Zuma da Madaci Hausa Novels

ZUMA DA MAD’ACI Na Maman teddy

*ALHERI WRITERS ASSO.*

*A.W.A*

“`Kungiya masu aiki da nazaru da ilimi,Alheri sai dan Alheri“`

_________________________

*Episode 1&2*

~Happy sallah to muslim Al’ummah,Allah kabamu falalar watan ramadan Ameen summa Ameen….~

*ABIN ALFAHARI NA*
Gare ku iyaye na,Abin Alfahari na,ina matuk’ar godiya abisa tarbiyan da ku ka bani,Allah yak’ara nisan kwana Ameeen ya Rabil Alameen.

 

 

Wannan littafin sadaukar wane ga duk wani mai kaunar labrn Mmn teddy, wannan yar k’aramar kuma Babban su,wanda ta saba nishad’antar daku da dadad’an littafan ta,mai sanya ku nishad’i da faranta ranku don nasan tabbas baxaku manta da littafin ta mai suna.

 

 

*YAR AIKI* ba, Ga kuma uwa uba*DIJAMA Y’AR FULANI* Hmmm ummmm ga kuma *BINTOTO* Hmm wannan shiru xanyi don nasan bakwa buk’atar sharhi dan gane ga wannan book d’in… To a yau ita ta taho maku da sabuwa mai dauke hankali da kuma sanyaya xukatan ku, wato *ZUMA DA MAD’ACI* Dajin sunan kunsan da badak’ala, labrn da ya xo maku da sabon salon,don Alkalamin ba irin tasu bace, ku dai keep following. Don tabbas xuma da Madaci shidin ko a littafan wannan marubuciya na daban ne.

 

 

wannan book kaman yanda kuka sani ta kudi ce labarin,Zaki turo #200 VIP, #300 SPC,#100 NORMAL. Duk ta k’ark’ashin wannan number 07064551049 / 07064551049 .

*__________________________*

*بسم الله الر حمن الر خىم*

Tafe nake ina mai yin wani irin sauri kaman zana tashi sama,ta kalmin k’afa ta ko wato slipers tuni suka sid’e kasan ya cinye,amma saboda tsantsan rashi da talauci ya hanani siyan wasu. babu muryan wanda
nakeji yana mani amo a kunnen na irin na Oum Rabi. K’wallah ne ya fara xubo wa a kan fuska ta,ina mai tunanin abun da xan tadda a cikin gidan namu. bana ko iyah kallon gaba na,buri na shine na ganni a k’ofar gida kawai.

 

Ga kuma tunanin Hajiya Zaituna da ya dame ni,don nasan yau tabbas zan fuskan ci hukunci a bangaran aiki na dana saba yi mata a cikin gidan ta.

 

Da wannan tunanin na riski gida, bin gidan namu nayi da kallo, a raina ina cewa” Allah sarki marayun Allah kenan,ko mu duniya ya xata kasance damu. tsayawa nayi ina mai kare ma gidan kallo,kaman wannan shine ganina na farko da shi. Wasu bulo suna mai gab da watsowa garun ya rushe,ga shi ko ina na garun ginin k’asa ne. bin kofar gidan namu nayi da kallo,abun ma anan tafi lalacewa don k’ofan falangyene,shima ya rabu da jikin shi,amma har ilah yau Ankasa gyara shi. girgixa kai nayi kurum ina mai sharan gwallah,sannan na kutsa kai ixuwa cikin tsakar gidan namu. Komai tsaf kaman ba mune muke cikin tsantsan ta lauci ba. Saurin shigewa Daki na nayi,ina mai godiya ga Allah da yasa Ban had’u da Zaid ba. da6e k’afata take a tur6ayan dakin da nake kwana,don ko arxikin Siminti babu,can gyefen yar filangyen Katifa ta na nufa hadi da dauko wani buhun gana must go,da yan kayana ke ciki wanda gaba dayan su basu kai Guda 5. duka kodaddun a tomfofi ne,sai kuma rober atampha guda biyu shima,wanda sam bana son saka shi saboda kama mani jiki da yakeyi. D’auko wasu fararan kaya nayi masu kama da uniform ina mai saka shi jikina,sai kuma arsh din hijabin da baifi iya kugu na ba,nasaka ina mai xura safa kaman wanda xan tafi makaranta. wani farin ta kalmi na saka,gaba daya na fito kaman yanda Hajiya Zaituna ke bukatan ganin ko wani ma’aikaci na cikin gidan ta.

