rk ****ZURFIN CIKI :-2**** ta dafa kafadata tana cewa kayi haquri mubarak na sani kana son nabeelah sannan itama tana sonka,sai dai kuma kayi kuskuren rashin bayyana soyayyarka gareta a sanda ta bukaci hakan,nayi kokarin dai- daita tsakaninku amma naji tsoron kada mutane suyi tunanin na aurar da nabeelah ga d’ana ba bisa son ranta ba sai dai bisa dole kasancewar ta girma a hannuna…….haka kuma yanzu bazan saka kaina cikin wannan matsalar taku ba amma zan goya muku baya bisa dukkan shawarar da kuka yanke,idan kuna nemana ku sameni a fallow*** na kalli nabeelah idona cike da hawaye na fara magana kamar haka’nabeelah ina sonki,kuma ina kaunarki, sai dai na kasance cikin irin mutane da sukan boye sirrin zuciyarsu,kiyi haquri ki gafarceni,nasan nayi miki laifi…nagode ki tashi ki tafi allah ya bada zaman lafia sannan allah yasa shine mafi alkhairi gareki……..na miqe zan fita daga motar,ta kamo hannuna ta zaunar dani tana magana hade da wani kuka mai tsuma zuciya gami da sa tausayi kamar haka’yamubarak da farko na yarda kana sona amma yanzu na gane cewar soyayyar batayi tasiri a zuciyarka ba tunda har ka yarda zaka haqura dani kan wani ya aura,lallai na yarda baka kishina baka tausayina irin zaman da zanyi tare da wani namiji wanda ba kaiba,ka sani cewar zuciya ba zata aminci rabuwa da kaiba,jikina na haramtashi ga dukkan wani d’a namiji idan ba kaiba dan haka na qudiri niyyar mallakarka ka ta wane hali,yamubarak kayi kokari ka soni kamar yanda nake sonka,yamubarak kada ka bani kunya’*** na share hawayen dake zuba kan kuncinta,na kama hannayenta na kwantar da ita bisa kirjina,nabeela h ki amince da soyayyata gareki kada ki zargeni da komi sai alkhairi,nabeelah ina sonki kuma nine mijinki da yardar allah,da sauri ta tashi daga kan kirjina ta dafa kafaduna tana kallon fuskata,ta sumbaci goshina sannan ta rungumeni kan kirjinta tana cewa hakika farincikina ya karu,burina ya cika sannan alheri ya tabbata gareni…..amma *menene mafita? *da wane zance zamu tunkari abba? *sannan kuma lokaci yana da karanci garemu…. Na kalli nabeelah dake kan kirjina nace zaifi sauki muje wurin kawu aminu mu shaida masa halinda muke ciki…ni nasan me zan fada masa kuma zai yarda. *kai tsaye na tuka motar zuwa gidan kawu na tarar ya gama cin abinci yana gindin bishiya yana hutawa..bayan mun gaisa ya cigaba da magana kamar haka’lallai daga ganinku akwai matsala dan naga alamun damuwa gareku, shin ko baki son auren ne? Ya tambaya’ na fara da cewa gaskiya kawu ita nabeelah ba wanda take son za’a bata ba,kawu yace wannan zancen banza ne dama shi yasa suke boye min to wallahi wannan maganar babu ita,ku tashi mu tafi gidan…. Na tuka mota har kofar gidan muka shiga shi kuwa kawu tun daga kofar gida yake ta fada..yana shiga su mama suka fito suna gaisuwa amma ko amsawa bayyiba ya cigaba da cewar’maganar auren nabeelah babu na soketa yanzu zata fada mana wanda take so kuma goben zan daura mata aure dashi…nabeelah ta kada baki tace’ya mubarak nake so’ kawu yayi dariya yace au to ai shikenan ta kwana gidan sauki kuda dan iskanci abin na gidane ma kuke bata lokaci,to ai ni yanxu xan daura auren idan yaso kuje chan kuyi ta bikinku,sannan baba ya shigo yaji meke faruwa amma ba yanda zaiyi da kawu dan yasan halins doe qura ya zama waliyina shi kuma waliyin yamubarak aka daura auren*** take yamubarak ya daukeni muka tafi gidan kunshi daga nan ya kaini nayi kitso muka wuce gidan aunty nafeesat nayi wanka na saka rigar atamfa kaina ba dankwali na fito gareshi,wow nabeelah amma kinyi kyau,ya kamo hannu daga inda yake zaune gefen gadon,ya sumbaceni har saida numfashina ya dauke,ya kwantar dani kan gadon ya fara cire kayan dake…….hakika ban taba sanin haka yamubarak ya iya soyayyaba sai yau,lallai da tuni nayi asar miji,haka muka kasance cikin nuna kaunar juna har zuwaN CIKI book 2 part 1
ZURFIN CIKI book 2 part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 – 22:05
Abba kwance kan gado,dare yayi nisa amma shi
ya kasa bacci sam.saboda matsalar da yake ciki
yanzun. domin kuwa matar shi in yaga bazai iya
ba sai ya sawwake mata,amma maganar auran
ummi koda Alhaji bai goya mishi ba bazai iya guje
mata ba. “yanzun menene mafita?”ya tambayi
kansa,wata zuciyar ta ce, “kayi shiru tamkar baka
ga wannan takarda ba,tunda ba wanda yasan ka
gani.” a fili ya ce,”haka ne.” ya ci gaba da
tunanin kila ma yanxun ya janye kudirinshi,tunda
yaga ummin bata da kan gado. don yaga rubutun
yayi shi ne tun ranar da aka haifi ummi,ko kuma
ranar sunanta. tunda gashi har da sunan ummi a
jiki.mafita kenan yayi shiru.wata zuciyar ta ce,”in
ko kayi haka kayiwa Alhaji da ummanka adalci?
koda yar su ba yar adam ba ce bai kamata ka
gujeta ba.ko don albarkacin son da suka nuna
maka. shin da ummi ta kasance mai jin magana
da nutsuwa,kuma mai tsananin kyau zaka
gujeta? Kada kayi zaton Alhaji yayi kudurin aura
maka yarsa ne don yasan zata zama mara ji,kayi
nazari. haka Abba yayi ta tunani har asubah
tayi,amma hukuncin da ya yanke shine yayi shiru.
sai dai ya janye batun rabuwa da matar shi,don
yasan yana sakinta zai zama mijin ummi,kai
batun nan hadiye ma cikinshi shine mafi dacewa.
dunkuna masu kyau yayi wa matarshi saboda cin
suna.haka yayi wa dan siyayya daidai karfinshi,ya
kawo ma umma. Taji dadi sosai nan ahj ya iske
su, shima ya shiga dakin umman ya xauna ya ce
a dauko masa abinci nan xai ci yau.ya dubi abba,
babana nayi sautun raguna xuwa qauye nace xa
a siyo nmanya.abba ya ce biyu?umma tace
hakan yayi.abba ai tuwan girma miyarsa nama,
aja rago daya xiqal a shiga wannan gida da shi?
abba yace,me xai hana tunda ban musu qaryar
arxiki ba sun san mu talakawa ne.ahj yace
xancanka dutse bacna,amma maganar ummanka
ita xa a bi, sannan xa a sai buhun shinkafa da
cefane a kai musu.ana gobe suna abba da
abokansa suka dira gidan da ragunan da kayan
mai jego da na yaro sannan ga kayan abinci. sun
samu anty a gidan,ta musu tarbar mutunci.da
yake abba xana waya da ita,ya fada mata komai
ta sani.hjy zainu da taji kukan raguna ta fito,anty
tace dan Allah momy kada ki musu magana,kin
ga shi da abokansa ne.da qar ta samu ta turata
sashin ahj,shi kuma murna yayi yace aje a daure
su.zainu tace ahj menene na numa farin ciki sai
kace ba ma cin nama?can ba xa a ka kada ba
dan kawai shagalin sunan, sannan tace harda
shinkafa suka kawo sai kace muna yunwa? nana
take ya hade rai tare da cewa,zainu kada dai ki ce
min kin sa an dawo da yarinyar nan gidan ne dan
ki kashe mata aure?tace haba dai. ya ce to hir
dinki dan bansan in kuma jin irin xantukan nan
yayi ma matarsa daidai arxikinsa. mu kuma mu
ma yarmu da jikanmu gwargwadan arxikinmu,in
ya fito daga gun mai jegon ki turo min shi,sbd mu
ji in da xa a yi sa sunan.tace ina xa ayi in ba nan
ba?ya dube ta an taba haka?ki dai turo minshi.ta
taba baki sannan ta wuce.lkcn da ta leqa dakin
abba da abokansa suna xaune,abba yana ta fama
da danne dannen waya,domin tun da suka shiga
ya qi ko kallan inda bishira take bare danta.tace
bishira ki eada musu in sun fito ahj na san
magana da su.ta wuce ba tare da jiran jin amsa
ba,ko amsa gaisuwan da abokan abba suke mata
bata yiba.bishira ta kalli abba wanda tana
hankalce da shariyan da yayi mata,tace kaji abin
da momy tace?sai lkcn ya dubeta me tace? yayi
maganar ne cikin tsare gida.dadynmu yana san
ganin ku. bai amsa ba,sai kurun ya tura mata
jakar kayanta,ki duba,ta xaxxage dinkuna ne na
gani na fada masu kyau,duk da xannuwan ba
masu tsada ba ne kala uku atamfa daya shaea
daya sai kuma leshi.sai ko kayan yaron.ta dube
shh an riga an sai mana kayan fitar
sunanmu.ahmad ya dube ta wannan din baki so?
tace ni bance ba.abba yace ku tashi muje.tace
ina san magana da kai.ya ce kiyi
maganarki.muktar yace kuxo mu fita ta dauki
yaran tare da miqa mashi ta ce ina lura da kai
rabon da ka dauke shi tun randa aka
haifeshi,alhalin mu kuma yana nan yana hana mu
baccin dare.kai kana can kana baccin ka.ta fadi
haka ne cikin sanyin murya.ya amshi dan tare da
cewa ai gara ya hanaku bacci tunda kunqi ku
kaishi gurin babanshi.ya tsura ma yaran ido,wata
qaunan dan ce take shigarsa.ta matso
jikinshi.abba ya kalli furkarta,ita ma kallansa
take,ta ce yanxu ko dan murmushin ka bana
gani.yace,in da kina san gani da baki dawo ghda
ba.yaci gaba da cewa na sha mamakinki
bishira,da har xa ki yarda ki dawo gidanku ba da
ixinina ba. kuma tun kafin ki haihu sai da na fada
miki ba za ki zo gida ba.Ta ce To Abba mony ce
ta ce sai an zo. Ya ce shi kenan ku zauna. ya
mike mata yaron ta amshe shi ta kwantar ta
kama mishi hannu. Abba wane suna ka sa masa?
