Hausa Novels

ZARRAH BY OUM HAIRAN HAUSA NOVEL

ZARRAH BY OUM HAIRAN HAUSA NOVEL

 

 

 

 

 

 

 

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

Zarrah :- Wani matsiyacin kallo yayi Mata ya watsar da ita sosai kalamanta sun Sosa zuciyarsa tunda yake baitaba katarin haduwa da tsageran daya taba duban tsabar idonsa ya fada Masa kwatankwacin wadannan tasassun kalaman ba sai wannan kucaka Kuma qazamar yarinyar almajira lallai ta daukowa kanta bala’in dazai addabi rayuwarta ko mutum me cikakken gata yace zaija dashi wahala yakesha balle matsiyaciya almajira da ko arziqin yar aikin gdansa batakai ba.
Juyawa yayi ya fice daidai lkcn da Inna ta bude idanunta ta saukesu akan Asma’u ta yafitota da hannu ta matsa da sauri ta tsugunna tare da cewa “sannu Inna inane yanzu yakeyi Miki ciwo?” Girgiza Mata Kai tayi cikin muryar ciwo tace “naji sauqi Asma’ul Husnah meye yasaki kuka” sunkuyar da kanta tayi tare da saurin goge hawayenta tace “karki damu Inna zaki iya tafiya mu fita mu samu dan sahu mu tafi wani asibitin?” Zuro qafarta tayi ta miqe tace “zan iya Mana Asma’u dama sarqewar numfashin ne kawai Kuma yayi sauqi ince dai ba wanine ya sake farautar mutuncinki ba?” Murmushi ta qaqaro cike da tausayin Innanta tace “aa Inna muje gda zan baki labari yau na hadu da wani taqadirin dan iska da baisan darajar uwarsa ba bakiga cin mutuncin da yayi min ba harda Marina kawai don na tareshi ya taimakemu ya kawomu asibiti qememe dake dan dudun maguzawa ne yaqi harda tukuicin baqaqen maganganu yayi tafiyarsa sai wanine ya tare Mana dan sahu mukazo nan asibitin ashe Wai na dan bamagujiyar nanne infadamiki yazo ya duba kowa yana ganina ya juya zai tafi nikuwa na rama maganganun daya fadamin nace indai bai dubaki ba kika mutu ya jira ZARRAH ta sai nayi shari’a dashi”…..

Dariya Inna tayi ta lalubota ta rungumeta tace “ho ma’u na baki barin ta kwana do Allah ki rage zafin zuciya Kinga ke macece gdan wani zaki ki rinqa hqr da lamarin rayuwa kinji” cuno baki tayi gaba tace “waike waike Inna saikiyita cewa mutum yayi hqr Kuma mutanen duniya ba mutunci da hqr suka sani ba Ni kawai in anyimin ramawa zanyi idan mutum ya cika zaqewa nace ya jira lkcn da zan zama babbar likita wlh idan tsohuwarsa tazo hanuna allurar mutuwa zanyi Mata”

Dariya sosai Inna tayi tace “Ma’ulele ma’un Inna tashi mu tafi kinji kar yazo yaci Mana mutunci” miqewa tayi ta Kama hannuta suka fito harabar asibitin cikin sa’a kuwa suka samu sahu suka hau zuwa unguwarsu Asma’u tabashi kudinsa a gurin bada kudin ma saida akaso ayi fada da dan sahu Saida Inna tasa baki sannan ta hqr suka tafi tanata mitar ita Inna komai akayi tace ayi hqr kamar wacce akayiwa wankan farko da ruwan alwalar La’asar🤣
Suna shiga gdan taci karo da Dije yar kishiyar Inna ta debo ruwa a bohol tana ganin Inna ta shige daki ta angije Dijangala ruwan ya tuntsire akan Lamunde dake tsugune gaban murhu tana hura wuta da bakinta, kafin kace kwabo kokawa ta rincabe tsakanin ita da Dije kiciki kiciki daqyar Malam Husaini dake shigowa ya raba fadan Dije ta tsaransa karya da gaskiya ya kuwa hau ya zauna ya dauki sanda ya shiga bugun Ma’u aikuwa ta angajeshi saura kadan ya fadi tayi waje ta zauna saman dakalin qofar gdan ta rinqa kuka.

