Zuciyar Mutum Hausa Novel Complete

Zuciyar Mutum Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*ZUCIYAR MUTUM…!*

 

*NA*

AUTAR MANYA

 

*ADABI WRITTER’S ASSOCIATION*

 

Bisimillahir Rahmanir Rahim

 

*001*

 

Tun da muka doso cikin layin gidanmu gabana yake faɗuwa saboda ina jin tsoron, abin da zai je ya dawo akan da ɗewar da mukai bamu dawo gida da wuri ba Ƙawata kuma aminiyata Habiba ta dube ni tare da cewa.

Zuciyar mutum

“Hafsatu ko mu wuce gidanmu ne, idan yaso sai mama ta kaimu gida taiwa Innarku bayanin abin da ya

tsaidamu?”

Na saki murmushi mai ƙayatarwa ina kallon Habiba wadda duk tsoro yagama baibaye saman fuskarta kamar ita za’ama faɗan jimawar dama kuma hakane Habiba takan ɗauki dukkan lamarina da daraja da mahimmanci don hatta mahaifiyarta mama ta ɗauke ni kamar ƴarta wallahi abin da Habiba take mini bazaka ce ƙawa ba sai dai jini.

“Habiba muje gidan kawai, Nina san yau innah sai tayi mini faɗan da gwara duka akan shi, Amman zuwan namu yafi alheri duk da ba wani wajan muka tsaya ba kece kika nace nai ma Salisu magana da wallahi ba zan tsaya ba”

Indo Nera Hausa Novel Complete

Ta saki murmushi tare da cigaba da tafiya wadda nima na take mata bayanta muna tafe muna hira wadda duk akan yadda Habiba ke rarrashina ne akan na amshi tayin soyayyar salisu wanda ya mato akan sona wanda ni kuma hankalina sam baya kanshi.

Har muka ƙarasa gida tana faman yimin maganganu akan shi wanda jinta kawai nake don ni sam karatuna ne a gabana wanda ni yanzu ina matakin Nce ne a makarantar kwalejin tarayya ta Fce kano.

 

Da shigarmu tsakar gida mukai sallama muka tarar da Innah zaune tana yin maficin kaba wanda shine sana’arta tayi kayanta ta saida kuma Alhamdulillahi Allah ya rufa mana asiri da hakan tunda muna ci mu sha har mu ɗinka sannan dashi take biya min kuɗin makaranta kasancewar ni ɗaya ta haifa a duniya kuma tun bayan rasuwar mahaifina bata ƙara aure ba anan gidan mahaifina muke zaune tare da ita.

Innata ba mace bace mai haɗama da zulama shiyasa bata shigewa ƴan uwan mahaifina waɗanda suke da kuɗi sai dai in zasu mata alheri sukan zo har gida su kawo mata shima kuma ba sosai ba.

See also  Alamomin Mace Mai Dadi Mace mai Ni'ima

 

Innah ta ɗago kai tana amsa sallamarmu ganina da Habiba yasa ta kama haɓa tana dariya tare da cewa.

“Dama tunda naji kin jima nasan kin biya gidansu Habiba ne to bani saƙon ki wuce kicin ki zubo muku abinci”

Ajiyar zuciya na sauke mai sanyi ina hamdala ga sarki Allah! domin habiba ba ƙaramar ƙwata ta, tai wajan Innah ba dama kuma hakane innah nason habiba fiye da zato.

 

Na rataye hijabina a saman igiya na shiga kicin na tattare kwanukan dake ƙasa na zuba a kwando sannan na buɗe tukunya ina zuba mana dafa dukan shinkafa ƴar hausa wadda taji daddawa da kayan ƙamshi, na zubo mana a wadace sannan na fito tsakar gida na dire a gaban Habiba wadda ta tuɓe hijabinta tana taya Innah gyara kabar maficin.

 

Zama nayi nima ina cewa.

“Innah ga saƙon mun karɓo tace tana gaishe ki”

Na miƙa mata atamfar a leda baƙa wadda na ajeta tunda muka shigo.