 

Kaman daga sama naji muryan Zaid yana bala’in da yasaba yi a kaina.

 

Oummah wai Suhaimah ta shigo kuwa,ko ko tana can yawon banxan nata. kallon sama da k’asa Oummah Rabi tayi masa sannan ta ta6a baki tana cewa ina xan sani,nima dan uban ta jiran ta nake tayimun sukola. ta fadi tana mai cigaba da watso da kayan dattin ta. cike da rawar jiki nayi saurin fitowa daga d’akin jikina banda rawa babu abun da yake yi. Murya na rawa nace Oummah Barka da gida”.

 

 

Cike da masifah ta dago kai tana cewa” au dama kin dawo?. ehhh nace da itah a takaice inah mai nufan ta da karban kayan dattin hannun ta,ina fadin Oummah bara nayi sauri na wanke kayan!!!. Shiru Oummah tayi don so da yawa idan tafara mata fitina,yanayin sanyin suhaimat sai yasa tayi shiru ta tsaya tana mai tunanin Rayuwar ta itah da d’iyar nata Suhaimart. Shiru tayi kawai sai Muryan Zaid mukaji yana cewa” Kehhh Suhaimart Ina kudin da nace kije ki nemomun iyeh? ya fadi cike da masifah da kuma muryan Yan Allah ka shirya.

 

 

Oummah na ne ta kalle shi cike da masifah tafara cewa” Fita idona na rufe Zaid, Suhaimart ne xata nemo maka kud’in da xaka sha abun shaye²? ke dama bana ce kar ki fita kije ko inah neman masa kudi ba,koda ko kasheki zaiyi da duka?. Jikin a ne yahau ky’erma a sanyaye cike da sanyin murya ta nace” Oummah don Allah kiyi Hak’uri.

 

Tsaki Zaid yajah hadi da ficewa yana mai banbami bata nemo masa kudi ba. Itako Oummah sai da ta gama tsitsayamun tsiya sannan ta bar tsakar gidan hadi da nufan soron ta.

 

Bayan shigewanta ne na tsaya ina rarraba ido,nan take komai tun daga farko ya fara dawo mun I LOVE YOU SUHAIMART”.I LUV U TOO HUDAY,. gigif nayi ina cigaba da aikin da Oummah ta bani inayi ina tunanin shikenan Huday ya mutu baxai dawo gare ni ba. hawaye ne yafara bin kuncinta. a haka na kammala wanki na,sannan ko d’aki na ban koma ba,nayi saurin nufan gidan Hajiya Zaituna.

 

 

Tun daga nesa nake bin Tanfatsetsen gidan da gabaki d’ayan sa kewaye yake da Sojoji kasancewar mai gidan Soja ne Babba,wato Gen. Yak’ub d’an larabawa… cike da sauri na kutsa kaina ixuwa wajen gate din, Da isana nan Sojojin da securities kowa ya Hau kiran suna na Suhaimart” Suhaimart…” cike da smilling face dina wanda yasa dimple dina suke k’ara shigewa ciki sosai,wasu ina bin su da murmushi wasu kuma ina gaisar dasu da ce masu Barkan su da Rana”. Kafin su bani amsa nayi saurin shigewa cikin dank’areren gidan hadi da nufan side din Doc. Zaituna da yan aiki irina suke acan suna mata hidima,don dama mu anan barayin ta muke mata aiki. Dai² wani coridour ne a palourn ta daya gaji da kayan alatu da more Rayuwa,komai ka gan shi a falon kud’ine d ya amsa kudi, komai na falon na zamani da tsantsan wayewa komai a falon Jah ne da milk. sai tum² da aka jera su a tsakiyan falon yyn dana Hango Doc. Zaituna zaune ta wani kishingid’a tana aikin isan k’adagin da tasaba,domun Doc. Zaituna irin matan nan ne masu isah da izzah,gata da iya gadara da arxik’i don a ganun ta a kullum talaka bawan tane,domun kudi xai mata komai a rayuwa,a ganin ta har mutum xata iyah siya.