Anan Saurayinta Sadiqu yazo ya sameta da qunshin kifinsa ya zauna yayita aikin rarrashinta daqyar ya samu tayi shiru shima Saida yace idan batayi shiruba mutuwa zaiyi aikuwa dake dama kukan na iskanci ne sai tayi shiru ta dago ta kalleshi tace “jiyafa a gabanka Dijangala ta angizani kwata na fasa qwauri sannan ruwana ya zube Amma shi malam babannan saboda suna bashi abinci baice Mata qalaba harma Kaine ka kaini chemist din Sallau shine yau danna rama ya Kama dukana Allah duk ranar da nacimma ZARRAH ta duk sai narama cutar da akayimin

Murmushi Saddiqu yayi yace “to Banda abinki Ma’una waye yake rama laifin mahaifa aisu sha kundum ne komai sukayi saidai ayi hqr abarwa Allah” harara ta galla masa tace “chabdi lallai ma Sadiqu Mai raken nan wato so kake kace na yafe makantar min da Innata da Lamunde tayi da ruwan zafi ko Kuma so kake kace na yafe hanamu abincin da baba yakeyi yake basu a boye duka Kai bari kaji harma satar kudi fah sukeyima Inna shiyasa na daina barin kudi a dakinmu nake baka kake ajiye Mana yawwa barima kaji yau da mukaje bara gdan Alh Qasim Dubu goma sha biyar yabamu kaga nasamu kudin makaranta na sauran musaiwa Inna magani musai kayan abinci ko?”
Numfashi Sadiqu yaja yace “kayy alhmdllh dama yau da tunanin kudin makarantar nan taki na yini Kinga yau har aikin gini nayi jiyama haka da ribar raken dana saro da kudin aikin ginin gaba daya dubu hudu da naira tamanin ne da so nake sukai sha hudu sai a biya kudin makarantar” Jinjina Kai tayi tace “Allah Sarki dan Sadiquna kaga kasai siminti da kudinka tunda ai kaima naga gini kakeyi Mana wanda idan munyi aure zamu zauna yawwa nadai fada maka ka ginawa Inna ta daki qur’anin Allah bazan tafi nabarta anan su kashemin itaba kaga saura wata biyar yanzu muyi candy Kuma Mal yace da munyi Candy aure zaiyi mana dagani har Dijangala da Zabba’u, Inna ce mataketa qoqarin ganin ya barni nayi ko Hygiene ce shikuma yace baza’ayi yahudanci a gdansa ba”

Jinjina Kai Sadiqu yayi ya dauko Mata kifin daya siyo Mata ya miqa Mata tasa hannu biyu ta karba harda tsugunawarta tace “angode Allah ya dada arziki da wadata yasa wataran kasiye duk kifin garin nan” 🤔 zaro ido yayi sukayi dariya a tare yasa hannu ya dauki daya tace “ka qara Mana” girgiza Mata Kai yayi yace “ki shiga gda ki gyarawa Innanmu bari naje gurin musa na siyo Miki taliya ki dàfa Mana yau gwaggonmu taje qauye Kuma qila sai dare zata dawo” miqewa tayi ta shiga gdan ta tarar da Inna ta idar da sallar La’asar ta zauna zata farayi Mata surutu tace “Ma’u zanci qaniyarki akan sallah maza tashi kije kiyi alwala kizo kiyi sallah” dake tasan batada gsky Bata jaba ta fita ta dauki buta tayi alwala har yanzu fadan be qareba yanzu ma Saida ta harari Dijangala tace “zamu hadu a filin baja koli wallahi sai nayi qasa qasa nayi sama sama na dumbuli miya a ludayin uwar yarinya naga ubanda zai tare Mata shegiya me kan qotar gatari…..”
Hadiye guntuwar maganar tayi lkcn da taji saukar ranqwashi a tsakiyar kanta tana dagowa taga yayansu ne da take masifar jin tsoro don tasan yayi sukuwa a ruwan cikinta ba abune me wuya a gurinsa ba aikuwa kamar yasa kwado ya datse bakinta haka tayi muqus ta tashi sumsum ta shige daki ta fara jera sallolinta bayan ta idar yaro ya shigo ya kawo cefanen Inna tace a Ina tasamo cefane nan tayi Mata bayani dake Sadiqu ba baqo bane a gurin Inna yasa batayi fadaba tanajinta ta kunna rishow ta dora jallop din qamshi kuwa ya gauraye gidan Asma’u badai iya girki ba Inna tayi fama Amma tayi saa an iya da taimakon aikatau din da sukayi a gdan masu kudi ita da innan yaron gdanne ya fara kawowa Asma’u hari dole tasa suka hqr da aikin suka fara wainar shinkafa da miya kafin iftila’in makanta ya fadawa Innah wadda tasa dole suka hqr domin Asma ita kadai bazata iyaba.

