Zuciya ce Hausa Novel Complete

Zuciya ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: ZUCIYA CE

 

( the heart)

 

Writing by Fadeelah s Utai

 

 

 

Dedicated to my roop ki rani ina maki sahihiyar kauna

 

Page 1&2

 

Bismillahirrahmanirrahim

 

Yammacine mai cike da niima gawata iska mai dadi datake kadawa garin kano yayi luf luf alamun damuna da alama ruwa yana gaf da sauka

Wani gida naleka dake anguwar dan dishe wata kyakkawar matashiya nagani dukda banga fuskartaba gefen fuskarta nahanga tana da kyan diri masha allah doguwace Ba canba sannan bazamu kirata da me jikiba sanye take da doguwar rigar atamfa diinkin ya matukar amsar jikinta das masha allah aysha naji wata mata takirata juyawa nayi wata kyakkyawar mata nagani mai matukar kyau da kwarjini ahankali naji sautin zazzakar muryarta mai cike da sanyin dadi juyowatayi fuskar ta cike da murmushi tace naam ummina yasalam nafurta ganin kyakkyawar fuskarta mai cike da murmushi ta bayyana tsaiwar mekikene tundazun turo dan karamin bakinta tayi cike da shagwaba tace ummi tundazufa nakejira kifito kibani sakon da zan kaiwa aunty hafsa naji shiru ashe kinshiga bayan gidane eh wallahi to aikuma auta naga kamar yamma tayi gakuma hadari agarin aa fa ummi harnaje allah tunda anguwa bawani nisa tacikaba kuma ma ai nafef zanje to shikenan baba tsari kardai ki zauna tunda kinga akwai hadari agarin insha allah ummi bazan zaunaba ayusha kyakkyawa ce ajin farko tana da oval face gashin girarta cike yake tana da manyan idanu masha Allah masu dauke da zara zaran eye lashers idanuwanta irin masu haske da shekine tana da dogon hanci mai dauke da dan karamin baki masha allah tana da pinks lips masu matukar kyau da tsari goshinta gashine akwance luf luf gawani dan saje daya kara kawata tsarin fuskarta dakyau tana da dogon gashi baki sidik masha allah duk da kasancewar su talakawa hakan be hanasu wadatar zuciyaba .

 

 

Yakukaji salon shin inci gaba koyaya

 

Fadeelah Khan ce

 

 

Comments

 

Share

Fisabilillah

ZUCIYA CE

 

(The heart)

 

 

 

 

By Fadeelah s Utai

 

Karanta Ni Da Yaya Sadeeq Hausa Novel

3&4

 

