Zulfa Hausa Novel Complete

●● ZULFAH ●● 1⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Dare ne mai cike da dumbin rahama, kowa na cikin gidanshi sakamakon Ruwan da ake tsugawa, masu abin hawa suna ciki, masu tafiya a kafa da mashin sun fake saboda ruwan yinshi akeyi kamar da bakin kwarya, ma’aikatan dare suna wajen aikinsu,
A wannan lokacin zulfa’u na cikin ruwan tana wanke kwanukan da aka ci abincin dare a gidan, yawan ruwan da akeyi baisa goggo marka ta tausaya mata ba, yayin da ita kuma take dakinta na kasa, kan rubabiyyar katifarta, rushi ne a gefenta suna shan dumi ita da yarta Salaha, can gefe kuma mahaifin zulfa ne zaune yayi tagumi yana leken yarshi dake faman aiki cikin ruwa, zuciyarshi na zafi amma bashi da yadda zaiyi saboda marka ta fi karfinshi, Allah Allah takeyi ta gama ta shiga dan karamin dakinta da bai wuce taku shida ba, tana gamawa ta gyara gurin da sauri saboda ruwan kamar dada ingizoshi akeyi, tayi maza ta tsaya bakin kofar dakinta ta cire kayan jikinta saboda kar ya jika mata daki dama ga dakin ba kofa ruwa duk ya jika kofarshi, matse kayan tayi ta shanya a saman kwanonta, tasa wasu yagaggun kaya da suka zaizaye saboda tsufa, da sauri ta hau kan katifarta wacce bata da maraba da tabarma, yunwa sosai take ji dan ragowar da take samu ma yau basu rage ba, gara ma na kabiru yayan salaha ya dan rage kadan saboda ta samu, amma saboda tsabar ta kosa taji muryar dake debe mata kewa tasata bacci cikin farin ciki, muryar dake sata manta ko wani irin bacin rai yasa ta share yunwar da takeji, ta dakko redionta da gurin kunnanawan a cire yake, in ka ga radion bazaka taba cewa in an kunna zaiyi aiki ba, kibiyarta tasa ta kunna shi, cikin zakuwa ta kamo tashar liberty ta kure muryar radion dan battery ya kusa mutuwa, ta tura kanta cikin zaninta ta kara radion a kunnenta, saura 5mints takwas tayi, ta dinga sauraren wakokin da akeyi, takwas dai2 taji ansa sassanyar waka mai tsuma zuciyar masoya, lumshe idonta tayi saboda tasan taken isowar gwaninta kenan, kara gyara kwanciya tayi ko kadan sanyin da takeji ya gushe, muryar “Abubakar sadiq marafa” ita ta daki dodon kunnenta cikin salonshi na isa da kasaita, salon dake burge dubban mata masu aji dake cikin garin kaduna da kewayenta, sallama ya fara yi cikin harshen hausa da larabci, ya mika gaisuwa gurin masoyanshi da turanci, sannan ya fara programme dinshi cikin harshen hindu (indianci) cikin kwarewa yake gabatar da program dinshi, duk wata mace da ta isa a duk ranar friday to tana manne da radionta tun takwas har tara na dare, wasu ma da radion suke fita tadi saboda gudun kar a barsu a baya, ko wata shida sadeeq marafa baiyi da fara program dinshi ba amma saboda kwarewarshi da yadda mutane ke sonshi zaka rantse tunda aka bude gidan radion yake aiki a gurin”””!,

kasancewarshi mutum mai girmama soyayya da son yanayi na damuna yasa aka kayata mishi wannan daren da wakoki masu sanyaya zuciya, karfe 8:40 bayan ya kammala da gabatarwa, ya rage amsa tambayoyin masoya, tambaya uku kadai yace zai iya amsawa a ranar saboda yana son yin bankwana da masoyanshi, gaban zulfa ya fadi hankalinta ya tashi, ta yaye xanin da ta lulluba dashi saboda wani gumi da taji ya keto mata””, cikin taushin murya zee gayu ta fara wurgo mishi tambayar farko, tace tambaya ta farko ta fito daga gurin “Salma Ibrahim, ” tambayar da akullum sai MARAFA ya amsata babu mamaki malama salma bakuwace a cikin wannan shirin namu, tambayar itace shin sadeeq yana da aure,,, dariya sadeeq yayi saboda yadda zee ta karasa maganar yace zeee kenan, malama salma bani da aure, sai dai kuyi min fatan samun mace ta gari kuma kamila, zee tace bakayi niyya ba dai ga mata nan kamar zasu ci kansu, murya can kasa saboda kar masu sauraro suji yace zee ban hadu da muradin raina ba har yanzu, ya lumshe idonshi yana siffanto irin macen da yakeso tun yana yaro, zee ta bude murya da karfi tace to masu sauraren mu marafa dai yace bai hadu da muradin ranshi ba har yanzu, sai ku tayashi addu’ar samu nan kusa, in kuma wacce zata kasance muradin ran nashi tana sauraronshi to sai tayi fatan Allah ya hada ta dashi komin daren dadewa, zo kuga mata a gidajensu yadda suke amsa ameen, zulfa ta share kwallar dake idonta, dama ita tasan bazata taba haduwa da sadeeq ba, saboda yayi mata nisa sosai yafi karfin ajin mace marar galiho da gata irinta, amma muryar dake sata manta bacin ran da ake mata a gida yau zata ma kunnenta bankwana, , to saboda me zaiyi bankwana?? Ta tambayi zuciyarta, kafin ta samo amsar tambayar har ya gama amsa tambayoyin, cikin taushin murya yace zanyi bankwana daku masoyana, zan ajiye wannan progrm din saboda bukatar hakan ta taso, ina rokonku da duk wanda na taba batawa a rayuwa ya yafe min, na yafe ma duk wanda ya bata min, wadanda basu sanni a fuska ba ina adduar Allah ya hada mu daku a aljanna firdausi, nagode da kaunarku Allah ya kawo wanda zai maye muku gurbina, a karshe ina bukatar addu’ar ku akan Allah ya taimakeni ya bani nasara akan abin da nake nema, nagode, nagode Allah ya barmu tare,,, wakace ta cigaba da tashi a kunnuwan masoyanshi dake kuka, zulfah ta wurga radion bayan yagalgalalliyar jakar kayanta ta shiga kuka baji ba gani, daren da ya kasance mai cike da sanyi da dadi ga ma’abota soyayya, ya kasance dare mafi zafi da kuncin a gurin baiwar Allah zulfah….