Lkcn data gama girkin ta zubawa Sadiqu nasa ta zubawa Inna itama ta zuba domin taci harta zauna zata faraci Inna tace “kin zubawa su Dijangala kuwa?” Turo baki tayi tace “ni gsky Inna kinayimin katsalandan cikin rayuwata su din bamu sukeyi naga ko yunwa zata kashemu ba sammana abincinsu sukeyi ba yanzu idan muka ajiye guntuwar da safe ai mayi dumame tunda ni makaranta zan tafi” murmushi Inna tayi cikin tausayin quruciyar yar tata tason ita duk abinda akayi Mata saita rama walau alkhairi ko sharri wanda rayuwa ba haka takeba tace,
Na haneki da barin yin ramuwa akan komai Ma’u rayuwa ta zahiri ba haka takeba kada ki zamo cikin mutane masu son dole sai sunyi qeqe da qeqe tabbas wadannan nau’i na mutane basa tsintar komai a rayuwarsu sai tarin nadama da danasani mara amfani to bandama quruciya irin taki Ma’u ai abinda ka bayar shine rabonka do Allah dauki kwano ki zuba musu inada naira dari biyu da safe sai baki dari kudin mota dari kisai abinda zaki karya kinji Ma’ulelena”
Janyo flat tayi ta zuba abincin kashi biyu ta dauka takai dakinsu Zabba’u ta tarar da Mama Jummai tana sallah ta dangwarar Mata da kwanon ta fice ta nufi dakinsu Dijangala ko sallama batayi ba ta dire kwanon tayo waje Lamunde da taya bera bari tace “kekam kin shiga uku da baqar rowa da nufinki muji qamshi a banza ko ho Ma’u albasa dai batayi halin ruwa ba” har ta bude baki zatayi raddi taga Yaya Mudan ya bude labule ya fito sumsumsum ta shige daki tana qwafa ta zauna tanacin abincin tana qunquni takaicinta Yaya Mudan daya hanata rawar gaban hantsi shigowa yayi dakin ya dokanta harara tayi qasa da kanta yace “Ya Inna Ina abincin nawa ni?” Tasan halinsa sarai idan tayi wargi yanzu zata gwabzu hakanne yasata samawa kanta salama tanaji Inna tace masa “duba tukunyar ko ta rage” da sauri Ma’u tace “bari na zuba maka yaya” miqewa tayi ta dauki flat ta zubansa ta debe sauran a yar qaramar kula ta tura qarqashin gado ta koma ta zauna.

Yanacin abincin suna taba Hira da mahaifiyar tasu Asma’u najin haushin rashin zuciyar yayan nata duk matasan gdan sune suke ciyar da iyayensu Mata da qannensu Amma shi ko kudin omon da zaiyi wanki saiya tambayi Inna gashi da ƙi faɗin masifa”

Shi gani yake dole shi wata tsiyane qwafa tayi yakai Mata naushi ta goce yace “wlh Inna badan keba da tuni na dade da barar da yarinyar nan batada aiki sai jan maganar masifa shegiya kullum baqi take qarawa Wai kwananki nawa ma bakiyi wanka ba ne?” Turo baki tayi tana qunquni ya miqe yayi kanta Inna tayi saurin riqeshi tace “Kaga Mudansir ka kiyayi tabamin auta qaniyarka zanci uwarme tayi maka da zaka wani zage kwanji kace zaka bugeta bakaganin ba qwari gareta ba” qwafa yayi yace “yawwa Inna wlh na qara ganinta da Sadiqu sai na kakkaryata nan Naziru abokina yazo yanasonta tayi masa rashin albarka har tana cewa nima din dana turoshi menene bare shi.
Murmushi tayi tace “to Banda abinka Mudan inakai ina shiga tsakanin Ma’u da Sadiqu Kuma ma meye laifin Sadiqu yarannan sunason junansu tun suna qananu bakace su rabu ba sai yanzu da aski yazo gaban goshi to ban yarda karna qaraji matuqar Ina raye saina dauki Ma’u nakaiwa Sadiqu dakinsa matsayin Mata insha Allahu na lura dagakai har babanku ba son zaman lfy kukeyi ba shikenan kowanne rashin albarkarku ya tashi akan Asma’u na zai qare yar tawa tilo bata damu kowa ba Amma kowa ya dameta”