ya ce Sunan Alhj babba. Da sauri ta saki
Hannushi . Sunan ‘yan da? ya kalle ta Na zaci
zaki ce suna mara ma’ana,tund da ne da sauki.
ya fice. Haushin hali irin na Bishira ya ke ji.dn
son shi yasan tana matukar sonshi,amma bata
son yin biyayya ga abn d yake so. Ya samu su
Mktr sannan suka shiga gurin Alhj ya tambaye su
in d za a sa sunan,Abba ya ce a masallaci kusa d
gidn babnshi ne za a yi addu a. Amma tuni an sa
wa yaro suna Sulaiman.sunan babana. Alhj ya ce
Madalla Allah ya raya mana shi, ba sai mun zo
ba dn yanayin sanyi ne. Nan dai Abba d
abokansa suka tafi suna yabn Alhjn. An ci sunan
shima Abba shi d abokansa sun yi walima da
Azahar. matar abokinshi Bala ita ce suka bai wa
girkin ta yi masu. Mai jego taci gaba d wnk. Abba
kan leka su lkc zuwa lkc,kusan dk lkcn d yaje ba
su cika rabuwa d dadi ba sbd mgnr d hjy zainu kn
datsa mishi. Umma shi ma bata yi fushi ba tana
leka su dk d rashin sakar mata fuska d mai jegon
tare d mahaifiyar keyi. Ummi tana tafe tana ‘yan
tsince-tsincenta,kmr yadda ta saba,sai ko taga
sim,take ta yarda dk wani abu d t samu t dauki
Sim din. Gefen zaninta t samu ta kulle,sannan ta
tafi,cikin jakr mkrntrta t saka.wata rana ta dauki
wayar umma ta shige daki,ta bude wayar ta cire
sim din ta saka wanda ta tsinto a cikin zani ta
soke wayar ta fito soro.Jikin dakin yaya Abba a
bakin kofar ta dauki lamar Abba da ya rbt sbd
masu zuwa nemanshi tana kira taji wayr tana
ringing. Ta kashe tana ta dry,hk tayi ta yi wa
Abba Flashing dg nan tayi gidn du Amina
kawarta,tana ba wa Amina lbrn abn d ta ke wa
Abba. Ta ce Amina nsn yanzun hk yana cn yana
jin haushi,shi yasa ki ka ga ina murna.Ta ce in ya
gane fa?Ummi ta ce Ai tsintar sim din nayi,Umma
kuwa ba za ta san na dauki wayarta ba,domin
yaya Abba da Alhjnmu kawai suke kiranta. Amina
ta ce Yadda za a yi ki kira shi ne in ya dauka sai
ki make murya ki canza suna. Ummi ta ce Tab,dn
in ci duka. Amina ta ce Dalla cn gane ki zai yi?
suka kira ya daga ummi ta sirantr d muryarta
tana fadin “Hello! Abba ya ce Ke wace ce ki ke
kiran layina? Ta ce Sunana ‘”Suhaila. ya ce
Menene ki ke kirana?Ina ma ki ka samu lambata?
Ta ce Gani nayi ni ma a cikin wayr. Tsaki yaja
Sannan ya kashe.Suka dinga tsuntsira dry. Amina
ta ce Sake kiranshi ki ce ma ke a kaduna ki ke.
Ummi ta ce Kai yin waya akwai dadi ni ina son
buga waya. Ta sake kira cikin Zafin rai ya ce Ke
lfy??kin dame ni fa!Ummi ta ce To tsaya mana
kaji ina son mu gaisa ne ni ina kaduna ne. Ya ce
To na gode. Sai ma ya kashe wayar gaba daya
suka yi ta kira a kashe. Tun daga ranar Ummi ta
samu in umma tana aiki ko tana bacci sai ta sace
wayar ta cire sim tasa nata ta kira Abba. Tun
yana kyararta hr ya daina ya koma rokon ta
daina kiranshi,dk a banza. Daga baya sai Abba ya
soma sauraronta, ranar kuma ta kira shi ne
misalin dayan dare,ranar taki zuwa dakin
Tsohuwa ta kwanta a dakin umma. umma kuma
dama dakin Alhj take kwana. A dai-dai lkcn ya
kwanta kadaici ya dame shi,ga garin yanayin
sanyi. wayar ta katse tunaninshi d yake yi na
matarshi zuwa yanzu ya haddace lambar Suhaila.
Ya daga ya ce “Hello ya ce Ke wai me ya hana ki
bacci?Ta ce Ni ba sunana ke ba,Ni sunana
Suhaila,kai fada min sunanka. Ya ce Abba Ta
danne dryr d taso kwace mata ta ce Abba ba
suna bane,Fada mn sunanka n gsky. Ya ce “Idris
Yadda ya fadi sunan sai da ta dage kwarai
sannan ta maida dryrta. Ya katseta d cewa Ina
ku ke a kaduna?tayi dim,dn dai bata san ko ina
ba a garin kaduna ba,ba ta ma ta6a zuwa ba.
Take ta tuno Amina sun ta6a zuwa unguwar
Sarki,dn hk ta ce “Unguwar Sarki. Ya ce, wai
shekaranki nawa? Ta ce Sha takwas. Ta sheka
masa karya.Ya ce Amma shi ne a ka ba kiwaya?
ta ce ta ka san wanene Babana? Ya ce A”a ta ce,
To shi ne mai bawa Gwamna shawara a jihar
kaduna. Abba ya ce Lallai, ki ce in nazo kawo
miki ziyara ba zan samun ganinki ba? Ta ce za
ka ganni mana. Ya ce To zan zo. Ta ce To, Ya
ce,Amma fa ina d mata ta haihu ne ta tafi
wankan gida. . Ummi ta ce Lallai to sai da safe.
Ya ce, Wa ke zuba miki kudi ne cikin waya?Ta ce
Babana mana. ita sai lkcn ne ma ta tuna cewa
ana saka kudi tunda ta ke kira bai taba kin zuwa
ba,aranta ta ce kila wannan ba a sa kudi. Sunyi
Sallama babu dadewa,wayar ta sake daukar
tsuwwa. Ga zaton Ummi Abba ne sai da ta daga
sannan taji muryar wani. Ya ce Da wa nake
waya? ta ce wa ka ke nema?Ya ce Me wayr. ta
ce Ummata ce kuma tayi bacci. Ya ce Yallabai
nake nema. Ta ce Ban san wani yallabai ba,kada
ka dame ni Ta kashe wayar tare da jan tsaki.
Sannan ta cire layin ta maida na umma Wasa-
wasa cikin kwanakin Abba ya soma damuwa da
lamarin Suhaila kaduna, lokuta da dama ya kan
kira layinta amma sai ya ji shi a kashe. Sam ba
ya samunta sai lkcn d ta kira shi,ko da ya yi
mata korafin hk,sai ta ce “Eh ita ce ke kashe
layin sbd ana damunta. Sun yi jarabawar (J. S.
C.E.)sakamako suke jira. dn hk yanzu tana gida
ko yaushe tsokana kuwa bata fasa ba. Kullum ita
d Amina cikin shirya yadda za su yi wa Abba
waya suke, kudin cikin layin ya kare,Abba shi ke
tura kati yanzun. Duk lkcn d Abba yazo gidansu d
ya ga ummi ya hade rannan yana muzurai,ita km
sai ta yi ta sheka dry,dmn tana tuno yadda yake
kwantat d murya a waya. Wata rana hr duka ya yi
mata sbd dryr d ta dinga yi daga sallamrshi a
gdn. Tsohuwa kam ranar yini tayi fada,wai ita za
ta bar gidan.Cin kashin d ake yi wa ummi ya yi
yawa. A ce rashin ‘yancin yakai ko dry ba a son
tayi. Da kyar umma ta sha kanta t hkr. Wannan
ta kaicin dukn yasa ummi tace ita kam sa tasa
shi wahala. dn hk ranar gdn su Amina taje. suka
shirya yadda in ta kira shi zata ce yaxo Kd ta
ganshi, ummi ta ce mugu dama in yaje ya 6ace in
huta. Hakn kuwa ta fada mishi, a ranar d suna
waya. Ta ce ‘”Idris.dn Allah yaushe za ka zo ne?
Ya ce Tun yaushe Suhaila nake cewa zan zo
amma kin ki,to yanzun yaushe zanzo? ta ce kazo
Juma’a ya ce A”a zan dai zo Asabar,Juma’a
rabin rana ce. Ta ce,To sai kazo.Nan d kwana 4
kenan?ya ce Insha Allah,sannan ina son ki toro
min da adireshin dn gdnk,sannan ranar d zan zo
ki bar wayarki a kunne. Ta ce To.” Ranar Asabar
misalin goma na safe Abba ya shigo cikin sabbin
kaya,ya yi matukar kyau tamkar sabon Ango.
Umma ta ce za ka je gurin su Maigida ne?Ya ce
A”a umma koda yake zan bi ta can.Kd zan je.
Umma ta rike baki “Kd,? Me a ke yi?ya ce sai na
dawo za ki ji.Ummi d ke wanke-wanke ta kwashe
da dry. Umma ta dirma mata dundu tare d
cewa,Ke wai ciwon dry ne y kama ki?Abba ya
dubeta cike da tsana. Ummi ba za ki shiga
hnklnki da ni ba?ta sunkuyar da kai tare d maida
dryrta ciki. Sannan ta ce Yaya Abba dn Allah ka
siyo min biredi,wlh biredin Kd dadi ne da shi.