Mrs tijjani shattima …
[15/12 14:47] Anty aisha ya’u kura: ●● ZULFAH ●● 2⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Washe gari tun biyar na asuba ta farka duk da ba wani isashshen bacci ta samu ba, tsakar gida ta fito taga tulin kayan wanki a kofar dakinta kayan goggo marka ne da na salaha, ta kalli kayan cikin faduwar gaba saboda yawansu ga danshin damina, ga kanta na masifar sara mata saboda rashin bacci da bata samu ba, ta zauna ta buga tagumi da buta a gabanta tana tunanin irin rayuwar da take ciki tun bayan rasuwar mahaifiyarta tana yar shekara goma take aikin bauta bata da wani lokacin farin ciki kullum tana cikin wahala, bata ko samun isashen abinci, wannan dalilin ne yasa ko da yaushe in kaga zulfa bata cikin walwala, bata kula kowa koda a makaranta ne, magana mai yawa tana yi mata wuya, in tayi magana ko kai wanda take ma maganar ba lallai bane kajita saboda tsabar sanyin maganar, tasha dukan asara gurin goggo saboda yanayin maganarta amma duk da haka bata sauya zani ba, saboda babu wanda zai iya canza nature, rankwashi mai karfin gaske shi ya katse mata tunanin da ta keyi, tayi maza ta sauka daga kan dakalin da take rike da kanta, goggo tace uban me kika zauna kikeyi agurin nan, duk ga ayyukan gidan nan babu ko daya da kika fara saboda tsabar iskanci da lalaci, to bari kiji kinga wannan wankin wallhy kika kuskura gari ya waye baki gamashi ba sai nayi mugun saba miki shegiya mai suffar mayu, ta wuce gurin kullun wainarta ta na masifa kamar zata ari baki, makota sun riga sun saba dajin muryar marka me waina a ko wace safiya, bare mahaifin zulfa malam ado da abin ya zame mishi jiki kuma bashi da yadda zaiyi ya fitar da yarshi daga cikin bautar marka, shiyasa a ko da yaushe yake fata da yi mata adduar samun miji tayi aurenta ta bar gidan, ya kudura a ranshi ko dan garuwa ne yazo neman aurenta in dai zai dauke mata ci da sha wallhy zai bashi, zulfa ta idar da sallah tayi yan adduointa, ta fito da sauri ta dauki katon bokitin penti ta shiga jido ruwa a mono din dake masallacin layinsu Allah ya taimaketa babu layi saboda gari bai waye ba,,,
saleem dan limamin unguwarsu kuma malamin islamiyyarsu shi ya ganta tana diban ruwa bayan ya fito daga sallah, cikin tausayawa ya karasa gurin mono din, tanata bugawa tana haki taji sallamarshi tayi murmushi a hankali tace ina kwana malam, lafiya lau yace mata yana kokarin fara tayata buga panpon, tace ka bari malam nama gama wannan shine na karshe, bai saurareta ba saida ya gama cika bokitin, ya sa hannu zai dauka ta rike gefen bokitun tace dan Allah malam ka barshi kar in baka wahala, kallonta yayi yace saki bokitin ki wuce muje, batayi musu ba ta saka suna tafe har suka kai kofar gidan, ya ajiye dai2 dakalin shiga gidan, shi kanshi da yake namiji saida kirjinshi ya dan amsa saboda nauyin bokitin,,,, ,
ya kira sunanta a hankali yace kiyi hakuri zulfa wuya bata dorewa, komai na duniya mai wucewa ne,,
kullum ki dinga addu’a Allah ya kawo sanadin da zai fitar dake cikin wannan bakar rayuwar, idonta ya ciko da kwalla tace nagode malam Allah ya saka da alkhairi,
yace ameen,, kinsan yau zaku fara jarabawa kiyi sauri ki gama ki taho makaranta, tace to nagode malam, ta dauki bokitin ta shiga ciki da sauri ta fara wanki sai gurin shida da rabi ta gama duk sanyin da akeyi zulfa bata ji saboda tsabar wahala, tana gama dauraya ta shanya wasu a gidansu ta shiga gidansu inna delu inda suke shanya ta shanya sauran,,,
hanne ce ta fito daga daki tana mika alamar yanzu ta tashi daga bacci, hararar zulfa tayi taja tsaki tace wahalalliya, a wahala zaki kare har karshen rayuwar ki sai shegen girman kan tsiya sai kace wata yar sarki, zulfa ko kallonta batayi ba saboda ta riga ta saba da duk wata masifar da inna delu da diyarta hanne suke mata, goggo ameena ce ta fito daga daki tace haba hanne ku sakar ma yarinyar nan mara tayi fitsari mana, da wanne zataji da na marka da salaha ko da naki ke da delu, ko dai wani ta kashe muku ya isa ace kun barta haka bare ba daya bare kanwar biyu,,,! haba ay nan goggo ameena ta kara harzuka hanne ta rufe ido tana surfa mata bala’i cikin raini har inna delu ta jita ta fito ta tayata suka dinga yi harda zungurin zulfa,,, faiza yar goggo amina ita ta taya zulfa shanya har suka gama ko kallon su hanne basuyi ba,
