*ZUMUNCINMU A YAU* °
By Aysha Ya’u Kurah
*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
”’BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM”’
Sadaukarwa ga mahaifi na kwarai *LATE ALHAJI YA’U KURAH* Allah SWT ya jikanka ya kai rahama kabarinka..
*SHIMFIDA*
“Assalamu alaikum” Ta faďi karo na uku cikin siririyar muryarta,
cikin ďaga murya taji ance,
“Wai wacece ta ke ta kwaďa mana sallama ne haka?!”
A hankali jikinta na rawa ta amsa.
” Ni ce.”
“Tooo!! Sannu NI CE, me ya kawoki?”
Cikin rawar murya ta ce “Mamma ce ta aikoni in kawo muku abinci.”
Daga cikin ďakin ta jiyo muryar dattijon wanda ya bata tabbacin shima yana ciki. “Toh ki ce an gode, je ki ďauki naira ashirin a saman tagar ďakina kiyi gaba.”
A hankali ta sauke ďankwalin da aka ďaure kayan a ciki ta kwance ta fito da sababbin samirun tuwo da miya ta cire ďankwalinta tace “Nagode BAFFA, Allah ya saka da alkhairi.” Ta ďauki ashirin ďin ta fita cikin k’unan rai.
A hanyar da zata sada ta da kofar gida taci karo da su Husna rik’e da manyan kuloli suna tafe suna nishi da kyar, rab’ewa tayi ta basu guri dan su wuce, suna karasowa dab da ita suka kwashe da dariya haďe da faďin “Nadiya roba-roba.”
Badariyya ta ajiye kular hannunta ta shafi kayan jikin Nadiya tace
“Kaiii!! Wannan ba roba bace rai fess ce.”
Suka sake tintsirawa cikin shakiyanci suka ce “Su Nadiya bana an samu canji, daga atamfar roba zuwa shaddar roba.”
Cikin sanyin jiki tayi gaba tana jiyo ihunsu har suka shige cikin gidan.
Tana fita tayi tafiyar minti biyar sannan ta isa titin da zata roki masu mota su ďauketa da naira ashirin ďin da aka bata, dan in tace zata tafi gida a kafa sai ta kai yamma saboda nisa,
zuciyarta cike take da mamakin yadda zumuncin zamani ya koma,
tun tana karama ta ga mahaifiyarta na fuskantar irin waďannan wulakancin saboda kasantuwarsu talakawa, sau tari takan tambayi mahaifiyarta anya Baffa ne ya haifeta kuwa?
Acikin gidan kuwa, su Husna na shiga babu ko sallama suka faďa ďakin,
zabura Baffa yayi ya sakko daga kan gado yana faďin. “Lale da matana, lale-lale.”
Badariyya ta faďa jikinshi tana faďin “Kakus, ina barka da Sallah na?”
Cikin rawar jiki yasa hannu a aljihu ya ciro yan ďari biyar-biyar sababbi ya k’irga goma ya bata,
yatsina fuska ta yi tace “Haba kakus, dubu biyar fa ka bani, ni gaskiya sunyi min kaďan Pizza kaďai zanci da su.” Washe baki ya yi yace “To yar lele, an gama.” Ya karo mata wasu biyar ďin ta mike a jikinshi babu ko godiya sai ma faďin “Ko kaifa, ai da na sake ka yanzun nan,,,
Husna ta matsa kusa dashi tace ” Saura ni kakus.”
Dubu goman itama ya bata saboda yasan sakon barka da sallan shi na tafe don tun safe y’arshi mafi soyuwa a gareshi ta kirashi tace zata aiko MUSADDIQ da sak’o, yasan sakon bai wuce na kuďi.
“Ina yayanku? Ko ba tare kuka zo ba?” Baffa ya tambaya yana gyara aljihu.
Badariyya tace “Ka ji kakus a kofar gidannan fa muka sameshi, yana fita muna shigowa dan ya riga Nadiya fita ma.” Kallon mamaki yayi musu yace “Aiko bai shigo ba.”
Goggo ta rufe kular da ta bude ta ce “Kasani ko ya manta da wani abu ne?”
“Hakane kuma.” Ya faďi tare da basar da maganar.
Nan suka hau hira da ciye ciye, sun ma manta da samirun tuwon da Nadiya ta kawo saboda sunsan babu wani abun arziki a ciki.
Zaune take tayi tagumi tana jiran shigowar Nadiya dan tasan in Allah Ya yarda zata samu ko ďari biyar ce a gurin su Baffa na barka da sallah,
Zainab ce ta taso rike da robar abinci tace “Mamma zan kara abinci.” Janyota ta yi jikinta tace “Yi hakuri auta, yanzu Anti zata dawo har madara ma sai kisha in kinaso kinji?”
Gyaďa kanta tayi cikin murna ta kurawa kofar gidan ido tana jiran b’ullowar yayarta.
A gajiye ta shigo gidan ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi,
da sauri Zainab ta mike ta ďauko mata ruwa, karb’ar ruwan tayi haďe da janyota jikinta tace ” Kin ci abinci?”
