubeta tana girgiza kanta”wannan shigar da y’ar tata keyi yana k’ona ranta”fuska a’daure tadubeta tace”.

wato anan ma d’in irin wannan shigar zaki dingayi ko?bazaki yiwa kanki fad’a ba dan Allah baby?yanzunma Ina zakije da wannan shigar?tana turo baki tace”.amma ummi ni miye aibun shigata dan Allah?harara ummi tamata had’e da cewa bansaniba! marar kunyar banza”kina zubar mana da mutunci agari”kinsanfa a *katsina*

haka kike wannan shigar banzar ko?shine anan ma dg dawowarmu shekaran jiya zaki koma da halinki ko?haba ummi”zamaninku daban namu daban”kinsan banwani san garin nan ba”zanje gidansu raudah!ta nunamun gari ne…

dan zakije shine zakiyi irin wannan shigar banzar?”to wlh indai kinason fita kije kisaka hijab koki canza kaya”idan ba hakaba baki zuwa ko Ina…

 

shagwab’e fuska tayi had’e da cewa”nifa ummi wlh ana takurani agidan nan” kinsan ni nafison k’ananun Kaya…

 

gidanku nace marar kunyar banza”sokike alh yadawo yaganki kinfita ahaka yayita fad’a ko?

 

baby batace komai ba ta juya zuwa upstairs”

 

babu jumawa tadawo sanye da hijab har k’asa”ummi na murmushi tace”.yauwa autana kokefa”amma irin wannan shigar da kikeyi beda amfani saikiga wasu namiki wani ZARGI daban…

 

Baby batace komai ba ta fice dg parlourn”

 

tana fitowa ta wuce parking space ta d’auki motarta”saidai tana shiga motar taja tsaki had’e da cire hijab d’in ta yafa mayafinta..

 

Ahankali take driving nata cikin nutsuwa da aji”ta nufi anguwar hotoro”gidan yayan raudah k’awarta.. sbd ita anguwar tafi sani acikin garin kano…

 

*wacece baby*?

 

Alh buhari kurfi!shine mahaifin baby”asalinsa d’an k’auyan kurfine dake jihar KT”danginsa na can shikuma a KT suke da zama da matarsa hjy maryam”amma anmishi transfer agun aikinsa na kwangilar gine gine..yadawo kano da zama shida iyalansa.yanada yara 4″ yaya bilal,yaya Ahmed sai salma(baby)wacce taci sunan mahaifiyar alh buhari…sai k’aninta usman”

 

baby yariny ce y’ar kimanin 24 yrs”ta kammala karatunta a b’angaren pharmacy”bata fara aikiba sai monday mai zuwa”sbd aminin abbanta

*alh nuhu*

 

yasamar mata aiki awata private hospital anan garin kano”baby yarinya ce maison gayu da wayewa”hakan yasa ita aganinta duk shigar dazatayi bata ganin aibun shigar..tanada son saka kaya k’anana..

 

bakuma wai dan batada ilimi ba”ah ah tayi saukar alk’ur’ani mai girma”alokacin dasuke KT da yawa maza namata maganar banza sbd shigar datakeyi”amma bata kulasu,sbd tatsani namiji d’an iska”kusan duk yawanci abinda ke kawo samarin nata kenan…

 

 

Amma ita takasa gane shigar banzar datakeyi kekawo mata hakan”shiyasa har yanzun takasa saurayi tsayayye..

 

Baby Fara ce !amma bacanba”tanada k’ira me d’aukar hankali”yarinyace ita dabata d’aukar raini”tanada hak’uri..amma idan aka tab’ota”wayyo Allah..

 

Abba da Yaya Bilal Babu irin duka da zagin dabasuyi mata ba.sbd tadena amma bata fasawa”idanma ance tasaka hijab data fita zata cire idan tadawo tasaka ta shigo gida.

 

Alh buhari bayada aminin daya wuce alh nuhu tun k’uruciya”kuma agari guda kurfi suke”bayan sun gama karatu kowane yazauna agarin da aka turasa aiki yana aiki”matayansu sunsan juna” saidai yaranne nasu basu san junaba.sbd ba gari d’aya ba!kuma anajima wa ba’a yi wata hidimaba..sai gashi Allah yasa anyowa alh buhari transfer zuwa garin kano.hakan yayiwa alh nuhu dad’i sosai…

 

Raudah k’awar baby ce tun a KT”kasancewar sunyi secondary skul atare”raudah na anan kano gidan yayanta zaune yana rik’onta.tana kuma karatunta”shine baby tasanar mata sundawo anan da zama”takumazo taga gidan sunje da baby taga gidansu”to kuma yanzun shine sukayi awaya taje tad’auketa su fita shak’atawa taga Yaya garin yake…..

 

Cigaban labarin

 

Cikin nutsuwa take tafiya tasaki kid’a na Musik”

 

Tana k’ok’ari shiga corner d’in da zata sadata da layin..

 

Wata had’add’iyar mota ta banko da gudu… duk yadda taso ta kaucewa motar kasawa tayi”

 

saida motar tadaki tata motar”tana salati ta tsaida motar…jikake kasssssss!k’arar glass d’in fitilar gaban motar ya tsage…wasu mutum 3 duk suka tsaya abakin hanyar suna kallonsu.

 

bayan tasamu ta tsaida motar”tajira taga me motar yajanye tasamu ta wuce”

 

Amma shiru bbu alamar hakan”

 

sannan motar me tintak ce”baya ganin naciki saidai naciki yaga na waje…

 

Motar daba’aganin na ciki na duba”wasu matasan mazajene su2 aciki…wanda ke zaune driver sit nakai dubana agaresa….Masha Allah!irinsu ake kira one in million…loll.. had’add’an guy ne”daya amsa sunansa namiji”kallo d’aya zaka masa kaga tsantsar aji”wayewa dakuma hutu had’e da ilimin zamani atare dashi…

 

fararen idanuwansa yaware yana kallon motar baby”

Cikin tsananin fusata da fushi DR HAKEEM yakalli abokinsa dake zaune kusa dashi”cikin dakakkiyar muryarsabme cike da haiba yace”.mus’ab me hakan ke nufi?”tana jira ne saina janye ta wuce kokuwa ita bazata janye mu wuceba??”

Mus’ab yace”.nikuwa big man taya zan iya ganewa?

 

Kafin Dr Hakeem yyi mgn baby ta fito dg cikin motar ta”cikin tsananin b’acin rai.

 

Aganinta kosuwaye sungama raina Mata hankali”subige Mata mota,suyi Mata b’anna”amma bazasu bata hanya ta wuceba kosu b’ata hak’uri….

 

Sosai mus’ab ke kallonta harta iso adede b’angaren da Dr Hakeem ke zaune ta fara musu knocking da k’arfi”tana mgn kamar haka…

 

Kokai wane wawane ya Isa kajanye k’ajagar motarka kabawa mutane hanya su wuce”kamun b’anna kafi k’arfin kabani hak’uri….kafin ta rufe baki anturo k’ofar motar da k’arfi.

 

Comments kawai guys zuwa dare kuga update kokuji shiru

Leave a Comment

error: Content is protected !!