Zuma a baki Hausa Novel Free Pages

ZUMA A BAKI

 

 

 

 

 

 

Bisimillahir Rahamanir Rahim dukkan yabo da godiya sun tabbata ga sarki buwayi gagara misali Allah mai saman bakwai Allah mai ƙasan bakwai Allah mai rufin asirin bayinshi, Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaba jagaba annabi muhammad s.a.w Amin, Alhamdulillahi ya Allah daka kuma dawo dani acikin wannan sabon littafin bayan na kammala AUREN BARE lafiya Allah yadda na soma lafiya kasa na gama lafiya kai riƙo da hannayena Allahumma Amin.

 

My fans yauma gani tafe da sabon littafi mai cike da sabon salo, ina roƙon ubangiji daya baku iko tare da ƙarfin biyoni acikin wannan labarin Amin summa Amin.

 

Gargaɗi wannan littafi mai suna a sama labarin ƙirƙirarre ne daga gareni ban yarda a juyamin shi ta kowace sigaba wanda yaga yayi dai dai da tasa rayuwar yayi haƙuri akasi aka samu amman labarin tsararre ne daga wajena.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*001*

 

GARIN KANO

ÆŠorayi Unguwar Bello

 

Cikin lokaci Æ™alilan na kammala shirina cikin shuÉ—iyar atamfa mai ratsin ja’ ajikinta senai amfani da jan mayafi mai adon stone mai yawa ajikinsa, jakata na É—auka mai kalar ja itama senai amfani da jan takalmi kasancewar kalar fatar jikina baÆ™a ce shiyasa wannan jar kalar dana ratsa cikin shigata taimin masifar kyau.

 

 

 

 

 

 

 

 

Kallon agogon dake cikin É—akinmu nayi da sauri na waro idanuna waje har ina É—an jan numfashi tare da saurin É—aukar lesson plan É—ina nai gaba har ina haÉ—awa da É—an gudu-gudu kaÉ—an sabida ganin lokaci yana ja kada nai latting zuwa makarantar danake koyarwa.

 

Abakin Æ™ofa na tarar da anisa Æ™anwata ta uku tana faman waya wadda daga gani da saurayinta takeyi, dan naga se faman kashe idanunta take tana faman Æ™asa da murya, tana ganina ta miÆ™e da sauri har tana Æ™oÆ™arin yarda wayar hannun nata, tana cewa, “YAYA HUMAIRAH’ har kin fito kenan?”  ina tafe ina É—aura agogo a hannuna na ce mata “eh! anisa sena dawo ina Anty take?”   “tana can cikin É“angaren Baffa Æ™arami wajan ganin lefen sadiya, “tom idan ta dawo kice mata na tafi school amma ta duba saman madubinta zan aje mata kuÉ—in cefane”   “tom anty ALLAH ya kiyaye hanya” aÆ™asan leÉ“ena na amsa mata da amin sannan na saka kaina nai gaba abina.

See also  Yar Malam Taki Halin Malam Hausa Novel

 

Da ƙyar na sami abin hawa zuwa cikin unguwar ciranci domin anan makarantar danake koyarwar take kasancewar tsakanin mu da ɗan tazara kaɗan, gashi makarantar private school ce sam basa yarda da yin latti ko kaɗan dan yanzu kace zaka makara se anemi korarka shiyasa iya yina nike domin  ganin na kare mutuncin kaina wajan mai makarantar dan kada ta cimun mutunci kamar yadda naga tanai wa sauran staff ɗinsu danni kam bata taɓa min ba dan ba makararar nikeyiba.

 

Duk da haka ban samu shiga da wuriba se wajan ƙarfe taran safiya na ƙarasa, da sauri na zaro naira hamsin cikin jakata na baiwa mai ɗan sahun tare da nufar cikin gate ɗin cike da kuzarin jiki.

 

Abakin office É—in da muke singh na tsaya tare da zaro biro daga cikin jakata na nufi cikin office É—in, da sauri najawo singh book din dake kan teburin na fara yin singhning É—in sunana, ina kammalawa na É—ago idanuna haÉ—a idanu mukai da malamar english cikin far,a tace  “a,a yau malama Humairah nake gani da ranar nan haka hala ko lafiya dai?” murmushi na Æ™ago akan fuskata tare da cewa “wallahi makara nai bara na Æ™arasa aji” na faÉ—a yayin danake mayar da birona na nufi cikin makarantar É“angaren ajin danake koyar dasu darasin social studies.

 

 

 

 

 

 

Cikin ladabi É—alibaina ke gaisar dani har na aje jakata akan tebur nan nafara binsu ina duba aikin dana basu na É—auki kamar minti goma ina faman yin abu guda kafin na kammala na koma wajan zamana tunda tsarin school É—in na teacher par class ne, cikin haka naga masinger dake aiki a office É—in shugabar makarantar yazo aguje cikin rawar jiki yake sallama cikin ajin danake.