Lkcn d Amina suka dawo ta sammin. Ya galla
mata harara,tare d fadin an ce miki nima bakauye
ne irinki?In ma ki ka sake min mgn sai na gabje
ki. . Ya kalli Umma Kada ki ce ma Alhj nayi tafiya
amma in na dawo zan fada masa. ta ce ,To” Allah
ya tsare. Abba ya fita. Ummi tana gama wanke-
wanke ta shige daki dn yin gyaran gado. Umma
na shiga kicin itama ta fito falo ta ciri wayr a caji
taje ta saka sim. Take kuwa kiranshi ya shigo, ta
daga ta matse murya kamar yadda ta saba, ka
taso ne? ya ce Ina mota mun kusa tasowa. Ki
turo mn adireshin. Ta ce Ba fa wahala,d kun
sauka tasha sai ka ce a kawo ka unguwar sarki
gidn mai ba Gwamna shawara. Ya ce Suhaila ma
su ba Gwamna shawara d yawa Ta ce Um to ai a
nan unguwar Sarki shi daya ne. Ya ce Ya sunan
layin?ta ra sa me zata ce,gabnta y shiga
faduwa.Ta samu kanta da cewa, Abuja Ya ce
Abuja kuma Suhaila?ko dai Abuja road? Ta ce Eh
gida mai lamba 6. ya ce To zan ci gaba da kiran
layin. ummi ta ce To,” Ta zauna tana sauke
numfashi. Tab da ya dogata d ta bani,Sannan ta
saka dry murna take yau yaya Abba zai sha
wahala. Jefi-jefi ya kan kira ya ce sun zo gari,dk
lkcn d ya kira in ta ji ringing sai tayi bayi da
gudu, har Tsohuwa da suke zaune tare ta ce, ke
takwara gudawa ki ke ko atini ne? Ta yamutsa
fuska, sannan ta ce Bacin ciki ne. Tsohuwa ta ce,
To taso uwarki ta baki magani. Ummi ta ce ya yi
min sauki ma. Can kuma masu kiran layin suka
kara kira. Ummi tayi kofar gida ta daga wayar a
ka ce ke ina ki ka samu wannan wayar? Ta ce
Oho ‘yan rainin wayau kada ku sake kirana. Ta
kashe wayar ta koma gida. Lokacin da Abba ya
ce sun shiga KD har ma sun kusa sauka, sai ta
cire layin ta ci gaba da harkokin gabanta ta
manta ma da labarin wani yaya Abba. KADUNA
Abba suna sauka a tashar kawo, ya sauka ya
shiga raba ido yana kallon garin kaduna. Yau ce
rana ta 2 d ya ta6a zuwa KD, daman sun zo
daurin auran wani abokin su bara waccan. Ya
kalli wani dan aca6a sannan ya yafito shi da
hannu. Ya iso yana cewa Ina za ka? ya ce
Unguwar Sarki. Dan aca6a ya ce Wane layi? Abba
ya ce Abuja Road. Ya dubi Abba Rigasa kenan,
unguwar Sarki babu layi mai wannan sunan.
Abba ya ce, Ina zuwa, bari dai in kirata. Koda ya
kira layin Ummi sai ya ji shi a kashe, yana ta kira
a kashe. Ya dubi dan aca6a ya ce, Kasan gidn
Mai ba Gwamna shawara? Dan aca6a ya ce, Hau
dai muje sai mu tambaya. Abba ya hau mashin
yana mai ci gaba da nemn layin Suhaila. Sun
zagaye unguwar Sarki layi-layi suna tambayar
masu gadi da ‘yan dai-daikun mutanen da ke
giftawa kasancewar unguwa ce ta manyan
mutane, daga karshe dan aca6a yaba Abba
shawar ya tafi gida kawai. Don haka sun gama
zagayen unguwar Sarki har da makotanta, amma
ba su samu ba. Gida daya ne aka ce musu da
akwai Suhaila, amma yarinya ce ta goye. Kusan
karfe 3 sannan suka koma tasha,ya biya dan
aca6a, sannan yaje ya yi sallah. Zuciyarsa cike
da takaici sai yanzu yake Sallah. gashi ya kasa
samun layin Suhaila. kila ma tana sane ta kashe
wayr dn kawai ta tazarta shi. Ya tuna d zagin d
wani mu2m ya masa lkcn d suka tambaye shi ko
ya san ina ne gidan mai ba wa Gwamna
shawara? Mutuminya ce,mai ba Gwamna
shawara a kan me? Ma su ba da shawara suna
da yawa, ya sunan layin da ka zo? ya sunan mai
gidan? kama ina lambarsu? Abba ya ce, Lambr
kadai gare ni,km taki shiga.Mutumn ya ce,”Amma
kai soko ne,gashi kmar wayayye.Ya ja tsaki ya
wuce. Shi kanshi sai yanzu yaga wautarshi. ko
me ya kawo shi gurin yarniyar?Shida dai ba za
ya ce sonta ya keba,km ba ya ce ba sonta yake
ba. Wani ma ya zaci dn kudi ubanta yazo,shi kam
in ya koma shiru zai yi ko abokanshi zai ce musu
bai gane ba kawai,dn yabi ya fada musu lbrn
Suhaila,sun km san d batun zuwanshi gurinta
sarai,km yasan hlinsu za su maida abn na
tsokanarshi. Cikin matukar takaici suke tafe cikin
motar kaduna zuwa kani,sun zo kwanar Dangora
tsautsayi ya akfa musu. in da tayar motarsu guda
ta fashe. . Nan take motar ta bar hannunta ta
mulmula da su suna ta salati,nan aka kwashe su
xuwa asibiti.wasu sun mutu take,wasu sun yi
dogon suma.masu waya ta cikin wayarsu aka yi
ta kiran yan uwansu,shi ma abba a cikin wayarsa
aka kira lambar ummanshi da alhj da sauran su
aka shaida musu cewa mai wannan layin sun
samu hadari,kuma an kawo su asibitin mlm
aminu kano yanxu.iyakan rudewa su umma sun
rude,tsohuwa kam take cikinta ya kada ta soma
xagawa bandaki tana kuka tana face
majina.ummi bata gidan tana can gidan su amina
suna ta hira suna cin dariya ,tace bari in je in
qara sa layin in ya kira sai ince wayata chaji ne
sai yanxu nayi.sadaf sadaf ta shige daki,kan
kujera taga wayar,ta dauka ta saka sim din ta
cire wancan. tana kunnawa sakuna suka soma
shigowa. kafin ta bude ta duba sai ta jiyo muryar
tsohuwa cikin kuka tana cewa wannan yaro ashe
ajalh ne ya kira shi,ko me xashi yi kaduna?ni ban
sani ba.ummi ta fito da sauri tana cewa,tsohuwa
me ya faru?tace ba kina can gun yawanki na
tsiya ba.Mai sunan mlm da ya tafi kd sun tafka
hadari, yanxun haka suna asibitin mlm. ana xatan
shi ma ya mutu.ummi ta saki ihu,sam bata san
ta damu da dan uwan ta abba ba sai yau,ko tana
kukan ita ce sila?oho.kafin kice haka,lbr ya watsu
a unguwa abba ya mutu.cikin kuka ummi ta
tambayi tsohuwa ina ummata? tace tare suka
nufi asibitin da ummarku.taqi yarda ta jira
su.ummi tana jiyo ihun kukan umman bashir ta
xaga gidan.gidan ya rincabe da kuka,ummi fa
hankalinta ya qara tashi.matarsa ta iso da kuka
da yan uwanta a motoci.yayyantamaza suka nufa
asibitin.can kusan qarfe takwas su alhj suka
shigo.alhj ya ba mutane haquri,ya ce bai mutu ba
dogm suma yayi.kuma Allah yayi taimako ba
karaya.likitocin sunce xast duba shi xuwa gobe
su gani.nan ko jama’a suka dinga fadin
alhamdulillah.ummi ma tadan ji dadi a
ranta,sanna fa kowa ya tafi dama wasu sunce xa
stje yin sallah su dawo.saida suka koma sannan
suka taho da umma,ummi cikin kuka tace umma
da gaske bai mutu ba, umma tace eh bai mutu
ba,muyi magana dashi. . Umma tace in sha Allah
gobennan xai dawo gida. ummi tace to,umma
tace kinga wayata? gaban ummi ya fadi ta tashi
da sauri ta shiga neman waya,taci sa’ar ganin
wayar,sai dai bata san inda ta saka sim din ba
sai wanda ta tsinto ne a ciki.ummi dai tayi shiru
ta miqa ma umma waya. kusan qarfe goma sha
daya wayar abba da umma ta taho da ita ta
soma qara,umma ta dauka.alhj ne ya ce ina
wayarki ina ta kira ana cemin a kashe?una tace,
a ku6e take gata ma a hannuna.yace to inata
kira.tace qila faduwan da tayi daxu ne ta samu
matsala.yace to dama zance ne ki dafa masa
ruwan xafi a xuba a flask dan uwan matansa xai
kawo mu yanxun a mota xai amsa ya kai.ta ce to
alhj wayn xai kwana gunsa?yace bashir na nan
kuma matarsa anyi anyi ta qi tafiya shi yasa na
haqura xan dawo dan ba na xauna gun su ba ko?
umma tace amma yaya jikin nashi?ya ce da sauqi
yanxu ma yana son shan tea ne.tace to xan hada
harda wayar tasa inya so ma dunga kiran shi
kafin gari ya waye.ya ce yauwa ki
bada.Alhamdulillah abba jiki ba matsala. Don hk a
ka sallamo shi zuwa gd.kai tsaye gdn su umma a
ka wuce d shi. A salin dakinsa a ka gyara a cikin
kwana nan 3 ya yi ras sannan ya koma shago.
Bishira kuwa lkcn mahaifinta ya ce maza ta koma
dakinta,tunda ga abn d ya samu mijinta.Sun
dawo hr da tafkeken injin Janareto wai yaron ba
ya son duhu. Sannan ga kayan kallo d
saraunsu.TabbasAbba ya ji dadin dawowar
iyalanshi,dn dama yana cike d bukatarsu. Ranar
yini suka yi gyaran gd ita da ‘yan uwanta,sai byn
magrib sannan ya shigo d tsarabobi.madara
tatacciya da kaji. Ya dauki dansa cikin jin dadi
yana kallonta cike da so da kauna,Nayi missing
din ku da yawa.URFIN CIKI book 2 part 3
ZURFIN CIKI book 2 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 – 22:08
Ai bama shiri. shi ne fa ya kawo ni mkrntr kwana
dn kawai baya son ganina. Suka yi ta mamaki.
Can jimawa ya dawo, sun fito rakiyar ‘yan
uwansu Safiyya da na Khadija, suka ganshi tsaye
yana danne- dannen waya. Ya taho ya gaida
iyayensu duka,sannan suka koma gefe d ummi,
ya ce Ni ma zan tafi. Ta ce, Ya Abba ko fa
gaisawa ba mu yi ba. Ta karkatar da kai,Cikin
raunin murya tamkar mai shawagaba,ta ci ga ba
da cewa Ya Abba su Umma ba wanda ya ce a
gaishe ni? Sai hawaye suka soma zuba.
Hankicinshi da ke hannunta tasa tana sharar
kwalla.Abba yana da matukar tausayin mace. Don
haka duk da tsanar da ya yi wa Ummi sai da ya
tausaya mata.Ya tausasa Murya. Sun ce in
gaishe ki sosai, za ki ga gyada mai gishiri,
Tsohuwa ta ce a ba ki.Umma ta miki miya, ta
kuma daka miki yaji. Ta ce Na gode, Alhj me
yasai min?ya ce kayan tea ne da lemun kwali. Ta
ce Na gode. Tana ci gaba da share hawaye. Ya
mike Zan tafi. yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi
ya mika mata, ta ce A’a ya Abba ka bar kudinka.