D’aga mata kai tayi, “Eh naci amma ban koshi ba. Mamma ta ce zaki kawo kuďi a siyo min madara.”
A hankali ta ďago jajayen idanuwanta ta sauke kan mahaifiyarta, kallon tausawa juna sukayi sannan suka kau da kawunansu, cikin sark’ak’ak’k’iyar murya Nadiya tace “Mamma na kai musu, Baffa ya bani naira ashirin, ki tayani yi mishi godiya dan ya taimakamin, da a kafa zan dawo gida.”
Cikin b’oye b’acin rai Mamma tace “Kai madallah!! Allah ya biyashi da aljanna, gaskiya naji daďi, tashi maza kije kiyi sallah.”
Tana kokarin mikewa taji anyi sallama, juyowa tayi haďe da amsa sallamar, suna haďa ido tayi saurin kau da kanta,
Mamma ta mike cike da murna tace “Maraba da Musaddiq, yanzu kake tafe?”
“Eh Mamma ina wuni.”
“Haba dai daga tsaye?” Ta faďi haďe da shimfiďa dadduma.
Zama yayi yana sosa k’eya suka gaisa sosai,
kuďi ya zaro a aljihunshi kusan dubu dari biyu yace;
“gashi inji mummy tace a kawo muku” bai jira jin me zata ce ba ya ajiye kuďin ya fice daga gidan da sauri dan yasan in ya daďe a gidan to asirinshi zai tonu..
Kasa tab’a kuďin tayi saboda firgici Kai anya Musaddiq yaji inda aka aikeshi da kyau kuwa?
Wannan kyautar tayi yawa dan tsakanin ta da yar uwarta bai wuce kyautar dubu biyar,
“Nadiya mik’o min wayar can” tace tana mai nuna ma nadiya wayar,
da sauri ta ďauko ta mik’a mata. Hannu na rawa ta fara neman lambar yar uwarta, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ďaga cikin isa da tak’ama,
murya na rawa Mamma tace “ina yini Hajiya”
“lafiya” kadai tace murya can k’asa, bata damu da amsawar ba dan in da sabo ta Saba, sai ta cigaba “yanzu Musaddiq Ya kawo min sak’o shine nace bar…”
Dakatar da ita tayi ta hanyar cewa “ina da abin yi Suwaiba nasan godiya kika kira kiyi, bakomai yiwa kai ne” tayi saurin kashe wayar, cikin mamaki ta ajiye wayar tana duban kuďin zuciyarta cike da farin cikin yar uwarta ta fara sanin muhimmancin zumunci….
Musaddiq na fita ya nufi motarshi ya kashe wayoyinshi ya ta da motar yayi gaba yana nazarin yadda zaiyi ya fahimtar da mahaifiyarshi da kakanninshi muhimmancin zumunci,
A kullum yana mamakin yadda zumuncin zamanin yanzu ya zama sai in kana da kuďi,
yana takaici matuka saboda irin wulak’ancin da Mamma suwaiba da ya’yanta ke fuskanta saboda kawai basu dashi, bashi da wani burin da ya wuce yaga kan zuri’arsu ya haďu, Mai shi ya taimaki mara shi, amma kullum abun k’ara lalacewa yakeyi saboda masu shi ďin basa taimakawa na jikinsu saidai na neman suna..
Mrs Tijjani Shattima…
[04/12 09:42] Meela Adeel: 2⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
BY Aysha Ya’u Kurah
“Nadiya amshi maza kira min yayanku,
cike da murna ta karbi wayar ta latso number,
Yana zaune ya kifa kanshi a wheel barrow yana tunanin ta inda zai fara,
‘Dan kudin dakon da ya samu na Sallah shi ya had’a yayi ma kannenshi kayan sallah, ragowar ya ba mahaifiyarshi tayi abincin sallah,
karar da wayarshi keyi ne ya dawo dashi cikin duniyar tunanin da ya tafi,
hannu ya zira cikin aljihunshi ba tare da ya d’ago ba ya danna ya Kara a kunnenshi,
Assalamu alai– “hello Ya Hafiz ta katse shi cikin kaguwa,
dago kanshi yayi cikin firgici yace “Nadiya Lafiya,?