Ummice tshiga daki tadakko kayan sakon tace auta dan allah karkibari ruwa yatabaki kinji . To ummi insha allah karbar sakon tayi ummi tabata kudin nafef Tace kigaisar min dasu zasuji ummi sai na dawo to adawo lafiya,ahankali take tafiya cike da natsuwa ,idan wani yaga yanda aysha ke tafiya sai ya dauka gayu take kokuma irin tacika izza amma kodaya, Bahakabne haka allah ya yita , me nafef ta tsayar tace masa nasarawa zai kaita hawa tayi suka tafi ,akofar wani milk din gate tanuna masa yatsaya tabashi kudinsa kana ta bude karamar kofar gate din tashiga gaida me gadi tayi kana tawuce cikin gidan.masha allah nace gaskiya gidan dr hisham hadaddan gidane,kofar falon ta kwankwasa bajimawa me aikin aunty hafsa tazo tabude mata kana tace aa autar ummi yau kece agidan eh wallahi larai ykk ya aikin Alhamdulillah tace;basma ce tazo da gudu tarungume aysha Tace oyoyo aunty oyoyo basmana ina bassam yana wajen dady aunty kinzo min da abun da ummi tace zata kawomin ,aunty hafsa ce tace kai bassam kibari tahuta mana .ina wuni aunty lpy yasu ummi tana lafiya,ayya ummina nayi missing nata wallahi tabe baki aysha tayi tace tab su missing manya kajifa aunty yaushe kikaje gidanne kosatifa bakiyi dazuwaba? Uhmm aysha kenan kema zakiyi auren ne ai bare ke duk inda ummi tayi kina binta kamar jela,allah sai kinyi kusan wata shida baki gantaba . Turo dan karamin bakinta tayi tace tab wallahi bazan iya kwana daya banga ummi ba bare har wata shida tab,suna cikin zancen dr hisham suka shigo shida bassam sakin dadynsa yayi yatafi wajen aysha aunty yaushe kikazo yanzun nazo my boy yakake? Ina lpy aunty ina ummi tana gaisheka,zaki tafi dani yafada yana me hayewa kan cinyarta kabari sai kunyi hutu sai inzo indaukeku to yace hisham ne yakatse masu hirar yace aysha yau agari ina wuni uncle lpy kalau amma kwana mana zakiyi ko ? Tab yanzuma zantafi dama aunty hafsa nakawo wa sako , kibari sai gobe bakya ganin hadiri agarin,sauri zanyi ummi tace kar inzauna ok gashi kuma bako zanyi dana kaiki ai , bakomai uncle kudi yabata yace tahau nafef tace tagode tayiwa aunty hafsa sallama tatafi.ahankali take takunta mematukar daukar hankali har ta isa bakin titi,babu alamun abun hawa kodaya takai kusan minti goma atsaye amma ba kodaya wanda yatsaya takawa tafarayi dakafarta gagarin hadarin yagama haduwa gawata sassanyar iska da ake kadawa mematukar dadi,da damshin ruwa ahankali ruwa yafara sauka kadan kadan ,rasa yanda zatayi tayi hango wata rumfa tayi agabanta ahankali takarasa wajen tafake kamar dawasa ruwa ya kece kamar da bakin kwarya,lumshe kyawawan idanunta tayi jin wani sanyi yana buso ta gashi magriba tagabato,ahankali ruwan yadan tsagaita fitowa tayi tafara tafiya kenan wasu arnayen motoci suka taho da uban gudu kusan guda uku bakace agaba kirar toyota sai wata me shegen kyau atsakiya fara da alamuma sabuwar fitace sai kuma wata bakar abaya kirar jeep maana dai sunsaka farar atsakiya, bata ankara ba taji saukar ruwa ajikinta irin wanda yake kwanciya agefen titin nan….

 

Tab kowaye me wanga aiki oho nayi nan

 

 

Fadeelah Khan ce

 

ZUCIYA CE.

 

(The heart)

 

 

 

 

 

Writing by Fadeelah s Utai

 

 

Page 5&6

 

 

 

Bismillahirrahmanirrahim

 

 

 

Saurin juyowa tayi taga wanene mai mata wanan dibar albarka, bata sauke idanta ako Inaba sai akan wadannan hadaddun motocin.

 

 

 

 

Wanda taga basu da niyar dakatawa dukdacewa sunrage gudun bakamar dazuba.

 

 

 

Wani bakin cikine yatokare mata makoshi wato suntozartata amma bazasu iya tsayawa subata hakuriba lol

 

 

Suyayan masu kudi dama jisuke titin tamkar na ubansu kokuma dansukadai aka yi titin matssss taja tsaki,

 

 

 

Jitayi bazata iya hakuraba wani dutse tahango tadauka saida tasaici wannan farar motar kana tajefa jikake tasssss akan glass din .

 

 

 

Saurin taka burki duka motocin sukayi kana bodyguard din suka firfito suka zagaye aysha itako ko ajikinta , hasalima cigaba tayi da masifa .

 

 

 

Zaune yake abayan motan hanunsa dauke da jaridar daily trust yana karantawa ko motsawa baiba , saida ya mula kana ya bubbuga glass din ahankali kamar wanda yake buga jikinsa.

 

 

Dasauri daya daga cikin bodyguard dinsa yazo yabude masa motan, ahankali yaziro dakafarsa guda waje saida yakai kusan minti biyu kana yafito baki daya.

 

 

 

 

Tsarki yatabbata ga ubangijin wannan halitta masha Allah hadaddan guy ne handsome wanda yan mata kerububinsa .