Ya ce Ba ni ne na baki ba,Alhj Karami ne ya ce in
ba ki. Ta sa hannu 2 ta amsa tare d godiya.Sun
raka shi kusa da Gate ita da su khadija,sai kuka
Ummi ke yi. Bayan sun dawo dakinsu ne ta zauna
tana duba kayan da ya lissafo mata,duk ta gani.
Sai kuma saitin sabulun wanka da manshi da
turaransa da hodarsa duk na (Aloe vera.) Shi
kuma bai fada mata ko daga wa ba,ko ba komai
ta dai yi murna sobada tana da ‘yan kuraje a
fuska,tasan kuma za su mutu. Sai kuma audagar
mata,tayi dan murmushi. . Tunda Umma taji
sallamar Abba ya shigo dakin ta bar komai tazo
ta zauna tana son jin lbrn Ummi. Abba ya fahimci
Haka,dn haka sai ya boye mata cewa, Ummi na
kuka hr yanzun. Ya nuna mata ai Ummi ta
kwantar da Hankalinta,km tayi hnkl dn ya bincika
ya ji ana ta yabonta. Umma taji dadi Sosai,Sai da
ya fara zuwa gurin Ummu,sannan ya je gida.Ya
samu Bishira tana zaune tana aikin nata,wato
Kallo. Tun da ta dawo daga wankan gida tazo da
janareto da kayan kallo,shi kenan ta sanu abn
yi.Kullum tana gabn (TV)da ta shi da safe in ta
kokarta shi ne ta dafa ruwan tea ko wanka ba za
ta yi wa dan ba,sai lkcn d man injin ya kare. Ya
nufi gurin injin ya kashe,dif din da ta ji komai ya
tsaya shi ne yasa ta zabura ta mike tana fadin
Ba dai har man nan ya kare ba? Ta fito da niyar
dubawa.Abba ta gani tsaye gabn injin yana bn
tsakar gidan da kallo cikin takaici. Ta ce Baban
Walid kashe min injin kayi??Ya ce Eh na kashe dn
Allah dubi gidanki?kalli wanke-wanke kuda na bi
dubi tulin wankin kayan Fitsarin yaronki. Dubi
kicin dinki,kuma ko da bn shiga dakinki da
wannan falon da ki ke kallo ba.na tabbata da
wanda ki ka dauke ko tsinkw a cikin sa.Kila ma
ba ki yi Sallah ba. Ta ce Dan karashe ne fa ya
rage min in gama kallon in zo in yi aikin.Haushi
ya sake kana shi,Sai kurum ya shige daki.
Tsakuwar da ya dora kafa a kai tasa tsigar
jikinshi tashi,sam ya tsani ya shiga daki ya dora
kafa kan datti. Ya dawo yasa takalmanshi ya
shiga da su,Walid yana kwance tun kayan da ya
bar shi da su da safe sune a jikinshi yana ta
bacci cikin fitsarin da ya shafka wanda ba wata
leda da zata hana katifar ta jike. Ko wankan safe
ma ba a mishi ba kenan.A fili ya ce,”,Inna lillahi
wa’inna ilaihinr raji’un. ya juya ya nufi shagi. Ita
kam sai ta kunna injinta ta karasa kallonta,
sannanta tashi ta dora girki.sai lkcn ta ma Walid
wanka. Ta dan dauraye kwanukan da za su ci
abnci,wai ta gaji sauran wanke-wanken sai gobe.
Fati ta shigo,Bishira ta ce Yauwa Fatima naji
dadin zuwanki.shuga dakina ki gyara min gado,ki
dan yo min shara. Fati ta ce To. Ta shiga ita ma
duk shegiyar darin ce gurin kuiyar aikin,dn haka
ta dan birbira ta fito ta ce ta gama. Bishira ta ce
Yauwa dan dauraye min kaya can na Walid. Nan
ma tasan sama ta shanya. Bishira ta ce Yauwa
ta ga abnci nan kici.sai ki dauki na Ummarku ki
kai mata. Har Fati ta kai waje,Bishira ta kwala
mata kira. ta ce,Zo ki tafi da wannan galan din
na man fetir kije shagon Babn Walid kice ya taho
mana da shi,dn man ya kare. Koda Fati ta same
shi da galan ta fada mishi sako ya ce Ba zan siya
ba,Maida mata galan din. Ta tafi,Shi kuma ya ci
gaba da mita a zcyrshi. Yana fadin Na daina
sayan man tunda ba za a bari sai dare a kunnan
ba.Gidan Ummanshi yaje,ba ta nan ma taje
barkar Haihuwa. Ko dakin Tsohuwa bai shiga
ba,ya zauna nan falonta.Ya za kula ya zuba
abncinshi ya ci.sannan ya dan huta sai ya fita
zuwa gidan su Ahmad. Cam ya samu wasu daga
cikin abokanshi suka shiga hira. Ranar dai Abba
bai je gida ba sai misalin sha daya ko daya shiga
bai nemi matar gidan ba,ya dibi ruwa ya yi wanka
sannan ya shiga dakin. Ya lalibo makunnan wuta
ya kunna,dn Nefa sun kawo wuta. Tana kwance
irn banzan kwanciyarta da ta iya,dakin sai tashin
wani irin wari yake kamar na ruma,kamar na
fitsari ko na datti.Ya kalli ko’ina kullin kaya ne na
wanki ne,na gaga ne ciki da guri.Ranshi ya
baci,Ya kuma dubanta ga wata kiba da ta tafka.
Tun da ta haihu ta zama rusheshiya,gashi bata
son kama jikinta.Tsaki yaja,sannan ya dauki fiko
ya fita. kan doguwar kujera ya jefa filo,ya kwanta
a gajiye.Amma me?sai ya ji dora gadon bayansa
acikin lema.Da sauri ya mike ya kunna wuta.Duk
fitsarin yaron ne a kan kujerun dakin,dn haka sai
ya nufi dakin da takw aje tarkace ya kunna
wuta,shi ma dai duk shirgi. . Ya share Ya
shimfida ta barma ya kwanta,a ranar ya dauri
aniyar maida dakin ya zama nashi din-din-dn.
Don haka washegari yasa a ka zo a kayi masa
fenti,ya siyo kati fa ya yar da zanin gado,dk wani
abu nashi sai da ya kwashe su. Kafin wata guda
ya maida dakinshi cikakken daki,ya zuba dk wani
abu da yake bukata. kafin ya fita kullum sai ya
gyara dakinsa fes. ita kuma sam bata zuwa
dakin,sai dai in yana da lalura yaje can ya sauke
ya dawo. kazantarta kam ta kai in da ta kai,tunda
hr kayan kashi tana zube su a cikin daki. Ya gaji
yaje ya samu Anty ya fada mata,hr gidan Anty
tazo ta zazzageta,ta tasata suka gyara gidan,
amma ko a jikinta.Washegari ta ci gaba da in da
ta tsaya. Sam babu wanda zai ganta ya ce
haihuwarta daya. ¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤ UMMI yau
ba wanda ya kaita murna,domin yau dai an basu
hutu..Sai dai tunaninta zata ko iya kai kanta
gida? Sunyi ban kwana bata da kudin mota, dan
duk tayi taba su safiya kudin gurinta, amma ta ce
yau ko da qafa ne xata gida.sun fito wajan mkrt
wata maryam tana cema,ki tsaya mota xato da
xata kaimu cikin kn.ummi tace baxan jira ba.sai
ga abba kamar daga sama,tsoro ya kamata karya
ce ta xauna gidan abokin sa da yace.hanka linta
ya tashi cikin in ina ta gaida shi ya amsa.ya
shiga mkrtn jim kadan ya dawo.hakan ta sha
alwashin yau ko da shiya saita je gida.shi kam
ma ya manta yai mata wannan maganan ma.ya
sabi akwatinta suka je suka shiga mota. abba
mamakin natsuwan ummi yake yi, ko da yake
baxai ce ta natsu ba, qila lafawa tayi.tundaga
soro ta saki jakanta da bokin tayi ciki da
gudu,cikin kuka tana kiran ummanta.umma ta
share do min tsohuwa tana cikin gida,kada tace
tayi rashin kara,sai tsohuwa ne ta tashi da sauri
tana fadin oyoyo takwara.suka qungume juna
tace to menene kuma na kuka?umma ta fito nan
fa ummi taje ta rungume ta.sai umma ta doje
tace bubi shirme,sakar ni ni.tsohuwa tace haba
suwaiba yarinya tana dokin, . Tsohuwa tace haba
suwaiba yarinya tana dokin ganinki amma ki
gwasale ta? abba ya ce daman nasan ba
natsuwan da yarinyan nan tayi,har ina
yabonta.dubi yanda ta xubarda kayan a soro.to
xaki debo su.tsohuwa tace bari ni in debo mata
tunda kai baka da tausayi.laile umma taga
canji,do min ummi dai tunda ta dawo ko qofar
gida bata fita ba,sai ko in an aike ta.sannan
yanxu ba gudu da tsalle tsalle bare tsokana.ga
aiki har girki ita kema umma komai.alhj yana
shan shayi da safe,ummi ta yi sallama ta shiga.