fizge wayar mamma tayi tace “Hafizu kana Ina ne, duk abunda kakeyi ka barshi ka dawo gida, mikewa yayi da sauri ya Sanya silifas dinshi, ya kalli abokin aikinshi yace “Haladu dan Allah ka Mik’a min baron nan gidan oga lukman in har ban dawo da wuri ba, Haladu yace “lafiya dai ko, “walhy ban sani ba mamma ke kira na, ya karasa fadi yana tafiya da sauri ,
“Allah yasa lafiya haladu ya fadi da karfi dan Hafiz ya kusa karya kwana,
zuciyarshi cike take da fargabar abinda zai je ya tarar a gida…
Hello Baffah, an yini lafiya,
baki har kunne baffah “yace lafiya lau ya sallar,
“sallah alhamdulillah,
“Dan Allah Baffa kace ma su Husnah su biyo MUSADDIQ na aiki Haruna driver,
to bakomai daga ya karaso zansa su taho saboda dare,
“kana nufin har yanzu bai zo ba baffah,
baffah yace “eh to sunce min sun ganshi d’azu amma ni har yanzu bansa shi a idona ba,
ikon Allah ta fadi hade da gyara zama,
ya rigasu fita gida fa, kuma saida na mishi kashedi akan yawo, Yanzu haka yana can gurin abokan banza, amma dai ya basu sak’onka ko? ,
“ko kusa bai basu ba, baffah ya fadi had’e da yak’e wanda yafi kuka ciwo dan ya kosa yaji makwafin kudin da ya ba jikokinshi da Karin wasu a aljihunshi,
“karka damu baffah bari in kirashi inji inda ya tsaya,
“too bakomai Kar dai ki matsa mishi kin San yaran yanzu saida lallami,
haka ne baffah nagode a gaida Goggo,”to zata ji Nima na gode,….
Kiran Musaddiq ta shiga yi, abin ya d’aure mata kai da taji wayoyin shi a kashe, lallai yau zan bala’in sab’a ma Yaron nan, duk fadan da na mishi akan shirman partyn nan baiji ba ko, Allah ya kawo shi gida wallhy Mai rabani dashi sai Allah ta wurga wayar cikin jaka ta d’auki gyale da mukullin mota ta fita…
“ji nake kamar a mafarki mamma, shafar kudin ya sake yi yace
“ban taba tunanin zan rike irin wadannan kudin ba a rayuwata,
Mamma da farin ciki ya mantar da ita damuwa da yunwa tace
“kaidai bari, Allah kenan maji rokon bawa, duk yadda mutum ya kasance cikin kunci da bakin ciki to in ya dogara da Allah sai ya samar mishi mafita,,
Hafiz yace “haka ne mamma, to yanzu ya zamuyi da kudinnan,
“shi nake tunani hafizu,
mu jira babanku ya dawo sai musan abin yi dashi,
dubu biyu ta ciro cikin kudin tace je kayo mana cefane da wannan muyi abinci kafin ya dawo,
Zainab da ke kwance Kan cinyar Nadiya tace “anty Madara ta, Nadiya tayi dariya tace “kiyi hakuri yanzu za’ayi abinci muci,
mamma na jinsu tayi kamar bata ji ba tace,
“au Hafizu na manta ka siyo ma auta Madara kaji, Nadiya tayi murmushi tace kamar kinsan maganar da takeyi kenan, Mamma tace au haba, taho auta ta kinsan ni namiki alkawari kuma bazan manta ba,, haka suka kasance cikin farin ciki a ranar, ji sukeyi kamar babu kamar su a doron duniyar Allah SWT, Allah sarki, kud’in da bai wuce kudin naman wani gida ba shi ya Sanya bayin Allahn nan murna har suke Jin babu kamarsu……
Mrs Tijjani Shattima…
[04/12 09:42] Meela Adeel: 3⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
BY Aysha Ya’u Kurah
*******10:56pm******
Zaune yake cikin motarshi kafafunshi duk biyun na waje yana latsa wayarshi da ko minti uku baiyi da kunnata ba,
text din mummy ya karanta yayi d’an murmushi had’e da shafa kwantaccen sajenshi,
rufe wayar yayi ya sake duba agogo,…
gyara zamanshi yayi ya rufe motar yace
“na tabbata yanzu mummy ta isa k’asar Singapore ita da k’awanta cikin mafarki,
tada motar yayi ya karaso kofar gida,
kiran mai gadin su yayi a waya dan ya bud’e mishi gate, yana tsoron latsa hon ya dawo da mummy cikin kasar Nigeria,
da sauri Mai gadin ya bud’e mishi, ya shiga yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye Motoci,
Kiran waya ya shiga yi kafin ya karasa kofar parlon..
Badariyya na zaune tana buga game taji land line din dakinsu na Kara,
pause ta danna ta Mik’e tana tsaki,
“hello.. ta fadi cikin muryarta Mai cike da izza da isgili,
“hey Badar zo ki bude min kofa kuma kiyi a hankali Kar mummy ta jiki kin gane ko,
katse wayar tayi ba tare da ta amsa shi ba ta juya ta fita daga d’akin,
d’akin mummy ta nufa, bud’e kofar tayi ta shiga ba tare da tayi sallama ba, dan a ganin Badariyya sallama ta talakawa ce,,
hasken da ya gauraye d’akin ne ya farkar da mummy daga bacci,
Mikewa tayi hade da mik’a tace “BADAR lafiya,
yaya Musaddiq ne ya kira ni wai in bud’e mishi kofa….
