Hausa Novels

Jejin Kwankwamai Hausa Novel Complete

Jejin Kwankwamai Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Jejin Kwankwamai Hausa Novel Complete

Mutum ne ya juya baya yana fitsari a bayan wata bishiya a cikin dokar daji. Lumshe ido yake yana rishi da alama yanayin yana yi masa daɗi sosai.

Gyara zanzaron wandon ya fara yana kokarin daurewa,shiru yayi jin ana shafashi ta baya a hankali,bai juyaba sannan bai bude idonsa ba yafara cewa,

“Lallai ma idi iskancinka yayi yawa,yanzu dan jarabar ta motsa shine bazaka bari mu bar wannan mokahon jejjin ba mukoma gida ba kaje cna wajen yan isakan kilakinna ka, shine kake lalumata,hajirin banza kawai”

Ganin yayi magana idi bai ce komai bane yasashi zuyowa a zuciye cikin masifa.

Maizai gani wata kuliyace tayi shi girma take shafa kanta a gadon bayan,juyowar da yayi ne itama take kallon cikin idonsa da idanuwanta irin na mutane fitik.

“I iiiii iddiiiiii wayyyo inna hu sulaimanu wa inna hu sulaimanu,salati ƙafa goma goma tare da alam tara kaifa buhurumati bihurumati,wayyoo idiiiiii bis bis bismati bismati!!!!!!!”

Numfashinsa ne yake sama yana kasa kaman zai fisge daga kirjinsa,wanda yake kirane yarugo da gudu zuwa inda yake da sauri,saidai kafin yazo ma har ya hantsila kan fitsarin da yayi din cikin firgici ga wando dama ba’a ɗaure tazugen saba.

“Kai Amanu lafiya naji ihunka kuma yamzu na ganka a kasa warwas,kodai farfaɗiya ce dakai kai”

Duk maganar dayake yi Amanu bai kulashi ba sai ma uban nishi dayake saukewa kaman yah goyi dutse.

Idi ne ya taimaka masa yamike daga cikin fitsarin daya gamashi sannan suka koma inda suka hura wuta jiya da daddare.

Lokacin da suka je ma duk maganar duniyar nan babu wanda Idi bai yiwa amanu ba amma yaƙi kukashi sai gumine yake feso masa duk da sanyin dayake ƙaɗawa a wajen.

Sai can wajen kimanin awa ɗaya da faruwar lamarin kafin ya ƙoƙarta yace,”uhm uhm ni idi kwanan mu nawa a jejinnane wai?”

“Wace tambaya ce wannan naga kaine mai kiɗaya kwannan mu nawa anan wajen jiya da daddare,ko ciwon mantau ne ya shigeka kai,nikuwa anya baka da ciwon farfaɗiya kuwa amanu?”

“Inma ciwon borine dani kai kan ka fadamin mana,ba mantuwa ba inma zaucewa ne ai zan yi kasan mai nagani kuwa da kaine ai har suma ma sai kayi dan allah yasa ni jarumine shiyasa”

Dariya idi ya kece da ita yana buga kafa tareda cewa,

“Kaine jarumin amanu,ai shiyasa na ganka a cikin fitsarin dakayi jiki yana rawa”

“Kai ni dallah inzaka fadamin abinda na tambayeka ka fafamin,batun jarumta kuma na yarda kaine jarumin baniba,allah ya haɗaka da abinda yafi nawa sannan zakaci bantan ubanka kuma wallahi idan na dunga dariya sai cikina yayi ciwo na daina”

“Kwanan mu uku mun waye na huɗu kenan anan wajen”

“Hmmm to wlh idi munga ta kanmu anan wajen,kaida kuma ganin yam uwanka kayi sallama kenan,inaganin kaman akwai abinda ya kafemu anan wajen,dan duk sanda muka yi yunkurin fita daga wajennan ba ma zuwa ko ina saidai muga mundawo inda muka bari a baya”

“To farfesan ƴan karya,nikasan basu audu bane da zan zauna kayi ta fesheni da karya bakai va gindi,batun fita daga wajennan kuwa batan kai kawai mukayi,rana tana fitowa zamu ɗaga zuwa fita daga wajennan,inga fah gaskiya akwai abinda yake damunka amanu,bari nayi maka tofin addu’a”

Tashi idi yayi daga inda yake zaune wajen amanu wai zai masa addu’a.