goggo Ameena tace faiza kice zulfa kar ta tafi ta tsaya taci tuwo, fa’ee tace to mama, taja zulfa suka zauna suna dan hirar jarabawa goggo ta kawo musu dumamen tuwon dawa miyar tafasa, nan suka wanke hannunsu da ruwa suka fara ci saida sukayi katt saboda yawan tuwon,
da sauri zulfa ta tashi ta deka dakin tace goggo nagode sosai bari in shiga gida, goggo ameena tace to zulfa ayita hakuri dai,, mai hakuri shi keda riba wata rana sai labari, tace to goggo nagode sosai, ta fito
tace fa’ee sai kin biyo ta fita da gudu da bokiti a hannunta, tana shiga ta tarar maza da yawa zagaye da goggo marka masu siyan waina sai hayaniya sukeyi, ruwan sanyi ta diba a ruwan da ta debo ta wuce bayi tayi wanka saboda yawan mazan dake gurin yasa ta dauko kodaddan uniform dinta ta shirya a bayin, dakinta ta shiga ta dakko robar vaseline ta dinga kwakuloshi saboda ya kare da kyar ta samu kadan ta shafa a fuskarta, gurin kitchen taje ta tsuguna tace ina kwana goggo, ta kalleta a wulakance ta amsa tace rikakkiya ina kuma zaki, tace goggo islamiyya yau zamu fara jarabawa, salaha dake zaune kusa da wani me napep sun hada kansu guri daya wai suna kallon waya tayi tsakii sosai tace uban waye zai gyara miki dakin,, haka zaki barshi da datti saboda ba a ciki kike kwana ba, zulfa ta marairaice ko kallon salaha batayi ba tace goggo yau zamu fara jarabawa kuma ance muzo da wuri walhy daga na dawo zanyi, murfin tukunyar dake gefenta shi ta wurgo ma zulfa ya sameta a jikinta duk manja da bakin tukunya suka b’ata hijab dinta, cikin tsawa goggo tace dan ubanki wuce kije ki gyaro ko ina kuma ki fita ki k’aro ruwa ki cika ko’ina na gidan nan, kiyi zaman jiran a gama waina ki wanke komai ki daura girki,,
idon zulfa ya ciko da kwalla ta mike ta shiga daki tanajin mazan gurin yan tasha suna shewa suna taya goggo aibata ta wasu ma har tafawa sukeyi da salaha da ke zaune a tsakiyarsu, ta gyara dakin goggo ,, ta fito ta dauki bokiti ta fita a kofar gida sukaci karo da fa’ee, fa’ee tace a’ah ina kuma zaki da bokiti, tace ruwa zan debo ki tafi kawai kar in bata miki lokaci, fa’ee ta fisge bokitin da karfi cikin tsiwa ta wurga shi cikin gidan taja hannun zulfa da karfi suka fita tana janta zulfa na tirjewa, hakan bai sa faiza ta saki hannunta ba har saida suka karya kwana, zulfah cikin muryar kuka tace fa’ee kinsan irin bala’in da kika jamin ne, meyasa zakiyi haka, kinsan bani da mafita dan wallhy goggo bazata yarda bani na wurgo bokitin ba, yau Allah ne kadai zai iya kwatata a hannunta dan yau kasheni ne kadai ba zatayi ba,
Kuka sosai ta tsuguna a kasa takeyi, fa’ee tace tsoronki shi ke ja miki matsala, kalleki zulfa wallahi kin wuce duka, amma kullum ayita kirbarki kamar jaka ke bazaki iya kwatar ma kanki yanci ba saidai ki zauna ki dinga kuka shiyasa duk suka raina ki, wani yanci fa’ee ni har inada wani yanci a rayuwata, mahaifina bai nemar min yanci ba sai ni zan nemawa kaina, fa’ee rayuwar nan da nake cikinta bana neman taimakon kowa sai Allah, shi kadai yasan dalilin barina cikin wannan halin, kuma ina gode mishi a ko da yaushe tunda ya barni da rai da—- da lafiya suka ji an karashe daga bayansu, fa’ee ta tsuguna tana murmushi tace ina kwana malam, ya amsa yana kallon zulfa dake ta faman kuka, itama ta gaisheshi, ya amsa a gajarce yace ku wuce maza makaranta dan lokaci na kurewa, fa’ee ta kamo hannunta suka wuce tana share hawaye, binsu yayi da ido cikin tsananin tausayi a ranshi yace Allah ka kawo sauyi cikin rayuwar baiwarka zulfa’u….