Bawan Allah yana waje yana jiran Badariyya ta bud’e mishi kofa,
ganin da yayi har minti 5 ta wuce bata bude ba ya fara mita cikin zuciyarshi, d’aga wayar yayi da niyyar sake kira yaji ana tab’a kofar,
tura wayar yayi cikin aljihu ya k’arasa kusa da kofar fuskarshi d’auke da murmushi,
“ina kika tsaya ne haka, har hakuri na ya fa—- maganar ta makale mishi a mak’oshi sakamakon ido hud’u da sukayi da mummy,
zaro ido yayi ya had’iye wani mugun miyau,
dariya ya fara yi yana fad’in mummy baki kwanta ba,
tun d’azu Ina nan k’ofar gida a zaune ni da Tinau Mai gadi yana bani Labarin k’auye,
sannan malam— juyawa tayi ta barshi a tsaye,
shigowa yayi ya rufe kofar ya bi bayanta da gudu,
can gefe ya hango Badariyya tsaye tana mishi kallon raini,
harara ya jefe ta dashi yace “tun kina yar ficiciya kin iya munafurci da makirci Ina ga in kin girma, wallhy kinji haushin rayuwar ki idiot,,
tsaki taja ta wuce d’akinsu,,
Kofar dakin mummy ya karasa,
a hankali ya murd’a kofar ya shiga had’e da sallama,
kusa da ita yaje yayi kneel down ya kamo hannunta yace
“kiyi hakuri mummy, wallahi ba party na je ba, ina gidan su Mahmud tun da na fita daga gida,
sai dare na bar gidansu na dawo kofar gida na zauna,
Dan Allah kiyi hakuri banason wannan fushin please ya karashe a shagwabe,,
bata tanka mishi ba ta zame hannunta cikin nashi tace “bani,,
zuciyarshi na dukan uku uku yace “me zan baki?,
K’ara tamke fuskarta tayi tace kud’in Baffa da na aike ka dashi,
dakewa yayi yace “ni gidan mama suwaiba kika aikeni saidai ko driver kika aika gidan Baffa,
“karka raina min hankali Musaddiq,
kalleni da kyau banyi girman da zan fara mantuwa ba,
dubu biyar na baka ka kaima “SUWAIBA”
dubu d’ari biyu na Baffa, sai dubu Hamsin na k’anwar k’awata “Hajiya Nafeesa dake layin su suwaiba,
bud’e baki yayi yace “Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun,
mummy ai banji duk lissafin da kika min ba, ni dai sunan mama suwaiba kad’ai naji, na bata dubu dari biyu da biyar,
ga dubu hamsin nan a aljihuna na manta inda kika aikeni dashi,
karki damu gobe in shaa Allah da wuri zan kai mata, kika ce gidanta na kusa da gidan mama suwaiba ko?
Wani mugun kallo ta bishi dashi had’e da taune leb’enta,
matsawa baya ya fara yi dan yasan in mummy ta fara taune leb’e to abin da zai biyo baya bazaiyi kyau ba,
dai dai kofa ya tsaya kamar zaiyi kuka “yace mummy kiyi hakuri dan Allah,
cike da takaici tace “Musaddiq Anya rayuwar da ka daukarwa kanka Mai b’illewa ce,
ka zama almubazzari Wanda baisan darajar kudi ba,
in ba iskanci ba me suwaiba zatayi da dubu dari biyu harda d’oriya, wallhy tun muna mu biyu da kai gobe kafin goma na safe kaje ka amso min kudi na, kuma ka tabbatar ka kaima Hadiza kanwar Hajiya Nafeesa kana ji na ko,
gyad’a kanshi yayi fuskarshi da bata cika nuna fushi ba ta canza launi saboda tsananin b’acin rai,
Takalmin kafarshi ya cire ya kwanta yayi ruf da ciki yana tunanin yadda zaiyi ya samu dubu d’ari biyu gobe ba tare da yaje gidan mama suwaiba ba,
Sai karfe daya ya yanke shawarar Kiran yayyenshi mata ya fad’a musu komai yasan a cikinsu bazai rasa Mai bashi ba…..
Mrs Tijjani shattima….
[04/12 09:43] Meela Adeel: 4⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya’u Kurah
Kamar a mafarki yaji ana bugun kofar dakinshi, mikewa yayi akan dardumar da bacci ya dauke shi bayan sallar asuba,
mik’a ya fara yi hade da addu’ar tashi daga bacci,
kara buga kofar da akayi ne ya sashi kallon agogo,
goma saura kwata ya fadi da karfi yana mai karasawa kofar dakin,
murda kofar yayi a hankali ya ja da baya hade da runtse idanuwanshi saboda tsoron irin kallon da zaiyi Karo dashi…
*HAPPY 17TH BIRTHDAY BROO*
Muryoyin su ya daki dodon kunnenshi,
bude idonshi yayi da sauri ya bisu da kallo daya bayan daya,
wani murmushi ya saki mai matukar kyau, take ya manta da damuwar da ta hanashi bacci ya fara rungumarsu yana fadin “thank u so much sweeries,,
” Happy womb escape uncle”
ya jiyo cikin siririyar murya,
”omg HINAD!! ya fadi da karfi,
murmushi tayi mishi hade da yi mishi nuni da hanyar shigowa dakinshi da idanuwanta,,
Ta madubin console din dake kallon dakinshi ya hangota tsaye cikin shigar jallabiya ta alfarma kanta yane da jan mayafi ta nade hannayenta a kirjinta tana murmushi,
ihu ya saki hade da kwasawa a guje ya nufi gurinta,
bude hannuwanta tayi ya fada kirjinta,
“Best birthday gift eva luvly sis, I love u so much,
dago fuskarshi tayi ta cire farin glass din Idonta tace
”Happy birthday little Diku nah, love you more,,
karasowa suka yi cike da mamaki suka ce ”saukar yaushe ANTY REEMA,
”yanzun nan!, ko gida banje ba, ta fadi tana maida glass dinta,
waigawa musaddiq yayi gurin Hinad ya lakace hancinta yace ”cutie pie ina handsome?