 

Ƙarasawa nai gabansa cikin mutuntaka muka gaisa dashi sannan na dubesa tare dace masa “masinja lafiya dai?”   “eh! lafiya daman ranki shi daÉ—e ce keson ganinki”   “ni kuma?” nafaÉ—a ina mai nuna kaina da yatsana guda tare da waro idanuna waje asual, “eh kefa malamar primary one koba malama Humairah Yusuf bace?” yafaÉ—a yana mai kallona, “eh nice jekace ina zuwa” da sauri ya juya nima komawa nai cikin ajin na dauki wayata batare dana dauki jakata ba na nufi cikin office É—in mai makarantar.

See also  Inayah Hausa Novel Complete

 

Cikin ladabi muka gaisa da matar wadda waÉ—ansu malaman ke mata kallon marar mutunci amman nikam bandani tunda bata taÉ“amin ba ko sau É—aya,  da far,arta da komi ta karÉ“eni harda cemin ga waje na zauna bayan na zauna ne ta dubeni sannnan tace “malama Humairah ya akai yau kika makara keda bamu saba ganin hakan daga garekiba?”  cikin jin kunya na dubeta tare da cewa “dan ALLAH kiyi haÆ™uri insha ALLAH hakan baze kuma faruwa ba wallahi yau É—inma akasi aka samu” murmushi ta Æ™ago kafin tace shikenan  babu komi tashi kije ALLAH yay maki albarka.

 

 

 

 

Sannan dan ALLAH idan babu damuwa kizo ranar juma,a ki karɓi addiress ɗin gidana ina son ganinki ranar asabar tunda babu school sabida da akwai maganar danike son yi dake.

 

“Babu damuwa nagode ALLAH ya nuna mana lokacin”   na faÉ—a ina mai tashi tsam na fita daga office É—in.

 

Harna koma class ina tunanin wannan wani magana ce da shugabar makaranta bazata gayamin ba harse na je gidanta, nifa bana son irin wannan shige-shigen sam duk da kasancewarta matar ƙanin umma matar baffa ƙarami ƙanin mahaifina amman sam har yanzu ban ko taɓa zuwa gidan taba duk da irin faɗan da umma takemin na rashin ziyarar dangi.

 

Ƙarfe ɗayan rana na mike tare da nufar masallaci salla nai tare dayin addu,a akan lamarina ubangiji ya isar min yay min maganin matsalata wadda take addabar zuciyata.

 

Ina idarwa na koma class na dauki jakata ganin lokacin tashin yaran yayi sallama nai masu tare da nufar gate  batare dana sha wata wahalaba na samu mai ɗan sahu nai masa kwatancen anguwarmu tare da shiga cikin adai daitan na zauna gaba ɗaya wata mahaukaciyar yunwa nikeji acikina sabida ban ko karya ba na fita duk yadda anty da umma ke min faɗan yunwa amman sam bana ji shiyasa in ulcer ɗina ta motsa min sena dangana da asibiti.

See also  Kalaman Soyayya Masu Dadi

 

Cikin mintuna goma mai napep ɗin ya kaini ɗorayi kasancewar layinmu da ɗan tazara da titi yasa na soma takawa da ƙafafuna duk jikina agajiye haka nan hannuna ya ƙage sabida nauyin jakar dake hannun nawa.

 

Tun daga farkon layinmu naga dan dazon matasan layin dama sauran da bana layin ba sunyi zaman jarabar kamar yadda na saka musu sabida yawancin su rashin aikin yine kan sakasu wannan zama domin inda suna da aikin yi da bazasu zauna zaman jarabar saka idanu ba, domin babu abinda ake a wannan majalissar face tsageranci da rashin daraja wasun suma kan ɗan taɓa shaye-shaye a wurin domin nakanji warin hayaƙi na tashi inna zo wucewa.

 

 

 

 

Sosai na haÉ—e raina tamau na kame jikina waje É—aya kaina sunkuye haka nazo gab da su zan gifta araina nake ayyana da ranar Allah amman bazasu huta ba.

 

Sautin dariya naji daga bayana kafin naji fitar sautin É—aya daga cikin samarin wajan.

 

“Waini kam B.smoll wannan ba tagidan su Æ™waro bace?”

Ina jin wanda aka kirawo da b.smool É—in yace.

 

 

“Sosai ma ai yayar Æ™waro ce Æ´ar gidan yayan babansa ce shegiya mai baÆ™ar fuska se uban girman kai kullum haka zaka ganta kamar ta faÉ—i, ita bata yarda ba Æ´ar boko, se tsabar baÆ™in jini duk Æ™annenta sunata É—agawa amman ita har yau babu wanda ya taya” Banji abinda É—ayan ke cewa ba na Æ™arasa gaban gidanmu.

 

Dab da zan shiga xauren mu naji hayaniyar su na tashi.

“Se OGA CIKA DAJI”

Haka naji majalissar tasu ta kaure da faÉ—i wanda sautin muryarsu tayi dai dai da sautin bugun zuciyata.

 

 

 

SANNU SANNU.

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top