See also  Aymana Part 1 Romantic Story Hausa Novels

Mrs tijjani shattima..
[15/12 14:47] Anty aisha ya’u kura: ●● ZULFAH ●● 3⃣
By Aysha Ya’u kurah

Tafiya nakeyi da sauri duk kafata ta gaji saboda rashin abin hawa ga unguwar da zanje da nisa, a wani katafaren kayataccen gida kafata ta tsaya, gidan da zan iya cewa duk cika da batsewar GRA babu gida kamarshi, a kofar gate na tsaya saboda na duba gabas da yamma kudu da arewa ban samu hanyar shiga ciki ba, gefe na rabe ina dan hutawa kusa da wasu flowers, kamar daga sama na hango sojoji sun wangame gate din gidan, da sanďa na shiga gidan dan kar su ganni in shiga uku, tsaye jikin wata ford 2014 na hango wani magidanci kyakykyawa mai cikar zati da kyawun fasali cikin white uniform din navy kuma da dukkan alamu babban sojan ruwa ne, gefenshi wata kyakykyawar mace ce black beauty rike da wata farar yarinya da bata wuce 4yrs ba, kamaninta da namijin gefenta yasa na gane y’arshi ce, daga nesa na hango wata yarinya mai masifar kyau wacce shekarunta zasu kai 18 rike da kannenta biyu masu kama da junansu cikin kaya iri daya suna tahowa, kusa da macen suka tsaya, babbar tace yaya ina kwana, ya amsa cikin fara’a yana shafa kan twins, taja hannun babyn dasuke tare da ita tace adda laila gud morning, tace morning dear, kunga ku wuce ku shiga mu tafi kar su daddy su dawo bamu karasa ba, motoci biyu suka shiga kowacce soja ke janta sai wata da sojoji biyu ke cikinta, suka fita daga cikin gidan sojoji na sara wa motocin,,

Farar mace ce kyakkyawa zaune cikin kayataccen parlon da sanyi da qamshi ke tashi a ciki, tana zaune cikin wasu lafiyayyun kaya masu masifar kyau, 40rabbna ne a hannunta tana dubashi, sakkowar mutum naji daga sama na daga kai na hango wata kyakykyawar mace itama cikin shiga ta alfarma, fuskar nan tasha makeup, ta karaso ta zauna kusa da matar dake parlon, ina kwana “yaya” naji tace cikin fara’a, wacce ke zaune ta dago kanta itama cikin fara’a tace anty amarya kin tashi lafiya, lafiya lau tace suka cigaba da hira anan na gane amarya da uwargida ne,
Awansu daya da fita suka dawo gida,, da sallama suka shigo parlon wani farin dattijo ne ya fara shigowa sannan duk suka take mishi baya, wani saurayi na gani cikin uniform irin na jikin dattijon da nakeda tabbacin mahaifinsu ne, ya karasa kusa da matan gidan dake tsaye suna tarbar mijinsu, yace mummy, antyna gud morning, anty ta amsa tana shafa kanshi tace morning my son hw r u, yace am fine mun sameku lafiya ko, lafiya lau suka ce dukkansu,,
kowa ya nemi guri ya zauna anata yan hirarraki cikin farin ciki,,

Mrs tijjani shatima…
[15/12 14:47] Anty aisha ya’u kura: ●● ZULFAH ●●4⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Nasan masu karatu zasu so suji tarihin wannan gida to muje zuwa..