yamutsa fuska tayi tace yana mota wai bazai shigo ba,
dalili? Musaddiq ya tambaya yana kallon Anty Reema,
”don’t ask me kasan halin d’an naka,
kallon Sauran kannenta tayi tace mummy fa?,
RADIYA ce ta fara magana, ”muma zuwan mu gidan kenan, ina ga bata tashi ba,
hannun RAUDHA ta kama tace ”ina kika baro WALEED,?
”yana gidan Anty RALLY can yayi sallah, nasan suna hanya yanzu,, Raudha ta bata amsa cike da girmamawa,
falo suka koma dukkansu banda musaddiq da tuni ya fita gurin HILAL….
Maganata ta karshe kenan babu wanda ya isa ya sake dawo da ita farko,
bazan mishi party ba wannan shekarar FAKAT!!! mummy ta karashe fadi tana hararar musaddiq dake zaune kanshi a sunkuye,
but mummy why,? RALIYA da shigowarta kenan ta tambaya tana karasowa parlon,
tsaki mummy taja ta tashi ta wuce kitchen,
Radiya da Raudha kuwa mamaki ne ya hanasu magana dan a iya rayuwarsu sunsan babu abin da mahaifiyarsu ke so sai bidi’a,
haka nan ma kirkirar party takeyi in kudi yayi mata yawa, babu d’a, ko jikan da shekara ta taba wucewa ba ayi mishi kwarya kwarya ba,
barin ma danta d’aya namiji tilo wanda partynshi ke banbanta da na kowa, shiyasa sukayi sammako dan ayi komai dasu,
”wow MIRACLE ya sakko kenan,
yau mummy ce da kanta take cewa bazata yi ma little birthday ba,
iko sai Allah Anty Reemah ta fadi tana mai mikewa,
Raliya tace ”kedai bari anty na Kasa ajiye jaka saboda mamaki,,
”’Ba abun mamaki bane laifi yayi ma mummy”’
waigowa sukayi suna kallon ta inda maganar ta fito,
karasowa tayi rike da cup a hannunta tace
”kwarai kuwa, almubazzaranci yayi da kudin mummy,
ta aikeshi ya kaiwa Baffa shine ya kai gidansu Nadiya Roba Roba,
kuma kudin da yawa har 200k,
mikewa musaddiq yayi a fusace yayi kanta,
rikeshi Anty Reemah tayi da sauri ta girgiza mishi kai alamar ya kyaleta,
Badariyya ta rike kugu tace da kin kyaleshi anty,
karya akayi maka, mtswww wanda bais—-”shut up” Anty Reemah ta katseta da karfi,,
”yaushe yarinyar nan ta fitsare haka,
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun,
duka nawa kike Badar?, Musaddiq sa’an ki,
”Ba sa’a na bane amma abin da zaiyi ni bazanyi ba, dan Sam bashi da hanka—–
wucewar walkiya da tsayuwar ji na wucin gadi ne ya hanata karasa maganar,
rike kuncinta tayi ta Sanya kara mai firgitarwa,
cike da firgici su Radiya suka karaso gurin,
kallo anty Reemah ta bishi dashi yana huci hade da zazzaro ido,
cikin zafi yace ”I usually give people more chances dan dey deserve, but once am done am done,!
waye sa’an ki anan, tun dazu kina ta zuba rashin kunya an kyaleki shine kike kokarin wuce limit dinki,
ya kalli musaddiq cikin kunan rai yace
”kanwar kanwarka ta tsaya tana fada maka magana kai kuma kana tsaye kamar gunki, u’r pathetic wallhi mtswwwwwwwww, yaja tsaki hade da daukar wayarshi yace ”wannan dalilin ya hanani shigowa gidan nan,
kallon Anty Reemah yayi yace ”plss lets go Mum,,
faduwa kasa Badariyya tayi tana ihu tana shureshure tana fadin ”Allah ya isa mugu azzalumi,
wayyo Allah na mummy ya tsinka min kunne,
da gudu mummy ta karaso ciki dan duk budurin da akeyi bata sani ba tana can bayan kitchen tana duba masu yi mata hidima…..