Innah ta ɗauka tana murmushi ta buɗe ledar atamfar ta bayyana.

“Wow ma sha Allah, muka furta a tare nida Habiba har muna rige rigen amsa muna ganin jar atamfar datai kyawu matiƙa”

Innah ta amsa ta maida cikin ledar tare da miƙawa Habiba tana ce mata.

“Ki kaiwa mamarku kice ta bawa salma yayarki kafin nazo barka”

A tare muka sa Ihu muna murna sai kuma habiba ta ɓata rai tana cewa innah.

“Dama mu kika ɗinkawa tunda sallah ta matso”

Innah tacewa Habibah.

“Kwantar da hankalinki wannan maficin da nake guda dubu ake so za’a kai katsina da zarar kuɗin sunzo san je na siyo muku leshi mai kyau a kwari in Allah ya yarda”

Rungume Innah mukai muna mata godiya sabida dagani har Habiba Innah ke mana ɗinkin sallah domin itama Habiba har gwara ni sabida babanta ya rasu tuni, kuma suna da yawa ƴaƴan gidansu wanda duk yayinta mata sunyi aure sai dai mazajen bama su hali bane nauyi yayi ma mamanta yawa ga yawan kai ƙarar maza na rashin zuciyar su nemo su basu wannan yasa Habiba yawanci agidanmu ma take ci da sha kuma ɗinki tare innah ke mana makaranta kaɗai ke rabamu wadda itama da zarar na dawo nake shiga gidansu wataran ma bana shiga gida sai na biya tunda ita habiba tunda muka gama sakandire karatun nata ya tsaya sabida rashin kuɗi niko Innah ce tace sai naci gaba wannan yasa na dage ina zuwa makarantar fce wanda kuma Ƙanin Mahaifina yace da zarar na kammala zai sama mini aiki tunda yana da ƙafa a gwamnati.

See also  Ya zanyi da auren Adnan Hausa Novel Complete

 

Abincin na janyo muka soma ci muna hira da Habiba jifa jifa Innah na saka mana baki bayan mun kammala cin abincin na miƙe na kai kwanon kicin sannan na dawo muka zauna muna cigaba da taya innah haɗa kaba wajan sha biyun rana Muka kammala Habiba ta share tsakar gida ni kuma na dinga ɗaukar mafican ina shigarwa ɗaki.

Ana Azahar muka yi sallah na zira Uniform ɗin islamiyya sabida ranar lahadi ce kuma bani da school.

Na dubi Habiba wadda ke kwance tana bina da kallo nace mata.

“Wallahi ya dai dace ki koma islamiyya tunda muka haɗa sauka kika daina zuwa wallahi baki ga yadda ake Hadda ba”

Ta dube ni tare da cewa.

“Hafsa kefa ganau ce ba jiyau ba mama tana neman abin da zamu ci, ina taga kuɗin makaranta ba laifi na san karatun sallah Allah sa albarka”

Na dube ta ina mayar da kaina ƙasa tausayin Habiba ya kamani wato duk yadda kake ganin kanka in ka dubi wani sai ka godewa Allah, Habiba nada kyan daya fi nawa dan fara ce jajir bafulatana saɓanin ni da nake baƙa kakkaura tana da kyan da zata yi soyayyah da maza masu kuɗi amman suma mazan basa zuwa wajanta sabida ƴaƴan masu dashi kamar su suke aura, sannan tana da kamun kan da bata bawa wani damar yaudarar ta da kyan taba domin yayi lalata da ita ya bata kuɗi ba.

Na share hawayen Ɓoye, tare da ƙaƙalo murmushi nace mata.

“Allah ya kawo mana mafita”

Tace.