 

 

 

Koda na shigo falon a sanyaye cikin takona na a hankali na tako inda Maikatan irina suke a tsaye,ko wanne sanye cikin shigarta na masu aikin wato farar wando,riga da hijaab Arsh colour iya kafad’a. yanda kasan mutum bai shigo ba haka Doc. Zaituna ta nuna don daukan ruwar roban gaban ta tayi tana kora ma makoshin ta. sukuwa sauran ma’aikatan kowa duk’ar da kansa kasa yayi yana mai tausaya mun,don ansan fitinan da xan sha a yau mai yawa ne,don karamun laifi kayi xata ce tayi maka dedoction din salaryn naka. Oumu Sulaym ne tahau washe mun Baki tana mai cewa a hankali Besty Suhaimart dina xonan. tana nuna mun inda take tsaye….

 

A hankali na matsa inda oummu sulaym take,ina mai gaisar da Hajiya Zaituna tunda sunan doctor ce mu kirar ta muke da Hajiya Zaituna, Ya tsina baki tayi kan daga bisani ta cigaba da bayanin ta batare da ta amsa gaisuwan nawa ba,don ita haka halaiyar ta ga talaka yake,samm bata son talaka,bb mahalukin da tafi tsana a rayuwar ta irin talaka,don ko fadin sunan talaka ba tayi,sai dai tace gayyar fitina”. Wannan kenan,ban wani damu ba,nasaki mata murmushi don dama wannan dabi’a tace, Muryan ta naji tana cewa” Okay don haka tun daga yau a fara shirin tarban d’ana. banason kuringa mun shirme don xan sallami mutum kuje can gidan iyayen ku kucigaba da cin k’asa,ta fad’i tana tabe baki,sai da ta bata mana kusan 15 muna a tsaye sannan tace mana,ku wuce ku bani wuri. Mhiss Caterine ne ta hau ce mana kowa ta koma bakin aikin ta. sum³ duka muka fara nufan bakin aikin mu,wanda Mhiss caterine ta kasance itace shugaban mu wato yan aikin Haj. Zaituna don aikin mu shine shara goge² cleaning dakuma Cooking.

 

 

Nufan side din mu maikata mukayi nida Oummu Sulaym don ana cewa mu wuce taja hannu na tana nufan wani side da aka bamu mai kama da Resting room. Tun a hanya tafara kallo na tana mai cewa” ohh ni Sulaym wannan duniya ina xata kai mu ne Besty!?, Ace talaka ya koma yanda kasan bawa daga aiki,ae wlh wannan Abun da ake mana ko bayin gidan sarki baxa’a masu haka ba, sai kuma ta dora hannu a fuska tana mai rafka ta gumi,wanda nidai ban da murmushi babu abun da nakeyi mata.

 

A haka muka shiga side din mu dai² na zauna ne tayi saurin cewa” Besty wlh har nafara tunanin zuwa mune mi aiki a cikin gidan sarkin Zaria,sarki mai Adalci kenan,mai mayar da bawa tamkar d’an gida. Jin yanda Sulaym ke xubo xance kaman wanda tasan sarkin yasani washewa da dariyan da ban shirya ba,don so dayawa ko banjin dry, Shiyasa kuma a kullum nake kara jin k’aunar Sulaym a xuciya ta.

 

 

Kallona Sulaym ta tsaya tayi galala da baki tana yi tana mai bin dimple da Hushirya ta da duk suka bayyana da kallo. Lumshe segxy eyes din ta tayi tana mai cewa” washh mashaallah gsky besty na Allah yy maki kyau matuk’a. Riko hannun ta nayi ina cewa” Hmm kedai Sam Sulaym bakya gajiya da surutu kaman gidan radio. Dariya tayi don Sulaym irin yaran nan ne washa,komai abun Dariya koda kuwa bata ranta kayi sai dai tayi murmushi. shiyasa halin nasu yaxo d’aya da Suhaimart, ita dai kawai bata da Hayaniya ne,itako Sulaym ta iya shi.