Mrs Tijjani Shattima….
[04/12 09:43] Meela Adeel: 5⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya’u Kurah
Ya ya, me yake faruwa? kukan wa nakeji kamar Badar,
da gudu ta ruga jikin mummy, Hilal ya bita a guje ya daga hannu zai kai mata duka mummy ta daka mishi tsawa, ”kulll karka sake ka taba ta, rasa kunya berar danga,
ko girgiza baiyi ba bare ya saurari abinda ta ce ya sauke hannunshi a bayanta,
wani ihun Badar ta sake saki kamar wacce ake yankawa,
kallon gurin da suke mummy tayi cikin bacin rai tace’
”Reemah dan iskanci kina tsaye danki zai raunata min ‘ya, babu Wanda yayi yunkurin hanashi,
kuma saboda rashin ta ido ya iya Zuwa har gabana ya narka mata gudumar hannunshi a baya,
to wallhy bazan dauka ba, ko ki rama mata ko kuma ni in rama mata da kaina,
Raliya tace ‘ ”haba mummy, ya za’ayi mu shiga fadan yara,
Badar ce fa bata da gaskiya, rashin kunyarta kullum dad’a k’aburi yakeyi,
babu Wanda ya isa ya fada mata taji,
daga fitowarta babu ko gaisuwa ta fara magana cikin isa da rashin kunya,
thank God akwai Hilal a nan, da dukan da zan mata wallahi sai yafi haka,
mummy ta saki baki cikin mamaki tace me tayi ne waiii,
Husna ta kwashe duk abinda ya faru ta fada mata,
mtswwwwwwwww mummy taja tsaki tace
”to karya ta fada, duk Wanda yaga musaddiq yasan baida cikakken hankalin zaman duniya,,
Sam baisan inda yake mishi ciwo ba,
bai San darajar kudi ba saboda baya nemosu, kashesu kadai ya iya yi,
da yasan darajar kudi bazai daukesu ya kaisu muhallin suwaiba ba saboda bata da bukatarsu,
bata ma San me zatayi da su ba,
bai San su kudi ana kaisu inda in suka shiga zasu fito da mafiyinsu ba,
a’a kawai shi ga mai tausayin banza ya dauki zunzurutun kudi ya kaiwa suwaiba,
K’ara kaurara murya tayi tace “wallhy tun muna Shaida juna ka fita kaje ka karbo kudin nan, kafin wani azal ya afka musu,
ka bar mata dubu biyar din da na saba bata kuma ka tabbatar ka kaima kanwar Hajiya Nafeesa kana Jina ko,?
kasa dago kanshi yayi saboda kwallar da ta taru a idonshi,
wani karamin tsaki Hilal yaja yayi waje cikin kunan rai,
Kiyi hakuri mummy, Anty Reemah ta fadi cikin taushin murya,
hakuri daya zanyi inji kudi na a hannuna,
Radiya da Raudha suka kalli musaddiq suka ja tsaki,
Radiya tace
”haba little dubu dari biyu fa,
kaima kasan kayi rashin hankali,
mutanen da duk iya rayuwarsu basu taba rike dubu goma ta kansu ba,
“Raudha miko min wayata maza in kira mama suwaiba dan Kar ma ganin kudin ya sa su kirkiri amfani da shi, dan su kudi kana ganin su amfaninsu ke zuwa ko ba budget,
gara ko man Mota mu Sha dasu Kinga sunyi mana amfani,
dauko wayar Raudha tayi ta fara latsawa,
”ba sai kin kira ba Raudha ga kudin nan nazo dasu ta fada cikin sanyinta had’e da karasa shigowa cikin parlon,
ajiye zainab tayi ta tsuguna har kasa ta gaida mummy,
ta ciro kudin cikin jaka ta mik’a mata tana murmurshi,
tun bayan tafiyar musaddiq ban yarda aiko shi kikayi ba,
nasa a raina ko mantuwa yayi shiyasa na biyo baya,
da na kiraki kika tabbatar min kin aikoshi sai na ajiye har Malam ya dawo shine yace in dai kawo in tambaya da kaina,
tunda na doso naji maganganu sai na tabbatar mantuwa yayi ya kawo,
nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,
ameeeen!!!
mummy tace hade da karbar kudin,
Matsananciyar kunya ce ta lullube Reemah da Raliya,
Musaddiq kuwa daki ya wuce ba tare da ya dago kanshi ba hawaye sai ambaliya suke a idonshi ,,
dambun kifi mama suwaiba ta dauko a Jakarta ta ajiye a Kasa kusa da mummy tace ”gashi ba yawa da fatan kunyi sallah lafiya,
”kalau suwaiba,!
to alhamdulillah Allah ya Maimaita mana,
“ameen ya Allah” mummy ta fadi ta wuce daki rike da kudinta a hannu,
waigowa mama suwaiba tayi fuskar nan dauke da murmushi tace duk Ina kwananku,
da sauri anty reemah ta karasa gabanta tace Ina kwana mamma,
lafiya lau Ant–Dan Allah ki daina cemin anty mamma, Reemah ta katseta da sauri,
murmurshi tayi tace to na daina, yaushe kuka zo,?