Gidan chief of air staff of the nigerian airforce “AIR-MARSHAL HASHEEM ABUBAKAR MARAFA”, nan na kaiku,, yanada mata biyu haj Aisha (mummy) itace uwargida, sai anty Hadiza ( anty amarya) yana da ya’ya 6 kuma duk ya’yan na mummy ne dan anty amarya bata taba haihuwa ba, Usman (Nurain) shine babba, sojan ruwa ne da ya samu nasorori da dama, yanzu haka shine NAVAL COMMANDER, yanada mata daya Laila da ya’ daya “Ayda”, yana zaune da iyalinshi cikin gidan iyayenshi, suna zaman lafiya dan laila mace ce mai kirki sosai da son mutane,
Abubakar sadeeq (abba) shine ďa na biyu a gidan, ya gama stanford univesity dake california, sannan yanzu ya samu training a university in “Montgomery albama”, “Air force university” inda zaiyi 2yrs yanayi, yanzu haka sunje sun gama komai na reg da mahaifinshi zai koma nan da 1wk, kafin samuwar training din ne ya fara programme a gidan radion liberty inda wata sec skool mate dinshi ke aiki “zee gayu”, tun yana yaro yake da son programs, dramer, da dai sauran abubuwan da ya shafi media, babu yadda baiyi ba akan mahaifinshi ya barshi ya karanci abin da yake so amma firr yaki saboda shi a ra’ayinshi yafi son jininshi ya yi soja kowane iri ne, da kyar mummy ta lallaba sadeeq ya yarda ya zabi sojan sama, basu sha wani wahala gurin samun skull din ba saboda matsayin mahaifinshi,,, sai Umar (farouk) shine na uku, yana Oxford uni, Jalila itace ta hudu, ta gama secndry skul dinta a dambo international skul, sai twins Afrah da Amrah yan shekara 7 suna primary 2 a legacy school,
Anty amarya ta damu matuka saboda rashin haihuwa, babu asibitin da ba’a kaita ba amma an tabbatar musu da bazata taba haihuwa ba, tun abun na damunta har ya daina damunta saboda yadda take samun kulawa gurin mijinta, ya’yanshi da matarshi, mummy na zaune tsakaninta da Allah da anty amarya, tana bata hakkinta saboda ta karanci hukuncin mai tauye hakkin dan uwansa, mace ce da zamu iya kiranta da mai kin duniya da kyalekyalen cikinta, kullum mummy kome takeyi bakinta baya rabo da tasbihi, anty amarya kuwa yar son a huta ce, rayuwarta gaba daya ta ginata ne akan karya, burinta tasa kaya mai kyau ta fita yawo sojoji na take mata baya, ta shiga cikin kawaye a fantama, dan ma Allah ya rageta da rashin haihuwa da abinda zatayi sai yafi haka abinda take yawan sakawa a ranta kenan,, ,,,,,

See also  Yaya Mustapha Hausa Novel A Romantic Love Story

Duk ranar jumma’a ake zuwa koyar da mummy karatun addini, wata yar bukka suke zama ita da matashin malaminta Saleem Abdulrahman, yauma suna zaune kamar kullum bayan sun gama karatu, jalila ta kwashe qurani da littafan tayi daki dasu, malam saleem yana dan kara ma mummy wa’azi kamar yadda suka saba, bayan ya gama, ya mika mata katin saukar dalibanshi da za’ayi nan da sati biyu, cike da murna ta amsa tace in shaa Allah zaka ganmu, amma bayan kun gama saukar zaka tafi law skool din ko, yace in shaa Allah hajiya, mummy tace Alhamdulillah to Allah yasa munada rai, yace ameen hajiya sukayi sallama ya tashi ya tafi…

Zaune suke da daddare a parlon gidan,, twins da ayda suna kwance suna home work jalila na koya musu, daddy da Nurain basu nan sun fita, sadeeq na kwance gefen mummy yana mata hira, can kuma anty amarya ce da lailah suke ta kai komo a kitchen,, murda kofar akayi babu sallama, helllo dearies ta fadi hade da tura kofar, jalila ta daga kai da sauri ta mike tace SANAH luv oyoyo, duk suka rungumeta harda twins, ta ajiye akwatinta ta karasa kusa da mummy da ke kallonta tana yake dan sam ďabiun sanah basu mata ba, ta rungume mummy tace mom ya gida mummy tace lafiya lau sanah ya ummanki, sanah tace fyn ta kalli sadeeq dake gefen mummy ya kasa dauke idonshi akanta, ta hura iska a fuskarshi, tace yaya abba ait, ya lumshe idonshi saboda wani qamshi da yaji a iskar, jalila ta jata suka dauki akwati suka wuce ciki, saida ta gama frshup cikin wata karuwar doguwar riga sannan suka fito parlor, anty amarya baki sake tace sanah yaushe kika shigo, mummy tace ay bazaki ganta ba tunda taga kawarta, sanah tayi dariya tace anty “dee” ya kike, tayi murmushi ta amsa tana cigaba da gyaran dining, sadeeq da yayi mutuwar zaune saboda kallon sanah, ya kara gyara kwayar idonshi ya tsaida su a kanta sosai, gaskiya yarinyar ta fisgeshi lokaci daya, wani irin sonta yakeji a can cikin ranshi, ta dace da irin matan da ya dade yana mafarki, shidai bai santa ba to a ina kowa yasanta a gidan su,
“SANAH HAMEED” yar yayar anty amarya ce dake zaune a abuja, mahaifiyarta yar siyasa ce babba, mahaifinta kuma custom ne, sanah ta tashi cikin gata da sangarta saboda ita kadai Allah ya ba iyayenta, rayuwar sanah gaba daya babu No a cikinta komai tayi dai2 ne, iyayenta sam basu kula da tarbiyyarta dan su a ganinsu komai tana yinshi bisa tsari, irin kayan da sana ke sawa in ka ganta zaka rantse ba musulma bace, kyakywace sosai doguwa ga kyan jiki ta hada komai na mace mai aji, sai dai hali daya mata cikas, Allah ya zuba ma sanah son kyawawan maza ko namiji baida kudi in dai kyakkyawa ne to ya gama da ita, dan sai tasan duk yadda tayi suka zama masoya, daga ta hadu da wani wanda yafi wancan zata yar dashi ta kama wani,
in dai akan namiji ne to sanah bata da alqibla ita kanta bazata iya kirga mazan da tayi mu’amala dasu ba tun tana js3 har kawo yanzu,, sadeeq yana makaranta lokacin da sanah ke zuwa hutu gidansu, har ta gama hutunta ta tafi basu taba haduwa ba, amma ita tasanshi sosai dan har hotonshi gareta….