can gefen su umma ta xauna,sannan ta gaida alhj
ta gaida umma wanda ta saka alhj agaba tana
masa fira.wannan qa’idan umma ne bata barin
mijinta shi kadai,in har yana gida.alhj yace
suwaiba kinga ummina ko?laile abba yayi namijin
qoqari. yarinya ta natsu.umma tace Allah ya
amsa addu’an mu ka duba tsayuwan daran da
muka dunga yi bayan tafiyan ta kan cewa Allah
ya kintsa mana ita.alhj yace hakane,ummi dai na
jinsu tana murmushi.can tace alhj anjima xanje
gidan inna saratu in gaishe ta. qanwan sahura ce
da ke aure a kabuga.ya ce to ummi, xanba
umman ki kudin mota ko? ummi ta ce,to na
gode.ta miqe ta fita ta bar mahaifanta cikin farin
ciki jin dadin natsuwarta, suna godiya ga Allah
mai shirya bayinsa.lkcn da ta shirya dan xuwa
kabuga.sai umma tace ki kwana dan bana san ta
fiyan yamma,kabuga da nisa.tace to sannan ta
dauki kayanta kala guda, sannan ta fito.har xata
wuce sai ta shiga gidan alhj qarami,sahura na
ganinta ta hade rai,daman daqar take amsa
gaisuwan ummi tunda ta dawo.ummi ta gaisheta
a ciki ta amsa,sam ummi bata damu ba,tace
umma ina fati?ta yatsine baki tace tana gidan
abba,tace to inta xo ki ce mata naje kabuga sai
gobe xan dawo.umman bashir tayi tsaki,tare da
cewa ni yar aiken ki ne?ita dai ta wuce.tun
dawowan ummi suke shiri da fati kamar me,ko
yaushe suna tare suna fira.ummi tana mata
labarin mkrtn su.ita kuma fati tana bata lbrn
saurayin da tayi fahad,da irin son da take
masa.ummi tace tab,ni ko xanyi saurayi nafi san
irin ya abba…… . fati ta dubeta da al’ajabi kina
nufin ya abba kike so?ummi ta xabura tana fadin
tir, ko a mafarki Allah ya kyauta.ina nufin mai irin
hirarsa da tsafta.fati ta qyalqyale da dariya tare
da cewa ai na xaci shi kike cewa,inko ya ji kici
duka ummi ta ce,ai ni ba ma da shi nake ba
tab,shi da yayi auran so?kusan ko yaushe
yanayin hiran tasu kenan.ummi tana tafe
wadansu samari suka yi ta binta, sun shawo
kanta ta tsaya da kyar,kuma har ta masu
kwatancen gidansu. kwanaki uku bayan haka tana
ki shingide kan kujeran dakin umma,misalin
takwas saura ma dare.krtn wani littafi take yi na
hausa da fati ta ara mata,sam ita bata taba krnt
irin littafin ba,amma fati ta ce mata ta karanta da
dadi sunan littafin NAGA TA KAINA na
(sodangi).kasance wan wannan ne karo na farko
da ta taba krnt lbrn soyayya,sai abin ya
birgeta.amma nata ganin gwarxon sojan nan xai fi
dacewa a ce abba ne, jefi jefi takan kalli abba da
ke xaune kan kujera kusa da umma suna wani
xance da bata jiyo su. ‘Amma tasan ko me suke
tattaunawa mai mahimmanci ne a gare
su.sallamar wani yaro ne ya katse su,umma da
abba suka amsa mishi a lkc gudu.yace wai ana
kiran ummi a waje inji wadansu.da sauri abba ya
kalla yaron,sam ba xai ce me yasa xance yaran
ya fadar masa da gaba ba.sai ya lumshe ido
sannan ya kalli ummi wadda kunya ta rufe
kasancewar yau ce rana ta farko da aka soma yin
sallama da ita.umma wadda kullum fatanta ummi
ta samu miji,sai tayi murmushi,sannanta ce da
yaron kace tana xuwa.abba ya dube ta da sauri,
umma kin san ko su waye?ta ce, a’a.yace ya
kamata a san ko su wanene dan kin san bata da
kan gado,kowa ma sai ta jajibo kuma ma duk
nawa ummin take da har xata soma tsayawa da
samari?umma tace,to abba ai gara ta kama
dahir, tana qare sakan dire ba sai ayi mata aure
ba?yace gaskiya umma gara ta dan taba krt,dan
yanxu xamani ne na krt.umma tace,tayi acan a
dakinta.ta dubi ummi tasgi kije.ummi ta miqe ta
fita.abba ya miqe shi ma,umma bari dai in gani
ma su kamun kai ne? umma tace to.., . Sun
gama gaisawa kenan sai ga abba ya fito.ganinsu
tsaye da ummi sai ya tsinci kanshi cikin wani
bacin rai.ya isa gun ya musu sallama, suka
amsa, sannan suka gaisa.yace daga ina kuke?
suka dube shi dayan ya ce lfy dai ko? ummi tayi
karaf ta ce yayana ne.anan suka sake gaida
abba.bai amsa ba, sai ma cewa yayi na tambeye
ku kai ma kana tambayana,wai lfy? suka ce,kayi
haquri,nan suka gabatar da sunansu.mai san
ummi shine nazir, abokinsa kuma sagir. sun 3a
masa cewa dukkansu daga kabuga suke.yace krt
kuke ko kasuwanci? sagir yace,eh krt muke,amma
muna taba kasuwanci a shagon mahaifinsa da ke
kwari.abba ya dan yi jim,sannan yace to kai ka
shirya aure ne?nazir yace eh to, nasan dai kafin a
tashi yi mata aure na shirya.abba ya ce, to ita
kam krt xata yi, kuma c ma buqatan ta hada krt
da soyayya. ya dubi ummi da fatan xaki sallame
su.ya juya gida.sagir ya ce, wannan wanki ne da
gaske? ummi tace qwarai kuwa. nazir ya ce to
yanxu ya kenan? kin ji abin da ya ce.ummi yayi
shiru tana tunani, ita fa basu kwanta mata rai,
tun randa ta hadu dasu,sam basu iya saka kaya
kalar yadda ya abba ke sawa ba.dan haka sai
tace, ina ganin xai fi mu haqura kada yaxo ni yayi
ta mun fada.nazir ya ce yanxun haka xaki ce?
ummi tace, um,sai da safenku.kada ku ja min
duka.sagir cikin jin haushi ya ce,ki xama
mangofak qarewan krt.sannan in kin gama wan
naki ya aure ki. ita dai ta shige gida.kusa da soro
ta iske umma da ya abba ta yo masa rakiya, tana
kuma ba shi aaki kan cewa yayi ta haquri,tace ina
fada maka ko yaushe ba fa fushi ko fada ne xai
saka matarka a hanya ba.lallashi da nashiha,ka
dunga koya mata giqki daka nutsu ka koya mata
ba gashi ka ce ta iya daidai gwargwado ba?abba
yace,hum lamarin yarinyan nan yayi nisa fa
umma,wankan jikinta ni xan koya mata? sallah fa
daga nake da ita.amma abin yaci tura.antynta
sau nawa tana xuwa tai mata fada duk a
cnxa,mkrtn ma ta qi xuwa.ni kuma da ce
ruwanta.umma cikin al’ajabi tace, sallah! sallai
ma bata san yi abba?abba yace umma baxan
mata sharri ba… Ta ce Tabdi,to kuwa ba kuwa
kazantarta ta wuce jiki hr d zcy. wannan ita ce
kazanta mafi muni. Don haka dole ne ka zage
damtse don ganin ta kama sallah,to menene
marabar arne d Muslmi in ba Sallah ba?Abba ya
ce Umma na mata nasiha na gaji. Ta ce To kasa
ta a mkrntr Islamiyya,kila ta ji tsoran Allah in
tana jin Wa’azi. Sannan ka dainga siyo mata
kasasuwan wa’azi.Abba ya ce Umma kaset nawa
na kawo mata bata sakawa,Kullum sai indiya da
Hausa fim,in naki sayan man fetur in tana da kudi
ta saya. In kuma ba a ta da shi sai ta dauki
ittafin Hausa ta dukufa.umma ta ce Allah ya
kyauta,kaje kayi ta hkr tare da addu’a. Ya kalli
Ummi,sannan ya ce ma umma,kada ta sake fita
gurin wadanan kananan yaran,sannan ya fita. A
daki umma take tambayar Ummi daga ina suke?
Ta ce um,Umma kyale su ni sam ma ba su min
ba. Umma ta ce to Allah dai ya miki za6i nagari.
Abba yana kwance a dakinsa ya yi lamo cikin
bargo,ya kasa amsa ma kanshi tarin tambayoyin
da ke yawo cikin kanshi. Haka tambayoyi suke
zuwa masa daya-bayan-daya ,me yasa ya damu
da lamarin Ummi??me yasa da a ka yi sallama da
ita ya samu kanshi cikin wani tashin Hankali? Me
ya sa ranar da zai je mata ziyara ya za6i ya sai
mata kayan kwalliya? A fili ya ce,don tana
kanwata.Zuciyarshi ta ki amincewa da haka. Me
yake shirin faruwa da ni ne? ya fada a fili. Ya yi
juyi zuwa rigingine,sannan ya dauki filo ya manna
a kirjinshi, ya ci gaba da magana shi daya. Bana
zaton cewa Son Ummi nake yi.don lkcn da na yi
tsananin Son Bishira bn ta6a samun kaina cikin
wannan yanayin ba. Kai Allah ya tsare ni da Son
ummi,wannan mahaukaciyar
yarinyar……….bugun kofarshi da a ke yi ne ya
katse shi. Murayar Bishira ce ta na cewa Babn
Walid!Babn Walid!! Ya bude kofar da sauri,ta ce
Walid ne ke ta amai. Ya fita ya dauki yaron daga
hannunta yana fadin Me zai hana shi amai,in ba a
ci sa’a ba har zawo sai ya yi,Saboda
kazantarki.Sam ba ki lura da me zai wawuro ya
tura bakinsa. Ta ce Yau fa bai ci komai ba,tun da
safe yake wannan aman.Ya ce shi ne ba ki sanar
da ni ba?Ya cire masa kayan jikinsa wadanda ya
ji suna ta doka karni.. . Ya isa igiyar shanya ya
ciri wasu yasa masa,sannan ya fita dashi.Wani
babban kyamis ya tafi da shi,mai kyamis din
likita ne,sai dai ba na yara ba ne,amma kowa
yazo sai ya duba shi.Nan dai ya masa bayani ya
ba su magunguna. Sha biyu dai dai ya dawo,tana
zaune tana kallo ya ce “A’uzubillahi,wai ke kallon
nan masifa ya zamarmiki ne?to ki sani na kusan
fita da kayan kallon nan. Ta ce,Tab,ka kaisu ina?
dadinta dai dafa gidan ubana a ka kawo su. Ya
ce ta za su koma gidan uban naki. Ta dafe kirji
“Zagina ka ke yi?ya dora mata dan a jiki “An
zage ki,ke din banza,kazama!yazube mata
maganguna ya fita. Ya jima zaune a kofar
gidanshi dafe da kai,yana tunanin shin wai shi
kadai ne bai yi sa’ar mata ba,ko kuwa duk maza
ne.Ya tuna abokanshi 2 da suka yi aure. Muktar d
Jamilu,sam ba su da wannan matsalar,duk lkcn
da yaje gidansu tsaf matansu,ga mutunci da
mutanta mutane. Shi kuma a cikin abokanshi
babu mai zuwa gidan sbd bata gainin kowa da
gashi. ‘Yan uwanshi sai wanda ta za6a sannan
zata yi hulda da su. ‘Yan garinsu kuwa can
¤ZAMFARA¤In suka zo kiri- kiri take nuna musu
kyama ga rowa,sam bata hulda da matan
abokanshi. Ya numfasa zai bi shawarar Umma ya
gani, amma gaskiya Bishira ba matar zama ba
ce. Tun da ya dawo sallarAsubahi dakinta ya
shiga tana ta shirga bacci. Walid kuma ya yi
faca-faca cikin kashi ya tausasa zuciyarshi ya ce
“Bishira! . Bishira!!Ya dan duki kafarta,sannan ta
tashi. Ya ce Ki tashi ki gyara masa jiki kiyi
sallah.Ta ce,Tab, me ya yi?ya ce, “kashi ya
yi.kurum sai ya ji ta ce Tab,wannan akwai dan
iskan yaro.Yanzun dan ubanka kashi ka min?