hannun zainab ta kama tace “dazu muka zo ina su Nadiya da Hafiz,
Hafizu ya tafi gurin aiki Nadiya kuma tana gida,
yau bata zo mana yawon sallah ba, Raliya ta fadi tana karasowa gurinsu,
har mun shirya tace Wai kanta na ciwo shine nace tayi zamanta a gida,
nan suka shiga taba hirar yaushe gamo da anty Reemah da bakin ciki da kunya sukayi mata katutu a zuciya,
kallon fuskar mamma takeyi wacce kyawu da fara’a suke boye ainihin bacin ranta,
Mama suwaiba jarumar mace ce mai tsananin kawaici da boye bacin rai, kullum fuskar nan cikin murmurshi take……
Kad’an daga cikin abubuwan dake faruwa cikin zuri’ar mu kenan anty,
laifin duk na su Baffa ne, su suke nuna fifiko saboda abin duniya,
soyayyar abin duniya ta rufe musu ido sun mance taimakon Yan uwansu na jini sai dai bare na neman suna,,
har ga Allah nayi niyyar kaiwa Baffa kudin dan na je har gidanshi,
abin da naga sun ma Nadiya shi ya karya min zuciya har zuciyar ta rinjaye ni da aikata hakan,
bansan abin zai kwabe haka ba, da ban kai ba,
da na jira dawowar Daddy sai in karba in kai musu, yanzu nasan “ransu bazai musu dadi ba” ya karashe cikin shashshekar kuka,
share mishi hawaye tayi tace
“Ya Allah ka karfafa min raguwar zuciyar Diku nah,
har yanzu kana nan da halinka na kuka,
lokaci ya canza Little, yanzu ka fara girma u are not a child anymore,,
tashi kaje kayi wanka muje gida,
akwai wani surprise din da na shirya maka,
cikin sanyin jiki ya tashi ya shiga bayi,,
Tagumi Reemah tayi tana tunanin hanyar da zata bi ta wanke zukatan bayin Allahn nan,
Allah ya sani bata da masaniyar halin kuncin da suke ciki, ita dai tasan suna da wadatar zucin da zaisa kullum ka gansu cikin farin ciki…
Mrs Tijjani Shattima….
[04/12 09:44] Meela Adeel: 6⃣
Ayi min Afuwa pls wasu hidimdimu ne suka rike ni, Ina Mai baku hakurin jiran da kukayi nagode matuka da kauna, Ina kaunarku har cikin raina Yan uwana… In shaa Allah zaku jini kullum yanzu
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya’u Kurah
Ashe gaskiyar babanku ne da yace kila mantawa Musaddiq yayi,
hakan ce kuwa ta faru, dan kudin na Baffa ne,
tayi tayi ma in amsa nace mata a’a kudin sunyi yawa, mamma ce ke maganar cikin sakayawa tana kallon ya’yanta,
Nadiya dake kulla kankarar kuka, tace “nima dai mamma jiki na ya bani ba namu bane,
dan dai naga kin kirata ne shiyasa na dauka da gaske ne,
Alwala Hafiz ya karashe hade da addu’a yace “mun gode Allah ma da yasa ba muyi amfani dasu ba, wannan din ma da ta bamu Allah yasa musu albarka,
“Ameen mamma tace hade da mikewa ta nufi cikin daki, babu wanda a cikin su ya karanci ainihin bacin ranta saboda fuskarta dake dauke da murmushi…
******
Hey handsome duk wannan cika da batsewar na menene?