Mrs tijjani shattima…
[15/12 14:47] Anty aisha ya’u kura: ●● ZULFAH ●● 5⃣
By Aysha Ya’u Kurah

A hankali take leķen gidan da ganin idonta a firgice take, ganin babu kowa a tsakar gidan yasa ta karanta addu’a tashiga ciki tana waige, ta kai dai2 dakinta taji an fisgota da karfi har saida hijab dinta ya yage sosai a wuya, fitsari ta saki a wando saboda yanda taga idon goggo marka babu imani a cikinsu hannunta rike da wani murďaďďen sanda wanda ta saba dukanta dashi, durkushewa zulfa tayi idonta yanata ambaliyan ruwa, cikin sanyin muryar kuka tace goggo dan girman Allah kiyi—- saukar sanda taji a bakinta ta fara ihun neman taimako, dukanta marka takeyi babu ko digon tausayi a ranta, saida ta tabbatar ta mata liss sannan ta kyaleta ta wurga sandar gefe tana huci, tace dan kutumar ubanki har ni zan saki aiki saboda ke tabbatacciya ce tsinanniyya, har kinada karfin gwiwar wurgo min bokiti daga waje, to tsaya kiji in kina ganin kin fara balaga nonuwa sun tsuro miki kina ganin yanzu kin ri’ka kamar rikakkiyar kubewa, tashen balaga zai fara bayyana kanshi, to bari kiji in fada miki wallhy kinji na rantse da Allah daga yau karfe hudu zaki dinga tashi a gidan nan, waina ma na daina zaman suyanta ke zaki dinga soyawa kina siyarmin, islamiyya kuma sai dai kiyi a lahira in anayi, haka boko ko kun koma hutu na haramta miki shi, duk ranar da kika kuskure abu daya cikin abinda na lissafa miki hummm”” zulfa’u ki kira kanki gawa kinaji na, eh ta fadi a hankali jikinta ciwo yake mata sosai, zafin da takeji a zuciyarta yafi wanda takeji a jikinta, yanzu shikenan an hanata zuwa islamiyyar da saura kwanaki tayi sauka, kuka ta dingayi a gurin taji an sa kafa anyi ball da ita, a tsorace ta fara rarrafawa tana kuka har ta kai ďakinta, hada kanta tayi da gwiwa ta cigaba kukan da babu mai rarrashi, yanzu shikenan babu wanda zai kwatar mata yancinta, shikenan ita haka zata kare cikin wahala, ta dade tana kuka kiran sallar azahar ne yasa ta ta mike dan taje tayi sallah, tana kokarin mikewa kafarta tace bata san zancen ba, ta koma da baya ta xauna hawaye na bin idonta, targade goggo tayi mata a hannu da kafa, da jan jiki ta fito ta shiga bayi ta dauraye jikinta ta canza kaya, tayi alwala ta koma daki tayi sallah, ta dan kwanta dan taga fitar su goggo da salaha, bacci ne yayi gaba da ita, bata san lokaci yaja har haka ba saboda baccin yayi mata dadi ko ba komai ta dan huta, ruwa taji an sheka mata a jiki, ta farka tana waige2 a firgice, ga warin da ya ishi hancinta, ta kalli jikinta cikin kyankyami ta kalli salaha, tace ruwan kwata kika watsa min, innalillahi kadai take fadi a ranta ga wani amai daya taso mata, salaha ta wurgo mata bokitin jikinta tace an watsa miki ko kina da abinda zakiyi ne, zulfa ta girgiza kanta tace babu,, Allah ya isar min, salaha tace kambuu lallai yarinyar nan, ni kike ma Allah ya isa, zulfa ta mike da kyar tana dingishi salaha ta kara tare kofar dakin rike da kugu tace dan uwarki wa kike ma Allah ya isa, zulfa tayi banza da ita zata bi ta gefe ta fita salaha ta hankada ta da karfi kanta ya bugu da bango, rike kanta dake juya mata tayi kwata2 bata iya gane zagin da salaha ke mata saboda azaba, ta dade a durkushe tana kuka kafin nan ta fita ta cire kayan jikinta tayi wanka ta yi alwala da kyar tayi sallah, ta fito jiri na ďibanta ta fara iza murhu har ya kama ta daura ruwan talge, a daddafe take aikin har ta gama abinci goggo marka bata dawo ba, ta gyara ko ina ta dauraye kayanta, sannan ta shiga daki ta dan kwanta idonta kamar an daura dutse, sallamar babanta taji a hankali bayan magriba ya dauka marka ta dawo daga gidan biki ne, ďakinta ya leka yaga bata nan, da sauri ya fito ya shiga ďakin zulfa, a hankali ya ďan bubbugata ta mike a firgice, yace zulfa’u ni ne, ta mike a hankali ta zauna tace ina wuni baba, idonshi ya ciko da kwalla saboda yadda yaga jikin yar tashi yace dukanki sukayi ko, ta fashe da kukan da take boyewa ya rike hannunta yaji zafi rau yace kiyi hakuri zulfau, nasan komai ake miki a