Sam bai san lkcn da ya watsa mata mari a baki
ba,cikin murya mai karfi ya ce “kada ki kuskura ki
sake ce ma dana dan iska!kar ki sake zagar min
yaro kada ki yi wa dana baki.Ba zan dauki
wannan ba. . Ta mike daga kan gadon tana kuka
Ni ka daka? wlh sai na rama. Kasancewar lebe
baya raina duka,sai jini.Nan da nan sai kumburi.
Ta cakumo shi,wlh sai na rama.Ya hankadata kan
gado ya bar gidan.cikin zcyrshi yana fadin
,”Wannan fitina da me tayi kama? Ita kam ruwa
ta dafa sannan ta wa yaron wanka, cukuikuiye
zanin gadon ta saka shi cikin baho,sannan tayi
kwaskwarima ta sabi danta baki suntum ta nufi
gida tana kuka. Mahaifinta bai nan yana
Abuja,Hjy Zainu ta kalle ta bayan ta gama kero
karyarta. Wai don yaro ya yi kashi ta ce yaron
bai kyauta ba shine ya hau ta da duka da zagi.
Hjy Zainu ta ce Amma wannan da muciya ya
dake ki ko?ta ce, Da hannu ne,nushina fa ya
dinga yi. Hjy Zainu ta ce Ai kin gani ba yadda ba
a yi ba ki tsaya kiyi karatunki kin ki,kin kafe sai
kin aure shi,wannan matsiyacin? Dama talaka
yana da wannan tsiyar.Yanzun za ki zauna mu
jiraZuwan Alhj,ba za ki koma ba.Ya dai baki
takardarki in yaso ki koma mkrnt.Su kuma su
dauki dan nasu. Bishira dai tayi shiru,zcyrta tana
jinjina rabuwa da Abba d kuma danata. Abba kam
gidansu ya nufa.Ummi ya soma cin karo da ita
tana sanye da doguwar rigar bacci,ta dora rigar
sanyu ta sakar ulu, a kai tana wanke baki da
busushi. Ta dube shi,mmkn ganinshi tayi a
wannan lkcn.Sai da ta dauraye baki sannan ta ce
masa sannu da zuwa,ya amsa a hnkl bai san mai
yasa ya kasa dauke idanunshi daga kanta ba,hr
ta gama alwala tayi addu a ta mike. Ta dube shi
da niyar yin magana,amma sai ta fasa don tana
tsoron kada ya daka mata tsawa. Ta daga
labulan dakin Umma zata shiga. Ya ce, “Ke!’ ta
waiwayo cikin hada rai,domin ta tsani kiranta da
yake da ke!Ya ce Ummana fa?ta kalli dakin Alhj
Ba ta fito ba,,Ta shige ta zura hijabi ta tada
Sallah. Ya shiga dakin ya zauna,yana kallonta
tana Sallah zcyrshi tana nazarin Rayuwar
Ummarshi. Tun tasowarshi ya ke ganin kulawa da
kyautatawa da take yiwa Alhj Babba ga biyya,
sam bata wasa da dk wani abu nashi daga lkcn
da ya shigo gida ta gama sauraron kowa sai lkcn
da ya fita. Bai ta6a jin sunyi sa’in-sa ba bare ta
daga murya sama da tasa.Shin sauran matan ba
su fahimci irin wannan ladabi ba ne?Ummi tana
addu’a zcyrta cike da tunanin shi kuma ya Abba
me ya kawo shi da wannan sassafen? Muryar
Umma suka ji daga waje tana cewa,”Ummi in kin
idae ki fito ki share gidannan,ki wanke bayi,Ummi
ta ce To”. Sam Umma ba ta san Abba ya shigo
ba,dmn da ta ba Ummi umurni sai ta sake
komawa dakin mijinta, Ummi ta wanke bayi
kansu,sannan ta share ko ina na gidan, ta kunna
risho ta dora ruwan karyawa, sannan ta shiga
firar doya. Gyangyadi yake daga zaunw, Muryar
Ummanshi ce ta farkar da shi tana cewa, “A’aha!
ya bude ido cike da bacci.ZURFIN CIKI book 2 part 4
ZURFIN CIKI book 2 part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 – 22:10
“A’aha! ya bude ido cike da bacci. Ya kalle ta tare
da yin mika,ta ce “Lafiya”? Ya ce,Umma lfyr
kenan.Ta zauna da sauri Me ya faru Kuma? Yayi
dan tsaki,umma na gaji da auran nan ina ga
wannan karan xan yar da qwallon mangwaro in
huta ta quda. umma ta ce abba! abba!! me yasa
baka da haquri? ban xace ka haka ba abba,ina ce
jiyannan ka min alqawarin kawo qarshen duk
wata matsala tsakaninka da matanka?shin ban
fada maka hanyoyin da xaka bi ka xauna da
matarka lfy ba?ya kamo hannun ta,umma ba na
san bata ranki, ban san yadda xanyi da halin
yarinyan nan ba ne. jiya fa ina kwance taxo tace
min yarona amai naje kai shi kyamis,ina dawowa
na samu ta xauna tana kallon,ina mata magana
ta hayayyaqo min da asuba na tashe ta
sallah,wai dan yayi kashi shine ta hau xagin
yaron nan,wai dan iska. ni ko na bige mata baki
har da cukume ni da dambe fa.umma tace kaine
harda duka abba? dukan mace?ta xuba tagumi
tana kallon shi,ya ce umma xaginshi fa tayi,kuma
kin san dai ba kyau uwa ta dinga xagin danta.dan
ba haka kikai min tarbiyya ba.kalli rashin ji irin na
ummi, amma ban taba jin kin ce mata yar iska
ba.tace to ba sai ka xaunar da ita cikin tsanaki
ba?? . Yayi shiru a xuciyarshi fadi yake umma ba
xata fahinta ba.tace, tashi kaje ka bata haquri, ka
lallasheta.matafa sai haquri,kasan da qashin
haqarqari aka yi su,dole ka ganta a karka
ce.saidai nasiha da lallashi,da xaran ka ce kan
dole xaka miqar da ita,sai ta karye.nan dai ta yi
ta ma abba fada, har sai da shi kanshi yaga
cewa eh,yayi saurin fushi.dan haka ya miqe ya
nufi gida da nufin bata baki.sai dai kuma kash!
lkcn da yaxo tuni tana gidansu.ya dawo ya sanar
da umma, tace to dole sai alhj yaji kenan.ta shiga
gun alhj yana shirin fita. yace yau dai suwaiba
akwai abin da ya dauke miki hankali daga kaina
ko? tace, me kagani? yace tunda kika fita ban
kuma jin duriyarki ba, hatta karin kumallo yau
uwata ce ta kawo min.ko taya ni shafa mai yau
ban samu ba, tace uhum, abba ne in gaya maka
na gani hankalinshi a duk tashe, matsala ce suka
samu da matarshi,wai ta yi yaji.alhj yace,yaji?
umma tace eh wai a ce kamar abba bai san
yadda xai yi haquri da mace ba, alhj yace ina
abban?ta ce yana daki yana karya wa. Ya ce kira
min shi.abba ya xauna ya xayyane ma alhj komai
duk abubuwan da ke faruwa wanda take
masa,hatta batun sallah da bata san yi duk ya
fadia.alhj yayi shiru,can ya ce in ko haka ne ba
qaramin haquri kake yi ba, amma kaje xamu je
gidan.abba ya ce, ni dama xa a baita can dana
huta.alhj yace ba xa ayi haka ba haquri dai xa ka
ci gaba da yi.xuwan su alhj biyu gidan amma ba
suyi dace ba ance musu mahaifinta baya nan.
antynta kuwa ta kira shi a waya ya ce yana nan
xuwa gidanta.da dare suka je da ahmad sun
same ta ita da mijnta,anty ta tare su cikin fara’a
aka kawo musu kayan shaye shaye.nan dai abba
ya fada mata komai.ya qara da cewa ban sani ba
ko dan ni talaka ne shi yasa bishira bata ji
maganata? anty tace dame ka gaxa mata?
iskancintane kawai, wai bishira har da rashin
sallah,xa ko taci qaniyarta gun alhj.mijin anty
yace,tabdi lalle kana haquri nan dai suka ci gaba
da hira har mijin antyn yayi mishi alqawarin cewa
ya kawo takardunshi.MD din gidan rediyon
tarayya na jihar kd, amininshi ne. Amininshi ne
tun da abn da ya karanta kenan za a sama mishi
aiki.Abba ya yi ta godiya. Bai san da wane baki
zai gode ma mijin anty ba,tun daga nemna auran
Bishira yake taimakoshi, darajar su shi da Anty
da Alhjn su Bishiran yake hkr da halayanta. Ya zo
ya sanar da su Umman,Sun yi murna hr Alhj ya
ce dole ne in in masa godiya. Umma ta ce To
Abba ka gani fa,ta dailin matarka gashi zaka
samu aiki,ka yi ta hkr fa. Abba ya ce Umma ba fa
ta dalilinta ba,in Allah ya rubuto zan samu ta
hanyarshi sai ki gani,ko ban santa ba Allah ya
kawo sila.Ta ce To yanzun dai ita ce Silar,Allah
yasa albarka.Sai dai ba zan ji dadin tafiyarka
garin Kd ka barni nan ba. Ya ce Umma ko ni
tunda ya ce kd ke kurum ni ke tunan.Umma tayi
Murmushi,Allah ya maka za6i na alkairi,dk in da
za ka je.Amin Ummata. Mahaifin Bishira ya dawo
kuma Alhj ya tasa Abba sun je in da aka kirata
gata ga shi ga kuma iyayensu. Abba ya jero duk
laifunkanta bai rage ko daya ba. Sannan ya ce,shi
ma yana son ta fadi tsakani ga Allah me yake
mata wanda ba ta So?Nan fa a ka ce ta fadan,
sai ta shiga Kame-kame, Wai in ya shigo gida sai
ya yi ta fadace-fadace sannan ba ya zama a gida
sai tayi bacci,km ga abnci ta dafa amma sai ya
amso na Ummarshi ya c. Alhjnta ya daka mata
tsawa.”Yi min shiru,yaushe ki ka bar musulunci?