 

 

 

 

Hadadene irin first class dinnan dogone kyakkyawa masha Allah farine yanada cikar zati fatarsa sai sheki take alamar hutu yazauna ana .

 

 

 

Yana da dogon hanci fuskarsa yar dadai mai dauke da siririn saje , idan kaganshi tamkar tiger shroff nakasar India.

 

 

Yanada murdaddan jiki dafadin kirji da alama dai yana motsa jikinsa

 

 

Rayyan Ahmad mahmud kwangila kenan kyakkyawan matashi maiji da kudi datashe ,

 

 

Lumshe kyawawan idanunsa yayi kana yabude ahankali yataka yaje har inda take,

 

 

Tana ganinsa saida gabanta yafadi ,amma saboda karfin hali irin nata sai tadake ahankali yakai dubanshi gareta idanunsa yayi jajir fatar fuskarshi tayi ja abunka da farin mutum miskilin murmushi yasaki wanda iya karsa kan labbansa .

 

 

Kana yakuma tsira mata manyan dara daran idanunsa wanda sukayi jajir yana kallonta dasu itako batama kula da yanayinsa ba .

 

 

Saima sake tsuke fuskarta datayi jinshirun yayi yawane yasa aysha dago kanta taga wanna isashenne saidai me tana dagowa tayi saurin yin kasa dakanta dan wani shegen kwarjini taga yayi mata.

 

Dakewa tayi tace malam baka iya bada hakuri bane shin baka gani kokuma direbobinka makafine,dazasu watsamun ruwan datti batare da suntsaya sunbani hakuri ba?

 

 

Zubawa dan karamin pink lips dinta ido yayi yar karama da ita sai shegen tsiwa shi abun natama dariya yabashi , amma sai yadake yasake tsuke fuska ahankali yamotsa labbansa who dare you dazaki fasamin glass na motana , yafada tamkar Ba bahausheba, domunkuwa hausar tasa abun dariya jin tayi shiru ,

 

 

Yasa ya buga mata uwar tsawa yace answer me I say who dare you, murguda masa dan karamin bakinta tayi tace oho nima bansaniba .

 

 

Wash yasin nagaji muhade gobe ko zuwa dare

 

Fadeelah Khan ce

ZUCIYA CE

 

(the heart)

 

 

 

 

 

Writing by Fadeelah s Utai

 

 

 

Page 7&8

 

 

 

Bismillahirrahmanirrahim

 

 

 

bige mata bakinta yayi kana ahankali yasunkuyo yace insake gani bakin ki yayi wanan abun sai na fasashi, shasha kawai Kuma bazaabaki hakurin ba kiyi abunda zakiyi .

 

 

 

 

Hawayen azabane yazubo mata kana tace allah sai kabani hakuri koba yauba , ok ni meyasa kika fasamin glass na motona, fuskarsa yatsuke sosai yace nima sai kinbiyani .

 

 

 

 

Tsuru tsuru tayi da idanunta kamar wata yar yarinya karama hanunta tasa abaki tace ayya fa to. Basune suka fesomun ruwan datti ba , ai sune sukajama dan haka sune zasu biyaka bani ba ehe,

 

 

 

Ahankali yaci gaba da kallon yanda take surutu kamar parrot ,sai fa kinbiyani yafada yana gimtse fuska.

 

 

 

 

Hawayene suka zubo mata kana tace allah ni bani da kudin dazan biya amma idan suka bani hakuri zan nemi aiki nabiyaka,tafada tana me juyawa tatafi tabarsa awajen , binta yayi da tsantsar mamaki ,azuciyarsa yace wanan wacca irin yarinya ce sam bata da tsoro har ta iya tsayawa agabana batare dataji shakka taba nikuwa nace aysha kenan.

 

 

Cikin ikon Allah tasamu nafefe tagaya masa inda zai kaita tatafi tabar rayyan da mamaki .

 

 

SHIN WACECE AYSHA?

 

 

 

Aysah shine cikakken sunanta subiyu mahaifiyarsu tahaifa ,hafsa itace babba sai kuma aysha mahaifin su alhaji aminu yahadu da mahaifiyarsu amina a inda yake aiki soyayya maikarfi tashiga tsakanin su da ita koda mahaifinta yatambayeta wata keso tace masa ameen dayayi bincike yagano bashi dawani aibu ya amince yace yaturo iyayensa.