“Amin, yanzu rayuwa ta sauya masu kuɗin ma ba kowa ke kyauta ba kaci ka sha amman maƙocin ka maraya baici ba bai shaba sai yayi abin da bana daidai ba a sami damar yaɗa shi, Nima kaina Hafsa ina son karatun amman babu hali niba saurayi ba bare ya soni ya tallafa mini Yayina ba ƙarfi ba kullum mama cikin raba case take a gidajensu ga Yaya Manu ya saka shaye shaye a rayuwarsa kullum ƴan sanda na farautarsa sabida suna zargin sa da yana sai da kayan ganye to yaya zamuyi Allah hafsa har kuka nakewa Mama watarana sabida tausayin ta”

Tana gama faɗan haka ta koma saman gadona ta kwanta tai lamo.

Na saka haɓar hijabina na share hawayen dake zubon ban iya bata amsa ba nasa kai na fita daga ɗakin.

See also  Adheenah Hausa Novel Complete

 

Na leƙa ɗakin Innah nai mata sallama Na fita ina tafe a hanya ina zancen zuci Habiba nada kirki da sanin yakamata tana da kamun kai sosai wanda tun tasowarmu bata da wata ƙawa sai ni tana da tarbiya daidai misali wanda zance tafi kaf ƴaƴan babarsu tarbiya duk da tasowa mukai daga cikin gari muka dawo nan Ɗorayi ciranci amman tunda muka dawo nan lokacin banfi shekara goma ba,bani da wata ƙawa kamar Habiba tasan sirrina nasan nata hatta mahaifanmu mu muka haɗasu ƙawance duk da Innah ba fita take sosai ba, Dan bana mantawa da babanmu nada rai har kayan abinci yake kai musu tunda su babansu ya jima da barin duniya.

Wannan halaiya ta habiba yasa Innah ta amince mini akan nayi tarayyar abota da ita.

 

Adaidai kwanar Gidan su Habiba sabida ba layinmu ɗaya ba, Naci karo da Salisu wanda ke ƙoƙarin shigowa cikin layin.

Nayi kamar ban san da ganinshi ba naja gefen Hijabina na rufe fuskata.

Ashe shiya ganni.

Salisu dogon namiji mai kalar fulani sabida kyawun shi da cikar haibar shi uwa uba ga nutsuwa nidai kawai bai mini ba shiyasa naji bana ra’ayin soyayyah dashi duk da, yana da kirki kamar yadda naji ƴan layinsu na Islamiyyarmu na faɗi.

Nice dai kawai nafi ganin dacewar na tsaya nai karatuna wanda nake shekarar ƙarshe na matakin Nce 3 Wanda dashi naci burin taimakon mahaifiyata da sauran al’ummah idan Allah ya bani dama.

“Gimbiyar mata”

Naji sautin dirin amon! muryar Salisu cikin dodon kunne na.

Na ratse zanyi gefe da sauri ya kamo gefen hijabina da rashin sabo da hakan nai saurin ɗagowa ina zuba masa harara.

Ya saki murmushin da gefan kumatun sa ya lotsa.

“Ina sonki hafsatu, amman ke bakya sona ko dan kinga ni talaka ne bani da aikin yi wanda zan riƙe ki?”

Ya faɗa da kalar tausayawa.

Ina ƙoƙarin bashi amsa don ya bani tausayi naji muryar Maman Habiba a kaina wadda ta leƙo tana cewa.

“A,a Hafsatu kece yau da saurayi to ku shigo nan mana kya tsaya a waje”

Murya a rarraɓe nace mata.

“A,a mama dama makaranta zani”

Na faɗa da sauri na raɓe na wuce salisu wanda ya kafeni da manyan idanunsa yana kallona dasu……

*SABON LITTAFI KUMA NA KYAUTA BANA KUƊI BA PLS AI MIN COMMENT DA SHARE IDAN AN GANI NAGODE*

08142105218

AUTA.

0 thoughts on “Zuciyar Mutum Hausa Novel Complete”

  1. Pingback: Jalaluddeen Hausa Novel Complete - Hausa Novel

  2. Pingback: Jalaluddeen Hausa Novel Complete - Hausa Novel

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top