Cikin jin haushi amanu ya bigeshi tareda cewa,

“Kai dallah can jahilin banza,a rasa mai yimin addu’ar saikai,banda alhandu babu komai akanka sai yanda ake sata da kuma zuwa gidan kara”

“Eh naji ina zuwa gidan kara amma ai bana caca da shan lofe ina,daɗinta ma kaima bana allah bane ai,bare kayimin zancen banza ehe”

Haka suka zauna jugum jugum kowa da abinda yake saƙawa a ransa,shikuwa amanu shiyasan abinda yagani a wajen yin fitsari.

      Karanta Matar Makaho Hausa Novel 

 

“Allah ko sweetheart shiyasa fah nake ji dakai sosai,kasan yanda kake farantamin raina ba kaɗan ba”

“Hmm ai honey ki bari kawai kedai sha kuruminki shaƙatawa zamuje,kedai kisan yamda zakiyi avarki a gida,ko ƙarya ma kiyi kawai”

“Karkaji komai idan ta hakane,ai kasan zan iya komai dan farincikin ka ni nasan abinda za’ayi ”

“Shikenan bye Bari na tafi gidan wani abokina zan sake kiranki idan anjim”

“Okay sweety”

Kara juyi tayi akan gadon da take,sai murmushi take tana lumshe ido,alamar soyayya tasamu wajen zama sosai. Wata yarinyace ta shigo dakin bazata wuce shekara bakwai ba tace,

“Adda saddiqa wai kizo inji ummah kiyi wanke wanke ankusa sauke abinci”

“Mtswww kice ina zuwa to,vaza a bar mutum ya huta ba,kema idan bakibar wajenba sai na bajemiki hanci shegiya mai kama da mayu”

“Ummansu ce daga waje take cewa,

“Ke saddiqa yanzu danna aiketa kike mara wannan zagin tijarar wallahi k8fita a idona na rufe,kuma karki zo ki yi wanke wanken ki gani,naga mai baki abincin rana a gidannan,bakida aiki said shegen danne dannen waya na banza”

Tashi tayi tana zoba baki da taji an hauta da masifa.

Tana hada kayan wanke wanken tana bugasu da haka ta gama tana mita da harare harare.

Tana gama cin abinci tashiga wanka akan zataje gidan kawarta wanda suka gama secondary tare.

Kwalliya aka sha da wani lace ya dameta kaman yar tsana dan yanda dinkin yakama jikinta.

Hijabi ta zunduma har kasa ta yanda babu mai ganin dinkin dayake jikinta,zuwa tayi dakin ummannata daga bakin kofa tace,

“Ummah na tafi gidan su nusaiba”

“Gidan su nusaiba kuma yaushe ma kikaje gidannasu shine zaki sake diban kafa kije?”

“Kai ummah yanzunfah ummanta ce bata da lafiya shine zanje wajenta”

“Shikenan ki gaisheta amma karki dade fah kidawo da wuri”

Daga kai tayi alamar taji kafin ta juya ta fice,saida ta bar layin gidansu kafin ta shiga wani kangon gida a bayan layinnasu ta cire katon hijabin tasaka wani dan figigin gyale wanda tasako shi a cikin jakarta,saida tagyara sosai kafin tasaka hijabin a jaka ta kama hanyar partyn da zasuyi wanda dan ajinsu ya hada musu.

Wow ga nan filter baby ta iso,uwar wanka a rasa komai a hawo wanka.

Ai kuwa wajen ya jube da ihun shigowar saddiqa sai fasa kai take an yabeta,duk da yabon rabinsa zagine na yanda iyayenta basu da komai amma take jinta wata shegiya.

Basu suka tashi a partyn ba sai can Bayan magriba,dan takaici da ta koma ummmanta ko magana batayi mata ba,sai cewa tayi allah ya kyauta.

 

KO a jikinta kuwa haka ta shige daki ta kwanta (sai muce saida safe)

 

 

Batun su amanu kuwa duk yanda yayi ya fahimtar da idi cewar bazasu iyah fita ba abin yaci tura,dan duk yawon da sukayi babu inda suke dawowa said tsakiyar dajin,da amanu yagaji zama yayi ya saka uban tagumi na zullumi,can kuma sai yace,

“Uhm ni amanu dana sani da banzo wannan tafiyar ta cirani ba,yanzu ana can ana zaton mun tafi mukuwa gamu nan a makahon daji”

” to kaima amanu ka tashi mu sake zagayawa mana ko zamu samu hanya ”

“Babu inda zanje kaje idan kasamu hanya allah yabada sa’a”

Amanu Yana zaune haka idi ya tsallake shi ya wuce yayi yamma daga inda suke zaunen.