Come on chill my guy,
yau fa is my day banason kowa yayi fushi a cikin ta,
Kara tamke fuska yayi hade da jan dan karamin tsaki ya mike yace
“bansan me ke damun zuciyarka ba, bana cika mu’amula da masu irinta saboda wata rana haushin su zai sa inyi musu tsana marar misaltuwa,
u’r my uncle nd friend as well bana son abun da zaisa inji haushin ka,
nowadays masu irin zuciyarka basa samun nasara a komai saboda sanyinsu,
“sanyinka yasa kana namiji kai kadai a gidanku amma kowa ya rainaka harda BADAR for dat matter,
yaushe aka haife su?, dey are just 9! if am nt mistaken,
kuma ka tsaya a gabansu kana wani kuka,
gaskiya ka bata min rai, just go nd have fun Kar in bata maka naka ran, Hilal ya karashe fadi yana nuna mishi kofar fita da hannu,
“sannu ubanshi, Anty Reemah ta fadi tana karasa shigowa dakin,
Hilal ka fita idona walhy, bana son iskanci,
kasan inda zaka dinga nuna wannan bakar zuciyar taka,
kai a kullum duk inda kaje sai Kasa mutane sun tafi da kai a baki,
meye amfanin rashin hakuri, abin da hakuri bai baka ba wallahi rashin shi bazai taba baka ba,
duka nawa kake kaima da kake barin zuciya tafi karfinka,
wallahi kayi gaggawar sauke bakar zuciyarka har mu bar kasar nan in ba kanaso inyi mummunan saba maka ba, sakarai kawai,
“haba anty sorry mana, ba fa wani abu yace min ba, musaddiq ya fadi cikin tausasawa hade da kama hannunta,
kallonshi tayi cike da son halinshi tace ko baice maka komai ba meye amfanin abun da yayi a gida,
“mum nifa babu abin da nayi, kawai dai gaskiya ce bakwa so, shiyasa Sam bana son shiga gidanku saboda ni ba na gani in kyale kuma in nayi kuce nayi rashin kunya, Allah ma yasan akan gaskiya na– rufe min baki anty reemah ta fadi hade da bige bakin a hankali,
Janta musaddiq yayi suka bar dakin tanata masifar da Sam bata karbeta dan ba sabawa tayi ba,
kullum cikin bakin cikin halin danta takeyi wanda Sam bai biyo halinta dana ubanshi ba,
da ya tashi sai ya dauko halin mamanta har ya damata ya shanye saidai shi Sam bashi da neman suna kuma komai zaiyi sai yanada hujja…
Ruwa musaddiq ya bata tasha yace “kiyi hakuri anty kin so ki bata ranki ne,
kinsan halin Hilal, babu mai iya canza shi sai Allah,
kuma kin San duk abin da zaiyi akan gaskiya yakeyi he is open,
baya barin abu a ranshi,
dole ya koyi barin abu a ranshi musaddiq, Reema ta fadi tana mai ajiye kofin da ta sha ruwa,!
meye amfanin duk abun da akayi ma mutum yace sai ya rama,
wani lokacin ma ba dashi akeyi ba sai ya sako kanshi saboda shi baya gudun bakin duni–
kwanciyar da taji anyi a bayanta ne ya hanata karasawa,
kamshin turaren da taji ne ya sanar da ita ko waye,
Kara tamke fuskarta tayi hade da Jan tsaki,
cikin muryarshi ta yan gayun yaran hutu yace
“ki daina gudun bakin duniya Momma na,
in dai duniya muke son mu burge to lallai munada aiki babba a gaban mu,
“chapter closed”,
am so sorry for hurting you mum,
wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta hade da kara kaunar dan nata,
duk iya inda yakai da zuciyarshi ya tsani bacin ranta,
baya daukar mintina sai yasan hanyar da yabi ya wanke zuciyarta,
dariyar farin ciki musaddiq yayi “yace komai ya wuce ”aunty momma!! ,
murmushi tayi hade jan kunnuwansu,
zama sukayi suka sata a tsakiya suna mata hira kamar babu wani abu na bacin rai daya gifta a tsakanin su,,
karar da wayarta tayi ne ya katse musu hirar,
zaro ido tayi ta mike tana fadin ya ilahi hade da daukar wayar, sorry Rally shaff na mance da ku,
daga dayan bangaren Rally tace ai na Lura da hakan, gashi har mun gama komai,
cikin farin ciki Anty reema tace kinyi komai simple dai ko, kinsan komai namu very simple muke yinshi,
saima kin gani anty, abin sai ya burge ki ta fadi tana gyara balloons din da sukayi kasa kasa, ok thank u babe,
gamu nan Zuwa,
juyowa tayi tace kuje ku shirya ku raka ni wani guri,
Hilal da ya riga ya harbo su yace ni a shirye nake mum,
bata kalleshi ba ta kamo hannun Musaddiq sukayi daki,
a cikin sababbin kayan da ta siyo mishi ta zaba mishi tace ya saka ta fita ta bashi guri,
saida ya dau minti goma yana shiryawa,
jar riga ya saka mai matukar kyau da deep blue wando, ya taje kwantaccen gashin shi, kyawun bakar fatarshi mai sanyi ya kara bayyana, hatta madubin da ya kalla yasan babu karya shi din mai kyau ne matuka,,
fitowa yayi cikin takunshi na nima na fara girma,
kallon kauna anty reema ta bishi dashi tana fadin wowwww kanina,
babu kamarka a wannan zamanin,
gaskiya kayan nan sun karbe ka,
sajenshi ta shafa tace “Allah ya nuna min aurenka dole in zauna da matar saboda kar ta cutar min da kai,
Hilal ya ajiye cup din coffee yana dariya yace saboda kinsan uncle din nawa is nt brave ko,
zanci ub– toshe mata baki yayi da sauri hade da rungumeta yana dariya harda kyakyatawa,
tureshi tayi tace “wallahi yaron nan ya rainani sosai,
zanyi maganin ka,
dariya suka saki Hilal ya dauko keyn mota Kan centre table yace oya mu wuce,
Anty reema ta kalleshi Sama da kasa tace da wannan wandon zaka fita,,,
pls mum karki fara muje kawai ya fadi yana wani narkewa,
hmmm kawai tace ta kama hannun musaddiq suka fita Zuwa gurin Mota…..