Ba kya sallah ko?sannan ki bude baki kina zagar
masa da a gabansa?Ya bige miki baki kin kwaso
kin taho gida,to a miki uban me?ya dubi Abba
“Idiris me yasa ma ka mata duka ba?Ai ke babu
abn da ya dace da ke irin duka. Maza ki kakkabe
mayafinki ki koma gidanki,bana son in sake
ganinki da sunan yaji a gidana, . Zan wulakanta
ki. Kuma game da batun sallah dk lkcn da bata yi
ba ka dakar min ita ni na saka,batun tsafta kuwa
kada tayi,ka nemi mata ka aura ka barta da
tsiyarta. kai dk lkcn da ka samu matar ma zan
biya maka sadakinta ko ‘yar wanene.Sai a lkcn
Alhjn Su Abba ya yi magana. Hakuri za ka yi
ranka ya dade,Allah ya saka da Alkairi bisa
karamcin da a ka yi mana,kuma insha Allah ba za
su sake ba. Abba ma ya yi godiya,sannan suka
masa sallama.Ita ko Bishira mayafi ta dauko tana
kuka suka tafi. Hjy Zainu ranta ya 6aci,taso a
kashe auran don dama bata son Abba sam,kafin
zuwan iyayen Abba da shi kansa Abban ta
fadawa mijinta karairayi,kamu ransa ya 6aci. Ya
kuma daukar wa kansa alkawari in ya bincika ya
tarar haka ne dukanta da zaginta yake ba tare da
ta masa laifin komai ba?sai yasa an raba auran.
Amma da yaji batun Abba gata a gurin bata musu
ba,sai ranshi ya baci da ita, har dai batun sallar
nan.dn haka ya bincike yana da kyau ayi shi,kada
ka yanke hukunci da maganar gefe daya,wannan
shi ne adalci. Bayan sun dawo Abba ya rakata
gida ya zo gurin Alhj da ya ce ya dawo yana
jiranshi. Alhaji ya masa fada cewa dk in da tara
tayi to ya kansace a gida. Sannan fadan da ta ce
yana yi in ya shiga shi ma ya daina,haka ya
dinga zama yana cin abncin.Abba ya ce to.Umma
ma da ya shiga suyi Sallama nan dai ta kara
masa fada tare da nuna mishi hanyoyin da zai bi
ta ce kuma cikin satin nan yayo mata rijistar
Islamiya tunda da ita a kusa. Ya shiga ya same
ta zaune bakin gado tana ta fushi,ya zo ya zauna
kusa da ita.Yasa hannunshi ya kamo nata,sannan
ya kira sunanta bata amsa ba bata kalle shi ba
ya ci gaba da mgn. Kin san dai ina sonki ko??ta
dube shi Da ba kafin a zuga ka.Ya ce wa zai zuga
ni? ta ce Wa kuwa in ba Ummar taka ba. Ya yi
tsam ya ji haushin maganarta sosai,amma sai ya
danne kada ki zargi Ummata tana sonki kin ki
fahimta ne kawai.amma mu bar zancan kiyi hkr
akan abubuwa da nike miki. ki yafe min nima na
yafe miki. . Ya jawota zuwa jikinshi,hr gobe ina
sonki sosai.Ranta ya yi sanyi don mata na son
wannan kalma daga mazajensu. Ya kira sunanta
ta dube shi cikin ido suke kallon juna,ya ce kin ya
fe min?ta daga gira,kina sona hr yanzun?Ta kara
mannewa a jikinshi “Ina sonka sosai ma.Ranar
dakin shi suka kwana,kuma ranar ce rana ta
farko da suka soma kwana a dakin nasa. Washe
gari tunda ya dawo Masallaci ya soma akin share
gida,lungu-lungu ya gama ya wanke bayi kan su
sannan ya yako ta da kyar ta tashi ya ce tayi
sallah ta yiwa yaro wanka. Tayi Sallar,wankan ta
kuke wai akwai sanyu,sai ranar ta daga. Ya ce,To
t dafa musu ruwan zafi su karya.Shi kuma ya
fitar da wankinshi yana yi ya gama ya ce ta fito
da duk wankinsu ita da yaron.Tsawaya ya yi yana
kallon tilin kayan,amma gudun kada suyi rigima
sai ya yi shiru ya ci gaba da wanki. . Ya cire
kayan yaron da zannuwanta hr ma zanin gado
wadanda yaron ya yi kashi ta aje su suka
bushe,,wasu kayan hr da tsutsotsi. Ya kira ta ya
ce “To kalli kayanki hr da tsutsotsi,wanna n ya
dac fisabilillah?samo leda ki kwashe su,ba zan
iya wanke su ba,in kuma za ki wanke to. Nan ta
samo bako ta kwashe takai gurin bola,ya ce
Bishira tsafta cikin addini ce,Annabi (S.A.W)ya ce
Babu mai shiga Aljanna sai mai tsafta. Don Allah
ki dinga kula,ke kanki za ki ji dadi in har ki ka
tsaftace ko’ina na gidanki.Ta tura baki ta wuce.
Ranar haka ya yini wanki kayan yaron dk sun
dafe kaya masu tsada da kyau irin wadanda a ka
sai masa daga gidan iyayenta,ranar dai ko shago
bai je ba. Cikin satin dai babu laifi suna ta
shiri,kuma tana daurewa tana yin tsaftar
jikinta,haka nan yasa ta wanke kai tayo kitso. sai
dai ita gani take dk an takura mata,amma tana
jin dadin yadda ya sakar mata fuska kamar
farkonauresu. Mitar da take masa kullum ya
daina dadewa a waje,ita don Allah ya zauna a
gida suyi hira. Ranar dai saiya gwada zama tun
da ya dawo sallar Isha’i ya shigo gida. Tana
zaune ba riga ya ce,Wai Bishira kayan kwalliyarki
sun kara ne? ta ce,Me ka gani?ya ce,Rabon da in
ga kwalli a idonki tun kina amarya bare dan jan
baki. . Taja dan tsaki “kwalliyar me zan yi sai
kace wata budurwa?Da dai nayi.Ya ce kin ji wani
shirme kuma,ban da ke ai matar aure me miji a
hannu ita ce da yin kwalliya. Ta ce, To ko ma
nayi ba zama ka ke ba.Ya ce “To yau dai gani na
zauna,kuma ina son a sheka min kwalliya. Ta
dube shi Gsky sanyi ba zan iya yin wanka yanzun
ba.Shiru ya yi yana kallonta,can sai ta zame ta
kwanta,sai kuma bacci. Ya yi murmushi.Dubi
matar da ta ce wai ba na zama a gida. to yau na
zauna amma kalli yadda ta bingire tana shirgar
bacci. Ya mike ya fice.cikin takaici korafin banza
kenan take yi tunda ba ta san yadda za ta yi fira
da mijin ta ba. haka dai abba yayi ta hakuri don
baxai yiwu ya ce shi kadai zai dauke mata duk
aikin gidanta ba. sai dai yayi wanda zai iya,amma
duk wanda ya shigo gidan shi ko ba a fada ba
yasan matar gidan kazama ce ta bugawa a
jarida. ummi tana zaune gaban umma,fuska
shabe- shabe da hawaye.ta rikewa ummar
hannu.”kinji don Allah umma kice wa ya Abba ya
dawo dani garin nan.wallahi bana son makarantar
kwana,ni dai bazan koma ba.”umma ta ce “haba
ummi xuwa yanzu ya ci ace kin saba da
makarantar” ta ce,”umma bazan saba da rashinku
ba…..”karaf a kunnen Abba. ya ce,”to sai ko ki
shirya sabawa,don wata rana ma aure zaki yi.”
umma ta ce sosai kuwa. tsohuwa dake zaune a
kofarta,tana jinsu ta sako baki da cewa,”ku dai
lallasheta,karatun nan fa da ake ta matsanta
mata bana ganin manzo bane.” Abba ya ce
mata,”in ji wa? kin ji ki,to ana neman aljanna da
karatun boko kuma ana neman wuta.” ta ce,”kai
ni raba ni da shegiyar karya tunda bata so a
barta.” Abba ya dubi ummi,”kada ma kiyi za ton
maganar tsohuwa za tayi wani tasiri,gara ma ki
shirya komai gobe da wuri zamu wuce.” ta dube
shi,”don Allah ya abba.” ya mike ki shirya da
yamma zanzo muje (sahad store). ya dubi umma
na tafi. . Ta ce,”abba bamu ko gaisa ba,ya mutan
gidan?” ya ce,”suna lafiya,sauri nake in karasa
wasu dinkuna,saboda gobe bana nan jibi litinin
zanje interview da gidan radiyo da talabijin na
(c.t.v) ta ce,”a’a ka samu anan din ne?” ya
ce,”eh bana fada miki ba da aka tura takarduna
can sai suka ce gurin da zasu saka ni akwai wani
wanda suke jin dadin aikinshi a gurin? don haka
zasu turo ni kano,suna ganin ana bukatar irina.to
shine mijin anty ya fada min to yanzu sun kirani
ranar litinin zasu min (interview).ummi dai na
jinsu bata ba kukanta ba.abba na ficewa umma
ta ce tashi kije kiyo kitso ummina,kin ji? dakyar
taje ta dawo.umma tana yankan kubewa wayarta
ta shiga ruri,ta dauka Abba ne.ya gaisheta ta
amsa,ya ce ummana ummi fa ta shirya? umma
takai duba cikin daki inda ta hango unmi nade
kan kujera tunda ta fito wanka. Tace can cikin
kujera,wai sanyi take ji.yace sanyin lfy kuma? ta
shirya ta sameshi gida,umma tace to gatanan
xuwa sukayi sallama.umma tace ke ummi fito
man in kin gama shirin.ummi tace umma nifa
sanyi nake ji,ina ganin xaxxabi ne xai
kamani.tace to ku biya ta kyamis kusai
magani.tsohuwa tace ke yi kwanci yanki, dole ne
fitan? umma ta miqe tana cewa, yanxu in ban je
ba da yaxo xai fara min masifan shi ne. ta shirya
ta fuce rai a bace.a nutse ta ke tafiya har daf da
qofan gidan ya abba. sallama taji anyi mata.wani
matashi ne suka gaisa, ya tambaye ta nanne
gidansu? tace a,a lafiya?ba tare da bata lkc ba ya
fara xayyane mata manu fanta,santa yake kuma
da aure,tace kaga mlm sai anjima.ta shige gidan
abba shiko ya kafe yaqi tafiya.da sallama ta
shiga gidan,qaran inji baisa aji sallaman ba,dan
haka ta jingina da rijiya tana kallan tsakar
gidan.mamakin daya yadda mace daya a gidan ta
kasa gyara gidan.sai kace gidan namiji, namijin
ma qaxami. . abba ne ya fita wanka sanye da
jallabiya fara.ya aje bokitin ya dube ta. yace ki
siga ciki mana, ai tana falo.tayi
sallama,bishiratana xaune da baso tana kalan tv,
ganin umma ta daga labule sai ta hada rai tare
da cewa lfy? ummi tace ina wuni. bishira tace
lau, nace lfy? ta fada hadi da xare ido. ummi tace
ya abba ne ya ce na xauna anan na jira shi. tace
baxa a xo nan adame ni ba, ehe dan kallo nakeyi.