Jinjina Kai yayi ya fice yana cewa “ai dama Mal yace kece kike daure Mata gindi a gdannan to Allah yasa na qara ganinta da Sadiqun a unguwarnan Kai nama daina zuwa ko Ina a qofar gidannan zan rinqa zama naga qarshen rashin kunyarki shegiya me idon aljanu” matsawa tayi ta kwanta jikin Inna tace “nifa Inna bansan me Sadiquna ya tarewa su Mal da Yaya ba dazuma da Mal yaganmu inaji Sadiqu yana gaisheshi yaqi amsawa nikuwa nace da Sadiqu dama ya daina wahalar da kansa aure ne dai dole a dauramin da wanda nakeso kamar yanda aka daurawa kowacce ya a gidannan ehe….”
Buge Mata haba Inna tayi tace “kinci malafar ubanki don qaniyarki bakisan cewa Allah uba yabawa damar zabawa yarsa budurwa miji ba to shine har kike wata taqama kul na kumaji yar jaka da qusa kawai tashi ki debi kayan makarantarki ki goge jiya Jiddah ma tazo bakyanan kinje debo ruwa tace ki taho muku ta tast book dinnan na biology zakuyi tast ranar laraba miqewa tayi ta fita ta aro dutsen guga ta dawo tana gugar suna Hira da Innanta rabin hirar akan Aseem Shaheed ne da irin alwashin da taci na yimasa rashin mutunci duk ranar da Allah ya sake hadasu, Jinjina Kai Inna tayi tace “amma da kin hqr da yafi Miki kinga shi namiji ne ke kuwa mace ce ko marinki ya sakeyi ya cuceki a sadakinki sai an rage wani abu balle ma ni banga laifin da yayi miki ba badan dai sakarcinki ba mutum nawa kika nemi taimakonsu sukaqi taimaka Miki baki qullacesu ba saishi wasu ma mutuncinki suka rinqa farauta Amma duk kin manta saishi da yayi fada dake da fatar baki Kuma tabakin nasa ai ba kunyar gareki ba qila abinda kikayi Masa ma yafi Wanda kika fadamin”

Shiru tayi don tasan idan ta cika magana yanzu Inna zata gindaya Mata sharadi ita Kuma tariga ta qudurta a ranta saidai idan Allah bai sake hadasu da Dr Aseem Shaheed ba Amma saitayi Masa abinda zai tsaya Masa arai kamar yanda yayi mata ita ba lusarar ƴa bace dazai zageta yaci mutuncin Innanta kuma ta ƙyaleshi dama iya ita kaɗai yayiwa da da sauƙi kamar yanda na bayan sukayi amma shi Innanta fa yacewa tsumma tab ai wlh ya taro march kwararo kwararo zatake bi don ta ganshi tashin farko rotse zatayiwa motarsa idan yayi yunƙurin yin wani abu ta kwankwatse masa yatsan ƙafarsa da dutse.
Dariya takeyi ciki ciki Inna tace “dariyar me kikeyi?” Saurin saita kanta tayi tace “tunawa nayi da wata tsokana da mukayi nida Jiddah a hanyar school ranar mun dawo dukkanmu bamuda kuɗin mota mukaga Mata da miji suna tafiya a qafa matar da tsohon ciki shine Jiddah tacemin lahh Asmah Kinga wata Mata ta haɗiyi wake ya kumbura Mata ciki nikuwa na matsa kusa dasu nace sannu Mata buhun garin kwaki kikaci ne yayi miki saqeqe a ciki shine mijin ya Kama zaginmu muka mayar dashi mahaukaci mukayita dariya kawai saiya biyomu da gudu na turansa dutse ya tungule ya faɗi…..” ]

KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇

 

 

Preview: [DOWNLOAD COMPLETE BOOK 👇]
 

Name: ZARRAH BY OUM HAIRAN HAUSA NOVEL
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: MYNOVELS.COM.NG
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books
Groups/Writers: Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: July, 2021

 

 

 

Leave a Comment