gidan nan nine sanadi, ki yi ta addu’a komai na duniya mai wucewa ne, kuma wata rana sai labari, zuciyar zulfa ta kara zafi a ranta tace kullum sai ace mata wata rana sai labari wai ita yaushe labarin nan zai zo har ya wuce ne,, cikin muryar kuka tace baba” goggo tace bazan kara zuwa islamiyya ba kuma jarabawar sauka mukeyi, dan Allah baba ka taimakeni kar a katse min karatuna, ya rungumeta sosai ajikinshi shima kukan yakeyi dan yasan marka baxata taba janye kudirinta ba, yace kiyi hakuri zanyi miki kokari zulfa share hawayenki, ya dagota yana share mata hawaye itama ta share mishi nashi, da sauri yasa hannu a aljihunshi jikinshi har rawa yakeyi ya dauko leda ya bude nama ne yanka biyu ya fito dashi yace dazu aka kawo naman walimar sunan y’ar datti shine aka raba mana kowa bibbyu shine na kullo miki nawa, karbi kici yakai bakinta, ta rike hannunshi tana kuka tace baba kaci daya nima inci daya ya kara share mata hawaye yana girgiza kai yace kinfi ni bukatarshi cinye duka kinji, tasa hannu zata karba taji an warce naman ana huci kamar kura, suka dago kai suka kalleta tana kallon naman tana huci kamar bata taba cin nama ba, tace nama, nama ne fa salaha ta fadi tana nuna ma ‘yarta, tabdi lallai ado ka cika munafuki, yaushe rabon da muci nama a gidan nan shine yanzu dan kaga bana nan ka kullo ka kawo mata, tayi kan zulfa da jikinta ke rawa tace dan ubanki nawa kikaci, yau sai kin amayar dashi duka, ta danneta zulfa na kakari tace wallhy ko daya banci ba goggo, da kyar malam yayi ta maza dan yaga ana kokarin raba yarshi da ranta ya tura marka da karfi, cikin zafin nama kamar namiji tayi kanshi tana dukanshi har saida ta yaga mishi riga, hakuri kawai yake bata tana kara turashi tana masifa, kabiru ne ya shigo da sauri saboda yaji hayaniyar tayi yawa, dakyar ya iya rabasu yana kuka yace haba goggo wai meyasa kike irin wannan abun ne, ji yadda—- mari ta kai mishi har biyu tana huci tace to sallamame watsatstse wanda baya kishin uwarshi, wallhy ka kara fadin kalma daya anan saina daga maga nono shege dan iska, kabiru ya rike kuncinshi ya fita ranshi a bace, zuciyarshi na kara jin tsanar mace, ya kudira aranshi bazai taba yin aure ba har ya mutu in dai haka mata suke, a cikin gida kuwa marka nata masifa,, abinda zai baku mamaki bai wuce duk damben da marka tayi baisa ta saki naman ba yana nan makale a cikin hannunta, saida ta gaji dan kanta tayi shuru ta wuce daki, salaha ta bita tace goggo ina naman, ta harari salaha tace yana can a waje na watsar, salaha ta fita da sauri harda daukar fitila, tana fita goggo marka ta watsa naman a bakinta duka biyu, salaha tayi ta neman naman harda dakin zulfa saida ta duba ko ina kamar mayya, daki ta koma tana nishi tace ban gani ba goggo babu mamaki wani a cikinsu ya dauke, ummm goggo tace saboda naman na bakinta bata gama taune shi ba, salaha tace goggo dazu kinsan yarinyar nan zagina ta dinga yi, goggo dai ta kasa cewa komai saboda kar salaha ta gane abinda ke bakinta, salaha tace goggo kinajina kuwa, uhumm goggo tace tana kokarin kwanciya, salaha ta matso kusa da ita ta dafata tace wai goggo me yasameki ne, goggo ta kifa kanta a katifa tafara kukan karya tana ummmm, salaha tace to goggo meye na kuka, ay tunda kin musu laga2 xasu shiga taitayinsu goggo bata dago ba tana kokarin hadiye naman ta kware sosai ta dago da sauri tana tari ragowar da bata hadiye ba suka zubo ta dinga tari tana kakarin amai, salaha ta debo ruwa da sauri ta bata ta sha zata ajiye kofin a kasa taga naman da goggo ta fito dashi, salaha ta kara haskawa ta tabbatar nama ne, ta dago kai ta kalli goggo, ta tabe baki tace walhy gogg—- cikin sarkakakkiyar murya tace Allah ya tsine ma wanda yayi min magana ta juya bayanta ta kwanta idonta zuru2, salaha ta tashi ta fita tana girgiza kanta aranta tace mugunta fitsarin fako, lallai goggo ta shahara a mugunta, dama hausawa sunce bazaka taba kwarewa a mugunta ba har sai kama naka, walhy saina rama abinda goggo tamin tayi kwafa ta fita daga gidan gaba daya………