 

Dafata nayi ina cewa” Sulaym don Allah ki taso muje mufara aikin mu kinga Hjy. Zaituna yanxun ta gama fad’a fah.
Ban rufe Baki ba ne Oummu Sulaym tace” Hmm ai wlh munga banu,don bamu fara rayuwar ta kura ba,yanxun ne xamu fara. Kallon ta nayi ina mai cewa” habawa Oummu Sulaym kowa na son sassauci ke kuma kirar mana bala’i kekeyi?. tabe baki Sulaym tayi hadi da fara mun mgn cike da muryan rada saboda gulma,nan ta fara cewa ” ke Suhaimart kenafi tausaya mawa

 

 

komai kina yin shi too lazy,a kasalance gashi wannan D’an nata baya da mutunci ko kad’an wlh sai mun gunmace xama da Uwar sa abisa shi. ga miskilanci issah da wulakanci…Uhnm tom Sulaym ai sai muyi kokari mu kiyaye duk wani abu da xai sa muja mawa kanmu matsala. Wai dama tana da yara?. nayi maganar ina mai d’an ya tsina baki na. Oummu Sulaym ne ta bani amsa da,tab kedama baki sani ba,ba yara ne dayawa take dasu ba,guda d’aya Allah ya bata shiyasa suke kaunar dan kaman su lashe,kuma wama yace maki yaro ne? tom Saurayi ne wanda akallah xai kai shekaru talatin xuwa da biyu a duniya. ke samarin nan irin butters masuji da Gayu da tashen kudi,hmmm Kedai Suhaimart bari,ni ne nake fada maki shi din ajin karashe ne,wlh Ajin Sir Khaleed yana burgeni.

 

 

Amma abu daya kebani haushi da shi shine son mata duk da matan ba irin su mu bane,Yara yayan masu dashi su xaki ga sunyo parcking a haraban gidannan kullum indai ya dawo, kowa so take tayi mu’amalan banxa dashi,shikuma dan iska sam baya gajiya,ni ban taba ganin Harijin fitinannan mutum Kaman Sir Khaleed ba. Shiru Nayi na wucen gadi,tom irin gidan danaxo aiki kenan. Muryan Sulaym ya dawo dani daga duniyar tunanin da nakeyi. Cigaba tayi da cewa ” Kuma kinsan abin Haushun ma? ta fadi tana kallo na. Girgixa mata kai nayi alamar A’a. wai Hajiya Zaituna cewa ma take yara mata sune sukw bibiyar mata d’a,su suke neman lalata shi. Haka xatayi ta bala’i tasa ayi ma yara koran kare,don wata xubin intana gida har sawa take a sakar masu kare,cin mutuncin duniya amma bashi xai hanasu gobe su dawo ba,kaman kar nuka mtswww…. Sulaym taja tsaki hadi da kama hannu na muka fara dosan side din wanda naji an kira da Sir Khaleed. Xufah ce ta hau karyomun shikenan na shiga uku na. Ban san lokacin da nace mawa Oummu Sulaym Yanxu mune xamu ringa kula dashi har yakoma ko!?. waya fada maki xaya koma? ai yadawo kenan. tunda ya kammala digiri din shi na biyu ne,a fannin ingineering,sai kuma na farko yy a bangaren Architecture. shiyasa ma aka fi sanin sa da Arch. Khaleed. mune da sauran Ma’aikatan sa na can companyn sa suke kirar shi da Sir Khaleed, amma da Architect Khaleed aka fi sanin shi. ai kawai gdyn da xamuyi ma Allah shine daya,da safe yake tafy Companyn sa baya dawo wa sai After 6pm.

 

 

sannan kinga kafinnan tuni mun gudu gida masu yin night duty sun amshe mu.
A sanyaye nace kuma wai anan gidan yake shek’e ayan sa ko? wlh sai naji bana son ganin shi sam. na fadi ina mai bin Sulaym da kallo ina tabe dan mitsulun baki na.