ummi ta ja tsaki tare da sakin labulan, ta koma
ta jin gina da rijiya.bishira ta fito.ke sarkin rashin
kunya wa kike ma tsaki? ummi ko kallanta batayi
ba.sannan tace baki isa kixo min har gidana
ba,kice xakimin rashin kunyan da kika saba.abba
ya jiyo hargowanta ya fito, yana qoqarin saka t-
shirt baqa akan faran singiletin shi,wandan jeans
ne mai laushi blue.yace,menene? tace, wannan
mara kunyan yarinyan nanne xata sameni har
dakina tamin tsaki.oa dubi ummi dake kallan
qasa tamkar bata san me akeyi ba. yace ke
ummi, ta dube shi da sauri,xan bata maki rai
kinsan bana san raini ko? tace nifa ya abba
banfa yi mata komai ba kawai fa.ya daga mata
hannu,yace banasan ji. yace na fada maki dai
bana san raini. takaicin duniya ya isheta,ta
sunkuyad da kai cikin qunan rai.wanna shine
gaba kura baya damisa.bishiqa kam sai ci gaba
da mita take, shiko abba tuni ya koma dakinsa da
qarasa shiri. ya fito fes, sam baxaka ce mijin
bishira bane.qamshin turaransa ya karade gidan
ya daga labule.ni na fita. tace sai ina? xan kai
ummi ta sai duk abinda xata nema dan gobe xata
koma mkrt. ta tabe baki. ya dubi ummi wadda ke
cika tana batsewa,sannan ga sanyi alamun
xaxxabi yana damunta.yace muje ko? ta dube shi
sannan ta bishi.a qofar gida ya iske wannan
saurayin,yace lfy, ko kana jiran wanine? saurayin
ya ce wata yarin….sai ya hango ummi,dan haka
ya katse batun da cewa yauwa gatanan. . abba
ya kalleta ke uwar rore rore wannan ke yake jira
ko? ummi tace oho mashi, bina yake tayi.abba ya
ce, kayi haquri dan samari,ba aure xa a mata ba,
krt takeyi. yace nima din bawai ina nufin yanxu
bane.ya ce na fahince ka.to ka bari sai nan
gaba,ina nufin in auran yayi sai kaxo ko???? Ya
dubeta ranshi bace,ke kuma wuce muje.suka bar
shi nan tsaye yana kallansu.yaga kishi qarara a
idon abba.yace wannan ba wanta bane shima
santa yake.ya raya aransa shima yayi gaba abin
shi.shi kam abba suna tafe yana yi mata fada,wai
tabi ta sakar ma maxa fuska kowane gaja sai ya
xo yace yana santa.maimakon ta tsaya tayi
krtnt,xamani na ilimi,ita dai ta qi kula shi,har
yanxu takaicinta abin da matarshi ta mata,kuma
ya nuna ya goyi bayanta.wayarshi tayi ringing,ya
kalli ummi muje shago na mashin din
nacan.sannan ya daga wayar,ita tana tafe ne
amma sam bata jin dadi.da yake tafiyanta yanxu
tamkar tana jin tausayin qasa take yinta,sabanin
da da sai dai tayi gudu,shi da ke tafe yana waya
ya riga ta isa.gefe ta tsaya ya shiga shago bayan
ya gama amsa wayar.ahmad abokinsa yaxo xai
shiga shagon ya ganta tsaye.tace ina yini ya
ahmad? yace lfy lau yar daru.daman haka ya kan
ce mata.ya shiga shagon yana
waiwayanta,abbana barma yan shagon sallahu
wasu kayan da xa a xo dauka,ahmad ya shigo.
suka tafa,sannan suka gaisa.ahmad yace naxo ne
in fada maka anjima xamu shiga gidan su hafsa
dan gaida iyayenta,sai dai kuma ganin ummi ya
sani jin wani abu.anya ba xan dawo gida da
neman aurena ba?a rude abba ya ce wace ummi
kenan? ahmad ya ce qawarka mana.abba ya ce
dan Allah saki xancen nan kada ma ta jiyo ta
raina mu,me ka gani naso a gun ummi? dan Allah
kada ka cta min rai. . ahmad yace, allah in xai
yiwu, nutsuwan ta birge ni .abba ya ce to ba da
ni xa aci amanar hafsa ba.ummi kuwa dan Allah
ka bar xancenta.yaea ahmad yaga abba ya sha
mur ya tsare gida,dole ya saki batun.suka yi
sallama ya tafi,abba na cewa sai yaxo da
dare.yasa yaron shagon ya goge mashi mashin
din sannan ya tada,ya kalli ummi fuskarshi daure
xo ki hau.itama tata fuskar a daure take.tahau
suka tafi,iskar dake kadata tasa xaxxabin dake
san kamata ta qaru.ya kafe mashin dhn ya
kalleta,muje mana.ta bishi suka shiga cikin sahad
store din.tsaye tayi tana kallanshi yana diba
kaya.da alama na iyalanshi yake diba,dan taga ya
soma da pampas. Hannuwanta harde a qirjinta
tana kallan shi,kome nashi yana birgeta.ya
waiwayo ya dubeta, tsayuwarme kike yi a nan da
ba xaki dauki abinda ya kawo kiba? ta rasa me
xata dauka,sai kurun ta dauki makilin ta riqe a
hannu,ya gama diban abin da yake so,sannan ya
aje gaban masu amsar kudi.ya dubeta,bakya
buqatar komai kenan? ta nuna mishi makilin din
hannunta,tana murxa shi.ya harareta baxa ki
dauki komai ba,kina da kayan tea dasu complex?
tace a,a.y2e to ki tsaya kada ki dauka.ya soma
dibo mata saitin sabulan nan daya taba sai mata
na aloe vera,dan yaga duk kananan qurajen sun
mutu.sannan ya hada mata da audugar mata
guda biyu.ya kai table.lkcn ta dauki madara da
milo ta kawo.yace wawiya,dalla matsa ki bani
gu.yaje ya qara tsinto mata ,sanna akayi musu
total ya biya.suka fita.kafin sukai gida haqoranta
sun s6a haduwa,gashi tana ta takurewa,yace
lfy,wani irim xama kika yi haka?tace,sanyinake
ji.tana magana muryarta na makyarkyata.wani
dan asibiti ya nufa da ita nan kusa da unguwansu
aka dubata. Wurin allura,nan fa a ka soma
daga.Ta ce,ita kam bata san allura.Abba ya daka
mata tsawa da cewa,Allurar ce abn tsoro?Na
gane sam ba ki son ki koma mkrnt,a gobe ne
kuma sai kin koma duk abnki. Ta ce, Naji zan
koma amma yanzun kam dn Allah Ya Abba kada
amin allura.Nurse dai sai kallonsu take yi tana
dariya. kwai Ummi sai ta soma hawaye ita fa har
ga Allah bata son allura.Nurse ta ce,To ka rike ta
mana ko ba Amarya ba ce?Naga shagwabar tayi
yawa. Abba ya ce,Me? cikin tsawa ya yi
maganar,hr sai da Nurse din ta tsorata,ya ce
kanwata ce fa,kin ga wannan kucakar tayi kama
tayi kama da Amare? Nan take Ummi taji ta
muzanta,sannan km ta tsorata da irin tsawar da
ya yi,ba ta san lkcn da ta shige a ka yi mata
allurar ba. Ta fito tana sharar kwalla suka koma
gida. Sai dai tana hada kayanta a Jaka,Sannan ta
ga wadannan sabulun da kuma audugar,kenan shi
ne dama ya sai mata wancan?ko me yasa ya sai
mata kuma hr da augugar mata? . wata zuciyar
ta ce,kila dn yaga Umma bata san kan abubuwan
zamani ba sosai.A fili ta ce,kai umma tasan
audugar mana. Haka dai ta ci gaba da tufka tana
warwarewa,hr ta gama shirya kayanta. Yau kuma
a bayan Tsohuwa ta za6i kwanciya,da dn komai
ba sai dn suyi hirar yaushe gamo. Sai dai
Maimakon hira sai ta tsunduma a tunani,ta bar
Tsohuwa tana ta zance ita daya. Fitarsu da Ya
Abba ta tsaya mata a rai,ita tayi ta tunowa tana
murmushi.Sai dai bata Son tuna lkcn da ya yi wa
Nurse din nan tsawa dn ta ce ko ba amarya ba ce
kom me yasa zai mata Tsawa? ita kam kalamn
Nurse din nan sun birgeta,shi kuma daga ganin
yadda ya yi tsawar nan kalamn ba su masa dadi
ba………. wai takwara bacci ki ka yi ne?Muryar
Tsohuwa ta katseta,ta ce,Idona biyu Tsohuwa.Ta
ce, Tunanin me ki ke yi ne haka?Ummi ta ce
“Um” ina tuna gobe yanzun ina can.Tsohuwa taja
tsaki,Ai mai sunan Malam ya san takan mugunta.
UMMI dai ta ce “Um.Tsohuwa kuwa sai yi take
da mai sunan Malam.Tun Ummi naji tana “Um”,
hr zcyrta ta soma tsanar kalaman Tsohuwa. Sai
dai bata da damar ta katse Tsohuwa tunda dn ita
take yi,bata da mafita da ta wuce ta bar
dakin,don haka ta suri butar Tsohuwa,wai zata je
kewaye(bandaki). Shi ma Abban da ke kwance a
tsakar dakinshi kan kafet ya tada kai da
katifarshi,ban da tunanin fitarsu ta dazun ba abn
da ya keyi. Sai dai damuwarshi daya,me yasa
samari da dama suke kawowa Ummi hari?Me
yasa ya ke jin zafin haka?Zuciyarshita amsa da
cewa,ka so ko ka ki kana Son UMMI.”a fili ya
furta “Haba dai so,Allah ya tsare ni.” Tun misalin
tara Ummi ta gama shirinta tsaf,cikin kayan
mkrnt mai ruwan hoda,mai gida-gida.Da kuka ta
bar gidan yau ma. Haka nan kuka take hr suka
isa mkrnt,ta samu Khadija hr tazo,dn haka tare
suka kwashe kaya.Kafin Abba ya tafi sai da ya yi
mata fada kwantankwacn wnda Umma tayi
mata.Waton ta kula d kanta,kuma tayi abn da ya
kawo ta,waton krt.Sannan ba ya son tayi
kawance d yaketa shari’a.irin wanda wasu
watsatstsun yaran ke yi.(Allah ya shiryesu).
Sannan ya jadadda mata batun ibada,sannan ya
kawo kudi ya bata,ta ce Umma fa ta riga ta bani.
Ya ce,”Ki kara.”ZURFIN CIKI book 2 part 5
Z