Tafiya yake yana fito tareda yin wakar irinna su ta yan duniya,yadanyi tafiya mai nisa amma bai ga yadawo inda amanu yake ba,murna ce ta isheshi yafara cewa

“Kai amma fah ni dan sa’a ne inaga dan da amanu ne shiyasa muka kasa ganin hanyar amma yanzu gashi naga hamya nikadai”

Shiru yayi jin wani abu yana dusowa a kansa,

Daga idonsa yayi domin ganin menene a samannasa.

Wata katuwar fuskace bakikkirin kaman ta mace tana cikina wahala ta mutu a haka,sai kuma wani ruwa yana zubowa daga bakinta shima baki.

Jikin idi ne ya debi rawa ga kuma dariya da ake tayi ta cika dukkan jejin.

Idon fuskarne ya bude tafara masa dariya,aikuwa kafa mai naci ban baki ba ya debi gudu kaman na famfalaki.

Karo yaji yayi da mutun,take kuwa numfashinsa ya dauke idonsa yafara kafewa,dan yayi zaton fusakrce,amma kuma said yaga ashe wani mutum ne dan adam amma ba amanu bane to waye.

Bai gama tantance hakan ba ya suma jikinsa ya shika yaraf.

Ruwa suke ta shafa masa amma babu alamun ya farfado,can kuma har sun cire tsammani suka ga yayi ajiyar zuciya tareda tashi da gudu furma cikin jejin Yana cewa,

“Amanu ina kake amanu,aradu yanzu kam na yarda dakai wayyo inna ina kike inna”

Samarine guda uku da yanmata suma guda uku kowannensu sanye da kayan hiking irin uniform din makaranta,da alama research suka zoyi wajen.

Suma binsa sukayi a baya suna cewa ya tsaya amma ko jinsu baiyi ba.

Sunyi tafiya mai nisa kafin suka samu ya tsaya yana maida nunfashin gudun yayi.

Wani saurayi ne daga cikinsu wanda yafisu fari yace,

“Bawan allah lafiya kake ta gudu kaman an biyoka?”

“Iye na’am kudin suwaye ku,koh kuma fuskarce kuma”

“Wace fuskrr kake magana akai?”

“To naji ku ba fuska bace,dan allah ta ina kuka shigo ku nunq mana dan sanku da manzon allah,allah zai taimakeku idan kunka taimakeni”

“Mai za’ayi da hanyar da muka biyo?”

“Nidai Ku nunamin kawai ko ba abinda zanyi da ita ku nunamin kunji”

Amincewa sukayi akan zasu nunamasa hanyar da suka bi suka shigo,suna tafe said zance suke akan makaranta suna ta iyayi,idi kuwa yana jinsu bai ce komai ba,dan shiya san abinda yake ciki,yanzu ya gasgata zancen amanu dari bisa dari.

Komawa sukayi da baya suna ta tafiya,har idi yafara murnar zasu fita daga wannan wajen,saidai mai murnar sa ce takoma ciki ganin sun dawo hanyar dayake ganin ya santa a dan zaman sa a wajen.

Amanu suka hango a karkashin bishiya inda idi ya barshi yana ta kwasar bacci hankalinsa kwance kaman ba shine yayi ta ihu da safe ba.

Tun kafin su karisa inda yake idi ya takarkara ya runtuma ihu tareda zubar da kayannasa daya lankaya a kafadarsa.

Kallonsa suke da alamar tambaya tareda cewa,

“Menene ya faru haka babba da kai malam kake kuka,anya kuwa lafiyarka lau,tun muna tafiya jikinka yake rawa kana muzurai mun tambayeka baka bamu amsa ba”

“Inna Baku amsa ma bazaku yarda ba yan matasa,amma tunda babu inda zakuje muna tareda ku da sannu zakuga koma menene yasakani rawar jiki”

Toh fah…………….

 

Barkan mu dasake haduwa a sabon littafi,zubin farko kenan cikin littafin jejin kwankwamai wanda zai dunga zuwa muku tareda ni …………..

 

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!