Dariya Sulaym tayi sannan ta cigaba da cemun” tom bakiga tafiyan da muke xukawa bane,ae side din shi dana iyayen shi dan karan nisa ne dashi,ga shi har da gate din da xai fita tacan batare da wani ya sani ba,shiyasa tanan karuwan sa da yan matan sa ke shigowa har su gama Hajiya Zaituna batasan ma anyi ba. sai mu da mike hidimta masa.

Tun daga nan ban kuma cewa komai,gabana ban da fadi babu abun da yakeyi. Addu’a nake tayi har muka shiga side din nashi,da komai nashi yafi na sasan Hajiya Zaituna kaman sama da kasa,don da shigan mu duka muka rufe ido muna mai shakan wani irin daddadan kamshi,sunan Baya nan ne amma komai na side din tsaff da shi,abun gunun ban sha’awa sai dai kura da side din yy kadan,tun a yanayin tsarin wajen xaka fahimci lallae mazaunin Side din gogagge ne,kuma cikakken Bature ne,don sam bai xauna cikin su a banxa ba.

 

 

Daura kyallen da muke dorawa kan Uniform namu duka mukayi sannan muka fara aikin mu,sosao a lokaci kadan mukaci karfin aikin,Muryan Mhiss Caterine muka jiyo daga bayan mu tana fadin Suhaimart,Sulaym ku kara cleaning din can coridon okay?. tom muka ce mata muka juya xamu nufah coridon da tayi mana nuni. sai tsintayar muryan ta mukayi tana cewa” Suhaimart”.Saurin juyowa nayi ina mai amsa kurar nata. Cike da daure fuska da nuna bacin rai tafara cemun sau nawa nake maki magana kan ki rage wannan xurmemen hijab din. ladern Hannun ta bude hadi da fiddo da hijab Half sunnah arsh,tana miko mun da cewa” kar nakara ganin ki da wannan,idan ba haka ba kuma xan sallameki a bakin aikin ki. barina har rawa yake haka jikina nayi saurin saka Hannu na amsa ina cure na jikina na saka wannan, hadi da mata godiya,duk da bana son hijab dun sam… Juyawa tayi hadi da barin side din.yyn da Sulaym taso yin mun wata maganar shirmenta kawai sai na kauda mata da kai don idan ta itane xamu kai dare a haka.

 

Haka muka cigaba da aikin mu wanda kan lokaci kadan muka kammala sannan muka bar sauran ma’aikatan don su cigaba da nasu aikin… A wannan rana a kakkauce na kammala nawa aikin yayin da wuraren magrib muka baro gidan Hajiya Zaituna. Sam oummu Sulaym bata barni naje gida ba sai da muka wuce karamar kasuwar cikin garin Zaria, ba wani nisa ne da gidan Hajiya Zaituna ba. itah Hajiya Zaituna a GRA Zaria take,yyn da Daga nan ne muka wuce kasuwar monday. Sai da muka isa ne na kwasa takaici don ashe gaba da kudin Oummu Sulaym Naira 150 ne. kallon ta nayi gami da ce mata” wai Sulaym mai xamu siya a kasuwar nan ne. ko so kike amana wulakanci abimu da kallon banza. Murmushi Oummu Sulaym tayi kana tace” waya fada maki aiko da dari biyu da Hamsin din nan sai kinga kayan da xamu siyo. kedai muje daga ciki kiga irin kasuwannan,ae komai nasu arhana ne dashi,nidai ban kuma ce mata komai ba,na cigaba da bin bayan ta kaman yanda tace. a wani wuri naganmu cikin irin maguxawan nan wato katafawa. tsumma naga sun xuba a gaban su suna 20 ². ko yar shugaban kasa albarka. bin mutumin da yake wannan maganan nayi da kallo,nan naga wata irin mutsitstsikakken riga wanda shida tsumma babu maraba,amma ya daga yana Ko yar shugaban k’asa albarka har da karin yanxun akayi odan su daga London.