 

 

Bakaramin dadi alhaji ameen yajiba Ba laifi yanada rufin asiri badau wani lokaciba akayayi bikin ameen da kuma ameena , yanada yan uwa biyu sulaiman wanda suke kiransa da kawu manu sai kuma gwaggo binta ,

 

 

Bayan wata uku da aurensu ciki yabullo ajikin amina zokuga murna wajen ameen bayan wata tara tahaifi yarta kyakkyawa masha Allah.

 

 

Ranar suna yarinya taci sunan hafsa bayan shekara uku allah yasake azurta amina dawani cikin cikin ikon Allah wanan karon ma tasake samun ya mace kyakkyawa masha Allah dankuwa mahaifinta sak ,

 

Kamar kasace kagudu ranar suna yarinya taci sunan mahaifiayr ameen

 

 

Alhaji aminu yadauki san duniya yadorawa aysha bata laifi sam agunsa shekarar aysha biyar allah yayiwa mahaifinsu alhaji amin rasuwa sanadiyar ciwon ciki lokaci daya .

 

Alokacin daya rasu yabarsu da komai dakomai amma kawu manu da gwoggo binta suka zo suka tattare komai dama kawu manu basa shiri da ummi kasancewarsu masu son abun duniya duk randa yazo gidan sai ya gaggayawa ummi magana yanacewa an auro musu jaraba.

 

 

Duk tazo ta mallakemusu yaya ita dai sai dai tayi murmushi kasancewarta mace me hakuri saida suka tattare komai sai iya gidan dasuke ciki .

 

 

Ummi tayi kuka tayi kuka sosai har saida takwanta ciwo hankali su aysha bakaramin tashi yayi Ba,

 

 

Gashi basu da kudin dazasu kaita asibiti hafsa ce tace aysha kula da ummi bari inje insamo menafef ina da kudin dazan biya registration sai mu kaita asibiti dashi.

 

 

 

Allah bazai bari muwulakantaba tafada tana me share hawayen idanunta, fita tayi dasauri bajimawa suka dawo tare dame nafef shiya taimaka musu suga shigar da ita nafef din kana suma suka shiga yajasu .

 

 

 

Wani asibiti yakaisu mafi kusa ganin yanda jikin ummi yarikice kaida gani kasan asibitin private ne,taimakasu yayi suka shigar da ita dasauri wasu noises suka karbeta dawowa hafsa tayi zata sallami me nafef din koda tamikasa kudin kinkarba. Yayi yace allah yabata lafiya dan bakaramin tausayi suka bashiba .

 

 

 

Godiya hafsa tayi masha kana takoma cikin asibiti har anshigar da ita taimakon gaggawa likitocin suka shiga bata .

 

 

 

Alhamdulillah anyi nasarar gano matsalarta jininta ne yahau sai kuma damuwa daya daga cikin doctors dinne yace suje office din dr hisham susameshi .

 

 

To sukace kana suka shiga inda aka nuna masu wajen zama yanuna masu kana yadago yakallesu yace ina mijin wacca kuka kawo ahankali hafsa tace allah ya masa rasuwa ayya Allah yajikansa to ina yan uwansa tace uhmm.

 

 

 

 

Tausayinsu yaji sosai kana yace insha allah zata samu lpy amma kudena bari tana shiga damuwa ko yawan tunani .

 

Insha allah dr zamu kiyaye to allah yayarda yafada yana me satar kallon hafsa ,tunda yakalleta yaji yayaba da nutsuwarta lokaci daya yaji yakamu da kaunarta.

 

 

 

Har aka sallameta shine yadauki dawainiyarsu ahaka dai sukaci gaba da rayuwa tunda dr hisahm yashigowa rayuwarsu komai yacanza har sukayi aure da hafsa shine yadauki dawainiyar karatun aysha harta kammala yanzun haka ta kammala karatunta aikine kawai bata samuba kasancewar samun aiki yanzun sai dan wane da wane amma haryanzun dr nanema mata ..

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.