See also  Download Kaddarar Mu Ce Hausa Novels

Mrs tijjani shattima….
[15/12 14:47] Anty aisha ya’u kura: ●● ZULFAH ●● 6⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Washe gari ta tashi da wuri kamar yadda goggo ta umurceta, aikin gidan tayi gaba daya tana yi tana hutawa saboda hannunta, karfe shida da kwata ta iza wutar waina, tana zaune hayaqi ya turnuke gurin idonta ya cika da ruwa tana ta fiffita ga yunwa tanaji sosai,,, saida tandar ta dau zafi sannan ta fara suyar wainar, maza da yara suka fara shigowa cikin gidan, ta na suya tana siyarwa,,,

sallamar wani wanda a kullum idan yazo gurin ke kaurewa da ihu saboda siyan ma duk wanda yake gurin yakeyi,, hannu ya daga musu yana zukar wiwi, ya kalli zulfa da ke iza wuta ya shafo gefen kunnenta, tayi maza ta ja baya ta dago kai tana kallonshi, yayi murmushi yace kuce yau yar kyakykyawa ce ke mana waina, ya daga murya da karfi yace a kira yara a basu waina yau waina ko daya bazata rage ba,,, wani yaro a gefe ya fita yana ihu yana fadin sai baban house Allah yaja zamanin baba uban baba, ya kara kallon zulfa ya matso kusa da ita sosai zai rike hannun ta, ta watsa mishi kullun wainar a fuskarshi, ta mike tsaye tace wani irin iskanci ne wannan, yan tashan dake gurin suka fara ihu suna bangis din kikayi wa haka, tayi tsaki ta cigaba da zuba kullun cikin tanda, sunata hayaniyar su, bangis bai kallesu bare ya tanka musu, hayaniyarsu ita ta fito da goggo da sauri tana hamma tace lafiya dai kuka cika min gida da ihu, ta kalli bangis da ya cika ya batse, ta dunkule hannu tace Allah yaja zamanin ka mai gidan masu gida, laminu dan koranshi yace dalla matsa can da wannan kirarin naki, in ba iskanci ba wannan kazamar yarinyar ta rasa wanda zata watsa ma kullu sai bangis, yau sai munga wanda ya tsaya mata dan uwarta, goggo ranta ya baci matuka saboda in bangis ya daina zuwa gurinta siyan waina ay ta kaďe, ta matso kusa da zulfa gadan2 har tana gurďe kafa, wani katon ice ta dauka zata buga mata, zulfa ta rintse idonta haďe ihu mai karfin gaske, da sauri bangis ya rike icen, cikin muryar kauraye yace haba haj markus, irin wadannan kayan masu tsada ay ba’a dukansu, barta taci bashi, zata biyashi nan bada dadewa ba, ya wurgar da icen gefe ya goge fuskarshi ya zaro dubu uku ya mika ma goggo yace ki raba ma yara wainar yau, ya shafi gefen hannun zulfa ya rintse idonshi hade da zukar wiwi, yasa kai zai fita goggo dai sai kallonshi takeyi cikin mamaki dan tasan bangis ba’a takashi a kwana lafiya, har ya kai kofa ya juyo yace zan auri yar nan taki markus nan da sati biyu, sai ku fara shirye2, ihu mutanen gurin suka Sá sunata fadin sai kayi wallhy,,
Goggo marka ta kasa dauke idonta daga kofar waje, tana mamaki aranta, ta waiga ta kalli salaha dake tsaye bakin kofa ta kumbura tayi fammm, dan ba karamin so takeyi ma babangida BBG ba, daki ta fada da gudu tana kuka, zulfa ma kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita, ya za’ayi ta auri bangis, innalillahi wa inna ilaihir rajiun shi ta dinga faďi, a ďaki kuwa baban zulfa ne ya dafe kanshi saboda jin furucin babangida, dan ba a unguwar “babbar saura” ba ko ina an sanshi a unguwar rimi da kewayenta, ya ďaga hannunshi sama idonshi na zubar da hawaye yace ya Allah kaine kake da hanyoyi da yawa wanda bamu san dasu ba, Allah ka kawo mana hanyar da take billewa cikin gaggawarka ni da ďiyata zulfa’u…..

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top