 

dariya lamarin ya bani,wanda sai nayi murmushi hadi da cigaba da bin Bayan Oummu Sulaym.
Dai² masu sai da safuna muka tsaya, daga kai tayi tana kallona sai tace inyamuran ta bata safa fari mai kyau. Bayan ta bata ne tafada mana kudin nan ta mika mata 50 sannan muka kamo hanyan dawo wa gida. A napep ne Oummu Sulaym tamiko mun Safan tana furta Besty naki ne fah,naga na kafan ki talalace ne,kuma ba’akusa bamu albashi ba,kar Hajiya Zaituna ta gani yaxa ma mana na sababi. Bude baki nayi ina fadin besty na bakya gajiya tom ngd. Haba meye na gdy Suhaimart aikin fi karfin safan naira 50. Nan kuma ta kauda maganan ta hanyar firar mhiss caterine tana kwaikwayon muryan ta wanda ta sani dariyan dole.
A dai² yan dusa zaria muka sauka yyn da Nan Oummu Sulaym ta dauko Naira 50 ta baima me napep,aiko da ganin Hamsin Me Napep ya kashe hadi da cewa shi sam kudin ba Hamsin bane. Hakuri na soma bashi,amma sai kara butsarewa yake shi sam bai san wannan ba. Hmmm Kaman mutuniyar Arxiki Oummu Sulaym ta kalleshi hadi da cewa’ tom bawan Allah nawa ne kudin naka tunda ba 50 bane.
Nan kanshi tsaye yace 100 ne kudin sa. Wani wawan Dariya Oummu Sulaym tayi cike da rainin Hankali tace ” Allah ko yaya na,tom gashi kuma bama da naira 1 yanxu,sai dai kayi Hakuri. Ganin Rainin hankalin da Sulaym tayi masa yasa me Napep kara tutsewa yana bala’i har mutane masu wuce mu a bakin Hanya sun fara saka mana ido. Wurgo ma Sulaym kudin yayi yana cewa wlh baxan amsa ba,sai dai ku rike duka. kai Hannu Sulaym tayi tana mai daukan kudin da ce A’a duk haka bai taso ba,kaje mayi ma sadaka. tana fadin haka taja Hannu na muka tsallaka titi hadi da barin me Napep da sakakkiyan baki.

 

A hanya kuwa sai da nanu mawa Sulaym rashin kyautuwar Abun da tayi,amma sai tace ai Besty haka shine dai² gobe baxai karayi ma wata ba. kinga ko ruwa da sabulu ai masiya. nidai shiru nayi mata ina mmkin Tsiwa irin na Sulaym. wanda da muka iso gidan su A unguwan Alkali tayi mun sallama,yyn da ni kuma sai da na dan kara tfy kadan sannan na isa gida…

 

 

A bakin soron mu na tadda Abokan Zaid da shi kansa zaune suna sana’ar ta su. yyn da kaina a kasa na wuce, muryan wani Abokin Zaid da ake ce mawa Aminu naji yana cewa” Babah wannan kanwan taka fa tayi,iya wuya zan fara tara kayan Aure naxo nayi ciki da itah. Banji mai Zaid yace da suba,abu daya ne najiyo tsakanin su shine zagin da zaid ke Auna masa. don fada har cikin gida ina jiyowa,arxiki na daya oummah Rabi bata nan,niko zama nayi nai shiru ina tunanin inda ta tafi da wannan yammancin.Mikewa nayi hadi da nufan rijiyar dake ysakar gidan namu na cika bokiti da ruwa sannan na nufi bandaki….
Niko Mmn teddy nan bayan shigewa n ta ban daki ne,na samu damar kare mawa Suhaimart kallo.

A takaice dai Suhaimart Yarinya ce budurwa da baxata wuce shekaru 17/18 a duniya ba. Fara ce mai kyau,wanda wuya ya disassar da hasken takoma choculate din karfi da yaji. wanda duk da haka bashi xai hana ka fahimci cewa ita din fara ce karrr ba….. Doguwa ce bacan ba,wato matsakaiciya. tana da diri mai kyau ga shape gashi kuwa har gadon baya kaman Bafillatana,amma su cikakkun Hausa Fulani ne. tana da Ball Eyes basu girma kuma farare tasss sai tsakiya baki kirin. idan tayi murmushi ko dariya dimple din ta bayyana yake sosai ga kuma hushirya kaiiii…

 

komai na Suhaimart na daban ce, irin sune ake cema cikin dubu da wiya a samu daya. bin gidan nayi da kallo tabbas ko makaho ya laluba yasan suna cikin Rayuwar Wahala. Bayan Minti 15 ne na fito hadi da nufan dakina,nan na dauko wasu ko daddaun atamfa mao launin kore da fari, shafa basilin nayi don ko arxikin powder bana dashi bare na saka.

 

Fitowa nayi hadi da nufan madafin mu don na girka abun da ya sauwaka mana. Anan na ga ma Oummah har ta kammala tuwo miyar yauki,nan na maida miyar wuta don takara xafi…. Komawa nayi na zauna ina tunanin Rayuwa ta. Lallae a Rayuwa na na baya maiye na dandana, Hmm Zuma ne ko mad’aci. hawaye ne yafara bin kuncina a sarari nace zuma,a yanxu ne nasoma dandanan mad’aci.

 

A haka ina a zaune har aka fara kirar sallahn magrib sannan na tashi nayo Alwala hadi da nufan daki na don na gayar da mai sama’u….

************************

Mom”mom…” iftihal ce mai kwala kirar sunan Hajiya Huwaila dake kishijgide ta dora kan D’an nata saman cin yanta tana mai shafa sumar gashin sa wanda da’alama tana rarrashin sa ne kan abun da ta saba yi kullum. Turus taja ta tsaya tana mai aikin turo Baki da kunkuni,gami da magana cikin ranta,wai shi kullum Ya Huday baya girma ne. kullum Mom ta dinga sangar ta shi,tana Rarrashin sa kan abun da ya wuce fiye da shekaru 10 da dori, Haba wannan naci dame yy kama. Muryan Mom ne taji tana ce wa oyoyo Ifteey na,wlcm back… Daurewa tayi hadi da fad’awa jikin Mom tana rungume ta. Huday ne ya tashi daga kwancen da yake fuska tamau a daure,daka ganshi xaka fahimci miskili ne na karshe gashi koba a fada maka ba,xaka fahimci sam baya son Raini.

 

Hajiya Huwaila ne tace” Huday yanxu yaushe ne xaka tafi Nigeria?. Mom a satin nan inshaallh. Kan ya rufe Baki Ifteehal ta amshe da cewa” What??? Nijeria?. Mom me xamuyi a wannan k’asar da mazaunan ta ma so suke su barta. Gsky ni baxan koma can ba nafi jin dadin xaman london. zan cigaba da xama da Daddy na anan. Ta fadi tana shiru sakamakon hararan da Huday ke watso mata. Murmushi Mom tayi Hadi da shafa fuskan ifteey tana cewa” No My Daughter bamu ne xa muje ba,Huday ne keson tafiya can. Saboda kula da Companyn shi. ki kwantar da Hankalin ki,Mom ta karke maganar tana mai rungumo Ifteey Jikin ta.

 

Shikuwa Huday mikewa yayi ya nufi side din shi hadi da kirar Mhiss Umiey wanda take Scatery din shi ce na companyn shi a Zaria, yana mai sanar mata da isowan shi.

Wannan kenan…

*GIDA NAGERIA*
Suhaimart’…Suhaimart… Oummu Rabi ke kwala kirana,wanda cikin sauri na fito daga daki na,wanda sanye nake cikin shigar uniform dina na Aiki.
Kaman daga sama naji anshekomun Ruwan xafi a jikina. saurin jah baya nayi ina ganin Abun da Oummah Rabi ta watsomun a jiki tana mai Aunah mun uban zagi kaman yar tasha….

LABARIN ZUMA DA MADACI TA KUDI CE, XAKI TURO KATIN MTN,VIP 200 VTU,#200 SPC #300 NORMAL GRP #100 DUKA TA WANNAN NUMBER 07064551049 .

*Mu tare a next episode*

*Mmn teddy*

Leave a Reply

Your email address will not be published.